(1)SIRRIN TASIRIN IYAYE AKAN BUN{ASUWAR ‘YA’YANSU
Gaskiya ne
maganar da ake fa]a cewa Nagartattun iyaye ke haihuwar nagartaccen ]a, koda
yake dai, mahaliccin mu Allah babu yadda bai iyaba, yakan samar da nagartaccen
]a daga iyaye lalatattu, kamar yadda yake samar da ]a lalatacce daga
nagartattun iyaye.
A wani
bincike da aka ta~a gudanarwa, ya nuna cewa kaf cikin hamsha}an attajirai da
sunansu ke ruri ko ina a sassan duniya, kashi biyu bisa uku basu mallaki komi
na daga dukiya daga iyayen su ba, kawai dai sun sami tarbiyya ne da koyarwa
nagartatta tun a gida, daga nan suka shiga gwagwarmayar tara dukiya, har kuwa
sukaci nasara.
Kashi ashirin
da ]aya a cikin ]ari kuma na attajiran, an samu cewa sun ]an samu wasu kuda]e
ne ta hanyar gado, ko wani taimako daga dangi, sannan suka ririta dukiyar har
daga bisani ta ha~aka.
Binciken yaci
gaba da cewa kashi goma sha uku bisa ]ari ne kacal na attajiran duniya aka samu
cewa gado ko kuma ace dukiyar mahaifansu ce asalin dukiyarsu.
Wannan ke
fito da wautar wasu iyaye masu aiki tu}uru wajen wawusu haramiya don a tarawa
iyali, a mafi akasari irin wannan dukiyar ba inda take zuwa, annoba ma takan
zamewa iyalin.
Abinda yaro
yafi bu}ata ba komai bane sai ilimi a aikace daga magabatansa gami da }warin
guiwa matu}ar yana yin abinda ya dace, wannan shi ne tarbiyya ta gari.
Fitaccen
attajiri na Afirka Alhaji Aliko [angote da bakinsa ya ta~a fa]a cewa “Bana
mantawa, ina firamare na kan siyo katan-katan na alawowi nazo na siyar ga
al’umma. Tun a lokacin ina sha’awar kasuwanci”.
Abin farin
ciki shine, iyayen sa basu kashe masa guiwa a fagen da yake sha’awa ba
ballantana su canza masa al}ibla kamar yadda wasu iyayen keyi, suce “Likita,
Injiniya, ko lauya ya kamata ka zamo”. Idan da sunyi haka wata}ila da yanzu bai
kai matsayin da yake ba.
Shima
matashin attajiri Mark Zuckerberg wanda ya }ir}iro shafin sadarwa mai sadar da
zumunta na yanar gizo mai suna “Facebook” har kuma a shekara ta 2010 jaridar
‘Forbes” ta lissafashi a sahun attajirai na 100 a fa]in duniya, an samu cewa
mahaifinsa ne ya fara koyar dashi yadda ake sarrafa na’ura mai }wa}walwa
(Computer).
Daga baya ne
mahaifinsa yayo hayar wani masanin masarrafa na’ura mai }wa}walwa, mai suna
‘David Newman’ ya rin}a koyar da Mark darasi a gida. Wannan fa duk ya faru ne a
sabili da mahaifin Mark ya lura da cewa ]ansa yafi sha’awar aiki da Na’ura mai
}wa}walwa fiye da komai a rayuwarsa.
Ance daga
abin da Mark ya fara yiwa mahaifinsa sakayya da shi ta alheri shine ya }ir}iro
wani masarrafi na kwamfuta wanda yake bada damar aikawa da sa}wanni na
karta-kwana tsakanin kwamfutocin gidan da Mark yake, da wasu kwamfutoci dake
ofishin aikin ha}ori inda mahaifin Mark ]in ke aiki kenan, sannan masarrafin
‘Zucknet’ daga bisani kuma gashi ya }ir}iro babban lamari “Facebook” abinda
sama da mutane biliyan ]aya ke amfani dashi a duk duniya.
