Wednesday, 10 January 2018

SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 4

TARIHI: SARAUTAR SARKIN MUSULMI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na huɗu.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

Bayan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya huta a gida, sai kuma ya sake ɗaura haramar yaki zuwa Anka a lokacin kaka.
  Daya gama haɗa rundunarsa, sai ya fita Wurno, ya riski wani gari Mada-rumfa akan hanya, ya cishi da yaki, ya warwatsa shi, ya kuma kafa ɗansa Ibrahim shugaba a garin.
  Sannan ya wuce gaba izuwa Bakura, nan ma ya kwace ikonsa, ya kuma ajiye ɗan ɗan Uwansa Ahmadu shugaba.
 Daga nan ya wuce Anka, yayi yaki da ita mai tsanani, ya samu nasara sannan ya koma gida.
  Ance Muhammadu Bello yayi yakuna akalla guda 47 waɗanda shine yayi jagorancinsu da kansa yana kan karagar Sarkin Musulmi, amma babu wanda zai iya tantance adadin yakunan da akayi a lokacin mulkinsa sai Allah.
 Haka kuma ance bai gushe ba yana yaki don ɗaukaka addinin Allah har saida lamurra suka koma dai-dai kamar sanda Shehu Usmanu yake raye.
   Wuraren da Muhammadu Bello ya zaune sune:-
 Da fari ya fara zama a Yamulu tsawon shekaru biyu a lokacin shehu na Degel yana ribaɗi, watau kai hare-hare da kuma taryar abokan adawa idan sunzo da hari. Sannan ya zauna a sokoto nan ma don Ribaɗi, ya kuma zauna Gwandu don Ribaɗi.
  A halin sarautarsa kuwa, ya zauna a Karandai, sannan Magarya, sannan wurno, kuma nufinsa ya rasu yana yawo garuruwa domin ribaɗi.
Har ma an jiyoshi yana cewa "Hakika mazaunin ribaɗi, idan ya mutu anan aka turbuɗeshi acikinta, ba za'a naɗe takardar saba. Zai zamo ana rubuta masa lada a kullum kamar yadda ake rubuta masa a lokacin rayuwarsa, daga nan har ranar tashin alkiyama".
  Don haka yayi wasiccin cewa koda ya mutu, kada a binne gawarsa a sokoto ko kuma awani wurin sai a wurno.
   Haka kuwa akayi, ya rasu da marece na ranar alhamis, 25 ga watan Rajab na shekarar 1253 hijiriyya, a wurno.
 Maganarsa ta karshe kalimatussashada ce sau uku, sai kuma Ayar Al-kur'ani maigirma.
 Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rasu yana da shekaru 57 da watanni 11. A lokacin kuma yana da shekaru 21 bisa karagar sarkin musulmi.
  Don haka a wurno aka binne shi. Kuma har yanzu acan kabarinsa yake.
  Dafatan Allah ya rahamsheshi Amin.

2. SARAUTAR SARKIN MUSULMI ABUBAKAR ATIKU
Bayan kwana bakwai da rasuwar Muhammad Bello, sai akayiwa Abubakar Atiku mubaya'a.
  Shikuwa ya kasance ɗane ga Shehu Usmanu ɗan fodio, watau kaniɓga Muhammadu Bello.
  Kuma ya kasance masanin sirruka.
  Har ma ance mahaifinsa ya sanar dashi sirruka 115, shikuwa sai ya sanar da 15 ga jama'a, ya bar 100 bai sanar da kowa ba.
 Amma ga maison samun sirrikan daya sanar, sai ya nemi lityafin 'Tabshirul Ikhwan' na Abdulkadir Macciɗo Waziri.
    Yake-yake
  Bayan Sarkin Musulmi Abubakar Atiku ya hau gadon sarauta, sai kafiran amana na zamfara dana gobir suka warware alkawari, don haka sai yayi tattalin yaki, ya fuskanci Burmi.
  Yayi tafiya har ya iske birnin Damri. Ya iske sarakunan zamfara sun taru cikinsa, yayi faɗa dasu, kuma ya samu nasara.
  Sannan ya ɗaura yaki ya isa karkarar Katsina, yayi sansani anan, sannan ya zabura zuwa birnin Cikaji yayi yaki dasu mai tsanani, yayi zamansa kwanaki da dama, sannan ya koma gida.
   Daga can kuma ya ɗaura yaki zuwa zurmi, ya aike Abdul Hasanu ɗan sarkin yaki Aliyu Jedi, ya fita garesu da runduna, yayi faɗa dasu ya komo gida.
  Sannan yayi tattalin yakin Attabu (yakin gayya) wanda ya kira sarakunan gabas ya gamu dasu acikin kasar zurmi. Ya tashi ya nufi Gobir, ya kokarta ya riski Tsibiri, ya sauka Rumka, ya iske mutanen Gobir, katsinawa, Azbinawa da mutan Borno sun taru acan.
   Ya fara yaki dasu tun hantsi har la'asar. Allah ya bashi nasara ya karya su  ya koma gida.
  Sanna ya ɗaura yaki zuwa kasar Gummi, ya kwana 8 ya ɓata abincin karkararsu duka, suka firgita dashi, sannan ya komo ta zurmi, ya dawo gida.
   Da lokacin kaka yayi, sai ya sake gayyatar sarakunan gabas, suka zo da shirin jihadi, suka fita da yaki har Zamfara, suka fuskanci Gobir.
   Ya shiga cikinta yayi sansani, Ya kwana uku, sannan ya nufi tsibiri da yaki. Mutanensa suka aukawa tsibiri da yaki mai tsanani. Anan suka wanzu har kwanaki biyar.
   A cikin haka sai ya lura mutane jikinsu yayi sanyi da yaki, don haka ya juyo ya tsallaka gulbi, babu wani alamun ciwo jikinsa.
  Lalura ta sameshi ranar 27 ga watan Ramalana, ya zamo ana ɗauke dashi a wuya har suka iso wani wurin da ake cewa Nasarawa cikin kasar Zamfara duka sauka.
  Ya kwana 18 anan, sannan yahau zuwa Kuturu. Ranar  alhamis kuwa ya rasu anan.
 Don haka Kabarinsa nanan a Katuru. Da fatan Allah ya gafarta masa Amin.
  Sa'ar da aka kare jana'izarsa, sai waziri Babba Abdulkadir ɗan waziri Giɗaɗo ɗan Laima yayi ban kwana da sarakunan gabas suka koma gida.
  Zaɓaɓɓun da suka rasu kuwa a lokacinsa akwai ɗan uwansa Buhari, da Alkali Bi'ali, da Mustafa marubucin shehu Usmanu, da mallam ishaqa da Mallam Mani da wasunsu.
  Sarkin musulmi Abubakar Atiku ne sarki na farko daya rasu yana dawowa daga yaki.
  Daga nan sarakunan Sokoto suka zaɓi Aliyu Babba ɗan Muhammadu Bello ɗan Shehu Usmanu ya zama sarkin musulmi.

No comments:

Post a Comment