Tuesday, 26 December 2017

TARIHIN ALH MUHAMMADU RIBADO

4.   ALH. MUHAMMADU RIBADO
  Sunan Tarka dana Muhammadu Ribadu ba bako bane ga dukkan tsohon ɗan siyasar Arewa, ko kuwa mai yawan sauraren hirar marigayi Maitama Sule ɗan masanin kano.
  An haifeshi a kauyen Ribaɗo, a shekarar 1909, mahaifinsa Arɗo Hamza shine dagacin garin Balala dake Gundumar Yola ta ta tsohuwar jihar Gongola kafin daga bisani a kirkiri jihar Adamawa.
   Yayi karatun addini a tsangayar Liman Yahaya dake kauyensu, sannan daga baya ya soma karatun boko, inda ya soma da Makarantar elementare, sannan midil daga shekarar 1920 zuwa 1926.
  Bayan ya kammala karatun midil, daga baya ya samu aikin koyarwa ga 'ya'yan turawan mulkin mallaka a gidajensu, da kuma a makarantar midil ɗin daya kammala dake yola.
   Haka kuma, da mahaifinsa ya rasu a shekarar 1936, sai ya gajeshi a matsayin dagacin Balala.
  A shekarar  1946 ya samu tallafin karatu zuwa turai, don haka bayan ya dawo gida sai ya kamu da sha'awar siyasa, inda ya tsaya takarar ɗan majalisar arewa a shekarar 1946 yaci, ya kuma sake cin zaɓe a shekarar 1951.
  Tun a wajajen shekara ta 1948, Allah ke ta ɗaukaka matsayin Muhammadu Ribaɗo da mukamai daban-daban a tarayyar Nigeria, domin kuwa ya zamo ɗan kwamitin tabbatarwa da 'yan Nigeria manyan mukaman kasa tun zamanin da aka soma shirye shiryen karɓar yancin kai.
Haka kuma ya zamo wakili a kwamitin Noma na Nigeria, da kuma mamba a kwamitin bada lamuni domin ciyar da Arewa gaba.
  A shekarar 1950 kuwa sai ya samu zama memba a kwamitin gyaran kundin tsarin mulki a Ibadan.
   A shekarar 1952, aka zaɓi Alh Muhammadu Ribaɗo a matsayin ɗaya daga cikin 'yan kasa akunshin ministoci, inda ya zama Ministan Albarkatun kasa na Nigeria.
   A shekarar 1954 kuma, sai aka zaɓe shi a matsayin mataimakin shugaban jamiyar NPC na biyu, yayin daya zamo shine na uku a shugabannin Arewa idan ka fara lissafawa daga Ahmadu Bello shugaban NPC ɗin, da kuma Tafawa Balewa mataimakin shugaban NPC na farko.
  Alh Muhammadu Ribaɗo ya sake zamowa ministan Kasa, Albarkatu da makamashi a shekarar 1954, sannan ya zama ministan Kasa da Fannonin Birnin Tarayya dake Lagos a wanzan zamani a shekarar 1956.
  A shekarar 1960 kuwa Muhammadu Ribaɗo ya zama ministan tsaro, a shekarar kuwa kowa ya sani aka karɓo 'yancin kan Kasa. Don haka shine ministan farko daya soma bunkasa rundunonin soji na kasar nan, tun daga kan rundunar sojin kasa, ruwa data sama, inda ya samar musu da kayayyakin aiki da kuma gina musu barikoki, ya kuma tabbatar da cewar 'yan kasa sun shiga aikin samar da tsaro.
   Ance abokansa a wancan lokaci suna masa lakabi da 'power of powers' Watau 'karfin karfafa', kuma har yanzu ana tunawa dashi a matsayin jajirtaccen ministan tsaro da ba'a taɓa samun kamar sa ba a kasar nan.
 A ranar da Allah ya karɓi rayuwarsa itace ranar ɗaya ga watan Mayun shekara ta 1965 da safe, a ranar kuwa an shirya bashi lambar girmamawa ne tare da firimiyan Nigeria Sir Abubakar Tafawa Balewa, da Kuma firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.
  Allahu Akbar, Alhaji Muhammdu Ribaɗo shine ya kafa ma'aikatar tsaro dake Kaduna, ya kafa  Makarantar horas da soji ta 'Nigerian Defence Academy' a  Kaduna da kuma mazaunin Soji na 'Second Recce Squadron' dake  Abeokuta.
  Kuma har zuwa yau, manazarta na kallon cewa idan da Allah ya kaddara cewar Marigayi Ahmadu Ribaɗo na raye har zuwa ranar 15 ga watan janairun 1966 da sam juyin mulkin da akayiwa su Tafawa Balewa da Ahmadu Bello bai samu nasara ba saboda basirar sa da jajircewarsa wajen samar da tsaro.. Haka kuma da matasan kasarnan basu samu kasar a yadda take ba yanzu.
  Hakika, Nigeria tayi rashin Gwarzon bafullatani mai jajircewa akan lamurori, kuma mutum mai kaffa-kaffa akan dukiyar jama'a.
  Bayan rasuwar Alhaji Muhammadu Ribadu a lagos, sai aka faɗaɗa gidansa ya shige cikin Dodan Barrack, inda shugabannin kasa na soji suka rinka zama tun daga shekarar 1967 har zuwa 1991 da aka komo Abuja.
   Da fatan Allah yajikamsa Amin.

No comments:

Post a Comment