Shima Patrice
Motsepe attajiri na (10) a fa]in Africa inji jaridar Forbes ]an kasar South
Africa ya koyi dabarun kasuwancin sane daga mahaifinsa tun yana yaro, saboda
jiran shagon mahaifinsa da yakeyi. Ance anan ya rin}a samun ilimi akan ha}o
ma’adinai daga abokan huddarsa da kuma ilimi akan kasuwanci, saboda haka daya
girma bai sha wata wahala ba, hikimomi ne kurum suka rin}a zuwar masa. Wahalar
da za’a iya cewa ya sha itace ta aiwatar da tunanikan da suka cika masa
}wa}walwa.
A gaskiya, ba
zamu iya ha]a kanmu da wasu }abilun duniya misalin turawa wajen baiwa yaranmu
tarbiyya gami da goyon baya ba.
Marubuci, marigayi
Abubakar Imam (Allah ya ji}ansa) ya tabbatar da haka acikin littafinsa mai suna
“TAFIYA MADUBIN ILIMI” wanda ya rubuta a 1943, a sa’ar da ake tsaka da ya}in
duniya na biyu, ya kuma bada labarin tafiyarsa zuwa Ingila a lokacin.
Ya fa]a a
wani waje lokacin da yakai ziyara filin renon yara na Hyde Park dake birnin
landan, yake cewa:
“Ina zaune
sai wani yaro ya dubeni yace “wannan ba}in mutum ne ko?”.
Sai mai renon
ta dukar da kanta kasa tace “Eh, ba}in mutum ne masoyinka”.
Wani yaron
kuma yace “wannan motar tawa ce ko?” sai mai renon sa tace “kai baka da mota
sai jirgin ruwa gashi”.
Yace “A ranar
nan na fara ganewa lallai irin hanyarmu ta reno ba dai-dai take da ta turawa
ba”.
Haka ma, wani
labari da jaridar New York Times ta ta ~a
bugawa mai taken “Babu kamar iyaye” ya ishemu abin koyi ga yadda ya kamata
iyaye su rin}a cusa ilimi ga }ananan yara ta yadda idan sun girma zasu zamo
masu taka-tsan-tsan gami da sanin abin da ya kamata.
Akace “wani
yaro ne ya tafi ga mahaifiyarsa a wani yammaci tana ]akin girki tana
aikace-aikace sai ya mi}a mata wata takarda don ta karanta.
Bayan ta goge hannunta da tsumma saboda laima,
sai ta bu]e takardar ta fara karantawa, ga abin da aka rubuta:
-
Ku]in sare ciyayin da nayi miki = Dala 5
-
Ku]in goge ]akina da nayi a satinnan =
Dala 1
-
Kin aikeni nayo miki siyayya akasuwa
ku]insa = Rabin Dala
-
Ku]in zubar da shara da nayi = Dala
1
-
Kinata }arfafa mini guiwa nayi karatu, da jarrabawa tazo nayi kokari, gashi
har sakamako yayi kyau. Ku]in hakan = Dala 5
-
Kaf satinnan ni nake share tsakar gidannan. Ku]in hakan = Dala biyu
Lissafin ku]a]en dana biyo ki nake son ki biyani = Dala 15
Da mahaifiyar
yaron ta gama karantawa, sai tayi nazari ka]an, daga nan kuma sai annushuwa ta
lullu~e ta, tayi murmushi sannan ta kar~i biron dake hannun ]an nata, ta juya
takardar da ya kawo mata, ta fara nata rubutun.
Ga abin da ta
rubuta masa:
-
Na ]auki cikinka tsawon watanni tara =
Banason ko sisinka.
-
Na shafe tsawon darare ba bacci ina rainon ka, kanamin kuka, ina maka
addu’a = Ban chaje ka komi ba.
-
Kayi silar zubar hawaye na saboda }aunar da kasha bani = Nan ma ban nemi
komi a wajen ka ba.
-
Bayan na haifeka, na cigaba da ]aukar ]awainiyar ka da ku]i, tufafi, abinci
da duk abinda kake bu}ata = Ban nemi ka biyani ba.
