Monday, 11 December 2017

KIMIYYA: BINCIKEN DUNIYOYIN SARARIN SAMANIYA

 Hukumar nan dake kasar Amurka mai suna NASA itace kan ja-gaba har
yanzu a duk duniya wajen binciko iliman da suka shafi sararin
samaniyya gami da watsa iliman don mallakar kowa-dakowa. Don haka a
wannan rubutu za'a ji sakamakon binciken waccan hukuma akan matsayar
binciken Samaniyya na wannan lokaci. Za kuma aji abinda akeson a cimma
nan bada jimawa ba insha Allahu.
 DUNIYOYIN SARARIN SAMANIYA
  Tunda jimawa ne  masana kimiyya da injinoyoyi suka duqufa don ganin
an kirkiro manyan maduban hangen nesa mafiya kyau da karfi fiye da
wadanda masanan da suka gabata misalin Galileo sukayi amfani dashi,
izuwa yanzu kuma akan iya cewa haka-ya-fara cimma ruwa. Babbar nasarar
da aka samu mai gwabi zuwa yanzu itace ta kirkirar wani babban madubin
kallon nesa a kusa wanda yake shawagi a sararin sama mai suna Kepler.
                  A wajajen shekara ta 2006 ne aka fara kokarin harba
madubin izuwa sama wanda ba'a samu damar yin haka ba har sai a watan
uku na shekarar 2009. Sannan kuma ance sai da ya dauki misalin tsawon
lokacu na watanni biyar aikin sa ya kankama.
    Wannan madubi na kefla yana biye da duniyar mune ta (earth) wajen
bin falaki domin zamar yadda duniyar tamu da sauran duniyoyi 'yan
uwanta irinsu Makuri keyi. Sannan an kiyasta cewa yana zagaya falakin
ne yaje ya dawo acikin kwanaki 373 (shekarar sa kenan), watau ya
gazarwa da duniyar mu sauri da kwana goma sha uku kacal, domin ita
kwanaki 360 takeci wajen zagayen falaki.
   Daga cikin manyan mnufofin samar da madubin kamar yadda NASA ta
bayyana sune;-
  1. Domin kayyade adadin duniyoyin (planets) dake cikin cincirindon
taurarin da Rana ke ciki mai suna Milky way.
 2. Domin auna girma da fadin wadancan duniyoyi.
 3. Domin fahimtar yanayin duniyoyin ta yadda za'ayi hasashen samuwar
rayuwa ko akasinta.
  4. Dadin dadawa shine domin fahimtar halayen taurari masu gewaye da
duniyoyi kwatankwacin Rana.
  Don haka idan mai karatu ya natsu, zai fahimci cewa ayanzu masana
sun rage dokin kai kansu duniyar taurari, sunfi damuwa dai da sanin
abinda ke cikin duniyoyin ne kurum.
 Ga kadan daga cikin nasarorin da aka samu tun daga fara aikin wancan
madubi izuwa yanzu;
  1. A Shekarar 2009 akaci nasarar binciko tulin taurarin da suka
wanzu acikin milky way ninkin ba ninkin din wadanda aka sani abaya.
 2. A shekara ta 2010 akayi hasashen cewa duniyoyin da rayuwa zata iya
kasancewa acikinsu sunkai kimanin miliyan 100.
  3. A shekara ta 2011 ne cigaban bincike yayi nuni da cewa akwai wasu
 duniyoyi da ake tsammanin samun halittu acikin su kimanin 1235,
saboda an hango ruwa da yanayi mai kyau irin namu aciki.
 4. A shekara ta 2012 ne NASA ta fitar da sanarwa mai nuni da cewa
taurarin da suke zagaye da duniyoyin planet acikin milky way sunkai
kimanin biliyan 160.
 5. A shekarar 2013 ne hukumar NASA tayi hasashen cewa adadin
duniyoyin planet yana daf da taddo adadin taurari duk dadai sun
tabbatar da cewa taurari sunfi duniyoyi yawa a sararin samaniya, amma
sunce idan aka tsaurara bincike, adadin duniyoyi na iya zama daga
biliyan 100 zuwa biliyan 400. Kuma sukace nisan dake tsakanin duniyar
wani tauraro mai kama da Rana mafi kusanci da duniyar mu shine nisan
zangon da haske zaici yana gudu a shekara goma sha biyu.

  6.  A watan yulin shekarar 2014 ne NASA ta saki sanarwa mai cewa
tana da tabbacin wanzuwar duniyoyi kimanin 1000 masu kamanceceniya da
duniyar mu ta earth wadanda kuma ake hasashen samun rai aciki. Wasu ma
na ganin mutane ne irin mu ke rayuwa acikinsu. Allah dai shine Masani.
  Yanzu kuma sai bangaren halittu.. Zamuciga insha Allahu
 Daga Sadiq Tukur Gwarzo
       08060869978
      Sadiqtukurgwarzo@gmail.com

No comments:

Post a Comment