ABINDA ALQADI IYADH YA RUWAITO A LITTAFIN SA 'ASH-SHIFA' DANGANE DA HUKUNCIN WANDA YA ZAGI ANNABI MUHAMMAD(S.A.W) KO YA AIBATA SHI.
A Qismi na hudu, babi na daya cikin littafin 'Asshifa bi Ta'arifi Huquqil Mustafa' Alqadi Iyadh yace "Ka sani, Allah ya datar damu, cewa daukacin wanda ya zagi Annabi Sallallahu alaihi wa sallam, ko ya muzanta shi, ko ya hada wani abu na nakasu dashi, ko da nasabar sa, ko da addinin sa duk zagi ne. Kuma hukuncin su kisa ne.
Abubakar Bn Munzar yace "Daukacin ma'abota ilimi sun hadu akan cewa duk wanda ya zagi Annabi sallallahu alaihi wa sallam Kashe shi za'ayi. Daka cikin wadanda suka fadi haka akwai; Imam Maliki bn Anas, Da Mallam Laisu, da Imam Ahmad, da Imam Ishaq.
Muhammad dan Suhnunu ya ce "Malamai sun hadu akan cewa duk wanda ya zagi Annabi Sallallahu Alaihi wa sallam don nakasu gareshi, ya kafirta. Kuma shi mai jiran azabtarwar Allah ne. Kuma hukuncinsa a wajen al'umma shine Kisa. Sannan duk wanda yayi shakkar kafirtarsa, da haduwarsa da azaba shima ya kafirta.
Haka nan, Imam Abu Sulaiman Alkhaddabiy yace " Ban san wani daga cikin Musulmai ba wanda yayi sabani akan wajabcin kisan wanda duk ya zagi Annabi idan ya kasance Musulmi ne.
Ibnul Qasim ya fada a cikin Utbiyya cewa " wanda ya zage shi, ko ya muzanta shi, ko ya aibata shi, ko yayi kalmomi masu nuna nakasu a gareshi, hukuncinsa a wajen al'umma shine kisa kamar yadda ake yiwa zindiqi. Hakika Allah Ta'ala ya wajabta ganin girman sa Sallallahu alaihi wa sallam, da darajanta shi tare da biyayya a gareshi.
Yazo a cikin Mudawwana Masbuda, cewa Usman dan kinanata ya fadi cewa "wanda duk ya zagi Annabi Muhammad sallallahu Alaihi wa sallam daga cikin musulmai a kashe shi ko a tsire shi ba tare da an neme shi da ya tuba ba.
Sannan an ruwaito cewa Malumman Qiyrawani sunyi fatawa da a kashe Ibrahimul Fazariy wanda ya kasance Mawaki, masani kuma a fannoni. Har ma ya kasance yana halartar majalisin Alqadhi abul Abbas bn Dalibin don daukar darasi. Sai wani lamari ya bijiro daga gareshi na aybantawa ga Allah madaukakin Sarki da Annabawansa da Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam. Sai Alqadhi Yahya ya isar masa da wasu masana, ya umarci a hallakashi ta hanyar tsirewa. Sai aka cakeshi da mashi, aka rataye shi a sama, sannan aka sauko dashi kasa ya kone cikin wuta.
Kuma an hakaito cewa a wannan lokacin mutane suna zagaye da wajen suna kabbara, kare kuma yana lallagi ga jinin sa. Sai Alqadhi Yahya bn Umar yace Manzon Allah (S.a.w) yayi gaskiya. Sannan sai ya ambaci hadisi mai cewa "Kare baya lallagi ga jinin musulmi".

No comments:
Post a Comment