Monday, 11 December 2017

KIMIYYAR KANANUN HALITTU

KIMIYYAR KANANUN HALITTU

   Tare da SADIQ TUKUR GWARZO

Cikin hikimarsa madaukakin sarki Allah, ya halicci wasu qananun halittu dake wanzuwa tare damu dare da rana, wadanda kuma sukan zamo sila a mafi yawa-yawan lokaci na rashin lafiyar dake aukuwa garemu, ko su zamo silar zamowar mu cikin qoshin lafiya, ko kuma kacokan su zama ingiza-mai-kantun da suke tunzura mu mu aikata wani aiki(ba illa wanda ya shafi katobara) ba tare da sanin mu ba.
Tarihi yayi nuni da cewa tun gabannin dubunnan shekaru da suka shude, masana masu bin qwaqqwafi da suka gabace mu sunyi hasashen wanzuwar wasu halittu (wadanda ido baya iya gani), wadanda kuma a cewar masanan ke zamowa tsumma maqunshin cuta ga mafi yawan mutane.
Wannan hasashe ya zamo irin na Ingarman doki ne a wajajen shekarar 1676, lokacin da wani mai bincike dan qasar italy “Antony Vanleewenhoek” (antoni banli-winhuk) ya qirqiri wani madubi mai maishe da qanqanin abu izuwa babba ta yadda idanuwa zasu sami damar gani gami da yin nazari akansu.
A wancan lokacin ne ya samu damar amfani da madubin wajen leqa kwatamin ruwa dashi a inda yasha mamaki, domin yayi katarin yin arba da miliyoyin halittu masu rai dake ta warkadamin su acikin ruwan cikin qoshin lafiya ba tare da sun tsangwama ko an tsangwame suba. Daga nan nefa, ya rubuta rahoton abin da ya gani, ya aika shi izuwa wata cibiyar masana ta bincike dake birnin landan( a qasar Burtaniya) tun a wancan lokacin, domin gudun sa na boye ilimi, gami da kwadayinsa na karkato da hankalin yan Uwansa masu bin diddigi izuwa bincike akan wadannan qananun halittu.
Ile kuwa, Abinka da masu jiran qiris, sai ba tare da bata lokaci ba gwanayen bincike suka duqufa bada tasu gudunmuwar ta hanyoyi daban-daban. Wasu suka fara qoqarin fahimtar rabe-raben jinsin qananun halittun, wasu suka wanzu binciken yadda halittun suke rayuwa, yadda suke samun abinci gami da yadda haihuwar su take, yayin da wasu masanan suka duqufa bakin rai-bakin fama don ganin an qarawa madubin binciken qarfi don a fadada binciken a kuma sauqaqa shi.
Abin farin ciki shine, a yanzu masana sun sami nasarar fahimtar abubuwa da dama masu dangantaka da qananun halittu. Sunci galabar fahimtar yadda halittun ke haifar da rashin sukuni ga dan Adam dama sauran halittu masu rai. Sun kuma samu damar fahimtar hanyoyin kariya daga garesu, a inda a yanzu haka, maganar sinadarai da magunguna wadanda ake amfani dasu don maganta matsalar wasu daga qananun halittun suka zamo kamar Janfa a Jos.
Don haka, a iya rubutun da zai wakana a wannan fannin ilimin, insha Allahu zai maida hankaline akan wadancan gida-gidan dama wasu qari na daban, ta yadda a qarshe, zamu qara samun Imani a cikin hukuncin sa Allah Ta’ala, gami da sallama dukkan lamura a gareshi.
ASALIN RAYUWA
Kamar yadda shimfida ta wakana, sai masana suka fara amfani da wannan ilimi don yin hasashen menene asalin rayuwa!
Abin daya fara kawo wannan tunani shine, na farko dai masana sun fahimci halayen wadannan qananun halittu kamar haka; Halitta kwaya daya mai kimanin girman kwayar zarra ko qasa da haka, na iya rubanyawa har ta zama biyu koma fiye, haka kuma biyu ko sama da biyun na iya curewa su koma daya. Saboda haka, sai tambaya mai rikici ta dabaibaye masanan, cewa ‘tayaya rayuwar mutum ta samu’, domin da yawan masanan kimiyya sun hadu akan cewa asalin mutum daga qaramar halitta ne.
Dama haka halin Ilimi yake, da zarar ka san abinda baka sani ba, sai wata qofa ta bude maka ta wani abin da baka sanshi ba kake kuma da buqatar sani… Zamuci gaba Insha Allah!
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978

No comments:

Post a Comment