-
[ana, idan duk ka lissafa ]awainiyata a gareka da soyayyar da nake maka,
farashinta ba zai misaltu ba, amma ban ta~a neman komi a wajenka ba.
Me yasa zaka nemi ladan aiyukan da kusan kanka ka taimakawa ba wani ba?
Daga nan ta
mi}a masa takardar.
Ance kafin ya
kammala karanta takardar hawaye suka fara zuba daga idanunsa ya fahimci wautar
sa kenan a aikace, wannan fa shine masu salon magana ke cewa “Ta inda aka hau,
ta nan ake sauka”.
A }arshe ga
kalamin da yaron yayiwa mahaifiyar tasa “Na rantse, ina matu}ar }aunarki
mahaifiyata”.
Sannan ya
kar~i takardar ya juyata a }asan rubutun sa ya rubuta “An biya ku]i, lakadan ba
ajalan ba, babu sauran bashi har abada”.
Zamu }ara
samun wadatuwar tasirin tarbiya wajen bun}asuwar manyan mutane idan mukayi duba
da tarihin “Henry Ford ‘da’ Howard Hughes”.
Shi dai
‘Henry Ford’ shine ya kafa kamfanin kera motoci na ‘Ford’. Da bakinsa ya ta~a
fa]in cewa “Mahaifina ya siya mini agogo tun ina }arami. Lokacin da na isa
shekaru (15) sai nayi wa]a-wa]a da agogon, sannan na }ara ha]ashi. Daga nan na
shiga gyaran agogunan abokaina da sauran ma}ota”.
A lokacin da
Henry ya riski shekaru 23 a duniya mahaifiyar sa ta rasu. Da bakinsa ya bayyana
irin gigicewar sa da wannan babban rashi sabili da goyon bayan da take bashi.
Shine kuma
bayan lafawar ba}in cikin nasa, mahaifinsa yayi masa tayin cigaba da bada
kulawa ga wata gonar su, aikin da mahaifiyarsa ke yi kenan kafin rasuwarta,
amma sai ya kasa yin wannan aikin.
Daga baya ne
ya rubutawa mahaifin nasa wasi}a yana mai cewa “ Ya Babana, ban ta~a jin son
gona a zuciyata ba. Daman mahaifiyata dake gonar nake so, yanzu kuwa }ere-}ere
ke bani sha’awa”.
Abinda da
akayi ke nan, sai mahaifin nasa ya ci gaba da bashi tallafi na ku]i har ya
kammala karatunsa a kwalejin koyon kasuwanci dake Detroit, daga baya kuma shine
wanda kamfaninsa mai suna ‘Ford’ ya }ir}iro motar nan da akayi yayi samfurin ‘Model
T’ wadda yawa yawan matsakaitan mutanen }asar Amurka suka rin}a amfani da ita,
wannan ne kuma asalin shaharar sa a duniya gami da zamowar sa hamsha}in
Attajiri a wancan lokacin.
Shi kuwa
Horward Hughes, tun yana ]an Shekara (19) hotonsa ya bayyana a jaridun Birnin
‘Texas’ na }asar Amurka, amatsayin yaro attajiri wanda kuma ya mallaki keke mai
inji sabon fitowa a wancan zamani.
Ya samu
]aukaka ne saboda bajintarsa ta }ir}irar wata na’ura da ake amfani da ita a
Rediyo mai suna ‘Transmitter’. Asalin hakan kuwa kamar yadda aka rawaito shine
kwaikwaya yayi daga kamfanin `Hughes Tool Company` , mallakin babansa kenan,
inda kuma yake aikin fisha a wajen.
Daga nan ne
mahaifinsa ya lura da cewa ]ansa yana da basira, kuma yana da sha’awar lissafi,
sarrafa jirgin sama da }ere-}ere, sai kuwa ya sakar masa bakin aljihu don yayi
karatu. Ance a shekarar 1920, Horward yana da shekaru 14, ya fara ]aukar
darasin tu}a jirgin sama. Da ya girma kuma, ya samu damar zamowa ]aya daga
cikin attajiran duniya.
