LABARIN MU NAYAU; ABU DAYA
A zamanin da, anyi wani Sarki a wani gari mai ilimi, yana son koyawa al'ummar sa darasi. Don haka sai ya sanya aka dauko wani dutse qato aka ajiye a babbar hanyar shiga garin ba tare da al'ummar garin sun sani ba. Lokaci-zuwa-lokaci, sarkin yana zuwa ya labe a wajen don ganin ko akwai wanda zai dauke dutsen da kuma sauraron maganganun jama'a akan dutsen.
Da yawan mutane idan sunzo wucewa ta wurin sai dai suyi tsaki da baqar magana akan sarkin, wasu suce "Sarkin garinnan bashi da adalci, kalli yadda ya bari aka lalata hanya" da sauran maganganu na batanci.
Ana haka sai ga wani mutum yazo wucewa yana dauke da kaya- niqi-niqi akan sa. Da zuwa wajen dutsen nan sai ya sauke kayansa a gefe, sannan ya fara kici-kicin kawar da dutsen daga kan hanya. Yayi ta qoqari, dakyar ya samu galaba ya ture dutsen.
Ya tsaya yana haki yana dan hutawa kafin yaci gaba saboda wahalar da yasha, sai ya hango wata jaka ajiye adai-dai inda ya ture dutsen. Nan take ya garzaya gareta, ya dauka kuma ya bude. Sai ya ganta cike da gwala-gwalai, ga wata 'yar takarda a gefe an rubuta cewa ' wannan kyauta ce ga duk wanda ya matsar da dutsen nan'.
Mutumi dai bai gama gamsuwa ba, yana ta waige-waige ko zaiga mai jakar, can sai kuma Sarki ya fito daga inda yake boye. Cikin rawar jiki Mutumin ya fadi gaban sarki yana tuba da rantse-rantse, tsammanin sa jakar sarki ce aka sato shikuma ya tsinta.
Sarki ya rarrashe shi gami da kwantar masa da hankali, ya kuma jinjina masa ga aikin dayayi, sannan yace "Ka sani, wannan kyautar kace kuma bata kai abinda Allah yayi tanaji ba ga duk wanda ya kawar da wani abu akan titi wanda yake cutar da mutane"
"Don haka na jinjina maka matuka, lalle ya kamata sauran mutane suyi koyi dakai acikin sauran fannonin rayuwa. Bai kamata mutane su koma gefe ba suna aibanta gwamnati akan abinda zasu iya magancewa ba..""
Kashe gari Sarki yasa aka tara al'mmar garin duka, ya sanar dasu abinda ya faru, sannan yayi musu nasiha da su rinqa kokarin kawar da duk wani abu wanda yake cutar da al'umma ba lalle sai akan titi ba, har ma da bangaren asiniti, ilimi da kasuwanci. Yace mutane ayanzu sunfi fifita abinda zasu samu anan duniya sama da abinda Allah zai basu, idan da mutane sun san kyautar dana ajiye aqasan dutsen da haqiqa anyi rububin ture shi, a qarshe ya kuma sanar dasu cewa yin abu don Allah yana daga alamomin Imani kamar yadda manzon Rahama annabi Muhammad (s.a.w) ya fada.
Da fatan muma zamu dauki wannan darasi wajen cike ramukan titi masu haifar da hatsari, taimakawa da magunguna kyauta ga marasa lafiya dake asibiti, taimakawa 'yam makaranta da kayan karatu, tare da rangwame ga al'umma acikin kasuwanci. Allah yasa mu dace amin
No comments:
Post a Comment