TARIHIN KAFUWAR DAULAR ZAZZAU
Kashi na bakwai
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
3. LIMAMCIN KONA
Kamar yadda yazo tun a farko, a tarihin Kona, ance wasu malamai ne da suka zo wucewa ta zazzau tun kafin ayi ginin ganuwa, suna neman inda zasu zauna. Sai babbansu ya kalli wani wajen yace musu "Ko nan zamu zauna? "
Wasu sun faɗa cewar waɗannan malamai daga wani gari mai suna Kulunfardu suke can kusa da Borno, kuma sun zauna a wani wuri cikin kasar zazzau Inda daga baya ya zamo kauyen kona tun a wajajen shekara ta 1350.
Don haka da aka gina ganuwa sai suka tashi daga Kona suka shigo zazzau.
An sanyawa kofar da suka shigo zazzau ta ciki suna Kofar Kona. Sunan Inda suka sauka kuma ya zamo 'Iimancin Kona', domin a lokacin sune malamai masu yin limanci a daular zazzau.
Haka kuma wannan unguwa ta zamo wurin karantaswa, inda malaman ke koyar da ɗalibai ilimomi na addinin musulunci daga littattafai misalin Bukhari, Jamiu Sagir, Ashafa, Samar-kandi da wasunsu.
Daga wannan unguwa ne kuma tarihin wasu unguwannin zazzau biyu ya ciro.
Unguwa ta farko itace Limancin Alfadarai, wadda akace wani balaraben Misra ne ya taɓa zuwa zazzau daga Borno ya sauka a limancin kona. Sunan sa Mal Salihu, kuma a tare dashi akwai alfadarai masu ɗauke da tulin littattafai na addinin musulunci.
Daga baya sai aka bashi wuri domin ya zauna.
Inda ya koma da zama ake kira da suna limancin Alfadarai zuwa yau, kuma sai daya fifici malaman kona ilimi har ma ya zamo limamin zazzau.
Unguwa ta biyu kuwa itace Limancin Iya.
Ita kuma akace akwai wani malami kuma limami a Kona wanda ya nemi auren ɗiyar sarkin zazzau.
Kasancewsr sarkin zazzau na lokacin ɗalibinsa ne wajen neman ilimin addini, sai ya aura masa ita.
Daga nan sai sarkin ya bashi wurin zama dashi da iyalinsa ya bar kona da zama.
Unguwar da limamin ya zauna ake kira limancin Iya.
4. ANGUWAR JUMA
Ance wannan wuri na daga cikin daɗaɗɗun wurare a birnin zazzau da ake tsammanin tun kafin gina ganuwa akwai mutane a wurin.
Amma dai abinda aka tafi akai shine, wurin ya haɓaka ne saboda masallacin zazzau na juma'a da aka gina tun karni na goma shabiyar zamanin Sarkin Zazzau Muhammadu Rabbo.
Don haka akace ainihin sunan Unguwar shine 'unguwar masallacin Juma'a', daga baya mutane suka yanke shi zuwa Unguwar Juma.
Akwai malaman Juma fulani da suke zaune a wurin. Ance Su jikokin mallam Abubakar ne da akace ya taso daga Futa Toro ya sauka a 'Yandoto, sannan ya zagaya Katsina, kano da Borno har kuma ya sauka a Zaria.
5. ANGUWAR ZAGE-ZAGI
Akwai labarai masu saɓani game da tarihin wannan unguwa, amma dai kusan kowa ya yarda cewar asalin unguwar ya samu ne daga wani gida dake wannan unguwa mai suna gidan zage-zagi.
Wasu suka ce su zage zagi larabawa ne masu yin fatauci da suka sauka a zazzau a karni na goma sha biyar. Sannu a hankali sai auratayya ta haɗasu da hausawa har suka ɓace cikin hausa.
Akace da kalmar Zak -zak ake kiransu, kalmar data samo asali daga 'Zakkatu', fassarar ta shine takobi da larabci. Ance anji suna yawan cewa 'tazakzaka' watau karike takobi shiyasa ake ce musu zak-zak, daga baya sunan ya koma zage-zagi.
