TARIHI: ASALIN BAK'IN MUTUM DA MAZAUNIN SA
(Kashi na biyar)
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
A cikin Littafin na 'The destruction of black civilisation' na Chancellor Williams, ya fadi cewa malaman girkawa da yawansu sun dauki ilimi ne a egypt wurin bakar fata, wani wuri da ake kira 'Temple of waset' wanda akace daga baya y zamo birnin 'Thebes' na egypt.
Hakika ance bakar fata sun taka rawar gani wurin kafuwar egypt. Marubuciya Drusilla Dunjee Houston (1926) tabi sahun masana da suka fassara kalmar 'KMT ko Khemet ko khem', wanda aka bayyana a matsayin ainihin sunan egypt da sunan 'garin bak'i' (The town of black) a littafin ta mai suna 'Wonderful Ethiopians of the Ancient Cushite empire'.
A cewar ta turb'ayar egypt ba bak'a bace, don haka kalmar khemet na nufin birnin bak'ak'en mutane.
Sai dai Marubucin 'The kingdom of Africa' Khaleed Muhammad ya musanta haka. Inda yace sam ba bakaken fata bane, kawai dai fatar jikkunan su launin turb'aya ce.
Abinda tarihi ya nuna shine, yankin tekun Nilu na dauke da mutane shekaru dubu sha takwas kafin zuwan Annabi Isa A.S. Kuma asalin mutanen suna zagayawa ne guri-guri domin yin farauta kamar dai yadda dabi'ar mutumin wancan zamani take. A haka wasu daga ciki suka riski yankin egypt a wajajen shekaru dubu biyar kafin zuwan Annabi Isa A.S. kamar yadda yazo a kundin 'The MacMillan Family Encyclopedia' vol E, shafi na 81.
Kafin wannan lokacin, an samu tabbacin wanzuwar wani babban birni a kusa da hasumiyar 'Tel al qaramel' dake yankin Syria, kusa da Aleppo, yankin dake makwabtaka da egypt, shekaru dubu tara da suka gabata. Da kuma wani birnin da akace ya wanzu a kusa da hasumiyar 'Tel al-sultan' dake k'asar Jordan a yanzu wuraren shekaru dubu bakwai zuwa dubu shidda kafin zuwan Annabi Isa A.S. Hakan na nufin akwai yiwuwar kwararorowar mutanen biranen wadanda ba lalle bakaken fata bane wajen kafa egypt ko kuma wajen k'ara hab'aka ta.
Sai dai kuma, wasu tsoffin zantuttuka na nuni da cewar daular bakaken fata dake kudancin Egypt ta riga egypt din kafuwa gami da samun wayewa ma.
Littafin 'The cyclopedia of Biblical literature' cewa yayi " Akwai dalilan dake nuna rarrabuwar masarautu da kuma fadin cewa gungun masana sun zo egypt ne daga Meroe (garin da daular bakaken fata ta kush ta kafu kenan)".
Masanin tarihi dan kasar girka Diodorus Siculus ya fada cewa " Bautar allolin Zeous da Osiri sun samo usuli ne daga Meroe". Watau daga baya ne ta riski egypt.
Ya kuma fada cewa " bakaken fata sune a egypt, su mutane ne da ruwa ya ciwo. Asalin egypt kuwa teku ne malale a yankin"
Wani masani Mr Rennel Ya gudanar da binciken kimiyya a kasar ta egypt. Kuma ya amince cewa wasu dubunnan shekaru da suka shude, egypt ruwa ne malale a wajen. Don haka yake cewa "asalin mutanen egypt daga ethiopia (tsohuwar kasar bakar fata) suka zo".
A bisa Zance mafi inganci, ance kabilu biyu ne suka fara zama a kasar egypt. Daya kabilar bakar fata ce, yayin da dayar take sabanin haka. Amma dai kabilar bakar fatar keda rinjayen mulki na shugananci. Watakila saboda bakaken fatar ne suka fara zuwa wurin, ko kuma sun fi sauran kabilun daraja da karfi.
Amma dai ance Fir'auna Narmer wanda akafi sani da 'Aha Mene' shine ya hade daulolin biyu yayi cibiyar mulkin egypt a Memphis. Shine fir'auna na farko da tarihi ya ruwaito duk da cewar an samu sabani akan shekarun dayayi mulkin sa.
Littafin 'History of modern world' na R.R palmer da Joel Colton ya sanya wanzuwar Fir'auna 'Aha-Mene' a wajajen shekara ta dubu hudu kafin Annabi Isa A.S. Idan hakan ta gaskata, muna iya cewa kimanin shekaru dubu daya ce ta gushe tsakanin fara zuwan mutane da kuma kafuwar masarauta a egypt din. Yayin da wasu littattafan kuma suka hakikance wanzuwar Fir'auna 'Aha-Mene' din a wuraren shekara ta dubu uku da dari daya kafin Annabi Isa A.S. Wasu kuma suka sanya shi a baya da haka sosai.
Har ila yau dangane da inda mutane suka fara zama tsakanin tsohon birnin bakaken fata na yankin Ethiopia da kuma egypt, ance yazo a tsohon littafin tarihin mutanen indiya mai suna 'The Puranas' cewa " Ethiopia ta girmi egypt. Sarakunan Kushawa (cushite) na zuwa Indiya tun kafin su fara zuwa Egypt."
Sannan ance yazo a littafin na puranas cewa " Mutanen da suka kafa egypt sun tashi ne daga yankin 'cusha-dwipa' na ethiopia. A lokacin birnin bakaken fata ba a Meroe yake ba, a wani wuri yake mai suna MERU. Daga baya mutanen da suka kafa babylonia suka bi bayansu"
Masanin Akiyoloji ma Dr Bruce Williams ya fada cewar akwai alamun cewa ilimin nad'a sarki ( ko fara sarautar fir'auna) ya zowa mutanen egypt ne daga tsohon yankin Nubia na bakaken fata.

No comments:
Post a Comment