Tarihi: Asalin Bakar Fata da mazaunin sa
(Kashi na daya)
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
GABATARWA
Jinsin bakar fata ya wanzu tun da jimawa a wannan duniya. Masana kimiyyar zamani sunyi rubuce-rubuce da dama akan dalilan da suka sanya bakar fata suka zamo bakake. Abubuwan da aka tafi akan su har izuwa yau sune 1. Sinadarin Melanin ke sanya fata yin baki yayin da sinadarin carotein ke sanya ta yin haske. 2. Yanayin muhallin da bakaken fata ke zaune ya taimaka sosai wajen duhun fatarsu ko ace sauyawarta izuwa yadda take din koda idan za'a iya cewa abaya fatar tasu ta kasance mai haske.
Littafin 'The Black Man' wanda James Morris Web ya rubuta, ya zayyana cewa Hamu dan Annabi Nuhu A.S shine uban duk wani dan afirka, domin a cikin 'ya'yansa aka fitar da kusan duk wani jinsin mutum (k'abila) dake raye a afirka (Kamar yadda akace Samu da Japheth ne iyayen kabilun turai dana Asiya).
Ance Ethiopia jika ne ga Hamu, shine kuma fatar sa ta kasance bak'a. Shi d'ane ga Cush wanda daga gareshi ne daular 'cushite' ta bak'ak'en fata ta wanzu wadda ta fara kafuwa a kerma, daga bisani ta koma Meroa da Napata. Itace kuma daga bisani ta sauya suna izuwa Nubia, daga gareta ne kuma har iyau daular 'Axum' ko ace 'Aksum' ta samu.
Littafin Bible mai tsarki ya fada cewa Cush dan Hamu ne, (jikan Annabi Nuhu ne). (Genesis 10:6-8)
Ance Hamu ya haifi 'ya'ya hudu ne; Cush, put, canaan, da Mizraim.
ABUBUWAN DA MASANA SUKA RUWAITO GAME DA BAKAR FATA
Da fari dai, mun samu cewar tsoffin littattafan girka na tarihi sun zayyana wani wuri mai dauke da wasu kalar mutane bak'ak'e. Suna kiran wannan yankin da suna Aethopia. Sunce yankin yana kudu da sahara ne, kuma kudu da tekun Atlanta.
Marubuci Homer (850BC) ya ambaci sunan Aethopia sau biyu a cikin Iliad, ya kuma ambace shi sau uku acikin Odyssey.
Ga abinda Homer din ya rubuta game dasu a Iliad " ana samun 'Aethopians' a gabashi da kuma yammacin duniya. Teku ne ya rabasu izuwa mahudar rana da kuma mafadar ta."
Wasu na danganta ma'anar Kalmar 'Aethopia' a girka da Kalmar 'Aethiops' tun a lokacin Homer. Ma'anar ta kuma shine 'k'onanniyar fuska'. Ance da ita girkawa ke bayyana launin bak'in mutum.
Daga baya ne taswirar kasuwanci mai suna 'Periplus of the Erythaean sea' ta bayyana a kasar ta girka, itace kuma wadda ta k'ara zayyana hanyar da akebi don kasuwanci daga Girka, Rum da kuma tsohuwar Indiya. Itace ta kara yin bayanin wanzuwar mutane a wasu yankuna dake kudancin Zimbabwe.
Hesiod (800BC) ya bada labarin cewa sunan sarkin bak'ak'en fata Memnon.
Memnon wani jarumin gaske ne da akace an tab'ayi. Ya kasance bak'in mutum ne, kuma sunan shi ya fito sosai a tarihin yakin da akayi a Troy.
Marubucin Rumawa da girkawa mai suna Diodorus Siculus cewa yayi "Memmon dan kasar Aethopia ne, garin dake kudu da Egypt."
Hecateaus (550BC-476BC) mai binciken tarihi ne gami da tafiye-tafiye. Ance ya rubuta littafi akan bakaken fata tun a wancan lokacin, amma sai ya b'ata. Sai dai kuma masanan da suka karanta abinda ya rubuta sun rinka sanya shi a matsayin hujja wajen bada nasu tarihin.
Ance ya taba fad'a cewa "Kasar bak'ak'en fata na nan gabas da tekun Nilu"
Haka ma, acikin tarihan da Masanin tarihi Herodotus (440BC) ya bayar, ance ya fada cewa " birnin bakaken fata yana nan a kudancin Sudan ne. Ya kuma bayyana kalmar 'Meroa' a matsayin sunan babban birnin nasu. Haka kuma ya fada cewar a lokacin fir'auna Psamlik I (650BC), sojojin egypt da yawa sun bar kasar izuwa cikin bakaken fata. Sannan ya kara da cewa anayin kaciya a kasar.
Herodotus ya fada cewa Sarki Cambyses II (570BC) na daular Achaemenid, ya taba tura yan leken asiri izuwa kasar bak'ar fata. Da suka je sai suka sauka a wani yanki dake kudancin Libya wanda yake kudu da teku. Sun samu mutane lafiyayyu a wurin. A lokacin sarki cambyses na fuskantar tarzomar cikin gida, don haka bai shirya musu guzuri mai yawa ba. A karshe sai sojojin suka karaya suka koma gida da gaggawa.
A Littafin sa na uku, Herodutus ya fayyace kalmar 'Aethopia' a matsayin yanki mafi nisa daga libya. Yace " daf da mahudar rana ake kira Aethopia. Nan ne kasar da dan Adam ke rayuwa na karshe a duniya. Akwai zinare, katakwaye, bishiyoyi da albarkatu duk a wurin. Mutanen wurin nada tsayi, kyawawa ne, sun fi sauran mutane dadewa a duniya".
Manetho (300BC) cewa yayi "Memnon yazo ne daga Aethopia".
Masanin tarihi dan kasar Rum, Gaius plinus Secundus (23-79AD) ya fada cewa "sunan sarauniyar bakaken fata kandake. Kuma sun cinye kasashen syria da yaki."
Daga baya kuma ya kara da cewa "bakaken fata sun mamaye yankin red-sea daga tekun Indus. Wurine inda sam babu mutane kafin zuwansu".
Abaya-bayan nan, wani masani Mai suna Charles Bonnet, ya gano tsohon birnin bak'ak'en fata mai suna kerma. Hakika ya samu daukaka matuka gami da girmamawa a shekarar 2003 yayin daya gabatar da wasu gunkina na kawunan sarakunan daular (cushite) kushawa da aka sassaka da duwatsu, wadanda kuma ya hako tare da gabatarwa a gaban masana.

No comments:
Post a Comment