ASALIN RUBUTUN HAUSAR BOKO DA BUNKASAR HARSHEN HAUSA
Daga SADIQ TUKUR GWARZO
Abubuwan Dake ciki
-Gabatarwa
Hausa kafin rubutun boko
Rubutun boko na asali
Karbuwar Rubutun Boko
Bunkasar harshen hausa
Kalubale
Kammalawa
Madogara
Hausa kafin Rubutun Boko
Kafin karni na sha tara, kuma kafin zuwan turawan mulkin mallaka kasar hausa, ɗaukacin masana sun haɗu akan cewa babu rubutun AaBaCaDa (da akafi sani da boko) a kasar hausa, rubutun larabci da kuma hausa da larabci (Ajami) kaɗai aka sani.
Shi kansa rubutun na Ajami, dattijo Marigayi Alh Muhammad Koki wanda yana cikin mutanen da suka tallafawa turawa wajen aikin tafinta har aka samar da Gidajen tarihi na kano dana sokoto cewa yaji kaka-da-kakanni ana cewa asalin hausa babu rubutu har sai lokacin da larabawa suka zo da musulunci. A lokacin ne aka rinka amfani da rubutun larabci wajen sadarwa da kuma yin rubuce-rubuce. Har ma yace a wancan zamanin, idan kanaso ka tura wani sako ga wani ɗan uwanka dake rayuwa acan nesa dakai, sai dai kaje ka samu malami daya kware a fannin larabci, ka faɗi masa sakon shikuma yana rubutawa da alkalami a takarda, sannan ka biya lada, kai kuma ka naɗe sakon ka turawa ɗanuwan naka ta hanyar fatake. Shima ɗan uwannaka idan ya samu sakon, haka zaije ga malami wanda ya iya karatun larabci ya karanta masa sakon gami da fassarawa.
Sai Alhaji Muhammad Koki yace:- sai a wajajen karni na sha shidda zuwa na sha bakwai wani Sarki a Zaria ya bada shawarar kirkiro da dabarar rubuta zantukan hausa da haruffan larabci domin saukakewa da kuma bunkasa harshen na hausa.
Watakila kafin wancan lokacin, malumman bogi sunyi sharafi a kasar hausa, irin masu fassara sako gwargwadon abinda suka ga mutum yanaso kenan kamar yadda misalin hakan tazo a hikoyoyin shehu Jaha inda akace wata mata tazo gareshi ɗauke da takarda domin ya karanta mata, daya tashi sai ya fara faɗin "bayan gaisuwa da fatan kina lafiya, ina so na sanar dake cewa ina nan cikin koshin lafiya.." Sai kuwa matar tayi sauri ta katse shi tana mai cewa 'Takardar Wasiyya ce fa ba wasika ba!', sai kuwa shehu jaha yace "aff aff, ai da saiki faɗa min haka tunda farko tayadda zan karanta miki ita da sigar wasiyya". Ko kuma muna iya cewa karancin fahimtar wasu kalmomi na larabci ya taka muhimmiyar rawa wajen dakile harkar sadarwa a kasar hausa, amma samar da ajami sai ya kawo sauyi a harkar.
John Edward Philips ya rubuta a littafin 'Hausa in the Twentieth century' cewa: Fara Rubuta ɗai-ɗaikun kalmomin hausa da haruffan larabci ya samo asali ne tun lokacin da aka fara rubuta littafi da larabci a yankin. Tunda a cewar sa Littattafan da aka rubuta a zamanin suna kunshe da sunayen Hausawa kamar misalin Muhammad Rumfa, sarkin kano dayayi mulki a karni na goma sha biyar.
Amma dai, littafi mafi daɗewa da aka samu wanda aka rubuta da Ajami shine littafin 'Riwayar Annabi Musa' da akace wani bakano mai suna Abdullahi Suka ya rubuta tun a wajajen karni na goma sha bakwai.
Daga nan kuma sai wakokin da aka samu Malaman nan na katsina sun rubuta, watau Dan Marina da Dan Masani, waɗanda suma ake hasashen anyi rubutun a zamani ɗaya da wancan na Abdullahi Suka, ko kuma wasu shekaru kaɗan baya da nashi. Daga nan ne kuma littattafai suka rinka samuwa da hausar Ajami, ta inda ake kara bunkasa rubutut-tukan da abubuwan da abaya babu su tun usuli, tun daga karni na sha takwas har zuwa na ashirin.
FARA RUBUTUN BOKO
Marubuci John Edward Philips yayi hasashen cewa hausar boko ta fara ne a lokacin da turawan mulkin mallaka suka iso kasar hausa. A cewar sa Sa'ar da Fredrick Lugard ya zama shugaban 'Royal Niger Company' a ranar ɗaya ga watan janairun 1900, kaɗan daga sojojinsa ke jin yaren Ingilishi, tunda an samu cewa ana fassarawa sojojin Jawabin da Sarauniyar Ingila Victoria ta aiko a karanta musu da yarukan Hausa dana Nupanci.
Tun alokacin, ance Lugard ya fahimci nisan da yaren hausa yayi a zukatan kabilun dake zaune a arewacin Nigeria. Tunda an samu cewa zaka riski mutum yana magana da harshen kabilar sa, yana kuma magana da harshen hausa. Har ma takai jallin da idan hurɗa ta haɗa wasu mutane masu mabam-bantan kabila da harshe, sai kaga sun ajiye yarukan nasu sunyi amfani da harshen hausa wajen sadarwa.
