Tarihi: Asalin Bakin Mutum
da Mazaunin sa
(Kashi na hudu)
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
FANTSAR BAKIN MUTUM IZUWA SASSAN AFIRKA
Kafin mu shiga jawabi akan Fantsamar kabilun bakaken fata izuwa sassan afirka, bari mu dan koma baya kadan don kara samun fahimta akan mutanen da suka gabace mu.
Littafin 'Origin and Evolution of Primitive Man' na Albert Churchward (1912) ya kawo tunanin sa ga yadda dan Adam na usuli ya fara rayuwa gami da dalilan da suke sanya shi tashi daga guri kaza izuwa wani gurin. A cewar sa, asalin mutanen farko mutanen daji ne. Da Kalmar "Bushmen" ya kira su. Aikin su shine su tashi daga nan zuwa can don yin farauta. Wannan shine silar farko data sanya suke yawan sauya muhalli. Shine Yace a hankali- a hankali wayewa ta rinka zuwar musu suna canzawa har suka riski matsayin Aryan (Indo-Europeans).
Littafin 'Ridle of Prehistoric Times' wanda James Anderson ya wallafa a shekara ta (1911) a shafi na 58 ya fadi cewa "mutanen farko da suka soma zama a turai, yammacin afirka, arabia, faransa da birtaniya kabilu ne masu dan jiki, wadanda tsawon su bai wuce k'afa hudu da inci biyar ba. Fatun su bakake ne, kuma asalin su mazauna kogunan duwatsu ne. Sun zone daga Lemoria.
Ya kara da cewa " sun fara binne matattun sune a kogunan duwatsu, daga baya da kogunan sukayi karanci sai suka koma binnewa a kaburbura masu tsayin misalin kafa 400, da fadin kafa 50. Asalin su mutanen afirka ne kuma hujjoji sun bayyana cewa a wasu lokutan suna cin naman junansu"
Haka kuma wasu masanan sun tabbatar da cewa mutanen farko da suka fara riskar yankin Ireland bakaken fata ne wadanda basu iya amfani da wuta ba. Suma ance daga afirka suka zo akan jiragen ruwa.
Wannan dai duk kari ne akan bayanan da muka kawo a farkon wannan rubutu.
Amma dai, binciken baya-bayan nan da akayi, ya nuna rayuwar da bakaken fatar sukayi a wasu yankunan na shekaru masu yawa ne, tayadda siffofin mutanen da ake nunawa ko ake zayyanawa yasha bam-bam da kalar mutanen dake rayuwa. Wannan na iya sanya tunanin ko Wadancan jinsin mutanen ba daya suke da namu ba?
Misali, binciken DNA da David Reich da Svante Peage suka gudanar mai taken ' An early modern human from Romania with a recent Neanderthal Ancestor' ya nuna asalin bakin mutum a turai sama da shekaru dubu talatin da bakwai da suka gabata. An samu wani k'ok'on kan mutum a kogon 'Carpathian' dake kasar ta Romania a shekara ta 2002. Binciken 'carbon-datin' da masana suka gudanar akansa ya sanya wanzuwar sa a wajajejen shekaru dubu 34 zuwa dubu 36 da suka shude. Amma kuma duk wanda ya kalli k'ok'on kan da aka samu, yasan kan mutumin yasha bam-bam da kawunan mutanen dake rayuwa a wannan zamanin.
Mun samu labarin kabilar 'AINU' ta bakar fata wadanda akace sun zauna a yankin China shekaru dubu hamsin da suka gabata. Ga misalin kabilar 'Grimaldi' wadanda matayensu keda manyan duwawuka, itama ta wanzu ne a yankin turai shekaru dubu arba'in da biyar baya.
Sannan aukuwar jinsin 'sciopodes' wadanda aka ce suna da sauri a tafiya da kuma manyan tafukan k'afafuwa tayadda idan zafin rana ya damesu suke kwanciya tare da yiwa kansu rumfa da tafin kafarsu wadanda aka sha ji a tatsuniyoyin girkawa na neman zama gaske.
Duk fa wadancan, na iya zamowa wasu jinsunan mutanene na daban ba kalar namu ba. Abinda kurum muke nuni dashi anan shine dadewar kabilar bakin mutum da kuma yadda yake tashi daga gurin da yake izuwa wani wuri mai nisa. Watakila kuma wannan dabi'a ce zata sanya asha wahala wajen bin diddigi tare da gane asalin mazaunin bakin mutum.
Idan har mun gamsu da jawabin Habashawa wanda muka kawo a baya cewa Cush dan Hamu shine ya taso da iyalansa bayan daukewar ruwan dufana izuwa yankin Aksum, da kuma maganar cewa Itiyopis dan Cush shine ya kafa garin Mazaber, wanda daman kowa yasan an fada a tarihi cewa shi bak'in mutum ne. To zamu iya gane bakin zaren don gano yadda bak'in mutum ya karaso kwaryar afirka ta yamma da sauran inda ayau ake samun sa.
Marubuci Chancellor Williams, ya fada a littafin sa 'The destruction of Black Civilization' cewa bakin mutum a baya shine shugaba a duk duniya. Yace kuma bama maganar Egypt ta taba kasancewa garin da bakaken fata keda rinjaye ba, kalmar egypt din ma an samo tane daga bakin mutum. Sannan yace bakin mutum ne ya fara binciken kimiyya, likitanci, gine-gine da rubutu, shine kuma ya fara gini da dutse.
Wannan littafin fa hamshaki ne, domin za'a iya cewa babu wani littafin tarihi sama dashi anan duniya dangane da tarihin bakin mutum. Marubucin sai da ya shafe shekaru yana binciken tarihi kafin ya rubuta littafin. Kasa-kasa ya zagaya na bakaken fata bisa tallafin kasar Amurka.

No comments:
Post a Comment