Hikayar Sagardatta, Ɗa ga wani Ɗankasuwa
Daga littafin Khalila wa Dhimna, wanda Vishnu Sharma ya rubuta shekaru sama da dubu biyu da suka gabata (300 BC) domin koyar da mabiyan sa sirrikan zaman duniya.
Sadiq Tukur Gwarzo
Sadaukarwa gareku don neman albarkar ku bisa murnar raɗin sunan yaron waje na Muhammad Tukur wanda akayi ayau Laraba 23/2/2021.
Sagardatta shine sunan wani kyakkyawan matashi, ɗa ga wani ɗan kasuwa da aka taɓayi a wani daga garuruwan tsohuwar daular Hindu.
Wata rana, sai wannan ɗan kasuwa ya samu labarin cewa ɗansa Sagardatta ya siyi wani littafi mai tsada sosai, wanda saɗara ɗaya ce tal a cikin sa watau "Abinda aka ƙaddarta maka kaɗai kake iya samu".
Ko da wannan attajiri ya ji haka, sai hasala matuƙa. Ya kira ɗan nasa yana masa faɗa, ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba, yana cewe "Ta yaya zaka yi nasara a harkar kasuwanci, alhali zaka iya ɓannatar da kuɗaɗe masu tarin yawa haka wajen siyen littafi ɗaya tal mai ƙunshe da saɗara ɗaya tal ajikin sa?! Fitar mini daga gida, kada na sake ganin fuskar ka anan!"
Daga nan Uban ya kori ɗan nasa daga gidan sa.
Wannan matashi ya shiga tsananin baƙin ciki bisa korar sa da mahaifin sa yayi daga gabansa, amma babu yadda ya iya, sai ya ɗauki littafin sa tare da kama hanya yana tafiya ba tare da yasan inda yake nufa ba. Ya haddace wannan saɗarar dake cikin wancan littafi, don haka yana tafe yana maimaita ta a cikin zuciyar sa.
Akan hanyar sa ya riski wani babban gari, sai ya nemi abashi masauki, mutanen garin suka tambaye shi sunan sa, sai ya amsa musu da waccan saɗara da yake ta faman maimaitawa a zuciyar sa, watau ""Abinda aka ƙaddarta maka kaɗai kake iya samu". Shikenan, sai aka rinƙa kiran sa da wannan suna.
Wata rana, sai ƴar sarkin garin ta ziyarci wani bikin al'ada na shekara-shekara da akeyi a wannan gari, anan kuma sai ta haɗu da wani kyakkyawan ɗan sarki baƙo wanda shima yazo kallon bikin daga ƙasar su, sai ya kasance ta kamu da sonsa nan take. Sai ta umarci kuyangarta ta bincika hanyar da zasu aika masa da saƙo.
Daga nan Gimbiya ta rubuta ɗan jawabi a takarda, ta baiwa kuyangarta don ta isar a gareshi.
Sai dai bisa kuskure, wannan kuyanga ta baiwa matashi Sagardatta wannan wasiƙa a maimakon wancan ɗan sarki, Sagardatta ya karɓaa ya buɗeta, ya soma karantawa kamar haka:-
"Na kamu da sonka tun sa'ar da na soma ganin ka. Ina rokon ka same ni a fadabta. Da zarar ka shiga, za ka samu igiya sarƙafe a ɗaya daga tagogin wajen wadda zata kawo ka kai tsaye zuwa inda nake. Daga Gimbiyar wannan birni”
Ya raya a zuciyar sa da cewa “Tabbas zan amsa gayyatar gimbiya tunda ta buƙaci haɗuwa dani.”
Da zuwan sa ya ga igiya an zirota daga tagar wani ɗaki can a bisan bene, ya kama ta ya soma ɗaɗɗafewa har ya riski ɗakin da gimbiya take. Ɗakin ɗan duhu, kuma gimbiyar tayi tsammanin Yariman nan data gani ne a wajen biki, don haka cikin rawar jiki ta shiga yi masa karɓa cikin girmamawa. Ta gabatar masa da abinci da abinsha kala-kala cikin karramawa.
