WANZUWAR HALITTU A DUNIYOYIN SAMA By
Sadiqtukur Gwarzo.
Duk da kasancewar ko anan duniyar mu ta
earth,
har yanzu masana na
tababar sahihiyar hanyar da rayuwa ta wanzu,
amma dai tun da jimawa
binciken masana ya nuna lalle da alamar halittu
masu rai dake rayuwa a
duniyoyin sararin samaniya. Akwai masanan da
suka tafi akan cewa
asalin rayuwar mutum a duniyar mu ta faro ne
daga cakuduwar qananun
halittu nau'in bakteriya, yayin da wasu kuma
suka
jajirce akan cewa
dukkan wani abu mai rai dake rayuwa a wannan
duniya asalinsa zuwa yayi
daga wata duniyar, dadai sauran zantuka da
dama.
Abinda ya fara tabbatar da wancan hasashen
aukuwar rayuwa a duniyar
sama shine dirar kumbo 'vickings' akan duniyar
mars a shekarar 1976.
Ance ya dira ne akan wani zagayayyen
dandamali
kusa da wani wawakeken
rami wanda masana sukayi hasashen cewa
shekaru biliyan hudu da suka
gabata Ruwa ne tunjim acikin ramin. Hotunan
da
kumbon ya turo nan
duniya kuwa sunyi nuni da shige-da-fice na
iskokin
numfashi ciki harda
oksijin. Wannan yasa gungunn masanan da suka
tura kumbon sukayi
hasashen akwai halittu a boye masu numfashi a
duniyar, har ma suka ce
binciken nasu kamar misalin kaji sauti ne amma
ka
rasa abinda ya fitar
da sautin.
Wannan binciken kuma shine ya bude kafar
samar da kirkirarrun
labarai da fina-finai akan halittun duniyar sama
misalin 'war of the
world', Apes of the planet of the sun' da
wasunsu,
a Inda aka rinqa
bayyana su da suffofi daban-daban.
Wani masanin kimiyyar sararin samaniya mai
suna Farfesa Chandra
Wickarama, ya tabbatar da cewa akwai halittu
masu rayuwa a sararin
sama bayan wani bincike daya gudanar. Shine
ma
yake cewa "Hakika
kauyanci ne ace mune kadai masu rai a fadin
daukacin duniya
(universe), ni inada tabbacin akwai halittu masu
rai a wasu gurare da
dama"
Daga nan kuma sai ya kafa hujja da hotunan
wata halitta mai kama da
mutum-mutumi da wani madubin bincike
mallakin
Farfesa Milton
Wainwright da tawagarsa ya dauko yana mai
cewa
irin wadannan abubuwa
daga wata duniyar sama suka nufo duniyar mu,
domin bazai yiwu ace daga
wannan duniyar ya tashi sama ba.
Shidai wancan
mutum-mutumi an bayyana cewa yana tattare
ne
da
sinarai samfurin kabon da oksijin, irin wadanda
suke ajikin mutane.
Kuma masanan da suke bincike akansa sunce
abin
yana yawo ne a saman
duniyar mu da misalin nisan mil dari biyu daga
dandamarin kasa.
A ra'ayin Farfesa Chandra mutum ma asalinsa
daga sama yake kamar
yadda yake cewa "idan akayi la'akari da
qwayoyin
halittar dan adam na
DNA, za'aga suna kamnceceniya ne da varus,
kuma akwai yawa-yawan
wadannan suffofi a sararin samaniya. Kenan zata
iya yiwuwa tun daga
can sama DNA suka fara harhaduwa sannan
suka
sauko nan kasa suka kara
haduwa da kananun halittu, daga bisani suka
rikita
zuwa mutum. Manufa
ta dai shine duk inda aka samu kananun halittu,
to
tabbas dayan uku
ne. Kodai ace suna tare da manyansu, ko anyi
manyan sun gabata, ko
kuma a hankali zasu rikide zuwa manyan."
A wata mukala da wasu masana biyu Dr. Seth
shostak da Dr. Dan
wethmer suka gabatar a gaban kwamitin
binciken
Sama na majalisar
dokokin amurka, sunyi bajekolin manyan dalilan
da
yasa masana keda
yakinin akwai rayuwa a duniyar sama, ga kadan
daga ciki;
1. A shekar 1976, kumbon Vicking bayan dirarsa
a
duniyar Mars, ya
hango wasu sinadaran mahadai masu nuni da
wanzuwar Rai acan.
2. A shekarar 1977 kuma wani madubin hangen
nesa na Jami'ar Ohio ya
jiyo wani sauti kamar ance WOW a sama wanda
har yanzu anrasa
ma'anarsa.
3. A shekarar 1996 ne aka samu sawun halittu
akan wani baraguzi babba
daya duro Atlanta daga Sararin Samaniya.
4. A cikin shekarar 2001 da 2002 duk anjiwo
motsin halittu a watan
Europa na duniyar Jupiter.
5. Har ila yau, a shekarar 2007 wani mai bincike
Joop Kooper ya
gaskata ikirarin da wasu masana 'yan kasar
Russia
sukayi dangane da
wanzuwar kananun halittu a duniyar Mars.
Domin
shima yace ya hango
alamomin hakan.
A wannan shekarar ta 2014 ne dai hukumar
NASA ta ware kudi dala
Miliyan Hamsin ga wasu gungun masa rukuni
bakwai don yi bincike gami
da samo amsar wasu tambayoyi guda uku da
hujjoji kwarara. Ga
tambayoyin kamar haka;
1. Shin akwai halittu irin mu dake rayuwa a
daukacin duniya?
2. Shin wanne hali ke wanzar da rayuwa daga
sinadarai?
3. Shin tayaya za'a iya gane abubuwa rayayyu
dake a wajen duniyar
mu?.. Allah ya bada sa'a Amin
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978
No comments:
Post a Comment