Thursday, 6 October 2022

YADDA AKA YI BAUTAR KURMIN JAKARA A KANO

 BAUTAR JAKARA


Ga abinda ya zo a littafin Tarihin Kano game da Bautar Kurmin Baƙin ruwa ko ace kurmin Jakara.

'Ma'abutan wannan ƙasa (Kano) waɗanda Bagauda ya same su a cikinta suna muljin garinsu, ba su bin kowa sai Tsumburbura da duhuwa tasa JAKARA. Ana ambatonta (duhuwar) da KURMIN BAƘIN RUWA, domin shi ruwa ne baƙi, duhuwa ta kewaye shi, ana kiyaye dukan musiba da ita da gunkinsu, mafarinta kuwa daga Gurgumasa har zuwa Dausara. Kiraranta da zartakenta ba su motsi sai idan musiba ta gabato wannan gari ta yi kuruwa sau uju, hayaƙi ya riƙa fitowa daga cikin Tsumburbura, wanda ke cikin tsakiyar ruwa. Sai su nemi baƙin kare su yanka a ƙarƴashin Tsumburbura, kuma su yanka baƙin bunsuru a cikin duhuwar.

   Idan hayaƙi da kururuwan sun daɗu, to babu makawa sai musibar dɗta sadu dasu. Idan kuwa ba su daɗu ba, babu masiba. Sunan duhuwan nan kuwa MADAMA. Kuma sunan Tsumburbura RANDAYA'.

Ƙarin Bayani game da KURMIN JAKARA

Ita Jakara ana kiranta da suna KURMIN-BAƘIN-RUWA saboda ruwan tafkin baƙi ne, kuma kewaye take da bishiyoyi masu yawa. A cikin bishiyoyin ne akwai guda ɗaya da aljani yake kanta, wadda suke yin tsafinsu a kanta, kuma wadda take yin hayaƙi idan musiba ta tunkaro Kano. Ita wannan bishiyar a tsakiyar ruwan take. Wannan daji mai yawan bishiyu sunansa MATSAMA, Bishiyar Tsafin kuma itace RANDAYA. Ɗaukacin wajen shine Jakara har zuwa inda Kasuwar Kurmi take a yanzu.

Daga Littafin KANO TA DABO TUMBIN GIWA na Alhaji Ahmad Bahago

Saturday, 17 September 2022

Sunday, 31 July 2022

HANYAR KANO: TARIHIN DA KE GURIN GAWA

 HANYAR KANO: TARIHIN DA KE GURIN GAWA


SADIQ TUKUR GWARZO

Kamar yadda marubutan littafin 'Urban Society ' Gist da Halbert suka faɗa, kuma kamar yadda yake game da asalin ita kanta Wayewar, tushen kowanne birni kusan ya samo asali ne daga hijirar mutanen ƙauyuka.

Birane sune cibiyar hadar-hadar kasuwanci, tsaro, al'adu, ilimi da bincike. Don haka ya sanya mutanen karkara na kusa da na nesa, da ma wasu mutanen da ke wasu biranen da dama kan ziyarci birane domin samun mafakar tsaro, ko kasuwanci, ko samun ilimi ko cimma wani dalili na al'ada da ma sauran muradai walau ziyarar ta kasance ta wucin gadi ko kuma ta-din-din-din. 

  Akwai ilimin tarihi mai yawa da mukan rasa yayin kawar da kawunan mu ga tafarkan da suke sadar da mutane zuwa waɗancan birane. Wannan kuwa ya haɗar da tarihin wasu muhimman abubuwa da aka taɓa yi ko kuma muhimman wurare masu dangantaka da biranen kansu.

Sau tari a ƙasar Hausa mutane kan niƙi gari domin ziyartar wani birni amma sai su shantake a wasu wurare na kusa ko na nesa da biranen bisa wasu dalilai. Haka kuma a wasu lokutan, sauyawar yanayai kan tursasa mutanen cikin birane komawa makusanta ko manesantan garuruwa ko birane da zama.

 Garin Gurin Gawa na ɗaya daga cikin ƙauyukan da suka kafu a turbar kano. Hasashe ya nuna cewar mabanbantan mutane da akasarin su ƴan tafarki ne suka kafa garin tsawon lokaci da ya shuɗe. Garin yana kudu da garin kano, akan turbar da zata shigar da mutum birnin kano ta ƙofar Ɗan Agundi (wadda aka sara a wajajen shekarar 1499AD). Don haka duk mutanen da suke son shiga kano daga yankunan Rano, Jos, sassan ƙasar Bauchi da makamantan su sai sun bi ta wannan turba.

ASALIN SUNAN GURIN GAWA

Akwai mabanbantan zantuka game da asalin sunan Gurin Gawa.

