BAKAN DABO: TUNAWA DA MARIGARI MAI-MARTABA ALHAJI ADO BAYERO.
(Dubu Jiran Mutum Daya)
Fitowa ta daya.
Daga SADIQ TUKUR GWARZO
08060869978
A irin wannan wata na sha'aban Allah Ta'ala ya qadarta rasuwar marigayi Alhaji Ado Bayero CFR, LLD, JP shekaru biyu da suka gabata. Kafin rasuwar sa, shine Sarki na goma sha uku a tsarin sarakunan fulani na masarautar kano. Ya hau karagar mulki ne jim kadan bayan rasuwar marigayi Sarkin Kano Muhammad Inuwa. An rantsar dashi akan mulki ranar ashirin da biyu ga watan okboba na shekarar 1963. Allah yayi masa rasuwa a ranar shidda ga watan yuni, shekara ta 2014. Allahu Akbar!
An haifi marigayi Alhaji Ado Bayero a ranar 25 ga watan yuli, shekara ta 1930. Sunan Mahaifiyarsa Hajiya Hasiyatu, Mahaifinsa kuwa shine tsohon sarkin kano mai adalci, farin jini da tsoron allah, sarki Abdullahi Bayero, wanda ya shafe shekaru 27 yana mulkin kano.
Indai maganar mulki akeyi, ko qasaita, ko tumbatsa, ko bautawa musulunci, ko samun kwarjini da farin jinin mabiya, ko alfarma a duniya, ko duk wata daraja da ake alaqantawa ga arziki da mulki, zamu iya cewa nan kurkusa, bamuji labarin wani sarki Sama da marigayi Alhaji Ado Bayero ba. Al'umammar kano na matuqar sonsa gami da girmama shi, kai kace tun suna qananu ake koya musu soyayyar sa.
Hikayoyi daban-daban sun faru a zamanin rayuwar mulkin sa, wadanda ke nuni da bunqasuwar mulkin sa gami da izzar da Allah ya hore masa akan sauran al'umma baki daya. Daya daga ciki shine hikayar shari'ar Limaman kirstoci da fadar mai Martaba Sarkin kano dan Abdu.
Ance tun da jimawa, kiristoci ke son gina Gagarumar coci a jami'ar Bayero, amma fadar sarki tana hanawa. Saboda a cewarta, wannan Jami'a sunan Sadaukin Musulunci taci, watau marigayi Bayero, don haka izgili ne a kafa gagarumar coci a cikinta. Rannan sai labari ya samu wasu jiga-jigan Hakiman Sarki cewa ginin coci yayi nisa a jami'ar Bayero, babu jimawa kuwa wadannan hakimai suka tura cewa aje a murqushe wannan gini tun kafin sarki yaji labari. Sannan a shaidawa limaman kiristoci cewa, ko shugaban qasa bai isa ya gina coci ba a wannan jami'ah. Ile kuwa, hakan akayi.
Zafin wannan abu yasa kiristoci suka kai qarar Sarkin kano wata babbar kotu. Akayi rashin sa'a, Alqalin kotun baida tarihin buwayar masarautar kano da sarakunanta, sai kurum yace yana son lalle Mai martaba Ado Bayero ya gurfana a gabansa. Subhanallahi, ashe Savo ya tafka gagarumi bai sani ba.
Ranar da za'a saurari qara, sai akaga sakataren Gwamnatin tarayya na wancan lokacin chief Anyim Pios Anyim ya shigo kotu fagam-fagam, sannan kai tsaye ya tsaya a dai-dai inda wadanda ake tuhuma ke tsayawa a kotu. Wa'iyazubillahi, nan da-nan Babban alqali da sauran alqalai masu taimaka masa suka miqe tsaye don girmamawa, suna masu kwasar gaisuwa ga Sakataren gwamnati.
Sakataren gwamnati yace ba wannan ne ya kawo shiba, suyi sauri su sallameshi akan tuhumar da sukeyi masa, yana da aiyuka a gabansa. Babban alkali yace Ranka ya dade ay bamu tuhume ka da komi ba. Sakataren Gwamnati yace amma kun tuhumi Mai martaba Sarkin kano Alhaji Ado Bayero CFR, LLD, JP ko?. Don haka daga sama na samu umarnin nayi gaggawar zuwa na wakilceshi. Hmmmmm, abu madundumi kenan wai inji mutuwa.
Ba shiri babban alqali ya fara tuba, sannan yace ya kori wannan sharia babushi-babu ita har abada. Allah ya huci ran sarkin kano, Allah ya huci ran sakataren Gwamnati da ita kanta gwamnatin tarayya.
Ai kuwa fitar chief Anyim keda wuya, sai babban alqali ya samu waya daga babbar mai shari'a ta gwamnatin tarayya a lokacin, Mai shari'a Maryam Alooma mukhtar, tana umartarsa lalle washe gari zasu je kano dashi, domin anja mata kunnen lalle da ita dashi sukai kansu fadar Maimartaba SAN KANO DAN ABDU...
Zaku jimu a rubutu na gaba insha Allahu.
Allah ya jiqan marigayi sarkin kano Alhaji Ado Bayero. Amin

No comments:
Post a Comment