Saturday, 27 January 2018

TARIHIN JIHADIN FULANI A ZAZZAU

YADDA JIHADIN FULANI YA KASANCE A DAULAR ZAZZAU

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

Saɓanin jihadin fulani daya auku a kano wajajen shekara ta 1803-1804, jihadi a daular zazzau bai auku ba a sai a wajajen shekara ta 1808.
  Dalilin haka shine karɓar kiran limamin yakin Jihadi, watau shehu ƳUsmanu ɗan fodio da sarkin daular Zazzau Isyaku Jatau yayi a zamanin rayuwar sa.
   Sarki Jatau ya aikewa shehu Usmanu sakon mubaya'ar sa a lokacin da Shehun yayi hijira zuwa Gudu. Haka kuma ya aikewa malamai masu yakin jihadi a kano bukatar aiko malami gareshi wanda zai koyar dasu addini, inda akace jakadun sarkin sun haɗu da malaman jihadin kano a gundumar Karaye, har kuma suka aike da Mallam Dan Zabuwa da wasu mutane gareshi.
  Daga baya mallam Danzabuwa ya faɗa ga malaman jihadi cewar sanda ya riski fadar zazzau, ya taras da Sarki Jatau abisa karagar mulki, sanye akansa rawani ne na mabiya sunni da Shehu Usmanu ya kawo saɓanin rawanin haɓe da sarakunan hausawa ke sanyawa kafin zuwan Shehu.
   Sai dai wannan abu ya tayar da kura a zazzau.
  Mutane da yawa basu ji daɗin yadda sarki Jatau ya bijirewa al'adun daya gada ba ya koma kan abinda shehu yazo dashi. Haka kuma yadda yasa aka rushe wurin bautar Iskokai tare da maishesu Masallatai yayiwa mutanen zazzau ciwo, ciki harda manyan fadawa masu faɗa aji ga Sarki.
  Akan haka akace wasu kusoshi a daular irinsu Magajiya, da Iya da Shebagu, da Wagu suka rinka haɗa kan mutane domin yiwa sarkin bore ko kuma a tilasta masa komawa tsohuwar al'ada, amma sarkin sam yaki biye musu.
   Ana haka sai sarkin ya gushe, masu zaɓen sarki suka haɗu akan ɗora ɗansa Makau amma bisa sharaɗai guda uku.
  Na ɗaya akace masa dole ya karya duk wata yarjejeniya da mahaifinsa Jatau yayi da Tubake, watau musulmai mabiya koyarwar shehu Usmanu ɗan fodio.
  ƁNa biyu dole ya hukunta waɗanda suka ɗora sarki Jatau bisa wannan tafarki na bijerewa abinda kaka da kakanninsu sukeyi a zazzau musamman limamin Kona da Limamin Juma.
  Na uku dole ya rushe masallatai da Sarki Jatau yayi, ya maishesu wurin bautar Iskokai kamar yadda suke a baya.
  Aikuwa da hawan sarki Makau mulkin Zazzau, abinda ya soma kokarin cikawa kenan.
  Akan haka yasa aka rushe masallatai har dana Jumu'a, aka maishesu wuraren bautar Iskokai.
  Sannan yasa aka kama Liman Mallam Muhammadu Lawal aka ɗaure a fadan-fadan, daga baya aka kashe shi. Shikuwa ɗaya limanin Mallam Hamidu mai Jan Rago sai ya gudu ya tsira da ransa.
 Koda labarun Waɗannan abubuwa suka riski Shehu Usmanu, sai ya haɗa tawagar mabiyansa karkashin Mallam Musa ya turo su Zazzau domin suyi yakin jihadi anan..
  A cikin waɗanda zasu taimaka masa akwai Mallam Yamusa, da Mallam Abdulkarim, da Mallam Abdulsalam waɗanda dukkansu sai da sukayi sarautar zazzau bayan sun samu nasarar karɓe iko da ita.
  Sai kuma malamai irinsu Mallam Usmanu Sabulu bahaushen kano wanda ya zamo Katukan Zazzau, da Dokaji bafullatani da akayiwa sarautar Galadima, da Mallam Hamma bahaushen kano da akayiwa Dallatun zazzau, da Mallam Gabdo bafullatanin 'Yandoto daya zamo limamin zazzau na farko bayan Jigadi.
  Sauran kuma mutane ne mabiya shehu Usmanu da suka fito daga wurare daban-daban, misalin Tofa, Yandoto, Borno, Katsinawa, Barnawa, Dan Dorori, Yeskwa, Joli, Gadidi, Bebeji da zaria.
  Sai dai tun kafin isowarsu har labari ya iske sarki Makau. Don haka ya tara dakaru masu ɗumbin yawa, ya aike da wasu kimanin dubu ashirin Hunkuyi domin tarar masu jihadi da ɗai-ɗaitasu.
  Ai kuwa dai, an gwabza faɗa da Masu jihadi a garuruwan Hunkuyi da Kudan har kuma an kusa cin galaba akansu, amma cikin ikon Allah sai suka samu taimako daga wasu sarakunan mulki na yankunan.
  Mutum na farko daya basu taimako shine dagacin Kauyen Durum, wanda ya kuɓutar dadu daga dakarun Makau.
  Na biyu kuma shine sarkin Fawan Likoro daya labarta musu yawan adadin dakarun dake gabansu a Hunkuyi. Don Haka sai suka yanke shawarar kauracewa yakin fito na fito, suka sulale ta Kudaru suka shige birnin Zaria ta kofar Bai ba tare da kowa ya sani ba.
   Wasu sunce Sarki Makau da mabiyansa na cikin gudanar da Sallar Idi masu jihadi suka karɓe iko da zaria, amma saboda hujjar kiyayyar Sarki Makau ga musulunci, wasu suka ce sam ba haka bane, yana bayan gari da dakaru yana sauraron yaji yadda ta kaya tsakanin dakarunsa da masu jihadi sai labari ya riske shi cewar masu jihadi sun karɓe ikon garinsa cikin ruwan sanyi.
  Wannan abu sai ya tsorata rundunar dashi kansa.
   Akace sai Sarki Makau yayi kudu tare da wasu tsirarun dakaru da basu wuce dubu uku ba, ya sauka  a garin Kajuru inda ɗan uwansa mai suna Albarka ke shugabanci.
  Daga nan sai sarki Makau yabar Kajuru ya tafi Abuja inda ya kafa mulki acan. Ance kuma shine dalilin da har yanzu ake kiran sarkin Suleja da Sarkin Zazzau ɗin Suleja.
  Shikuwa Albarka sai ya taho zaria tare da ɗan wani malami mai suna Abduljalil dake karantaswa a Kajuru, sukayi mubuya'a ga Mallam Musa, aka kuma karɓe su da martabawa.
  Ance shine Aka baiwa Albarka gida a kusa da Fada, kuma daga gareshi Sunan Unguwar Albarkawa ya fkto.
  Shikuma Ibrahim Tsoho aka bashi gida kusa da gidan wasu masu kakaki, kuma daga nan sunan unguwar Kakaki ya fito.
  Mallam Musa kuwa shine ya zama sarkin Zazzau na farko bayan jihadi. Kuma yayi mulki ne a gidansa dake Unguwar Kwarbai, bayan fadar Zazzau ba tare da ya shiga gidan sarautar Bakwa ba saboda tsoron kada ya sauka daga tafarkin Sunna zuwa aikata abinda sarakunan Haɓe suke aikatawa.
Kunji yadda Jihadin Fulani a Zazzau ya kaya.

No comments:

Post a Comment