1. Na ɗaya: Gurin Gawa daga Gurin Gawarwaki. Ance an samo sunan ne daga kasancewar wurin filin daga. Watau a zamanin yaƙi, da zarar kano ta samu labarin an tunkaro ta da yaƙi ta wannan shiyya, sai ta turo dakarunta ta jibge su a wannan wuri. Don haka anan za a fafata yaƙi, anan kuma za a samu tulin gawarwaki bayan ƙarewar yaƙi. 

2. Na biyu: Gurin Gawa daga 'Gurin-Ge'

Wannan ra'ayin yana cewa an samu sunan ne daga wani Bafillatani mai suna Gurin-ge, wanda kiwo ya biyo dashi ta wajen har kuma dabbobin sa suka gano masa wani kwarmin ruwa, don haka ya mayar da wajen mazaunin sa, daga bisani ƴanuwansa fulani suka riƙa riskar sa da zama.

3. Na uku: Gurin gawa daga Gurin da aka samu  gawar Kuyangar Sarkin Rano

Ance akwai wani rafi tsakanin Medile da Gurin Gawa wanda ake kira 'Ci-kuyangi', saboda yadda yayi silar mutuwar kuyangi da dama a ciki har da wata amintacciyar kuyangar Sarkin Rano wadda ta rasu a wurin akan hanyarta ta shiga Kano, ance daga nan aka samo sunan na Gurin Gawa.

  Zuwa yanzu, garin ya kasu kashi biyu, akwai Ruga inda fulani masu sarautar garin suke, da kuma ɓangaren Hausawa inda ake kira Dausayi. Anan ne mahaifiyar shahararren masani marigayi Sheikh Nasir Kabara ta ke.

TASIRIN SHAHARAR KANO GA SAURAN MAKUSANTAN GARURUWA

 Kasancewar birnin Kano birnin kasuwanci ne ba birnin Siyasa ba, ya samu ɗaukaka tsawon lokaci saboda yadda fatake ke tururuwar zuwa gare shi bisa dalilan kasuwanci. Wannan ya taimakawa birnin wajen zamowa shahararre, shahararsa kuwa ta yi tasiri ga makusantan ƙauyuka wajen karɓar baƙi a ko-da-yaushe, da kuma hada-hadar kasuwanci.

Kamar yadda aka sani, a baya babu tsarikan otal ko masaukai a ƙasar Hausa, sannan akan rufe ƙofofin shiga birane  idan dare yayi. Saboda haka, matafiya a zamanin baya sukan samu waje da suka aminta da amincin sa su yada zango idan dare yayi kafin su ƙarasa cikin birni. Don haka kafuwar ƙauyuka a kusa da birane kan zamo masaukai ga baƙin da suke haramar shiga kano yayin da dare yayi musu.

 A irin haka ne aka samu wani mutumi daga ƙasar Bade ta cikin jihar Yobe a yanzu haka ya yada zango a Gurin Gawa tare da soma sana'ar Kwarami (awo), inda ya samu shahara a wannan sana'ar, ya rinƙa sauƙaƙawa fatake masu zuwa kano da jakuna siyan hatsi da kuma masu fitowa daga kano neman haja ba tare da sunyi dogon zango ba. (Har yanzu ana yiwa mazaunin wancan babarbare laƙabi da suna 'Marken Bade').

  A ƙarshe, ina da ra'ayin cewar muhimmancin buƙatar bibiyar tarihin manyan tafarkan da suke sadarwa zuwa biranen mu tamkar na sanin tarihin biranen ne.

HANYAR KANO: TARIHIN RIMIN GADO

 HANYAR KANO: TARIHIN RIMIN GADO


SADIQ TUKUR GWARZO


Akan yiwa garin Rimin Gado kirari da cewa "Rimin Gado garin ƴan lalle", silar hakan kuwa shine, Allah ya baiwa garin yalwa ta bishiyoyin lalle, wanda a zamanin baya ya kasance itace mai daraja wanda mutane ke rububin neman sa domin yin amfani da shi a matsayin sinadarin tsaftace jiki da magani da sauran su.

 Wannan gari, a zamanin baya, ya zamo kasuwa matattarar fatake inda mutane ke niƙo gari daga mabanbantan sassa domin siyen lalle da sauran hajoji.

A binciken da Mallam Muhuyi Magaji Rimin Gado yayi, ya sanya kafuwar garin Rimin Gado da kimanin shekaru 300 da suka gabata. Kafin zamowar Rimin Gado gari, inda Rimin Gado yake a yanzu ya kasance (zango ne) wurin saukar matafiya ne masu kara-kaina tsakan-kanin birnin Kano da biranen da ke yamma da ita misalin Sokoto.

