Thursday, 7 December 2017

HIKAYAR GIMBIYA JINA DA WANI SARKI

HIKAYAR GIMBIYA JINA DA SARKIN DAKE SON SANYATA FARIN CIKI.
    ...Kada kayi kuskuren siyan soyayya...

Daga Sadiq Tukur Gwarzo
      08060869978

   A wani zamani mai tsawo daya gabata, anyi wani shahararren Sarki a kasar China. Wannan sarki yana da duk abinda mutum ke bukatar samu a duniya. Yana da kuɗaɗe cike da baitul Mali, da kasaitacciyar fada, kyawawan dawakai, da sadaukan Fadawa masu kula masa da kasar sa, sannan uwa uba shi abin soyuwa ne ga al'ummarsa.
   Abinda ya rageshi kaɗai shine rashin mata.
    Duk macen da aka nuna masa ya aura sai yace sam batayi masa ba.
   Rannan sarki ya kirawo wasu amintattun bayinsa sadaukai su bakwai, yace suyi sirdi zasu rakashi shiga duniya, yanaso lallai bazai dawo ba sai ya samo matar data kwanta masa a zuciya ya aura.
   Bada jimawa ba kuwa, wannan sarki da jama'ar sa suka shiga duniya suna keta darare.
   Akan hanyarsu, har sun wuce wani birni wanda wata sarauniya ke mulki, barorinta duk mata ne kyawawa, amma Sarkin yace sam babu wadda tayi masa acikinsu, don haka sai suci gaba da tafiya.
   Ana haka har saida suka kure babban tafkin Kasar, wanda ake cewa shine bangon duniya. Don haka sai suka ɓige da bin gefensa ko zasu samu wani gari a kusa.
   Basu wanzu suna tafiya ba kuwa rannan da dare sun yada zango a bakin teku, sai suka jiyo sautu na nufoso daga ruwa. Zura ido da zasuyi sai ga wani jirgin ruwa karami na isowa garesu, aciki kuma yana ɗauke da wata budurwa kwance da alama ruwa ne ya ciwo ta, sautin da sukeji ashe  numfashin tane.
   Hasken farin wata ya haske wurin, sarki ya kyalla ido ya hango mace kyakkwa kwance a cikin jirgi.Koda ganin wannan mata, sai kuwa sarki yasa barorinsa suyi maza su fito da ita daga ruwa, yana mai cewa ya haɗu da abinda yake nema. Don haka suka fito da ita daga jirgi tare da bata abinci da abinsha.
  Bayan ta huce gajiya sarki ya gabatar mata da kansa tare da bijiro mata da maganar zai tafi da ita birninsa don ya aureta.
  Budurwa ta nuna bata amince ba tana mai cewa tayaya zai aureta a matsayinta na bakuwa a gare shi? Amma sarki ya shiga lallaminta yana faɗa mata cewar tunda yake a duniya bai taɓa haɗuwa da macen data kwanta masa arai ba sai ita, sannan yace zai bata duk jindaɗin duniyar nan da takeso, zai sanyata a cikin daula kuma da farin ciki.
   Daga bisani dai budurwa ta amince, ta sunkuyadda kanta cikin girmamawa tace ta amshi bukatarsa. Ta faɗawa sarki cewa sunanta Jina, amma da sharaɗin ba zata faɗawa kowa labarin taba. Sarki saboda tsabar kiɗimewa akan abinda yakeso, yace ya amince.
   A kwana a tashi, sarki da mutanensa suka dawo gida. Aka shirya gagarumin bikin aurensu.
  Sai dai tun kafin su dawo birnin, sarki ya lura da cewa jina bata murmushi, kullum acikin ɓacin rai take.
   Da fari yaso ya nemi dalilin haka, to amma saboda sharaɗin da suka kulla, sai kurum ya yankewa zuciyarsa cewa da alama har yanzu gajiyar ruwa ce bata sake taba, amma idan ta huta sosai a gida zata koma kamar kowa.
