NI DA MATATA- LABARI MAI SOSA ZUCIYA
Tare da SADIQ TUKUR GWARZO
Wannan labari yana da sosa zuciya tare da darussa ga dukkan ma'aurata, har ma da masu niyyar yin auren.
Isma'il ya fara bamu labarin sa kamar haka "Rannan na koma gida da dare, matata ta kawo min abincin data girka min, ko kallan abincin banyi ba. Na kalle ta raina a bace, nace ina son zamuyi wata maganaa".
Haqiqa na fuskanci kaduwa da bacin rai a tattare da ita, sai dai hakan bazai sa na zartar da hukuncin dana yankewa raina ba. Shekaru goma kenan da auren mu, amma bana tunanin nayi shekara daya dindi a cikin walwala. Aure yazo mini da wani irin abu, na rasa farin ciki a gida na, matata bata burgeni ko kadan.. Rabuwa da ita kurum shine maslaha.
"Samira, na sakeki Saki daya". Na fada mata alokacin da take cikin zaquwar jin maganar da zan fada mata. Cikin nutsuwa gami da kwararowar hawaye daga idanunta tace "Laifin me nayi maka haka yaya na?" Daman sunan da take fada mini kenan. A haqiqa, bani da wata takamaimiyar amsar dazan bata, don haka na mantar da tambayar tata, abinda ya qara baqanta mata rai kuma kenan har ta fusata, cikin kuka da daga murya, ta fara fadamin lafuza kamar haka "wallahi ka bani mamaki, baka cika mutum ba yayana, yanzu sakayyar da zakayi mini kenan? Shekaru goma muna tare dakai, tun baka da komai, duk wahalhalun danasha akanka, na saida farin cikina don na faran ta maka, amma sakayyar da zakayi mini kenan..."
Maganganun nata naji sun ishe ni, domin bani da buqatar sauraron su. Saboda a gaskiya sam-sam bana son samira a yanzu, ba kuma ta burgeni, duk wata soyayya data wanzu a tsakanin mu ta dusashe, ban san dalili ba.. Jamila kawai nakeso, ita kuma zan aura. Na raya wannan a zuciya ta.
Na daga ido na kalleta, tausayi ya kamani, ba kuma don ina son ta ba, kawai dai banson naganta acikin mawuyacin hali ko kadan. Don haka, ban tsaya sauraren kalmominta ba na shiga daki na rubuta mata takardar saki, sannan nayi mata albishirin cewa na mallaka mata gida, da kuma motar da nake hawa. Sannan zan rinqa bata tallafin kudi a duk sanda take buqata.
Hmmmmm. Mata kenan, a tsammani na wannan zai faranta mata rai, amma wataqila tunda ta san cewa inada Sabon gida da sabbin motoci gami da dukiya, idan nayi haka bazan damu ba, sai naga kurum ta yayyaga takardar bayan ta karanta, ta rushe da kuka.. Nidai a zuciya ta cewa nake sai dai kiyi hakuri, bakin alqalami ya bushe, bakya faranta mini rai, don haka bazan iya cigaba da zama dake ba, ba kuka ba, komai zakiyi kin jima baki soma ba.
Da sassafe ban biye ta tata ba, tunda a tsammani na na sallameta zata hada yanata-yanata ne ta bar min gida, na fita aiki cikin farin ciki, domin ina zaquwar farin cikin da masoyiyata Jamila zatayi idan taji labarin na saki Samira. Ban kuma dawo gida ba sai da dare, yayin da na sami Samira, tsohuwar matata a falo tana ta rubutu a takarda. Ko sallama banyi mata ba saboda bacin rai, na shige daki na nakwanta bacci.
Cikin dare na qara farkawa, na leqo falon dan naga halin da gidana yake ciki. Nan ma ga mamaki na, sai naganta a zaune tana ta rubutu. Naja dogon tsaki, sannan na koma daki, naci gaba da bacci na.