  KAFUWAR RIMIN GADO

Ance akwai wani mutum mai suna Magili, mabaraci ne, wanda ya taso daga Degel; wani ɗan ƙaramin gari dake jamhuriyar Nijar ayau zuwa inda garin Rimin Gado ya ke, don haka ana iya cewa shine asalin kafuwar wannan gari.

Bisa al'ada ta mabarata, sukan samu gefen turbar da mutane ke shigewa su fake suna addua ko zikirai ko waƙoƙin nasiha ga matafiya da makamantansu da nufin neman sadaka daga masu shigewa. Magili ya gina gadon ƙasa a inda garin Rimin Gado ya ke a yanzu, a gefen turbar da matafiya ke wucewa zuwa birnin Kano, akan wannan gado yake zama yana bara a ko-da yaushe.

ASALIN SUNAN RIMIN GADO

Ance Magili,  wanda yake zama akan gadon da ya gina na turɓaya yana bara da rana sai kuma ya kwanta bacci idan dare yayi, ya samo ƙwanson Rimi da ya tattara a matsayin matashin kai wanda yake ɗora kansa yayin bacci. A kwana a tashi sai ƴaƴan rimin da ke cikin ƙwanson ya rinƙa zuba daga gadon nasa zuwa ƙasa, har kuma aka yi sa a tsiron bishiyar rimi ya fito a wajen wanda daga bisani ya girma ya zama bishiya gagaruma wadda ake zama don hutawa ko don gudanar da cinikayya a ƙarƙashin ta. Daga nan ne fa aka samo sunan 'Rimin Gado' wajen nuni da bishiyar Rimin da ya girma a ƙarƙashin ko a kusa da gado. 

  Sannu a hankali wannan wuri ya haɓaka ainun tare da zamowa dandalin yada zangon fatake masu son shiga kano waɗanda akasarin su suke tafiya a ƙafa, ko a jakuna da sauran ababen hawan lokacin daga birane irin Alƙalawa, Sokoto da sauran su.

  TURBAR KANO TA SASHEN RIMIN GADO

  Wannan turba ta soma ne daga ƙofar Kabuga wadda take a yammacin kano, ta keta ta shacin Janguza, ta wuce ta Yalwan Ɗan ziyal har zuwa wannan gari na Rimin Gado. Daga nan kuma sai ta cigaba da nausawa sashen yamma har ta keta Gwarzo zuwa wasu sassan ƙasar Katsina. Kuma kamar yadda tarihi ya nuna, ta wannan turbar ne aka rinƙa samun sadarwa a tsakanin biranin Kano da biranen da suka kafu a zamanin baya waɗanda a yanzu suke cikin jihar kanon kanta, da Katsona da Zamfara daa Sokoto da Kebbi har zuwa sassan ƙashen Mali da  Nijar. Kuma haƙiƙa, ba iya Rimin Gado ba, akwai garuruwa da dama da kafuwar su ya samu ne daga albarkar wannan turba.

Wednesday, 16 February 2022

WAƘE: RABBI KARE MIN MIJINA

 Rabbi kare min mijinaaa

Abin kirana farin ciki naaa


1. Ni ina sonsa sahibina

Shi nake so nake wa ƙauna

Shi yake sanya murmushi na

Shi yake yaa yen fushi na

      Shi nake yiwa kwalliya ta

      Ina adon gyara fussskata

      Na sanya kwallin idaniyata

      Na fesa ƙamshi ga suttura ta....

     Rabbi kare min mijina!!!


Rabbi amsa min kira na!!!

Rabbi kare min mijina!!!


2. Ni a guna sam bai da tamka

Duk sirrikana shi zasu riska

Da nay fushi, in yazo na sauka

Hidimtakarsa ke sani kuka

      Ya abin so farin cikina

       Na mallaka maka dukka kaina

       Ina ƙaunar ka dare da Rana

      Ina yawan sonka sahibiyna...

Abin kirana farin ciki naaaa!!!


Rabbi kare min mijinaaa

Abin kirana farin ciki naaa


3.  Yau da kullum na ayyukansa

Hawa da sauka a lamurransa

Yana cikin sauke haƙƙunan sa

Yana yawan bani lokacin sa

      Shi ya sanya nake ta son sa

      Ina ta Rama don ambaton sa

       Ina shirin kare lafiyar sa

       Ina nufin na zama garkuwar sa...

Haba masoyi ka ceci raina!!!

Rabbi amsa min kira na!!!

Rabbi kare min mijina!!!


4.   Son ka ya keta zuciya ta

   Yayi cafkar idaniya ta

   Yana ta yawo a jijiya ta

   Son ka shineee Rayuwa ta

       Zan biyayya a lamuranka

       Zan yi tamkar Sa ɗakar ka

       Zan duƙursawa zantukan ka

       Zani girmama ƴanuwan ka...