Ga abinda aka taba jiyo Lugard yana cewa dangane da wannan batu:-
Na gamsu matuka wajen samar da daidaito a ɗibar sojoji ba kawai tsakanin kabilu ba, sai dai tsakanin mabiya addinin (Annabi) Muhammad da kuma sauran mutane marasa addini. Ina matukar girmama addinin (Annabi) Muhammadu, don haka bana ɗaukar rashin sanya mabiya addinin na (Annabi) Muhammadu a harkar soji a matsayin siyasa.. A yanzu mun fahimci cewar Kabilu marasa addini irinsu Gwari, Kedar da sauransu duk suna iya magana da harshen hausa, don haka zanfi so nasanyasu a aikin soja da zarar babban wurin atisayen mu ya Kammala..
Sai dai, duk da kasancewar Lugard yafi son ɗaukar sojoji masu fahimtar hausa waɗanda suka fito daga sauran kabilu saɓanin Hausawa musulmai, ko kuma ace yafi son ɗaukar mutane marasa addini sama da mabiya Addinin musulunci, amma sam-sam ance baya koyar da sojin nasa harshen su na Ingilishi.
Wannan kuma wani wayo ne da masu dabarar yaki suka nakalta. Tunda shi dai yare kamar sirri ne, idan har baka jin yaren da ake yarawa, ba zaka iya fahimtar sirrin da ake tattaunawa ba. Wayon anan kuwa shine, su turawa da sojojin su suna jin harshen hausa, harshen da mafi yawan waɗanda suke yak'a ke amfani dashi, amma kuma sunki bada wata kafa dasu waɗanda ake yak'a ɗin zasu koyi turanci balle har su san wani abu daga sirrikan da turawa ke yaɗawa a tsakanin su.
Da wannan Lugga ya nunawa 'yan uwansa turawa muhimmancin kowannensu yakoyi harshen hausa. Ance ma shine asalin wanda ya kirkiro da jarabawar auna fahimtar hausa ga ma'aikatansa turawa kwatankwacin wadda akace Marigayi Sardaunan Sokoto Ahmadu Bello ya kirkiro ga ma'aikatan gwamnati a zamaninsa. Sai dai turawa da yawa sunga baiken Lugard, sai sukayi turjiya kuma akan wannan bukata.
Daga cikin fitattun su akwai Kyaftin C.W Moloney, wanda akace ya nuna kyamar sa a fili ga yaren hausa tunda acewar sa Larabawa masu yaɗa addinin Islama ne suka kafa shi, ai kuwa shine wanda akace ya haɗu da hatsarin rashin koyon hausa a Fadar sarkin zariya.
Yadda abin ya auku shine, ance Kyaftin Moloney na gabatar da Jawabi ga jama'ar Zazzau ne a fadar sarkin Zariya a ranar uku ga watan oktoba na shekarar 1902 (tun kafin turawa su gangaro Kano da yaki kenan) shikuma mai tafinta yana fassarawa ga jama'a. Sai rashin fahimta ta dabaibaye tafintan, inda ya rinka sauya zantukan da Kyaftin Moloney ke karantawa da wasu zantukan na daban gwargwadon fahimtarsa. ( Watakila saboda tsauraran kalmomin dake cikin jawabin ko kuma saboda karancin ilimin fassara ga tafintan) A ciki ne yake nunawa jama'ar zazzau cewa Matayensu mallakin turawa ne, kuma turawa na matukar bukatar su, duk wanda yaki amincewa da hakan kuwa zai haɗu da fushin turawa... Haba, kafin a ankara sai ganin kan Kyaftin Moloney akayi yana mirgin-mirgin a kasa, wani zakakuri ya sare shi saboda bacin ran abinda yaji... Nan take kuwa sai faɗa ya kaure.
Bayan kura ta lafa, sai Gwamna Lugga ya tura sako ga kasarsu Ingila a rohoton da yake turawa lokaci zuwa lokaci gami da labarta musu abinda ya sami Kyaftin Moloney. Shine har yake faɗa musu cewa ba lalle ne ace tafintan Kyaftin Moloney da gayya yayi wannan kasassaɓar ba, sai dai watakila hakan ta faru ne saboda rashin samun wata fahimta da Kyaftin Moleney yayi dangane da yaren hausa tayadda har ya kasa tantance tsakanin abinda yake karantawa da abinda tafintan sa yake faɗa.
Don haka a karshe Lugga ya bada shawarar cewa a ganinsa mafitar kare aukuwar irin wannan hadari anan gaba shine turawan mulki 'yan uwansa su koyi hausa.
(D.J.M Muffet, concerning Brave Captain, London 1964.)
Ai kuwa hakan akayi, domin an samu cewa Ingila ta bada odar kowanne jami'inta ya fara koyon harshen hausa, an buga sanarwar fara yiwa jami'an mulkin mallaka jarabawar auna fahimtar harshen hausa a jaridar Northern Gazette ta ranar 30 ga watan satumbar shekarar 1902.
RUBUTUN BOKO NA FARKO

No comments:
Post a Comment