Da safe bayan na tashi, nayi shirin ofis, na fito zan fita, sai tayi sauri tasha gabana. Ta miqo mini wata takarda data rubuta. Kamar dai bazan karanta ba, amma sai wata zuciyar ta shawarceni da lalle na karanta. Sai kuwa na fara karantawa kamar haka "Yayana, kamar yadda kace ka sakeni, ina farin cikin shaida maka cewa bana son duk wata kyauta daga gareka, amma ina neman alfarmar ka qara mini wata daya kafin nabar gidan ka. Ka sani munyi shekaru muna gina rayuwar danmu, a yanzu kuma yafi buqatar taimakon mu, kuma bacin ranmu zai iya ruguza rayuwar sa, saboda yana fuskantar Jarabawa a makarantar su, da kuma Gasar alqur'ani a islamiyyar su, kuma nike koyar dashi a gida kamar yadda ka sani.
Kuma don girman Allah, ina neman alfarmar a kullum ka dawo gida, ka rinqa bani lokaci koda minti goma ne kana zama a inda nake koda kuwa ba zaka ce komi ba, kamar yadda mukayi rayuwar mu ta amarya da ango.. Nagode!"
Nayi shiru ina tunani bayan na gama karanta wasiqar tata. Sannan na gyada kaina sama, alamar na amince, daga nan kurum na fice daga gida. Daga baya nake labartawa Jamila alfarmar da Samira ta nema daga wuri na, shine tayi tsaki, har ta kira ta da suna 'Mayya'.
Tun daga wannan rana, nidai ban sanar wa da kowa na saki matata ba, itama bana tunanin ta sanarwa da wani haka. Mun cigaba da rayuwar da muka saba ne cikin rashin magana. Allah-Allah nake wata ya cika, mu rabu da ita. Idan dare yayi, nakanyi qoqari na dawo gida da wuri, na zauna a falo ina kallo, ita kuma sai tazo ta zauna kusa dani. Wani lokacin a gaba na take koyar da danmu Yasir karatu na boko dana islamiyya. Har takan tambaye ni wani abu idan bata sani ba, nikuma maganin kada danmu ya fahimci akwai matsala tsakani na da mahaifiyarsa, sai kaga nayi murmushin qarya, Idan nasan amsar na fada musu, idan kuma ban sani ba sai nayi browsing dinta na fada.
Abu kamar wasa, sai wani yanayi ya fara zuwa. Tun bana shiga tattaunawar dasukeyi, har ya zamo dani akeyi tsulundum, saboda a gaskiya ni mutum ne mai son tattauna maganar ilimi, wannan kuma sai ya qara jefa soyayya da fahimta tsakanina da dana Yasir. Sai kuma ya kasance, firar duniya na shiga tsakani na da samira, har mu na shafe dare muna fira musha dariya sosai.
Ita kanta fa ta canza. A kullum cikin tsafta take, ga ado da take cabawa adai-dai lokacin da tasan zamu hadu, akwaita da fesa turare mai dadi, irin wanda nakeso. Tun ina satar kallon ta, har ya zamo bana kunyar na qura mata ido, ita kuma sai naga kamar bata san inayi ba.. Akwai lokacin danaso na kusance ta ma, amma taqi yarda saboda acewar ta musulunci bai halatta haka ba har sai idan na dawo da ita a matsayin mata.
Wannan abu ya sani tunani, na fara hango kyawun matata da kuma darajar ta, har ina tunanin sauya shawarar dana dauka ta saki da kuma auren Jamila. Saboda a zahiri, a yanzu farin cikina ya fara dawowa, kullum fa cikin zaquwa nake na dawo ga samira.. Ta zamo mini aminiya, da ita nake shawarta muhimman matsaloli na, kuma sai yanzu nake qara fuskantar ladabin ta, ilimin ta da kuma hazaqar ta!
Wata rana kafin wa'adin mu ya cika, na fito zan fita ofis, sai banga Samira a falo ba kamar yadda ta saba, zakaga taci kwalliya, data ganni na fito zatayi murmushi sannan tayi min adawo lafiya. Wallahi tun banaso, har abin ya shiga zuciya ta, don haka yau da ban ganta ba, sai nake tunanin akwai matsala, don haka na yanke shawarar leqawa dakinta don ganin abinda ke faruwa.
