. HIKAYAR WANI ATTAJIRI DA BAWAN SARKI
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Wannan hikaya an ciro tane daga Littafin khalila wa
Dimna, wani dadadden kundin labaru masu fadakarwa
wanda Masani Bipdai ya rubuta tun a zamanin mulkin
Annabi Zulqarnaini.
Hikayar ta fara da cewa "A wani gari mai suna
Baudamana, anyi wani attajiri mai kyauta. Babbar
sana'arsa itace fatauci, inda yake siyen kayayyaki daga
garizuwa gari.
Sarkin wannan gari na Baudamana inda attajiri yake
yana sane da ayyukan karimci da wannan attajiri keyi
ga jama'a, don haka ma ya janyo shi a jiki tare da nada
shi matsayin galadima a fadarsa.
Wannan attajiri, ya kasance mai yalwar hannu.
Kyautarsa ta game sarakuna da talakawa. Idan yaso,
ysna iya sanyawa a tara masa talakawa yayi ta raba
musu dukiya, idan kuma yaso, yana iya gayyatar
manyan attajirai da sarakuna walima tare da
gwangwajesu da kyaututtuka.
Rannan bikin 'yarsa ya taso, sai attajiri ya gayyaci
sarkin garin da wasu manyan mutane walima a gidansa
kamar yadda ya saba. Wuri yayi wuri, manyan baki duk
sun zazzauna akan kujerun alfarma da aka tanadar
musu. Sai kwatsam attajiri ya hango wani bawan sarki
akan wata kujera wadda aka tanadarwa manyan
mutane, ya harde yana shan kamshi abinsa. wannan
abu saiya bakanta masa zuciya. Tun daga nesa ya
daka masa tsawa, sannan ya umarci askarawansa suyi
waje dashi.
Akayi taro lafiya aka gama. Ashe bawannan na Sarki
yayi matukar kufula da cin mutumcin da Attajiri yayi
masa, duk da shima yasan yayi kuskure. A ranar da
abin ya faru ma, bai iya bacci ba. Yana ta kulla
Makircin da zaiyi don daukar fansa akan attajiri.
Sai bawan ya fara rayawa a ransa "Idan da zan san
hanyar da zanbi don Sarki ya wulakanta Tajirin nan, da
na dauki fansa ta. To amma tayaya kaskantaccen
mutum iri na zai iya daukar fansa akan mutum mai
daraja irin sa?".
A karshe dai, wata dabara ta fado masa a rai.
Bayan wasu yan kwanaki, wannan bawan ya shiga dakin
Sarki shara da sanyin safiya, a lokacin sarki na kan
gadonsa yana bacci, amma da alamun baccin da sarki
yakeyi ba mai nauyi bane.
Da bawannan ya gane haka, sai kuwa ya fara
maganganu kasa-kasa shi kadai, yana cewa "Duniya da
abin mamaki take, yanzu ace har Attajirin bafatake ya
sami sukunin rungunar matar sarki?..ooo."
Caraf kuwa sai a kunnen sarki. Yayi firgigit ya farka, da
yake mutum neshi mai kishi. Ya kalli bawan nasa
fuskarsa a murtuke yace " da gaske kake? Ka taba
ganin attajiri ya rungumi matata?"
Bawa ya duka gaban sarki, yace "ya shugabana, kwana
biyu bana samun yin bacci, yanzu ma gyangyadi ke
diba ta. Idan kajini na fadi wata magana da bata
gamsar dakai ba, ka yafe ni".
Shikenan, Sarki bai sake cewa bawa uffan ba. Sai dai
tunanika da suka Yawaita zagaya masa a zuciya.
'Wannan bawan nawa bashi da shamaki a gidan nan,
shima wannan attajirin haka, watakila akwai abinda
bawan ya hango yake tsoron fada mini'
Daga nan fa sai sarki ya cika da kishi, ya fara yanke
alakokinsa da attajirin nan. Kana ma, yace da
dakarunsa kada su kara barin attajiri ya shigo masa
gida.
Duk abinda ake Attajiri bai sani ba, wata rana yayi
niyyar zuwa kawowa Sarki wata kyauta bayan ya dawo
daga fataucinsa, da yazo shiga sai masu jiran kofa
sukace sam ba zai shiga ba, suka sanar masa da cewa
sarki ya hana su yin haka gareshi.
Wannan abu yayi matukar girgiza attajiri. Sai ya shiga
kokwanton dalilin da yasa sarki ya dauki wannan
hukunci a gareshi.
Ashe bawan sarkin nan yana bisa bene, kuma duk yana
hangen abinda ke faruwa. Daga can nesa ya daga
murya yana cewa "kai dakaru, wannan Bafatake abin so
ne ga sarki, mutum ne mai daraja, zai iya sanyawa a
daure mutum ko a sakeshi kamar yadda ya sanya aka
koreni a ranar da ake walima a gidansa. Ku kula da
kanku, abinda ya sameni na iya samunku"..
Dajin haka, sai wannan attajiri ya gano bakin zaren. Ya
daga kansa ya kalle shi, sannan yayi murmushi. Bai
kara ce musu uffan ba, ya juya abinsa izuwa gida.
Attajiri yayi tunanin matakin daya kamata ya dauka. Har
wata zuciyar ta shawarceshi da ya haifarwa da sarki
matsala a mulkinsa kasancewar shi mutum ne da kowa
keso a garin, amma sai ya tuna da cewa shi matafiyi
ne, ya zaga duniya, ya san illar rikici, don haka zaman
lafiya ya kamata ya nema ba tashin hankali ba.
Bayan wani lokaci sai ya aika aka kira masa wannan
bawa na sarki. Yayi masa karramawa sosai da
kyaututtuka, sannan ya nemi gafarar sa akan abinda
yayi masa a baya.
Wannan abu ya farantawa bawan sarki rai. Har ma yake
cewa attajiri " Ranka ya dade, na gafarta maka, ka
girmamani, ka kuma nemi afuwa ta. Don haka zanyi
kokarin juyo da hankalin sarki gareka tayadda zaku
cigaba da mu'amala kamar yadda kuka saba"
Abinda akayi kenan, kashe gari da Sassafe bawa ya
shiga dakin sarki shara kamar wadda akayi kwanakin
baya, sai ya hau surutunsa kasa-kasa yana cewa
"a'aha, muna da wawan sarki a garin nan, kalli yadda
yaci kabewa ya zubar a dakinsa. Abar da ake miya
amma ita yake ci.."
Nan ma dai sarki yayi wuf ya juyo gareshi, yace "kai
wanne irin wawa ne, a ina kaga naci kabewa na watsar
a dakin nan?"
Bawa ya fadi gaban sarki yana neman yafiya, ya bada
uzurin rashin bacci ne kesashi yin gyangydi idan yana
aiki kamar yadda ya bayar a baya.
Tun daga nan, sai sarki ya gane karya bawan yake fada
a duk maganganunsa, sai kuma yayi da-na-sanin
hukuncin daya dauka akan Attajiri ba tare da yayi
bincike ba. Nan take yasa akira masa shi don ya nemi
afuwar sa, ya kuma yi masa tanajin kyauta gagaruma.
Karshen hikayar kenan.
Darussa:
*Kada ka raina mutum duk kaskancinsa.
* kada kakai kanka matsayin da ba naka ba.
* kada ka rinka saurin yadda da magana tare da daukar
mataki.
* kada kayi girman kai wajen neman afuwar laifin daka
aikata.z
No comments:
Post a Comment