Labarin Dorugu, Bahaushen daya fara zagaya Turai.
Kashi na goma sha biyu
Tare da Sadiq Tukur Gwarzo
Dorugu yaci gaba da cewa "bayan jimawa kadan a
London muka barta zuwa ga Germany. A garinsu uban
Abdulkarim Hamburgh muka sauka. Muka zaga kofar
gidan ubansa ya shiga ciki da gudu, suka shigar dani da
Abega wani daki a bisa, muka ajiye kayanmu, muka
canza wankakkun kaya sannan aka kira mu kasa aka
bamu gurasa kekasasshiya, banso cinta ba, suka kawo
mana gahawa muka sha.
Naga uban Abdulkarim da uwatasa, har Abdulkarim
yace nayi musu wak'a, na rera musu wata wak'a
gajeriya wadda ake cewa "Dan dauda yana gida, ko
kuwa ba shinan gida". Dana k'are sukayi tafi,
Abdulkarim yace hakan gaisuwa ce. Da safe
Abdulkarim ya kira baduku ya dinka mana takalmi, ya
kira tela ya dinka mana taguwa mai kauri, saboda
germany akwai dari, idan banyi k'arya ba, idan aka
yanki tsokar mutum, jini bashi fitowa.
Wata rana wani mutum ya zago, Abdulkarim ya kiramu,
yace musanya fararen tufafi. Haka kuwa akayi, muka
zaga cikin dakinsa, Abega ya zauna bisa kujera, nikuma
na tsaya a tsaye da hannuna kusa da aljihu. Nagani
mutumin yana da alk'alami da in ya dubemu, shina sa
kansa k'asa da takarda a gabansa. Daya k'are muka
fita, amma ban sani ba menene yayi. Abega yana
tsammanin kamace yayi.
Muka tafi wani gari Gotha, Abdulkarin yana da aboki
acan, sunan sa Jetermann. Da matarsa Dorothea
Beker. Muka samu yara suna worgi, ta bani littafi,
acikin littafin akwai hoton biri, bushiya, zaki, kura,
rakumi, dabino, kada, hawainiya, da sauran abubuwa.
Muka gaisheta muka tafi.
Akwai kuma wani wanda na sani mai suna petermann
mutum neshi nagari, wani lokacin yana son yayi min
magana da hausa amma baya iyawa. Shine ya bani
wani littafin duniya daya rubuta da hausa, ban sani ba
menene a cikinsa ba don bana iya karatu da rubutu, sai
dai na dauka don in tuna dashi.
Da muka bar gotha sai gamu a Berlin. Muka isa wani
gida mai girma. Abdulkarim yaja Abega suka shiga ciki.
Sai da Abega ya dawo ya bani labarin abinda ya gani.
Yace "mun shiga gidan babban mutum yana cike da
zinariya ga rigunan sa, yana jan takobinsa k'asa,
Abdulkarim ya bashi zabira mai kyau ta kano, idan
mata suna tafiya samari suna daukar musu alkyabba
daga bayansu".
A cikin Berlin koyaushe ina ganin kayan yak'i, ga ginin
gidansu mai kyau dogaye. A cikin germany naga uban
Tebib ubangijin mu na farko wanda ya 'yanta ni, tsoho
ne mai tsayi, kansa duk furfura, muka gaisheshi sosai.
Idan muna yawo acikin gari sai mu rinka ganin wani
abu fari akan soro ko a gefen hanya, muka tambayi
abdulkarim menene wannan, sai yace mana sukari ne.
Sai rannan naje na dandana, Abega yace me kaji? Nace
masa zo ka dandana. Sai ya dandana yayi tsaki yace
wannan ai duk ruwa ne. Abdulkarim ya rinka mana
dariya.
Muka samu wani saurayi mai magana da larabci, da fari
yace "Assalamu alaikum", gaisuwan larabawa kenan, ya
jiramu ga dakinsa muka zauna tare dashi, yana shan
taba. Yace Abega yasha, dama kuwa abega yana son
taba kamar tuwo, nidai ban taba ganin garin da ake
shan taba kamar germany ba, sai kaga yaro dan
shekara sha biyu yana shan taba, amma ni bana sha.
Rannan mun shiga cikin dokin wuta sai nake kallon
wata hanya ta taga, sai nace da abega kazo kaga
wannan hanyar. Yana zuwa yana tsammanin babu
gilashi, dazai fitar da kansa waje sai gilashi ya fashe
ko ya tunkude shi. Na fara dariya, yace da maganan
borno "a foro kasutu dimmi?" Yana nufin don mi kake
yin dariya. Nace masa don madubi ya fashe. Wani
mutumi ya zagayo, yana da riga ta gashi, tagiyarsa
kamar tana da kunnuwa, yayi dariya. Abega yace
Dariyarsa ta mugunta ce, Abdulkarim ya bashi kudi
saboda gilashin daya fashe, sannan yace mana mu
rink'a lura da gilashi.
Na mance ban fadi muku ba, munje wani babban gida
Abdulkarim ya kai kyautar da sarkin sokoto ya bashi, a
hamburgh kuma Uban abdulkarim ya kaimu gidan wasa
munga biri yana sukuwa da doki, munga giwa mai abin
mamaki, munga wasanni da yawa Munji dadi.
Daga nan muka hau jirgin k'asa muka isa ga london,
nan ma muka shiga gari...
Anan labarun Dorugu yazo k'arshe..
Daga Sadiq Tukur Gwarzo. 08060869978
Shafin Hausa kokarin ilimantar da al'umma akan fannonin ilimi mabanbanta da suka shafi Tarihi, Kimiyya, Falsafanci da makamantansu.
Sunday, 10 December 2017
LABARIN BAWA DORUGU 12
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment