MAHANGAR MU AKAN TALAUCI DA MATSALAR TATTALIN ARZIKI A NIGERIA.
(Gaskiya daci gareta)
Tare da SADIQ TUKUR GWARZO
Assalamu alaikum
Duba da matsanancin halin da talakawan qasa ke ciki, gami da tsare-tsare wadanda hukumomi ke dauka don saisaita lamurori a qasar nan, ya sanya mu yin duba gami da yin wannan rubutu.
DALILAN DAKE SANYA TALAKA CIGABA DA ZAMOWA CIKIN TALAUCI, ATTAJIRI KUMA YA CIGABA DA ZAMOWA CIKIN ARZIKI
A shekarar 2007, wani hasashe da ofishin mai kula da hada-hadar kudi na al'ummar qasar amurka (Congressional Budget office) yayi, ya nuna cewar duk wasu tsare-tsare da gwamnatoci ke aiwatar wa 'yan qasa, attajirai kurum yafi amfana, domin kuwa talakawa na qara cigaba da zamowar su cikin talauci.
Ga kadan daga abinda bincikensu ya nuna;
TALAKAWA: A tsawon shekaru talatin, samun kudin su ya habaka ne da kaso goma sha takwas kacal. (Ma'ana talakan da yake samun dollar daya a tsawon wancan lokaci, har yanzu baya samun dollar biyu)
MATSAKAITA: A tsawon shekaru talatin, samun kudin matsakaitan mutane ya qaru ne da kashi 40 kacal.
ATTAJIRAI: A tsawon shekaru talatin, samun kudin attajirai ya habaka ninkin-ba-ninkin da kashi 275. ( wannan labari yana da matuqar kyau idan aka hada shi da yanayin da talakawan nigeria suke a daga shekaru talatin zuwa yau)
Haka kuma a shekarar 2010-zuwa-2011, lokacin da tattalin arzikin amurya ya fadi warwas, hasashe ya nuna cewa rashin aikin yi da talauci sun qaru sosai, har ma akace amerikawa miliyan arba'in da shidda, wadanda abaya suke da rufin asiri (matsakaitan mutane) suka fada sahun talakawa. Hakan ne ya nuna cewa a duk amurkawa guda shidda, biyar talakawa ne, daya ne attajiri. Mutanen da abaya suke daukar dawainiyar wasu, ya zama sun koma ta kansu sukeyi. Wannan kuma sai ya haifar da qaruwa munanan laifuka gami da rashin kwanciyar hankali a qasar.
Har ila yau, a wani bincike da masana siyasar duniya suka gabatar, sun lura da cewa manyan shugabannin duniya masu farin jinin mabiya, suna haduwa da baqin jini, ko dusashewar farin jini yayin da suka hau karagar mulki, saboda yadda suke gaza aiwatar da ainihin muradun da mabiyan nasu suka zabe su akai. Misali; Franklin Delano Roosevelt da Adolf hitler, dukkansu shugabanni ne da tarihi bazai mance farin jinin su a wurin mabiyan su ba, har ma sun hau karagar mulki cikin soyayyar al'umma madaukakiya, amma kuma sun bar mulki cikin baqin jinin jama'a.
Amurkawa sun zabi Franklin Roosevelt ne a lokacin da suke mawuyacin talauci, tsammanin su daya hau mulki zaiyi qoqarin magance wannan matsala, amma sai akayi rashin sa'a, ya tunkari yaqi tare da qara tsunduma amurka cikin qangin karyewar tattalin arziki bayan hawan nasa. Haka ma Adolf Hitler, jamusawa sun lamunce masa ya hau kan mulki saboda suna tsammanin shine kadai zai iya warkar da annobar talauci data biyo bayan yaqin duniya na diya, amma da hawan sa sai ya qara cusa qasar acikin yaqin da yafi na baya tsamari. Makamancin haka ne ya auku ga shugaba obama, wanda ya hau mulki cikin farin jini sosai a karo na farko, amma a karo na biyu ya gamu da raguwar masoya.
Wadannan duk abubuwa ne da zasu haska mana abinda zai iya faruwa a qasar nan dai-dai da abinda yake faruwa ayau. Tunda dai munji Imam ibn khaldun na cewa "abinda ya faru a jiya, shine ke bada labarin abinda ke faruwa ayau. Abinda ke faruwa a yau kuwa, shine ke haska abinda zai auku a gobe".
A qasar nan, muna iya cewa mutane biyu ne attajirai. Daya sunan sa Dan siyasa, dayan kuwa Dan kasuwa ake yi masa laqabi. Dukkan su, suna amfanuwa ne da gwamnati, suna kuma taka doron bayan talaka ne don samun arziqi. Dan siyasa, sai jama'ar talakawa sun zabe shi zaici mulki, haka dan kasuwa wanda yake samun arziki ta hanyar sayarwa da al'umma hajojinsa.