Ni ina sonka ya miji na..


Rabbi kare min mijina

Abin kira na Farin cikina 


5.     Shine mijina farin ciki na

Shine yake gyara laifuka na

 Shine yake saita lammura na

 Shine yake ɓoye kuskure na

      Bautar sa Bautar Ubangiji ne

      Fushin sa wannan abin gudu ne

       Ka ɓata rai ko nayo kure ne

        Haba masoyi, rashin sani ne..

 Ka ceci raina, ya kai mijina!!!


Ni ina son masoyiyata

Son ki ke mulka zuciya ta.

haƙƙin mallaka @Sadiq Tukur Gwarzo

Sunday, 30 January 2022

MUYI KOKARIN KARE KAWUNAN MU DAGA RIBA

 MUYI ƘOƘARIN NESANTA KANMU DAGA RIYA, ƘARAMAR SHIRKA. 

   Allah Ta'ala ya umarci masu imani a cikin littafin sa Alqur'ani da cewa su bauta masa, kada kuma su haɗa wannan bauta da ta waninsa. Harma ya kira aikata haɗa bautar Sa maɗaukakin Sarki da ta wanin sa a matsayin zalunci wanda yake abu maigirma. 

  Annabi Muhammad (s.a.w) ya bayyana Riya a matsayin shirka wadda take ƙarama, wadda kuma Allah ba ya amsar aiki komai kyawunsa matsawar akwai ta a ciki.

 Malamai sun fassara riya a matsayin 'yin abu don neman yardar mutane, ba don neman yardar Allah ba'. 

   Shin yardar Allah muke nema ko ta murane a ayyukan da muke aikatawa? 

   Mallam Umar Sani fagge yayi tsokaci akan haka, inda yace "Idan kana so ka auna cewa akwai Riya acikin aiyukanka, to kayi duba acikin waɗannan abubuwan guda biyu;

   1. Na farko, Ibadar Ka.

Mallam yace, ka auna Sallar ka da sauran ibadun da kake yi duka, idan har ka samu cewa kana yin su da kyau acikin/gaban jama'a sama da yadda  kake yinsu kai kaɗai, haƙiƙa kana aikata Riya; ƙaramar shirka. 

Mallam Ya ce "Ba ibada kadai ba, hatta sadaka, kyauta da sauran ayyukan alheri, indai kana fifita yinsu akan idon jama'a don jama'ar suyi maka shaidar kai mai aikata aiyukan alheri ne, a bayan idonsu kuma ba ka yi, haƙiƙa kana aikata Riya. "

A ranar alqiyama kuma Allah zai tozartar da duk mai aikata Riya, Allah Ta'ala zaice masa 'kayi abu kaza da abu kaza don mutane suce kayi, kuma sun faɗa, don haka baka da lada a wurina'. Daga nan sai mala'iku su kifa fuskar mai aikata Riya da qasa, su jashi izuwa wutar jahannama. (Allah yayi mana tsari da ita).

  2. Abu Na biyu: Rayuwar ka

Mallam Umar Sani Fagge ya labarta mana wata ƙissa, inda  yace "watarana wani mutum yana yawo, yana sanye da riga mai tsada, wadda farashinta zai tasarwa dirhami arba'in, sai Sayyadina Umar(R.A.) ya kirashi yake tambayar sa nawa ne jalin kasuwancin sa da har yake sanya irin wannan tufafi? Sai wannan mutumi yace Jalinsa yakai misalin dirhami dubu daya. Sai kuwa Sayyadina Umar (R.A) ya dakeshi da sanda, sannan yace "Amma kake sanya irin wannan tufafi saboda Riya?" Akace ana cikin haka kuma sai ga Sayyadina Abdurrahman bn auf (R.A) yazo wajen yana sanye da tufafi wadanda darajarsu takai ta durhami dubu hudu (Mallam yace sama da miliyan dari kenan a yanzu), amma Sayyidina Umar bai ce masa komai ba."

 Sai Mallam ya cigaba da cewa "dalilin haka shine, wannan mutumi mai jarin durhami dubu, idan aka ƙyaleshi yana sanya tufa kurum na durhami arba'in, watarana sai ya karya jalinsa da kansa, domin yana yin abinda matsayinsa bai kai ba, yin hakan kuma nau'I ne na Riya. Shikuwa sahabi Abdurrahman bn auf, Allah ya bashi mamakon dukiya, yana da ikon sanya tufafi masu tsada ba tare da ya girgiza ba".