Dama dai zamowa
attajiri ko wani shahararren mutum a duniya wani lamari ne da yake faruwa tun a
wajen tarbiyya, abinda ke faruwa shine: Na farko, akwai su kansu iyayen,
aiyukan da suke yi na alheri yakan shafi ‘ya’yayensu ta inda darajoji zasu
rin}a zuwar musu ta ko wanne fanni.
Tarihin
dattijo Alhaji Isyaka Rabiu, ya nuna haka, mahaifinsa ya kasance malamin
al}ur’ani wanda kuma yake koyar da ]alibai ba don komi ba sai don neman yardar
Allah.
A yau Allah
yayiwa zuri’ar sa baiwar nasara a kasuwanci (Kamfanin BUA da IRS ya isa misali)
gami da ilimin al}ur’anin ma baki ]aya, jaridar ‘Forbes’ dai ta bayyana
Abdussamad Isyaka Rabi’u amatsayin Attajiri na (5) a fa]in Najeriya.
Abu na biyu
shine jajircewa akan yaran don suyi abinda ya dace; Iyaye da yawa suna
gwammacewa su nuna tsagwaron soyayya ga ‘ya’yayensu har ma su rin}a nuna fifikon
yaransu akan saura. Ha}i}a wannan gurguwar dabara ce mai lalata yara.
Tarihi game
da haka yazo a cikin rayuwar babban attajirin Afirka ta yamma marigayi Alh.
Alhassan [antata. Ance lokacin da ya ziyarci mahaifiyarsa dake can Ghana tana
kasuwanci, yayi tunanin wahalar sa ta yanke, arzikinsa ya wanzu kenan. Amma sai
abin ya canza domin bai jima tare da ita ba ta turashi karatun allo a hannun
wani malami, acan ya rin}a koyon karatun al}ur’ani da sauran ilimai yana kuma
yin bara don samun abinda zaici da wanda zai kaiwa malaminsa. Da ya samu damar
yin karatun, daga baya ya shiga kasuwanci don haka bai sha wahalar samun ]aukaka
ba, dalili kuwa yana da ladabi ya kuma samu ilimi.
Tarbiyya anan
na nufin iyaye su tsaya tsayin daka don ganin ‘ya’yaye sunyi abinda ya dace a lokacin da ya dace.
Su sami ilimi
na addini dana zamani, sannan su zamo masu ladabi.
Abinda Shugaban
}asar Amurka na (16) Abraham Lincoln yayi }o}arin samarwa da ]ansa ‘Tad’ kenan lokacin
daya soma girma. Don haka sai ya turashi wata makaranta nesa da inda yake
rayuwa, harma ya rubuta wata wasi}a doguwa zuwa ga Malamin da zai koyar da ]an
nasa. Ga abin da yake cewa a wasi}ar:
Zuwa ga
maigirma malamin ]ana.
..Ka sanar
dashi cewa a kowanne ma}iyi akwai aboki. Ka nuna masa yayi aiki tu}uru don ya
samu dala ]aya shi yafi amfani da daraja a gareshi akan ya tsinci dala biyar,
ka kawar dashi daga hassada.
A makaranta
kuwa, ka sanar dashi cewa fa]uwar jarabawa yafi }asaita a fagen daraja fiye da
satar jarrabawa ka koya masa yadda zai saurari kowa daga mutane da yadda zai
tantance magana }wa}}wara guda ]aya wadda zaiyi aiki da ita.
Ka sanar
dashi yadda zaiyi dariya a halin ~acin rai, ka fahimtar dashi cewa babu wani
abin jin kunya a cikin zubda hawaye. Ka koyar dashi yadda zai tsaya kyam yayi
ya}i indai akan gaskiyar sane, ka kuma sanar dashi yadda zaiyi imani ga
mahalicci da yadda zai gaskata kansa”.
