Sunday, 10 December 2017

TARIHIN ASALIN BAKIN MUTUM 3

Tarihi: Asalin bakin mutum da mazaunin sa
      (kashi na uku)

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Littafin babil maitsarki dai ya fada cewa Cush jikan Nuhu ne, d'a ne kuma ga Hamu. (Genesis 10:6, chronicles 1:8-10)
   Ance jikokin Cush sun zauna a mesopotamia, Arabia da kuma Afirka. Littafin Kitab al magal ya ruwaito cewa Havilah dan kush Na biyu ya zauna tare da 'ya'yansa har sun kafa gari mai suna Havilah, 'yan uwansa kuma sun kafa garin sheba dana Ophir. Wasu kuma sun ce Ethiop dan Cush dan Hamu ya zauna a yankin sudan ne, daga shine kuma zuriyar bakar fata ta fantsama.
   Littafin babil na 'king james' ya fassara ma'anar 'cush' ko 'kush' da 'ethiopia', ma'ana konanniyar fuska da girkanci. Wasu littattafan kuma sun fassara kalmar da 'sudan', kalmar da itama ke nufin 'bakar fata'.
   Marubuci Muhammad Ibn Jarir Al Tabari dan kasar Farisa (915AD) ya ruwaito cewa "Sunan Matar Cush Qarnabil. Ita 'ya ce ga Batawil dan Tiras dan Japheth dan Annabi Nuhu A.S. Itace ta haifa masa Abissiniyawa (Habashawa), Sindiyawa da kuma Indiyawa."
  Matafiyi kuma mai bincike james Bruce ya ziyarci kasar Ethiopia a wajajen shekara ta 1770 har ma yayi rubutu dangane da zancen daya jiyo na tarihin al'ummar yankin. Ga abinda ya samo  ya kuma rubuta a littafin sa mai suna 'Travels to Discover the Source of the Nile' shafi na 305:-
"bayan daukewar ruwan d'ufana, Cush ya tafi da iyalansa izuwa gabashin tekun Nilu har ya riski tsibirin 'atbara' a lokacin babu wani abu mai rai a yankin. Daga nan kuma suka haye tsibirin suka riski yankin Aksum, inda suka fara zama kafin daga baya suka koma garin Meroa (wanda ya wanzu a kasar Sudan) da zama. Wannan kuma ana iya cewa shine asalin daular kushawa wadda daga bisani aka sauya mata suna izuwa Nubia.
  Littafin tarihin masarautar Aksum mai suna 'Book of Aksum' (Liber Axumae) ya bayyana garin Mazaber a matsayin usulin daular masarautar ta Aksum wadda ta biyo bayan Daular Kushawa. Abin nuni anan shine, yadda littafin ya nuna cewa  (Itiyopis) Ethiop dan Cush dan Hamu dan Annabi Nuhu A.S ne ya kafa garin tun farko. Daga baya akace masarautar ta fadada izuwa yankin Eritrea, ethiopia, sudan, Egypt, Yemen, Saudi Arabia da Somalia a wajajen shekara ta 300 miladiyya.
   A wani rubutu da marubuci Isma'il Kushkush yayi a jaridar 'The Newyork Times' ta ranar 31 ga watan maris na shekarar 2013 dangane da binciko tsohon garin Meroa da Charles Bonnet yayi bayan shekaru kusan 44 yana bincike a yankin, marubucin cewa yayi
    "Mutane da yawa a duniya suna kallon Sudan a matsayin kasar rikici, yaki talauci da rashin zama lafiya. Hakika duk wadannan abubuwa suna faruwa kuma ababen tausayawa ne, sai dai kuma an mance da cewa tsohuwar daular kushawa data wanzu a yankin ta taba yin gogayya da egypt, Rum da kuma Girka".
   Shima Claude Rilly, daraktan binciken Akiyoloji na kasar faransa a Sudan yayi magana yayin da aka binciko tsohon birnin na Meroa, wanda a yanzu yake kusa da wasu kauyuka da ake kira Bajrawiyya, tafiyar kilomita 200 daga Khartoum. Ga abinda yake cewa " tarihin sudan zai taka rawa sosai wajen binciko tarihin kabilu da sauran kasashen Afirka kamar irin rawar da kasar Girka ta taka a Turai. Mutane sun rayu a wannan wuri sama da shekaru dubu biyar da suka gabata, don haka zaiyi wuya ace babu abinda zamu iya samu mai muhimmanci anan".....
Sai dai kuma menene magana akan fantsamuwar kabilun bakar fata izuwa sassan afirka?

No comments:

Post a Comment