 Don haka Mallam yace, "duk wanda yake ƙuƙutawa ya sayi wani abu, ko yayi wani abu sama da matsayin da Allah ya ajiye shi don gama da nuna isa, wannan Riya ne, Allah ba yaso, idan mai aikata haka kuma bai tuba ba, zai gamu da fushin Allah a ranar alqiyama". 

  Lallai Riya babban lamari ne da ya kamata mu yi ƙoƙarin kare ayyukan mu da shi. Lallai Allah Ta'ala ne mafi kyautatuwar miƙa lamura da kuma neman yarda daga gareshi ba sauran mutane ba. 

  A sani cewa duk wanda Allah Ta'ala ya so, kuma ya ƙaunata, to Mala'ikun sa masu tsarki zasu ƙaunace shi, hakanan  al'umma zata ƙaunace shi kamar yadda yazo a cikin Hadisi.

  Dafatan Allah ya kiyaye mu daga dukkan wani nau'I na Shirka. Amin. 

#Sadiq Tukur Gwarzo

Friday, 21 January 2022

WAƘAR NEMAN MAFITA DA RIBA BABBA

 1. Allah sarki ne mai yawaita

   Falala da tsari da kyauta

   Bismillah zan karanta

   Waƙar mafita da riba


2. Zamanin nan ya ƙazanta

Lamurra duk sun jirwanta

Ayyuka da halin mugunta

Ga cin amana bai tsaya ba.


   3.  Garkuwa don kuɗi da sata

     Ga yawan fyaɗe da ƙeta

     Ga rashin ladabin ƴammata

     Duk ba zai mana mafita ba.


4. Tur da sauyi maras nagarta

Mai ɗorawa mutum kurumta

Ayyukan sharri ko mugunta

Mance Allah ba zai mana ƙa'ida ba


5. Son kuɗi duk ya tsananta

Burin kowa ya huta

Da kuɗi mata da mota

Babu cas, ko as dat ta'abba.


6. Shiyasa ayyukan mugunta

Munana, masu raba zumunta

Ayyuka na rashin aminta

Sun yawaita ba ma huta ba.


7. Ga uwa ta saida ɗanta

Ga uba ya haiƙewa ƴar ta

Ga ɗa yay fansa da wauta

Ya subhanallahi ka tsare mu gaba


8. Ran Hanan dai ya salwanta

Malaminta ya ha'inta

Ya aikata abin mugunta

Aikin sa gareshi babu riba


9. Aisha mai kasshe kanta

Wani jami'i shi yai lahanta

Cin zarafi mai muni na mata

A zamanin nan ana yi ba da ƙa'ida ba


10. Shugabanni da halin mugunta

An sa talaka yana ragaita

Daɗin haraji, tsada, duk an azabta

Janye tallafin mai ba abune mai kyau ba

 

