Monday, 11 December 2017

MENENE HAKIKANIN ABINDA AL'UMMAR MU KE BUKATA?

   Abin tausayi ne matuka garemu idan muka kalli halin da yawa-yawan mutanen wannan al’umma suke ciki. Idan muka dauki misalin asibitoci da gidaden yari, a iya nan kurum mai tausayi zai fahimci wannan al’ummar tana cikin rudani da fagaf-niya.
    Sau da yawa zaka hadu da marasa lafiya wadanda suke bukatar kudin magani ko kudin aikin tiyata da likitoci zasuyi musu, amma sai abin ya gagara. Kullum muna ji yadda kafafen yada labarai suke kawo muryoyin dangogin wadancan mutane, wasun su idan anyi sa’a sai kaga an biya musu kudaden, amma da yawansu ba-haka abin yake ba.
       Da alamun har yanzu al’umarmu bata fara la’akari da yadda a kullum ilimi ke qara tabarbarewa ba. A yanzu haka dai kasuwanci ya mamaye harkar ilimi. Idan kana nemarwa ‘ya’yanka mai inganci dole sai ka fitar da kudi, idan kuwa bahaka ba sai dai kana-ji-kana gani yaranka zasu kasa karatun AaBaCaDa. A kullum gwamnatocin mu suna ikirarin gyara fannin ilimi, amma abin yaci tura, saboda jagororin da zasu kawo gyaran sun sanya son kudi a zuciyar su sama da son gyaruwar al’ummar da suke jagoranta.
     Su kansu malaman da yawan su basu fahimci ainihin abinda ya kamata su koyar ba. Da yawansu ma sun riqi harkar koyarwa ne a matsayin alaqaqai, ko kuma ace wucin gadi, tunda sai sun nemi aiyuka a NNPC, SHELL, Bankuna da sauran manyan gurabe basu dace ba zasu zo suna fafutikar neman aikin koyarwa. Ta haka zaka samu daliban ma basa fahimtar karatun, burinsu kuru su gama makaranta su karbi sakamakon, daga nan sai su shiga sahun masu neman aiki mai gwavi, don ganin anyi hannun riga da talauci.
     A yanzu kowa ka gani, kudi ne matsalar sa, don haka kudi yake son samu. Iyayen mu sunfi son muyi karatu don muyi arziqi, tunda atsammanin su da kudi kadai zamu iyayi musu sakayya. Adduoin da mafi yawan mu sukeyi shine ‘Allah ka bamu kudi’, abinda yawa-yawan mu bamu sani ba shine ‘samun kudi ba shine maganin matsalolin mu ba gaba daya’. Babban abin baqin cikin ma shine yadda hadama da handama sukayi mana babakere a zuciya, tunda zaka samu talaka kamar ni yana da tarin buqatu, yana son gina katafaren gida, yana son siyan mota mai tsada da sauransu wadanda sai ya samu miliyoyin kudade zai cika burinsa.
      Mu kalli yadda arziqi ya wadatu acikin mu. Yara qananu zaka ga suna riqe wayoyi na dubunnan nairori, duk talaucin mutum zaka same shi da tufafi sama da daya, zan iya cewa a yanzu babu unguwar dazaka rasa masu ababen hawa tun daga kan motoci da babura, gidaje kuwa gasu nan a kullum yinsu akeyi sabanin zamanin kakannin mu daya wuce inda zaka same su da tufafi daya jal, zaka samu babban gari amma mota bata fi daya ko biyu ba. Sai dai kuma duk da haka wadancan kakannin namu sun fimu zama lafiya, saboda basu maida matsalar ‘son kudi’ a matsayin gagarumar matsalar dake addabar suba.
        A wannan zamanin namu, duk da arzikin da Allah ya wadata mu dashi, kullum hanqoron qari mukeyi, don haka a kullum din zakaga ayyukan ta’addanci sai qaruwa sukeyi. Zaman lafiya sai qara qaranci yakeyi. Mun dorawa kanmu buqatu wadanda basu zamo dole ba, so mukeyi tilas mu cin musu. Attajirai sunfi kowa son kudi, don haka suke qin fitar da zakka, suke qara handame kudaden talakawa gami da qin taimakawa masu qaramin qarfi.
Mu kalli yadda qasar mu ke kashe maquden kudade wajen samar da tsaro ba tare da an samu shawo kan matsalar ba. A baya an ware tiriliyon na nairori don a siyo makamai, amma sai ‘yan uwan mu masu son kudi suka wawure kudin, a qarshe munga sakamakon abin, dubban al’umma sun rasa rayukan su da dukiyoyinsu, sannan an rasa zaman lafiya a lokacin. Talakawa kuma na cikin rashin kudi, shi yasa sai wasunsu  ke fadawa cikin fashi, sata, karuwanci, dillancin miyagun qwayoyi  da sauran miyagun aiyukan alfasha wadanda zasu samar da kudade cikin qanqanun lokaci za su kuma hana zama lafiya.
   Ga duk mai fahimta wataqila zai gamsu da cewa wadannan abubuwa sune manyan matsalolin mu. Idan da muna da zaman lafiya, sanatocin Najeriya basa buqatar a ware musu biliyoyin nairori domin siyo motoci masu sulke, haka nan kudin tafiyar da gwamnati zai zama qanqane tunda shugaban qasa ko gwamna zai iya yawo acikin gari daga shi sai direba baya tsoron wani abu. Idan kuwa har haka ne, zan iya cewa ba KUDI ne matsalar mu ba matsawar zaman lafiya da cigaba muke da buqata, tunda gashi son su da rashin su duk yana haifar mana da matsaloli.
    A nashi bangaren, babban malami, kuma shugaban majalisar malamai ta kano wato Mallam Ibrahim Khalil cewa yayi “Rashin son juna ne matsalar mu”. Ta yadda zamu gane haka shine, mu auna cewa mun samu kanmu a wata alqarya, attajiran gari suna da kyauta, sun eke daukar nauyin karatun kowa dake garin, harkar lafiya ma sune, duk mai matsalar abinci gurinsu yake zuwa, da sannu zaka samu cewa babu mai tsoron talauci a garin. Babu wanda zai ce idan baiyi fashi da makami ko sata ba bazai iya biyan kudin jarabawa ba, ko kudin maganin maras lafiya da sauran buqatu. Su kuwa masu kudin zaka samesu cikin lumana da kwanciyar hankali, basu da tsoron komi don kuwa talakawa na qaunarsu, suna musu biyayya, basa son wata annoba kuma ta auko garesu.  A qarshe zaka samu cewa matasa masu tasowa suna qoqarin koyi da attajiran gari, kyauta zata zamo abar so ga kowa tayadda kowa zai rinqa fafutikar yin wani abu domin ganin ya  farantawa danuwansa. A tunani na wannan shine zaman lafiya…
Zamu cigaba insha Allahu
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
      08060869978

No comments:

Post a Comment