TARIHIN HAUSA DA HAUSAWA
Hujjojin dake nuna Asalin Hausawa Daga misira suke daga Littafin 'Gamsasshen Asalin Hausawa da Harshen su' wanda Comrade Zakariyya Abdurrahman Shu'aibu Kabo ya wallafa a shekarar 2013.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Kashi na biyu.
Waɗannan mutane sun iya nau'ikan sana'a irin nasu na tsarin zamantakewa kamar noma, kiwo, sassaka, kira, rini gami da saka.
Sunan Dala wanda ya zauna a saman dutsen Dala dake kano nada alaka da sunan yankin daya baro, watau Dahalak. Don haka an rinka kiransa da sunan garinsu ne, shine kuma daga baya sunan ya koma Dala.
Haka suma ragowar Rano da Gaya, duk sun zauna ne a wuraren da yanzu ake kira da sunayensu a hausa.
Marubucin kuma ya faɗa game da Daura cewa:-
An samu a tarihi cewa al'umomin da suke zaune a Misira na wancan lokacin suna fita izuwa yankin larabawa dan yin kasuwanci wanda kuma mungani a tarihi cewa Kabilar Hausawa na ɗaya daga cikinsu, mungani a cikin littafin tarihin nan mai suna 'Masar Wa Hadaratul Alam Al khadima' cewa sarakunan masar na wancan lokacin watau (Faraina) suna aika mutane garin Banɗa mai wuyar zuwa domin kasuwanci, garin na saman sahara ne kuma sai an ketare kogin Baharul Ahmar ake riskar sa.
Sarakunan kasar Misra sun rinka aikewa da waɗannan yan aike akai akai, acikinsu akwai misalin Sarauniya Hatash-basuut wadda ta taɓa aikewa da jiragen ruwa kyauta domin akaiwa sarkin Banɗa.
Don haka, saboda wahalar zuwa wurin ya sanya hausawa suka rinka zama a wannan yanki.
Sai Marubucin yace "Ina ganin daga cikin irin waɗannan mutane aka samu hausawan cikin su suka hauro daga falasɗinu ta Masar suka shigo ta Libya, suka hauro Niger sannan suka riski Daura ta jihar katsina ayau..
Yace kuma An samu irin waɗannn zantukan a matsayin labarin kunne ya girmi kaka, amma shi kuwa yana ganin ai kowanne tarihi kunne ya girmi kakan ne.
Yace kuma " An samu a bakunan mutane dayawa asalin mutanen daura daga kasashen Asia sukayo kaura zuwa nan. Haka Farfesa Saidu Muhammad Gusau ya faɗa mana a littafinsa mai suna wakokin Baka a kasar hausa wanda ya kawo tarihin Daura a shafi na bakwai.
Haka shima Mamman Siya Abubakar Wakilin Tarihin Daura ya faɗamin a wata ziyara dana kai ta bincike ranar 16/02/2010.
Har ma ya kara min da cewa Mutanen Falasɗinu ne da ake kyautata zaton larabawa ne asalin daura. Kuma kafin su karaso Daura sai da suka zauna a kasar Libya da Turabulis.
Haka kuma, marubucin tarihin Sarauniya Daurama (Tsiga, 1978:5) shima ya nuna cewar ana kyautata zaton asalinsu larabawan falasɗinu ne."

No comments:
Post a Comment