11. Masu tsafi kun ƙazanta

Masu caca kuna da wauta

Luɗu da cin zali duk sun haramta

Wanda duk bai bi Allah ba ba zai zauna lafiya ba


12. Yau fasadi ya inganta

Mai bin shaiɗan zai kafirta

Ayyukan sa duk sun muzanta

Annabin Allah ya hane mu da cin riba


13. Masu shirka sun yawaita

Masu kiran haram saboda wauta

Ayyukan gaskiya ya ƙaranta

Lalle masifa a duniya ba ta gushe ba


14. A yau ƙarya itace mai tsafta

Wasu ma sun ƙware akanta

Samun kuɗin su shine mafitta

Ai kuwa hakan ba abune mai kyau ba


15. Aikin ƴan ta'adda ya ƙazanta

Zubar jini a yankin mu ya yawaita

Asalinsu akwai cin hanci da ƙeta

Jami'ai masu cin amana ƙarshensu ba zaiyi kyau ba


16. Ƴan siyasa ya kuke ta

     Yaudarar talaka da sata

     Kun hana arziƙi ya wadata

  Kawunan ku kuke so ba talaka mai wahala ba


17. Ya kamata fa mu fahimta

Arziƙi ko da ya tsananta

Ko talauci in ya rabanta

Ga bawa ƙaddara ce wadda ba a guje ba


18. Tun gabannin yin halitta

Rabbuna Allah ya hukunta

Arziƙin ɗa, bawa ko jarrabta

Duk abinda mutum zai yi ba zai keta ƙa'ida ba


19. Yanzu menene mafitta?

     Ga zukata sun firgitta 

     Rashin natsuwa ya yawaita

 Duk abinda mutum zaiyi ba zai sake ba

20. Fahimtata a rayuwa ta

     Sai mun sauya jigon nagarta

    Sai mun rage raɗaɗen masu jinta

Sai muso juna da alheri banda gaba


21. Jama'ar mu akwai nagarta

A basu ilimi shi na fahimta

 Zai kawar da talauci mai kanta

Duk mai aiki da hikima ba zai sha wuya ba


22. Ilimi mai sa nagarta

   Mai gyara ayyuka da fahimta

   Jahilci kuwa idan yayi kanta

   Dole ayyukan jama'a ba zasuyi kyau ba


23. Tarbiyya ko mafi inganta

      Turbar Islama binta

      Ba fasadi babu cuta

   Komai aka mayar ga Allah ba zai zama mai wuya ba


24. Ladabi abu mai kyau ga mata

      Rufe tsiraicin su zusu kuɓuta

      Bin iyaye da magabata

     Barin fariya, yin ɗagawa abune ba mai kyau ga lahira ba


25. A koyar da yara jarumta

       Aiki tuƙuru shine za a huta

       Lalaci, sakaci ko sata

 Ayyuka ne haramtattu da ba za a yisu da ƙa'ida ba.


26. Mu kalli Japan, Sin da Kolkata

      Matasa na fafutika, kai hatta

     Yara ƙananu da mata

Kowa nason ceton ƙasarsa ba cutar da ita ba


27. Neman halak abune mai tsafta

      Mai gyara ƙasa da zukata

      Idan zukata suka ladabta

    Ayyukan bayi da dama ba zasu ƙetare ƙa'ida ba


28. Wajibi zalinci ya huta

      Adalci shi ake buƙata

      Tsayar da haddi ga masu gata

      Matsawar kuɗi suka rinjayi adalci ba zamu zauna lafiya ba


29. Ya Allah ka bamu mafitta

      Ya Rahmanu sarkin Nagarta

      Ya man iza da aka fa ajibta

    Ya Laɗiyfu ka yaye mana  rashin aminci da gaba


30. Ni Sadiq Gwarzo na yawaita

      Damuwa shiyasa na rubuta

      Waƙar ina kewa da buƙata

    Ina adduar samun tsira da rabo babba.

ALHAMDULLAHI

      










Thursday, 13 January 2022

CIN ZARAFIN ƘANANUN YARA DA KARIYA A BISA HAKA

 CIN ZARAFIN ƘANANUN YARA DA KARIYA A BISA HAKA


SADIQ TUKUR GWARZO

GABATARWA

'Child maltreatment':- Cin zarafin ƙananun yara na nufin cutarwa ko wofantarwa da ake yiwa yara ƴan ƙasa da shekaru 18. Hukumar lafiya ta duniya   WHO ta sanar da cewa a duk faɗin duniya, kimanin yara biliyan 1 ne suka fuskanci cutarwa ta taɓuwar lafiyar jiki, ko ta ɓangaren jima'i ko kuma ta ɓangaren damuwa mai jiɓi da ƙwaƙwalwa. Wannan na nufin, rabin yara masu shekaru 2-17 dake rayuwa a wannan duniyar tamu sun haɗu da wancan tasgaron. Lallai wannan abin tashin hankali ne. Don haka ne yake da matuƙar muhimmanci a gare mu manya mu ɗauki mataki a game dashi.

   Kawar da cutarwa da wofantarwar  da ake yiwa yara haƙƙi ne da ya shafi al'umma baki ɗaya, saboda haka ya kamata ace mutane daga rukunan al'umma mabanbanta sun fahimci matsalolin dake tattare da cutar da ƙananun yara tare da ɗaukar matakai don daƙile aukuwar hakan.

  BAYANAI NA GASKIYA GAME DA CIN ZARAFIN YARA

Bisa haƙƙaƙewar ƙungiyar ISPCAN (International Society for the Prevention of Child Abuse and Neglect), hujjoji na ƙara ƙamari masu nuni da cewar wofantarwa gami da cutarwar da ake yiwa ƙananun yara ne silar aukuwar rabin matsalolin da al'ummar mu ke fuskanta a halin yanzu.

Cin zarafin ƙananun yara laifi ne, kuma saɓa dokar kundin tsarin mulkin Nigeria ne, kamar yadda yazo a;- Chapter 21: Offences against morality"  Criminal Code Act, Chapter 77, Laws of the Federation of Nigeria 1990. Retrieved 2 April 2016.

Haka nan, rahoton binciken ƙasashen duniya ya bayyana cewa kusan a duk yara 4 masu shekaru tsakanin 2-4, ana samun yara 3 waɗanda suka fuskanci azabtarwa ta jiki da/ko cusa musu damuwa daga ɓangaren iyaye ko masu reno, haka kuma ana samun a duk  mace 1 a cikin mata 5, da namiji 1 a cikin maza 13 cewa sun miƙa koken an ci zarafin su ta ɓangaren jima'i a lokacin da suke yara.   

