MAFITAR KASAR MU DON FARFADO DA
TATTALIN ARZIKI.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Tun a tsakiyar shekara ta 2014, hukumar auna bayanai
da suka shafi tattalin arziki ta Amurka mai suna 'U.S
Bureau of Economic Analysis' tayi hasashen aukawar
Nigeria cikin tsaka mai wuya sabili da wurare uku data
kalla a kasar masu bunkasa ma'aunin (GDP: gross
domestic product) tattalin arziki.
Wadannan wurare uku sune; 1. Harkokin Samarwa;
Abubuwan da Nigeria ke samarwa sun fara yin kasa
sosai. 2.Kudaden shigar kasar sun fara raguwa. 3.
Facaka da almubazzaranci suna dada karuwa a kasar.
Shekaru goma sha biyar da suka gabata, kashi 75 na
kudin shigar kasarmu daga siyar da danyen mai suke
zuwa, ragowar 25 na zuwa daga noma, kudin fito,
masana'antu da sauransu. A yanzu kuwa juyin juya hali
yazo, Hukumar bada bayanin tattalin arzikin Nigeria ta
'National Bureau of statistics' ta tabbatar da cewa
kashi 89.71 na kudin shiga a yanzu na zuwa ne daga
fannin da bana man fetur ba (wanda abaya ake
wulakantawa), sauran kason ne ke zuwa daga
manfetur. Farashin man fetur ya karye a duniya daga
dala 116 a tsakiyar shekara ta 2014, izuwa dala 30 da
doriya a yanzu. Sannan kuma adadin man da ake
hakowa yayi kasa sosai sabili da rikicin Niger delta.
Wannan ne yasa Gwamnan babban banki hasashen
gazawar gwamnati ga biyan albashi nan da watan
oktoba na shekarar 2016 matsawar aka cigaba da
tafiya a haka.
Babban abin haushin shine, shugabannin mu na baya
sun gaza yin tanaji da hangen nesa, sun kuma yarjewa
cin hanci da rashawa lalata tattalin arziki. Dukkan mu
munsan bala'in tattalin arzikin daya fadawa manyan
kasashen Turai, da Russia a wajajen shekara ta 2010 ,
amma Sam basuyi tunanin 'da-na-gaba ake gane zurfin
ruwa ba', suka ki sanya masana suyi musu binciken sila
da tanaji akan haka.
Kowa kuma ya gamsu cewa cin hanci ne ya lalata
kasa; an sace kudaden da za'a samar da tsaro, ilimi,
lafiya, da wutar lantarki. An danka amanar tattalin arziki
akan wadanda kodai zamu iya cewa basu cancanta ba,
ko kuma basu da kishin kasar su. Irin Mutanen nan da sunfi
bukatar Naira goma ta shigo
aljihunsu sama da Naira dari ta shiga aljihun kasarsu.
Don haka, akoda yaushe, suna iya yanke mummunar
dabara akan tattalin arziki. Tayadda idan kasa ta
ruguje, suna da kudin guje mata, sai dai subar
talakawanta da shan ukuba.
Labari mai dadi shine, shugaba Buhari ya gamsu da
cewa cin hanci da rashawa ne babbar matsalolin kasar
mu, a kuma shi yake yak'a a wannan lokaci, don haka ga wasu 'yan
shawarwari don bunkasa
tattalin arziki.
1. Tun kafin rantsar da Shugaba Buhari akan mulki, Alhaji Aliko
Dangote ya taba fadar cewa
"Gwamnati mai jiran gado na iya samun gagarumar
nasara idan ta ayyana dokar ta baci akan rashin aikin
yi, ta kuma yi yaki da rashawa". Abin nufi shine; a
inganta wutar lantarki, a kuma sawwaqe dokokin kafa
masana'antu. Da sannu kamfanoni zasu yawaita, aikinyi
zai karu, tattalin arziki zai habaka.
2. Da yake Arziki na nufin tarin abubuwa masu daraja, ya kamata
Nigeria ta koma cinikin 'Ban gishiri in baka Manda'
don farfado da Naira. Tayadda zamu koma ciniki da
ma'adinan kasar mu maimakon dala. Misali; Amurka
nason danyen man najeriya, sai muce ta siye shi da dala.
Indiya nason danyen mai, sai muce ta bamu kayan
abinci da magunguna. Haka ma china, Russia da
sauran kasashe, duk akwai ma'adinan da suke so a
Nigeria, muma akwai abinda suke dashi wanda muke
bukata. Hakan na nufin Nigeria zata zamo mai tarin
kayayyaki masu daraja, wadanda ita kuma zata rinka
siyarwa da kamfanoninta, 'yan kasuwa, da makotan
kasashe da Naira. Daga karshe zai zamo bukatuwar mu
da dala tayi kasa, masu bukatar Naira kuma sun karu,
don haka tilas farashin ta yayi sama.
3. Muna bada shawarar a bude boda gami da inganta tsaro a wajen. Hakan
zaisa Abinci ya
yawaita, farashin sa kuma zai ragu. Amma fa wannan
don amfanuwar 'yan kasa ne ba don farfado ta tattalin
arziki ba kamar yadda marigayi shugaba Abacha ke cewa
"An gina kasa ne don al'umma suci moriyarta, ba don
aci riba ba". Idan kuwa hakan ba zai samu ba, to shugaba Buhari ya
kamata yayo odar kayan masarufi domin siyarwa a farashin gwamnati mai
rahusa, kamar yadda yayi a mulkinsa na farko.
4. Abu na karshe shine addua. Ya kamata 'yan kasa
muciga da neman taimakon Allah wajen fita daga
dukkan tsanani. Tunda munyi imanin, duk wani salo da
zamu dauka, sai Allah ya yadda zamu samu biyan
bukata.
Da fatan Allah ya taimaki kasar mu, ya baiwa
shugabannin mu ikon kamanta adalci. Amin.

No comments:
Post a Comment