   Bayan kwana biyu da aure, sai ran sarki ya fara dugunzuma domin kuwa Amarya Jina bata murmusi, bata dariya kuma. Kullum ranta a haɗe yake murtuk.
  Sau tari sarki na yin ta maza ya tambayeta dalilinta na ɓacin rai, amma sai tace masa kada ya damu, lokacin farin cikin tane bai yiba.
   Sarki yasa aka rinka gayyato masa shashashun duniya gwanayen bada dariya suna zuwa fadarsa gaban gimbiya Jina suna jarraba aiyukan shashanci domin gimbita tayi dariya, amma sam hak'ansa bai cimma ruwa ba.
   Rannan dai sarki yayi wani shiri da baransa akan yadda zai baiwa matarsa Jina dariya.
   Da sassafe kuwa, Jina na taje laya-layan gashin kanta bayan ta tashi bacci, shikuma sarki na kwance yana ɗan taɓa wasanni da wasu kayayyaki, sai ga baran nasa ya shigo a firgice yana mai cewa Ran sarki ya daɗe, kasa ba lafiya, ga dakarun makiya can a kofar gari suna shirin dirkako mana da yaki.
  Sarki ya tashi firgigit, yana ta juye-juye kamar wanda kunama ta harba, yana faɗin ina sadaukan mu suke, ina sarkin kofa, ina sarkin yaki, kai yau mun shiga uku.
   Da yake wannan abu duk akan idon Jina akayishi, sai kurum sukaji ta kyalkyale da dariya. Tayi sauri ta rufe bakinta da tafin hannunta. Ganin haka sarki yayi tsalle ya kama hannun baran nasa da musabaha yana jinjinawa, yana mai faɗin shirinmu yayi kyau matuka nagode.
Daga nan ya bashi gagarumar kyauta, sannan ya sanar da Jina gaskiyar lamari. Jina ta kara yin murmushin farin ciki, sannan suka cigaba da rayuwarsu a haka.
   Anyi haka da kwanaki kaɗan, sai Gimbiya Jina ta kara komawa gidan jiya, fushinta na neman fin na baya ma. Ran sarki fa duk ya ɓaci, ya rasa meke masa daɗi.
  Sarki ya shiga binciken wakoki da labaru ko zai sanu mafita. Shidai a tunaninsa wani abune mummuna ya auku a rayuwar Jina wanda yasa a kullum take tunashi har yake hanata walwala. Amma kuma yayi iya kokarinsa taki sanar dashi ko menene.
   Wata rana da safe sarki na ɗakinsa, sai yaji wata gagarumar kara, babu jimawa saiga wannan baran nasa ya banko kofar ɗakin ya shigo da gudu yana haki.
  Baran ya russuna gaban sarki yana faɗin ya shugabana, gari fa babu lafiya ga makiya sun dirkako mana da yaki.
  Sarki yayi murmushi, tsammaninsa wasa baran yakeyi, yace Ya kai barana, kai mutum ne nagartacce, amma kasani, a wannan lokaci, shirin mu bazai cimma nasara ba.
   Baran nan ya tashi haikan yana mai sanar da sarki cewa bafa da wasa yakeyi ba, da gaske ne makiya sun shigo musu da yaki.
  Sarki ya tashi da marmaza yana faɗin to ina sadaukaina, ina su wane da wane... Sai dai lokaci ya kure, shagaltuwarsa ga kokarin sanya Jina cikin farin ciki ya kawar masa da hankali akan mulkinsa da yakeyi wanda ya kamata ace yayi masa riko mai karfi, har makiya suka yi shiri suka shigo masa ba tare daya sani ba.
   Ahaka har saida dakarun makiya suka shigo cikin ɗakinsa suka hallaka shi, sannan shugaban tawagar ya mallake fadar tasa da kuma matar da yake burin farantawa rai...
Ance Jina da wannan sabon sarki sun rayu cikin farin ciki. Ashe daman shine bataso.... Koma dai yayane, yakamata duk mai neman Aure, ya nemi zaɓin Allah ba zaɓin zuciyar saba.
 
   

No comments:

Post a Comment