Abu na uku
shine yadda iyaye suke godewa mahalicci bisa baiwar ‘ya’yan daya basu gami da
baiwar daya baiwa ‘ya’yan.
Labarai nanan
dangane da wa]anda suke rayuwa har su koma ga Allah ba tare da sun samu haihuwa
ba, kenan ya kamata iyaye suyi matu}ar godiya bisa baiwar haihuwar da aka basu,
idan sukayi hakan, Allah cikin karamcinsa sai ya }ara baiwarsa ga iyayen da
kuma ‘ya’yan baki ]aya.
Baya da haka
sai baiwar da yara ke dashi, kowanne yaro ha}i}a yana zuwa da wani }wazo duniya
wanda ya kamata iyaye suyi nazari har su fahimci wannan haza}a.
Ba lallai ne
yaro sai ya zama mai haza}a a makaranta ba za’ace yana da }wazo ba, wasu suna
da tunane-tunane wa]anda idan aka taimakesu, suka bun}asa tunanikan zasu samu
damar kawo sauyi a duniya baki ]aya.
Attajiri
‘Bill Gate’ na ]aya daga cikin wa]annan yara kamar yadda ya ta~a fa]a da
bakinsa cewa “A lokacin da nake makaranta, mu ake yiwa dariyar marasa }o}arin
aji, masu }o}arin kuma ana }arfafa musu guiwar su }ara }o}artawa ta yadda a
gaba zasu zama injiniyoyi, likitoci da sauransu. A yau gashi na kafa kamfanin
‘microsoft’ wanda ya samarwa da wa]ancan }wararrun injiniyoyin aiki”.
Shima
marubuci ‘Robert Kiyosaki T.” Yayi fashin ba}i a irin haka a cikin littafinsa
“Why a student work for ‘C’ student”, a wani wajen ma ga abinda yake cewa “Bamu
da matsalar bun}asuwar arzi}i, sai dai muna da matsalar tsarin ilimi. Babbar
matsalarsa kuwa shine ya tafi kachokan ne don samar da }wararru kuma gogaggun
ma’aikata (ko ace masu neman aiki) alhali kuwa abinda muka rasa shine masu
}ir}iro aiyukan”.
Ha}i}a
basirar wani a aji wajen warware matsalar “ X + Y =Z ta sha bamban da basirar
fuskantar matsalolin rayuwa. Shi fa amfanin ilimi ba komai bane sai don ya bada
hanyoyin ku~uta daga matsaloli gami da samar da sauyi, littatafai da dama sunyi
dogon sharhi akan tarbiyar yara, misalinsu shine “How Children Learn” wanda
“John Holt” ya wallafa ya fa]i ra’ayinsa mai cewa “iyaye su rin}a baiwa
‘ya’yayensu dama suna aiwatar da tunanin kansu, iyayen kuma dai su rin}a lura
da hikimar yaransu a duk aiyukan da suke gudanarwa maimakon su rin}a hantarar
su ko daka musu tsawa.
Idan sunyi
kuskure kuma, kamata yayi a fa]akar dasu a ilimance, a nuna musu kuskurensu a
aikace ta yadda ba zasu manta ba ballantana su }ara kwatanta irin wannan
kuskuren.
Abin da dai
ake so shine, yara tun suna }anana su saba da aiki da }wa}walwa, ta yadda a
kwana a tashi zasu samu }warewa a fagen warware matsalolin da kan iya auko musu
a rayuwa, shi yasa wasu masanan ke ganin amfanin “Games” ga yara da cewar yana
bada irin wannan dama ta aiki da }wa}walwa. To amma dai, ko da za a bar yara su rin}a yin
wasannin ‘Games’ a kwamfuta ko a wayoyin hannu ya cancanci a san irin wa]anda
za’a basu. Idan kuwa iyaye zasu mi}e tsaye wajen koyar da yaransu ilimai cikin
hikima, da hakan yafi komai amfani. Sannan gudummawa ta abinci mai gina jiki da
kariya daga cututtuka ma suna matu}ar taimakawa.
No comments:
Post a Comment