Thursday, 28 December 2017

TARIHIN MARIGAYI SA'ADU ZUNGUR

MALLAM SA'ADU ZUNGUR

Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

  Mallam Sa'adu Zungur tsohon malamin makaranta kuma ɗan siyasa, sananne ne a duniyar adabi da gwagwarmayar hakkin talaka.
   An haife shi a garin Bauchi, a zuri'ar Limamin Bauchi cikin watan Nuwamban 1914.
Ya kasance mutum mai matukar kaifin basira, hazaka da hangen nesa.
Shine dan arewa farko da ya fara fita daga lardin arewa zuwa wuri don neman ilmi. A 1934 ya tafi Yaba College a Lagos.
Shine kuma dan arewa na farko daya fara rike mukamin siyasa, lokacin da ya zama Sakataren jam'iyyar NCNC a shekarar 1948.
A tarihi Mallam Sa'adu Zungur ne ya fara rubuta korafi ga turawa, yake bayyana musu rashin gamsuwarsa da yadda ake tafi da harkokin gwamnatin arewa ta wancan lokaci.
  Mallam Sa'adu zungur Amini ne ga Marigayi Mallam Aminu Kano, kuma shine wanda ya kafa Jamiyyar Mutanen Arewa, wadda su Ahmadu Bello da Aminu kano suka shiga kafin ta sauya izuwa NPC.
A lokacin rayuwarsa ya wallafa wakoki na wa'azi da jan hankalin al'umma, musamman mutanen arewa.
Allah yayi masa rasuwa a 1959
  Ga wakar Arewa Jamhuriya ko Mulukiya daya rera:-

“Matukar a arewa da karuwai,
yan daudu dasu da magajiya.
Da samari masu ruwan kudi,
Ga mashaya can a gidan giya.
Matukar yayan mu suna bara,
Titi da Loko-lokon Nijeriya.
Hanyar birni da na kauyuka,
Allah baku mu samu abin miya.
Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu mai tanyonsu da dukiya.
Babu shakka yan kudu zasu hau,
Dokin mulkin Nijeriya.
In ko yan kudu sunka hau,
Babu sauran dadi, dada kowa zai
sha wuya.
A Arewa zumunta ta mutu,
Sai karya sai sharholiya.
Camfe-camfe da tsibbace
tsibbacen,
Malaman karya yan damfara.
Sai karya sai kwambon tsiya,
Sai hula mai annakiya.
Ga gorin asali da na dukiya,
Sai kace dan annabi fariya.
Jahilci ya ci lakar mu duk,
Ya sa mana sarka har wuya.
Ya sa mana ankwa hannuwa,
Ya daure kafarmu da tsarkiya.
Bakunan mu ya sa takunkumi,
Ba zalaka sai sharholiya.
Wagga al’umma mai zata yo,
A cikin zarafofin duniya.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya ,
Zaya sha kunya nan duniya “.
“Mu dai hakkin mu gaya muku,
Ko ku karba ko kuyi dariya.
Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.
Gaskiya ba ta neman ado,
ko na zakin muryar zabiya.
Karya ce mai launi bakwai,
ga fari da baki ga rawaya.
Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.
Marigayi Sa’adu Zungur a cikin
waken sa mai suna “
Arewa Jamhuriya ko Mulukiya”.

No comments:

Post a Comment