Da leqawa sai na ganta tsaye a jikin dressing mirror, doguwar rigace a jikin ta ta bacci, kuma kwalliya takeyi, amma da alama ta rasa kayan da zata sa ne. Nayi ajiyar zuciya gami da gyaran murya, a lokacin ne kuma ta fahimci isowa ta. Tayi saurin dauko zani gami da lulluba jikinta, sannan tace "Yaya na ya zaka shigo min ba tare daka qwanqwasa kofa ba". Ni kuma zura mata ido nayi ina kallon ta. Tabbas ta rame, amma kuma ta qara kyau. Da alamun damuwa ce ta ramar da ita. Na qura mata kallo, nace gani nayi ban ganki ba kamar yadda na saba, tsammani na ba lafiya. Tace "wlh tun dazu na rasa kayan dazan sa, saboda duk sunyi mini yawa.."
"Naga duk kin rame, meke damunki ne?" Na fada. Tayi ajiyar zuciya, gami da kawar da kanta daga kallo na, tace "kafi kowa sani" nace "indai nine matsalar to kiyi hakuri, daga yau na dawo dake a matsayin matata, daman babu wanda yasan abinda ke tsakanin mu, kuma yanzu kishirya mu tafi store ki zabi kayan sawa masu kyau.
Abinda akayi kenan, mun fita izuwa store, acan kuma mukayi kicibus da Jamila wadda nake shirin aura. Tazo wajena wai tana son magana dani, Samira tace ita sam bata yarda ba, nikuma nace to gaskiya tunda matata bata bani izini ba, bazan iya kebewa da ita ba. Wannan abu saiya hargitsa jamila, ta cakumi Samira a gaban jama'a, Samira tayi sauri ta fincike ta gefe. Na kalli Jamila nace "ya kamata ki shiga hankalinki, wannan matata ce wadda shekaru goma muna tare, da dadi ba dadi bata rabu dani ba, don haka bazan wulaqanta ta akanki ba, aurenki kuma na fasa" Daga nan naja Samira mukayi tafiyar mu.
A yanzu dai na fahimci inda matsala take ga aurenmu, kullum cikin fafutikar nema nake, bana samun lokacin zama da iyali na. Babu abinda ke shiga tsakanin mu sai gaisuwa, sai kuma maganar abinci, sai dai ko idan zata fada mini suna, ko biki, abinda akasari ma ba zuwa nakeyi ba. Don haka naci damarar gyara wadannan halaye domin dawo da tsohon farin cikin daya wanzu tsakanin mu tun muna ango da amarya.
Babban tashin hankalin da bana mantawa shine ranar da nayo siyayya gagaruma domin burge samira. Na siyo su ice cream, abinda nasan tana matuqar so, da kayan ciye-ciye kala-kala, amma ina zuwa na tarar da ita matacciya..
Ashe ta jima da kamuwa da ciwon daji (cancer), ga bacin rai kuma da take fama dashi, ni inacan hankali na ya tafi ga jamila ban san halin da take ciki ba, ita kuma ta kasa sanar dani saboda halin ko-in-kulan da nake bata, har sai da cutar tayi zurfi ajikin ta. Ashe ita aranta tana jin cewa ta kusa mutuwa, shiyasa tayi qoqarin rufe bacin ran dake ranta da kuma cusa soyayya tsakanina da dana yasir. Nima nasan, idan da Yasir ya fahimci zaluncina ga mahaifiyarsa, da qima ta zata zube a idonsa kuma har abada bazai mance ba.. Don haka mutuwar samira ta sanya ni cikin kuncin rayuwa, wayyo Allah, har ma na rasa meke mini dadi.
A yanzu da nake baku labari na fahimci cewa nayi kuskure gagarumi wajen bigewa da neman duniya tare da mancewa da farin cikin iyali na... Haqiqa wannan hatsari ne babba daya kamata magidanta su kiyaye.. Ina roqon Allah yajiqan samira, kuma a kullum cikin addua nake mata, tsammani na hakan zai goge laifin danayi mata.
No comments:
Post a Comment