Wasu kuma suka ce ai kalmar Zak-zak na nufin tafiya sannu-sannu da larabci.
A Wata ruwayar kuma ance wannan suna na Zage zagi ya samo asali ne daga wani balaraben Fezzan mai suna Usman bn Ismail wanda ya baro gida bayan rigimar data biyo bayan mutuwar mahaifinsa acikin danginsu a wajajen (1786-1806) har kuma ya sauka a zazzau.
Da saukar sa sai Magajiyar gari ta nemi izinin sarki ta bashi wannan wuri domin ya gina gida ya zauna. Kuma wata korama dake kusa da wajen ake kira Zage zagi.
Ita koramar ta zamo kamar dandali ne da ake yin bukin al'ada a duk shekara wanda sarki da sauran mutane ke haɗuwa a wurin ana kiɗa da rawa, abinda wasu ke ganin yayi kama da bikin 'gyaran ruwa ' da aka samu anayi a wasu sassan kasar hausa..
Amma dai ance a lokacin jihadi mazauna gidan zage zagi basu goyi bayan fulani ba, don haka aka kore su daga gari. Amma daga baya da suka dawo sai aka basu wani matsugunin, aka kuma sauyawa unguwar suna zuwa Unguwar Katuka, amma dai har yanzu ance anfi sanin ta da asalin sunanta.
6. UNGUWAR KWARBAI
Itace ungjwar bayan gidan sarki.
Ana ganin sunan ya samo asali ne daga kofar bayan gidan sarki. Watau Kofar Bai.
Amma wasu sunce sunan daga wasu dakarun sarki ya samo asali waɗanda suka zauna a arewacin unguwar masu suna 'yan kwarbai.
UNGUWAR MAGAJIYA
Asalin unguwar ance gidan magajiya zaria ne, watau ɗiyar sarkin zazzau Bakwa Turunku.
Amma daga unguwar aka fitar da Unguwar lalle, Unguwar kaho, da Unguwar magajin aska.
7. UNGUWAR KUSFA
Shima wannan wuri tsohowar mazauna ce da akace anyi bautar iskokai a ciki tun kafin zuwan musulunci.
Amma a hankali malamai suka soma zama a wurin.
Wani mai suna mallam Tankiru akace ya soma zama tare da tulin ɗaliban sa a wurin.
Daga baya sai mallam Shitu ya maye gurbinsa, wanda ya shahara sosai har ake zuwa daga sassa ɗaukar ilimi gurinsa.

Gaskiya labarin anguwan zage zagi bahaka take ba akwai labaru Wanda tarihin wajen batasan dashi ba Kaman Inda marubuchi yafada awajaje mabanban ta kaman inda yace magajiya tasaukar dash, to ba haka bane ita magajiya na waccan lokacin bata sa Alaka da su mutanenen zage zagi Dan su Malamai ne kuma iqidar zuhudu suke bi,sannan na biyu marubuchi yafada da Cewa basu goyi Bayan Jahadin sheik Usman bin fodio wannan zancen bahaka take ba, marubuchi yasani lokacin da sheik Usman bin fodio Ya turo musa da yamusa da Abdul Karim da tutar musulunchi Ya umurcesu da su Shiga ta Kofar bai Idan sun shiga su Fara zuwa Gidan zage zagi sufada mawa malaman Gidan zage zagi abin da yakawosu kafin su tafi izuwa fadar sarki Dan alokacin duk laifin da mutum yayi idan Ya gudo yazo Gidan zage zagi ya Tsira, Bayan da sukkayi masu Bayani GA abin da sheik Usman bin fodio Ya turo su, Sai malam Gidan zage zagi sukayi na am da sakon sheik Usman bin fodio Sai malam musa gwarzon mahimmanchi yabar mutum da a Gidan zage zagi domin shi yazamto shaida lallai yazo kuma yacika umurnin sheik Usman bin fodio wanna mutumin sunansa malam Usman tsoho sabulu shine zuri'arsa gidan fagachin zazzau.
ReplyDelete