3. HASSAN USMAN KATSINA
An haifi marigayi Hassan Usman Katsina a birnin Katsina a shekarar 1933. Shi ɗane na uku ga marigayi Sarkin Katsina Usmanu Nagoggo ɗan Muhammadu Dikko.
Ya soma makarantar elementare a garin Kankia, sannan yayi makarantar Midil a birnin katsina. Inda daga nan ne ya samu damar shiga kwalejin Barewa dake zaria.
Bayan ya kammalata kuma ya shiga Makarantar Nigerian school of Arts and Sciences dake nan zaria, sannan ya shiga aikin soja a shekarar 1956.
Marigayi Hassan Katsina ya shiga aikin soja cikin nasara, duba da yadda ya rinka samun ɗaukaka akai-akai da kuruciyarsa da kuma damarmakin karo karatu, a cikin haka yayi karatu a makarantun the Royal officer training school Ghana, the Mons Officer Cadet School da the Royal Military Academy Sandhurst inda akace anan abota ta haɗu tsakanin sa da Iliya Bisalla.
Ya zama laftanal kanal a shekarar 1966, wanda daga nan akayi masa mukamin Gwamnan Arewacin Nigeria a shekarar 1966 bayan hamɓarar da Gwamnatin Su Ahmadu Bello Sardaunan sokoto. Don haka shine gwamnan arewa na biyu ɗan Arewa bayan Sir Kashim Ibrahim.
Zamowarsa Gwamna a wannan lokaci wayau ne nasu Major Chukuma Kaduna waɗanda akace sune suka kashe su Tafawa 'Balewa, domin samun karɓuwa daga 'Yan Arewa bayan sun karɓi mulkin kasa.
Don haka sai sukaga cewa Kasancewar Hassan Katsina ɗan Sarauta ne, bashi mulki zai sanya aminci a zukatan sarakuna da talakawan Arewa.
Watanni goma sha shidda da soma mulkinsa sai akayi jahohin Arewa, inda aka fitar da Jihar Kano, Kaduna, Arewa ta tsakiya da Arewa ta Kudu, a wancan lokacin sai aka karawa Hassan Usman girma a aikinsa na Soja
An naɗa shi mukamin Army chief of staff daga shekarar 1968 zuwa 1971 sannan ya samu daɗin girma daga shugaban kasa na lokacin Gen. Yakubu Gowon bayan hamɓarar da Major Aguiy Ironsi kenan izuwa mukamin 'Deputy Chief of staff supreme military headquarters'.
Haka kuma yana da mukamin Major-General aka naɗa shi Federal commissioner of establishment na tsawon shekaru biyu sannan da kansa ya ajiye aiki watanni biyu bayan kisan Janar Murtala Muhammad a wani juyin mulkin da baiyi nasara ba, zamanin Ulusagun Obasanjo kenan ke kan mulki da kakin soja, a ranar 29th na yulin 1975.
Tun daga nan kuma ya dawo gidansa na Kaduna da zama, kuma bai sake karɓar wani mukamin gwamnati ba duk kuwa da tayin da shugabanni suka rinka yi masa, sai dai ya bada gudunmuwa wajen kafa jam'iyyun Siyasa.
Kafin rasuwarsa a ranar 24 ga watan yulin 1995, shi shahararren ɗan wasan Polo ne, kuma ya rike sarautar Chiroman Katsina har zuwa mutuwarsa.
Haka kuma, tun kafin rasuwarsa wasu mutane suka rinka jefa masa zarge-zarge na laifukan soji. Misali, wasu Inyamurai na ganin ya tsanesu kuma dasa hannunsa akayi musu kisan kare dangi a Arewa a zamanin yakin Basasar kasa, wasu kuma na kokarin shafa masa bakin fentin cewa dashi aka kashe Sardauna.
Sai dai a zahiri, duk manyan Abokansa sun karyata haka, bisa hujjar cewa ADC ɗinsa ma Inyamuri ne, kuma bashi da hannun kitsawa su sardauna juyin mulki, an ɗauko shine kurum domin a nemi soyayyar 'yan arewa bayan juyin mulki.
Ance tun bayan shekarar 1993, ba'a sake ganin Marigayi Janar sani Abacha tare da Janar Ibrahim Babangida a wuri ɗaya a wani taro ba sai lokacin mutuwar Marigayi Hassan Usman Katsina, inda mutane da yawa suka haɗu bisa jimamin rashinsa.
Kuma an sanyawa wurare da dama sunansa a yankin Arewa domin tunawa dashi, mksali shune Hassan Usman Polytechnique.
Da fatan Allah yajiqansa Amin

No comments:
Post a Comment