Bayan sunci sun sha, sai ta shiga yi masa zantuka tana mai cewa “Nayi matukar kamuwa da sonka. Hakika babu wanda ya kamaci zama miji na sama da kai, ina rokon ka sanar dani menene ra'ayin ka game dani”
Sagardatta yace "Abinda aka ƙaddarta maka kaɗai kake iya samu"
Sai tayi mamakin yadda Yarima ɗan sarki zai amsa maganar ta da wannan maganar, da hanzari ta kunna manyan fitulun ɗakin waɗanda suka haskaka shi sosai. Ranta ya ɓaci matuƙa yayin da ta gane ashe ba wanda ta buƙata bane a gabanta, nan take ta fatattake shi tare dayi masa korar kare daga gareta.
Wannan matashi ya cika da baƙin ciki bisa wannan abu da ya sake samun sa ba bisa laifin sa ba, sai yayi shawarar tafiya wani wajen bauta dake kusa da wajen domin shafe yammaci da daren sa acan, jim kaɗan da isar sa sai bacci ya kwashe shi.
Da lokacin rufe wajen yayi, masu zuwa bauta duk sun gama tafiya gida, sai wani maigadin dare ya hango matashi na bacci, don haka yazo ya tashe shi yana mai umartar sa da barin wurin, yace masa "Wannan wajen bauta tsoho ne kuma talautacce, idan kai baƙo ne zo muje ka kwana a gida na"
Shikenan, matashi Sagardatta ya bi maigadi zuwa gidan sa dake kusa da wajen, daga nesa ya nuna masa ɗakin da zai shiga ya kwanta kafin safiya. Sai dai cikin kuskure, wannan matashi ya shiga wani ɗakin saɓanin wanda aka nuna masa, wanda aciki ɗiyar wancan maigadi taci ado tana sauraron saurayin ta.
Mai gadin ya kasance yana da ɗiya wadda take soyayya da wani mutumi, amma ba bisa son ran sa ba, har ma ya hana shi kusantar duk inda take. To amma saboda tsabar soyayya, sai wannan ɗiya ta shirya da masoyin nata yin aure a wannan dare yayin da mahaifinta ya tafi gadi a wurin bauta da dare, ta yadda wajibin sa ya amince da matashin a matsayin surukin sa.
Kasancewar akwai duhun dare, da shigar Sagardatti ɗakin, sai ɗiyar maigadi tayi tsammanin masoyin nata ne ya gabato, nan take ta tarbeshi da murna, taje gaban gunkin su ta ɗauko awarwaron ƙulla aure ta sanya a hannun ta, sannan ta sanya a na Sagardatti. A bisa al'ada, ta ƙulla aure tsakanin su kenan.
Matashi Sagardatti cike da mamaki yace "Abinda aka ƙaddarta maka kaɗai kake iya samu"
Ko da taji haka, sai nan take ta gane ashe ta tafka babban kuskure, sannan nadama ta dabai-baye ta tana mai rayawa a zuciyar ta cewa 'dama aduk sanda mutum yake gaggawar aikata wani lamari ba tare dogon nazari ba, tabbas yana iya tafka babban kuskure.'
Nan take ta shiga masa masifa da ci masa mutunci tare da korar sa daga gidan ma baki ɗaya.
Har ila yau dai, Sagardatta ya fito daga wannan gida tare da kama hanya a cikin daren sannu a hankali cike da tsananin ɓacin zuciyar faruwar wannan abu ba tare da ya aikata wani laifi ba, yana cikin tafiya ne ya ga wata tawagar masu ɗaura aure a gefen hanya suna tafiya ana kaɗe-kaɗe da bushe-bushe.
Mutanen suna sanye da kayayyaki na ƙawa, sunyi kwalliya sanye da jawhari da azurfa. Kawai sai ya yanke shawarar shiga cikin su. Yabi bayan ango da tawagar sa, wanda a kusa dashi amaryar sa ce da zai aura ba da jimawa ba, kuma a lokacin suna kan hanyar su ne ta zuwa gidan kawunnan amarya a inda za ayi ƙwarya-ƙwaryan bikin ɗaurin aure.
Ana cikin haka, Kwatsam sai ga mahaukaciyar giwa ta kutto tare da tunkaro wannan tawaga, cikin firgici kowa ya dare tare da arcewa, amarya kaɗai tayi tsira yayin da ta gurɗe ta faɗi ƙasa a tsorace tana maƙyarkyata cikin firgici.
Ko da ganin haka, sai matashi Sagardatti ya zaro wani kullin kusoshi dake rataye dashi, sannan yabi bayan giwa ya buga mata, giwa ta tsorata tare da rugawa da gudu.