Maganar gaskiya itace, dukkan wani tsare-tsare da gwamnati ke dauka, wadancan mutanen biyu take taimakawa. Sauran talakawa kuma take quntatawa. Yawansu kuwa dai-dai yake da biyu bisa goma, ma'ana ayanzu, muna iya cewa acikin mutanen najeriya goma, mutane takwas talakawa ne masu neman na abinci, mutum biyu ne attajirai. Ita kuwa gwamnati, wasu mutane da ake kira 'Bureaucrats' ne ke tafiyar da ita. Kamar misalin Ibe kachiku da makamantansu masu kula da harkar mai gami da juya tattalin arziqin qasa, mutane ne 'yan jari hujja wadanda basu san zafin talauci ba, idan za'a siyar da shinkafa buhu daya akan naira dubu dari, litar man fetur akan naira dubu, ba zasu damu ba.
Ku duba ma'anar kalmar 'Pain' a dikshinari, talaka shi dakai yasan zafin talauci, tunda a cikin sa yake. Talakan nan kuma ya zabi wannan gwamnati ne don tayi masa maganin matsalar tsaro data talauci data addabeshi. Kamar misalin mutum ne yana tsananin jin qishirwa, sai ya aiki wani ya kawo masa ruwa, idan dan aiken yayi jinkiri, dole wannan mutumi ya qara tura wani dan aiken. Don haka matsawar wannan gwamnati zata yi nuqusani wajen sassauta tsadar rayuwa, dole ne farin jinin shugabanta ya ragu kamar yadda abin ya faru a amurka da jamus.
Masana ilimin tsimi da tanaji, sunyi mana bayanin yadda abubuwa keyin tsada ko arha. Shine suke cewa "idan kayayyaki suka yawaita a kasuwa, dole farashin su ya karye. Idan kuwa sukayi qaranci, dole darajar su ta hau". Don haka, idan har dagaske gwamnati tayi shirin sauqaqawa talakawa, muna iya cewa bata kyauta ba yadda ta samar da qarancin shinkafa da kayan abinci a qasar nan (gwamnati ta hana shigowa dasu) domin batayi wani tanaji na azo a gani ba. Ya kamata ta fara baiwa 'yan qasa taki da iri na nomanta, sannan ta baiwa 'yan kasuwa damar kakkafa kamfanoninta, in yaso idan aka nomata sai tace ta hana shigowa da ita yadda tilas ayi amfani da 'yar gida, amma wallahi abinda tayi a yanzu ya sanya al'umma cikin tsanani, kuma hakan kuskure ne.
Batu na gaskiya, tilas ne mu fadawa shugaban mu kuma masoyin mu gaskiya. Idan har ya samu matsala amulkinsa, dukkan mune muka samu matsala.
Abinda zaiyi maganin karyewar tattalin arzikin qasa shine gwamnati ta bada agajinta wajen ganin an bude qananun masana'antu, sannan tayi tanajin duk abinda take tunanin ana buqatar sa a cikin gida, daga bisani sai a tilastawa 'yan qasa dogaro da wadannan masana'antun. Wannan ne kurum zai habaka dogaro dakai, gami da samar da dunbin aiyukan yi a qasa. idan da zaku bibiyi tarihin qasahen china, indiya da iran, da kun tabbatar da wadannan abubuwa. Amma a yanzu, tsarin da gwamnati ta dauka na nuna cewar talauci zai cigaba da wanzuwa a qasar nan har nan da shekaru biyu da rabi, babbar matsalar shine, dole ne rashin zaman lafiya ya qaru a qasar saboda talaucin da yawa-yawan 'yan qasa ke fama dasu, sai dai idan gwamnatin zata qaro makamai ne yadda zata rinqa kashe 'yan qasarta da kanta.
Shifa mulki dan Hikima ne, shiyasa hausawa ke cewa idan aka ciza, sai a hura. Idan bala'I yayi bala'I, sai kaga talaka ya daina tsoron mutuwa, daga nan sai ya fara fito-na-fito da gwamnati. Wannan ne yasa Marigayi Umar 'Yar aduwa yaci nasarar mulkinsa (Allah yajiqansa) domin yayi hikimar sulhu da 'yan tawayen Naija delta wadanda talauci yasa basa tsoron mutuwa. Shi kuwa talakan qasar nan, ya kamata ya mayar da kai wajen neman ilimin neman dukiya gami da sarrafa ta, ta yadda zai matsa daga halin fa yake ciki zuwa na gaba,sannan kuma ya sani, duk abinda gwamnati zatayi, attajirai zata qarawa arziqi. Kuma ba zata iya karya suba. Idan aka cire tallafin mai, attajirai aka taimakawa domin zasu siyo a waje da sauqi, suzo su siyar da tsada a gida. Haka kuma idan an hana shigowa da shinkafa, attajiran dai aka qara taimakawa, domin sune keda kudin yin gagarumin noma, wasunsu kuwa tuni sunyi hasashen aukuwar hakan, kuma sunyi tanajin kayan abinci daro-daro, don haka a hankali zasu rinqa fitowa dasu suna siyarwa al'umma da tsada.
Madalla da Abraham Lincoln (tsohon shugaban amurka) wanda yake cewa. "You cannot strengthen the week by weakening the strong.
You cannot help the wage earner by pulling down the wage payer"
A qarshe, muna fatan Allah ya ganar da shugannin mu, Allah ya dora su bisa tafarki na gaskiya. Amin
Dg Sadiq Tukur Gwarzo

No comments:
Post a Comment