2. SIR KASHIM IBRAHIM
An haifi Marigayi Sir Kashim Ibrahim a Kauyen Gargar na gundumar Yerwa, wanda a lokacin shine babban birnin Maiduguri kafin a koma Borno.
Ya soma karatun addinin sa a gida kafin daga baya mahaifinsa Ibrahim Lakanmi ya shigar dashi makarantar Borno provincial a shekarar 1922.
Bayan shekaru uku, sai kuma ya samu gurbin karatu a kwalejin horas da ɗalibai ta katsina inda ya samu takardar shaidar malunta a shekarar 1929.
Daga nan sai ya soma aiki a makarantar middle ta Borno a wannan shekara, a hankali yana samun girma da karɓuwa a wurin jama'a, har zuwa lokacin data kai aka bashi lakabin Shatiman Borno a shekarar 1933. Aka soma kiransa da Shattima Kashim.
Ya soma siyasa ne a shekarar 1951-52, sanda aka zaɓeshi a matsayin wakili na majalisar arewa, daga nan kuma aka tura shi wakilci izuwa majalisar kasa daga Arewa.
Ya zama wannan wakili babu jimawa sai kuma akayi masa naɗi izuwa Ministan walwala, sannan ya koma ministan Ilimi daga baya.
A shekarar 1956, aka yi masa mukamin Wazirin Borno, haka kuma ya samu zamowa Gwamnan Arewa ɗan arewa nafarko a shekarar 1962 kuma yana rike da wannan mukamin akayi juyin mulkin ranar 16 ga watan janairu na shekarar 1966 wanda Major Janar Aguiyi Ironsi ya zama shugaban kasar tarayyar Nigeria.
A lokacin da akayi juyin mulki aka kashe manyan mutane daga arewacin Nigeria, sai aka garkame Sir Kashim Ibrahim a kurkuku, amma daga bisani aka sake shi, ya koma gidansa a maiduguri, ya sadaukar da mafi yawan gidan ga makaranta, sannan bai tsira da komai ba sai kuɗi kaɗan da gidansa da mota ɗaya ta hawa, kuma tun daga nan bai sake komawa harkar siyasa ba.
Sir Kashim Ibrahim ya rike matsayin Chancellor na University of Ibadan daga 1966 zuwa 1977, haka kuma ya sake zama chancellor na University of Lagos daga 1977 zuwa 1984.
Kafin rasuwarsa a ranar 25 ga watan yulin 1990 sai daya shigar da gwamnatin tarayya kara saboda ta hanashi Fanshonsa na Gwamnan arewa domin ya samu abin taɓawa, kuma ya zamo abin so da alfahari ga kowa saboda gaskiyarsa da kiyayewa daga satar kuɗin jama'a tayadda aka rinka saɓyawa jarirai sunansa.
Haka kuma marubuci neshi, tunda ya wallafa littattafai biyu a zamanin rayuwarsa masu suna 'Teachers guide to Arithmetic' na ɗaya zuwa na huɗu da harshen kanuri. Da kuma 'Kanuri reader for elementary school'.
A karshe, rayuwarsa abar koyi ce ga dukkan matasa saboda yadda ya sadaukantar da kansa ga gina arewa da kuma irin nasarar daya samu a rayuwa.
Shine sir Kashim, wazirin Borno, Order of Nigeria, Order of british empire, LLD's.
Da fatan Allah yajikansa Amin.
No comments:
Post a Comment