Saturday, 9 December 2017

YADDA WANI FASIHI YA TABBATAR DA WANZUWAR ALLAH


LABARIN YADDA WANI FASIHI YA TABBATAR DA WANZUWAR ALLAH.
Tare da SADIQ TUKUR GWARZO
08060869978
A wani lokaci, an taba yin wani sarki gawurtacce kuma shararre, yana mulkin wana alqarya babba. Sarkin ya kasance mai nazari da wayo, haka ma al'ummar garin nashi suke. Babbar matsalar Sarkin tare da yawa-yawan al'ummar garin itace basu amince akwai Allah ba, 'yan qalilan ne daga ciki sukayi imanin cewa Allah wanzajje ne.
Watarana, sai wannan shirya taron gangami wanda za'ayi 'yarqure tsakanin wadanda sukace akwai Allah da wadanda sukace sam-sam babu shi. Aka nada wani matashi domin ya wakilci tsirarun masu imani da wanzuwar Allah.
Da ranar tazo, mutanen gari suka hallara amma matashin nan bai qaraso ba. Mutane suka jira-suka jira amma matashi bai zo ba. Sai jama'ar gari suka fara sowa da habaici, suna cewa tsoro yaji shiyasa yaqi izuwa, idan banda rainin hankali tayaya ma za'ace akwai wani wanda ya halicci sama da qasa da duk abinda ke cikinta? Ai kawai yanayi ne ya haifar dasu gaba daya. Don haka rashin zuwansa na nuni da cewar ya fadi, mune mukayi nasara kenan.
Ana daf da watsewa kenan, sai aka hango shi ya nufo wajen taro. Tun kafin qarasowarsa kuwa mutane ke hargowa, suna cewa "me yasa ka makara? Ka fadi "
Shidai bai tanka musu ba, har sai da Sarki ya umarce shi yayi bayanin dalilin dayasa ya makara, tun kafin a ladabtar dashi.
Sai wannan matashi ya fara da cewa " Ya mai martaba, haqiqa na fito gida da wuri domin na samu halartar wannan taro, sai dai lokacin da nazo tsallake tekun dake tsakanin qauyen mu da wannan gari, sai ya kasance babu jirgin ruwa dazai tsallakar dani"
Mutane dai sukayi shiru suna sa.
Yaci gaba da cewa " a haka naci gaba da jira, har izuwa lokacin da wasu falankai na katako suka fara fitowa daka cikin ruwan izuwa saman sa"
Yana zuwa iyanan mutane suka fara qarya tashi. Kowa na kalamai kala-kala masu nuni da abin bazai yiwu ba "Qarya kakeyi, wannan abu bazai yiwu ba, tunani bazai dauki wannan ba.. " Da sauran makamantan irin su.
Sarki dai ya tsawatar musu, sannan aka bashi damar cigaba da bayaninsa. Yace " ya mai martaba, falanki-bayan falanki haka suka rinqa firfitowa, sannan suka daddatsa kawunan su, suka jeru da kansu, sannan suka mannu da junansu da qusoshi, suka bada siffatr jirgin ruwa. Nikuma ganin haka yasa nahau jirgin ya tsallakar dani. Ya mai martaba, rashin wannan jirgi tun da farko shine yasa na makara"
Da rufe bakinsa fa sai mutane suka fara surutai. Masu tsaki nayi, masu dariya nayi. Wasu ma sun dauke a sayin shaha, domin kuwa babu wanda a ainta da labarin nasa.
Daga nan sai qara daga muryar sa izuwa garesu yana cewa "yaku taron jama'a, na fuskanci cewar baku gamsu da labari na ba, don haka inaso kuyi hukunci da gaskiya, ku kalli rana da wata da taurari, dukkan su a shirye suke, shiryuwa wadda take qasaitacciya, tayaya zaku bijirewa wanzuwar Allah wanda ya halittasu kuma ya shiryasu kuce babu wanda ya shiryasu hakanan suka shiryu da kansu???"
Nan take guri yayi shiru, babu mai cewa uffan. Kowannen su ya gane wautarsa wajen kafirta da cewa akwai Allah. Don haka, wannan matashi yayi nasara akansu.
Nan gaba insha Allahu zakuji manyan dalilai guda goma daga bakin wadanda ma ba musulmi ba wadanda ke tabbatar da wanzuwar Allah.
Allah bamu dacewa amin.

No comments:

Post a Comment