Bayan ɗan lokaci tawaga ta dawo, ƴanuwa da abokan arziki suka shiga yiwa amarya jaje da barka da auna arziki, ita kuwa sai ta murtuke fuska, shine ma take cewa "Ayanzu na sauya shawara, domim a lokacin da rayuwata ta shiga cikin haɗari, an rasa wanda zai cece ni sai wannan baƙon, don haka babu wanda zan aura sai shi. Wannan shine abinda na yanke"
Wannan mataki na Amarya ya ɓatawa mutane da yawa na cikin wannan tawagar zuciya. Nan take sai gaddama da cece kuce ta ɓarke a cikin su..
Da muhawara tayi tsanani, hayaniya yayi yawa, duk mutanen kewayen wajen suka firfito don ganin abinda ke faruwa. Sai kuma ga Sarkin garin shima ya fito, ashe yaji labarin abinda ya farundon haka ya taso domin yin hukunci. A cikin mutanen dake wannan waje har da gimbiya ɗiyar sarki da kuma budurwa ɗiyar maigadi.
Sarki ya tambayi matashi Sagardatti da cewa "Kana cikin tawagar biki wannan ibtilai ya auku, sannan kai ne ka kuɓutar da wannan yarinya da ake gab da ɗaura mata aure daga cutarwar giwa, Ina so kayi mana bayanin yadda wannan abu ya faru!"
Ko da matashin Sagardatti ya yunkura don yin magana, kaɓar kulluɓ, maganar sa dai itace karatun nam da ya haddace, watau "Abinda aka ƙaddarta maka kaɗai kake iya samu".
Gimbiya da ɗiyar maigadi duk sunji maganar sa, kuma sun tsargu da ita. Sai suka shiga cikin nadama da damuwa, har sai da Sarki ya lura da hakan.
Koda sarki yaji haka, kuma ya lura da alamar damuwa a fuskokin waɗannan mataye biyu, sai ya ƙara neman cikakken bayani na gaskiya game da wannan lamari.
Ɗiyar maigadi ta bayar da labarin yadda ta ɗaurawa kanta aure cikin kuskure da wannan matashi, sannan ta rufe cewa "Ƙaddara ta kenan, kuma bana tuba game da faruwar hakan"
Gimbiya ma ta yiwa sarki bayanin yadda ta shafe lokaci da matashin cikin kuskure, tare da rufewa da faɗin "Ƙaddara ta kenan, bana da-na-sanin faruwar hakan!"
Ko da jin haka, sai wannan budurwa da za a ɗaurawa aure tace "Ya sarkin duniya, abinda ƙaddara ta bani fa, babu mai karɓe mini shi daga gare ni!"
Sarki ya cika da mamakin wannan abu, sannan ya shiga shawarwari da na kusa dashi, daga nan sai ya yanke ɓatsayar sa game da abin, ya sallami mutane.
Da gari ya waye, ya shirya biki. Ya yiwa matashi Sagardatta kyautar ƙauyuka dubu na ɓasarautar sa baya da zinariya da tarin dukiya. Sannan ya aurar dashi ga ɗiyar sa Gimbiya, tare da naɗa shi a matsayin magajin sarautar sa bayan rasuwar sa.
Ita ma waccan amarya da ɗiyar wancan maigadi, duk sun samu cikar burikan su na auren matashi Sagardatta daga iyayen su bayan an shirya biki gwargwadon ƙarfin n su.
Daga nan matashin yasa aka gina masa gagarumar fada, sannan bai yi fushi da mahaifan sa ba kasancewar ya gamsu da karatunsa cewa"Abinda aka ƙaddarta maka kaɗai kake iya samu", ya gayyato iyayen tare da yanuwan sa zuwa wannannfada dominmsu rayu tare dashi, haka suka wanzu cikin farin ciki.
Darasi: Akwai darussa masu yawa a hikayar gwargwadon fahimtar makaranci, amma dai kaɗan daga ciki sun haɗar da:-
Duk abinda aka ɓatar wajen samun ilimi (hikima) matsawar anyi aiki dashi za a ci riba a gaba, haka kuma a sani cewa sai ansha wuya akan sha daɗi. Sannan, yana da kyau Kayi iya kokarin ka akan lamurorin rayuwa, amma ka barwa ƙaddara dama tayi aikin ta.. domin "Abinda aka ƙaddarta maka kaɗai kake iya samu"