MATSALOLIN DA CIN ZARAFIN KANANUN YARA KE HAIFARWA A YAN-KUNAN MU

Matsalolin da cin zarafin yara ƙananu ke haifarwa suna da tarin yawa, kamar yadda a baya muka kawo rahoton binciken kungiyar WHO cewa kusan rabin matsalolin al'ummar mu na da tushe ne daga cin zarafin ƙananun yara, wanda hakan ke nuni da cewa matsawar zamu tashi tsaye wajen kawar da waɗannan matsaloli to kuwa tabbas yawaitar rashin zama lafiya da ƙananun laifuffuka har ma da manya zasu ragu matuƙa a garuruwan mu.

NAU'IKAN CIN ZARAFI

Nauikan kashi huɗu ne, amma suna da rukunai ko yanayai da dama.

1. Cin zarafin yaro ta hanyar cutar da lafiyarsa

2. Cin zarafin yaro ta hanyar jima'i. Wannan ya danganci wasa ko cusa wa yaro wani abu na al'aura ko makamancin sa a al'aurar sa, da kuma ɗaukar hoton al'aurar ko sanya yaro yin wasa da ita.

3. Cin zarafin yaro ta hanyar cusa masa damuwa

4. Wofantarwa; watau rashin sauke wani nauyi na yaro da ya rataya akan wani mutum.

YADDA ZA A KAWO KARSHEN CIN ZARAFIN KANANUN YARA

YA KAMATA MU SOMA MAGANTUWA: Cin zarafin ƙananun yara kan faru cikin sirri, don haka muna da buƙatar samar da kyakkyawar hanyar jan ra'ayin al'ummar mu su soma magantuwa akai domin wannan batu ne wanda mutane ba kasafai suke jin daɗin tattauna shi ba.

  Don haka muna da buƙatar sanya abubuwa da dama domin gina 'shingayen kariya' (safety nets) a cikin mazaɓun mu.

Matakan bi domin kare cin zarafi sune:-

1. Ilimantar da al'umma

A. Koyawa alummar mu alamomi na kai tsaye da suke nuni da cin zarafi ga ƙananun yara.  

B. Ilimantar da Malamai

Malamai kan iya zamowa bangon samun rabauta jallin-jal wajen kawar da cin zarafin ƙananun yara idan har ya kasance malaman sun fahimci abin sosai tare kuma da basu tallafi na musamman.

C. Ilimantar da Yara

Ƙananun yara basu da buƙatar sanin cikakken bayani game da cin zarafi, to amma akwai buƙatar koyar da su sauƙaƙan dokokin kare kai daga haɗuwa da cin zarafi, misali ya kamata a koyar da yara cewa :-

-Babu wanda zai kasance yana cutar dani

-Babu wanda zai taɓa min al'aura

-Babu wanda zai ɗauki hoton al'aura ta.

- Idan ina da wata matsala, zan sanar da ita ga wani na

-Kada na bar duk wata cutarwa da wani ke yi mini a matsayin sirri musamman wadda ta shafi taɓa al'aura ta.

-Na sanar da wani/wata idan wani na ƙoƙarin haiƙe mini

2. DOKOKI

  Wajibi ne masu zartar da dokoki su samar da doka mai ƙwari da hukunci mai raɗaɗi ga duk wanda aka samu da laifin cin zarafin ƙananun yara. Wannan shine babban mashinfiɗi da zamu samar domin kawar da duk wata barazana mainfuskantar manyan gobe.

Mun samar da kwas na musamman game da cin zarafi a kwalejin Hausa ta yanar gizo mai suna AAGHOLI. Ana iya ɗaukar cikakken kwas ɗin a kyauta ra nan hanyar:- https://aagli.com.ng/courses/child-maltreatment-and-prevention/

Friday, 7 January 2022

FALALAR MALAMAI DA TA'AZIYYAR MASANI SHEHU AHMADU BAMBA (Qala Haddasana)

 FALALAR MALAMAI DA TA'AZIYYAR MASANI SHEHU AHMADU BAMBA (Qala Haddasana)


SADIQ TUKUR GWARZO


Sahabi Aliyu R.A ya faɗa ga Jabir ɗan Abdullahi R.A cewa "Duniya ta dogara ne akan abu huɗu; Addini, da Malami, da Mai yin aiki da ilimin sa sai Jahili wanda baya girman kai wajen neman sani, da kuma Mawadaci wanda baya rowa da dukiyar sa.

  Marigayi Sheikh Dr.  Ahmad Bamba ya faɗa mana cewa ilimi ba komai bane sai sanin abu a zuciya da kuma gaskatar sa a zahiri, yayin da jahilci ke nuni da kiyaye abu a zuciya wanda a zahirance ba gaskiya bane. Saboda haka a  cewar sa ba kawai rashin sanin abu ake kira jahilci ba, a'a har ma da sani gami da riƙo na abinda bai gaskata ba. 

