Monday, 11 December 2017

ADDINI: HUKUNCIN WANDA YA ZAGI ALLAH TA'ALA


HUKUNCE-HUKUNCEN WANDA YA ZAGI ALLAH TA'ALA, DA WANDA YA ZAGI ANNABAWA DA SAHABBAI

  Tare da Sadiq Tukur Gwarzo

Alqhadi Iyadh Bn Musa acikin littafin "Ashshifa Bi Ta'arifi Hukukil Mustafa" qismi na hudu babi na biyu,  yaci gaba da cewa "A cikin alqur'ani, Allah Ta'ala ya la'anci wanda ya zagi Annabi (s.a.w) a duniya da lahira. Kuma Allah ya sanya zagin Annabi a cikin Zagin Allah. Don haka kuwa babu sabani acikin kashe duk wanda ya zagi Allah. Allah Ta'ala yace "Innallaziyna Yu'uzuunallaha wa Rasuulahu.. Al ahazab:57)

  Amma daga hadisai, an samu hadisi daga shaikh Abu Abdullahi Ahmad bin muhammad bin Galbun, wanda sababin sa yake tikewa izuwa sayyidina Aliyu (R.A) cewa manzon Allah (s.a.w) yace "wanda duk ya zagi Annabi, ku kasheshi. Wanda kuwa ya zagi sahabbaina, ku dake shi".
   Acikin wani hadisi Ingantacce, Annabi Muhammad (s.a.w) yayi umarni da kisan Ka'abu binil Ashraf da fadin sa sallallahu alaihi wa sallam cewa "Wanene zai isar min da ka'abu dan ashraf, domin shi ya cuci Allah da manzon sa" (sai wani daga cikin sahabbai ya amsa yaje ya hallaka shi)
  Haka kuma Annabi yayi umarni da kisan Aba Rafi'u. Bara'a yace wannan mutumi ya kasance yana cutar da Annabi sallallahu alaihi wa sallam da zagi.
   Haka nan, Annabi ya umarci kisan Dan Khaddali da kuyanginsa a ranar fathu makkata. Wadannan kuyangin sun kasance suna rera wakoki na zagin Annabi sallallahu alaihi wa sallam.
    A wani hadisin kuma, an samu wani mutum yana zagin Annabi Muhammad (S.a.w). Sai Annabi yace "Wa nene zai isar min da makiyi na"? Sai khalidu yace "Gani nan". Sai kuwa Annabi ya turashi ya hallakashi.
    Akwai fadin Abdurrazaq ma a game da Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Cewa wani mutumi ya zage Annabin.  Sai Annabi yace "wanene zai isar min da makiyi na?" Sai zubairu yace "Ni". Daga nan sai Zubairu yayi fito-na-fito dashi har ya hallaka shi.
    Sannan an ruwaito cewa wani mutumi yana karyata Annabi Muhammad Sallalahu alaihi wa sallam. Sai Annabi ya tura Aliyyu da zubairu su hallaka shi.
   Haka kuma an ruwaito cewa wani mutum ya zowa Annabi Muhammad (s.a.w) yana cewa " Ya ma'aikin Allah, naji mahaifina yana fadar munanan kalmomi a gareka, sai na halaka shi". Sai Annabi bai tuhume shi akan abinda yayi ba.
    An ruwaito daga Bazaari, cewa Ibn Abbas wanda ya fito daga kabilar dan Ma'aydin, yazo yana kira, yana cewa "ya ku taron kuraishawa, me nayi da za'ace za'a kashe ni alhali ina cikin ku amma zakuyi shiru? Sai Annabi (S.a.w) yace "saboda kafircin ka da kuma kirkirar karya ga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam"
     Yana daga haka, wata wasika da wani dagaci ya turowa Umar bin abdul'aziz yana neman shawara akan kashe mutumin daya zagi sayyidina umar. Sai umar bn Abdul'aziz ya tura masa da amsa yana cewa "Baya halatta kashe wani mutum musulmi saboda zagin wani mutum sai dai idan Annabi Muhammad (s.a.w) ya zaga. Wanda ya zagi Annabi kuwa, hakika jininsa ya halatta"
    Khalifa Rashid ya tambayi imamu Malik dangane da hukuncin wanda ya zagi Annabi (S.a.w). Wanda kuma masana fikihu na kasar iraq suka bada fatawar ayi masa bulala. Sai Imam maliku yayi fushi sosai, yace "Ya amirul muminin, menene amfanin wanzuwar al'umma bayan an zagi Annabin ta? Ay wanda ya zagi Annabi daga Annabawa kashe shi akeyi, wanda kuwa ya zagi Sahabin Annabi (s.a.w), sai ayi masa bulala.
   Allahumma sallai Ala sayyidina Muhammad Wa Sallim.

No comments:

Post a Comment