  Rayuwa irin ta Dr Ahmad madubi ce ga ɗaukacin al'ummar musulmi. 

  Shi mutum ne mai kyakkyawar fahimta ga lamurran addini, amma mai zafafawa wajen kare martaba irin ta Annabi Muhammad s.a.w

Mai kimanin shekaru 82 da haihuwa, wanda ya rasu ayau Jummu'a 7/1/2021, Marigayi Dr Ahmad Bamba ya shafe ɗaukacin rayuwar sa wajen nema da kuma bayar da sani. Ya shafe sama da shekaru 20 yana ɗaukar darasi a Madina, masallacin Annabi Muhammad s.a.w. Sannan ya fassara Littafin Muwaɗɗa wallafar Imamuna Maliku ɗan Anas daga harshen larabci zuwa harshen Hausa, baya da karantarwar sa ga manyan littattafai irin su Sahih Bukhari, Sahih Muslim, Sunnani Darimi, da makamantan su duk acikin harshen Hausa. Tabbas, rasuwar sa babbar asara ce ga kafatanin al'ummar musulmi musamman Hausawa.

  Ya zo a cikin littafin 'Al ilmu Huwal Imamu' na Shekh Ibrahim Nyasi cewa Hanyar aljanna ta na hannun mutane guda huɗu; Malami, da mai gudun duniya da mai ibada da kuma mai jihadi fi sabilillahi. Shi Malami idan ya kasance mai gaskiya ne cikin zuciyar sa, tabbas Allah zai azurta shi da Hikima. Duk kuwa wanda aka baiwa Hikima alal haƙiƙa an bashi gagarumar baiwa anan duniya da gobe lahira kamar yadda yadda yazo a cikin littafin Allah Alqurani.

  An tambayi Ɗan Mubarak cewa suwanene mutane?, sai yace 'Malamai', sai aka ce masa su wanene sarakuna? sai yace masu gudun duniya, sai akace su wanene kaskantattu?, sai yace masu cin duniya da addini. Don haka, ana iya cewa lallai malamai mutane ne masu daraja a cikin al'umma.

   Abdul-Aswad yana cewa babu wani abu wanda yafi Ilimi ɗaukaka. Sarakuna masu yin hukunci ne ga jama'a, yayin da Malamai ke yin hukunci a garesu.

AHNAF R.A yana cewa Malamai sun kusa kasancewa iyayen giji.. dukkan ɗaukakar da ba a ƙarfafe ta da ilimi ba, ƙarshen ta ƙasƙanci ce.

Annabi Muhammad s.a.w ya faɗa cewa "Malamai, sune magada Annabawa" (Tirmizi, Abu Dawood da Ibn Maja duknsun ruwaito shi)

Allah Ta'ala kuwa ya faɗa cewa "Iyaka dai masu jin tsoron Allah sune Malamai" (Suratul Fathi, 28).

  Babu buƙatar zafafa yabo ga marigayi Mallam Ahmad Bamba, domin shi ba mai son yabo ko kwarzantawa bane a zamanin ratuwar sa, amma shine wanda ya jaddada Sunnah a ƙasar Hausa bayan da ta ɗauko dusashewa, shi mutum ne wanda yake son Allah da Manzon sa, wanda yake tarbiyantar zukatan bayin Allah akan bautar Allah ta tsanin manzon sa Annabi Muhammad s.a.w da mayar da lamurra a gareshi, kuma mutum ne maras kwaɗayi, mai darrajanta ilimi da darrajanta kansa, gami da faɗar gaskiya walau ga shuwagabanni ko ga mabiyansu.

Allahu Akbar, shi mutum ne mai daraja a duniyar musulunci, tushen darajar sa kuwa bai wuce ga riƙon sa ga sunnar Annabi Muhammad s.a.w ba, da tsantsenin sa kai kace shine Imam Maliku bn Anas ko Imam Hasanul Basri. Hakika, rayuwar sa ta kasance abar koyi ga al'ummar musulmi.

  Wani sashen masana sun faɗa cewa An fifita Imam Hasanul Basri akan sauran Tabi'ai, saboda abubuwa guda 5;-

1. Baya umarni da aikata wani aiki face ya fara aikatawa.

2. Baya hanuwa ga barin wani aiki face ya fara hanuwa daga gareshi.

3. Duk wanda ya nemi wani abu daga abinda Allah ya hore masa zai bashi.

4. Ya kasance tana wadatuwa da ilimin sa ga barin neman wani abu a wajen mutane.

5. Ya kasance ciki da wajen sa duk ɗaya ne.

 Tabbas, duk waɗannan siffofi guda biyar sun tabbata ga Marigayi Shekh Ahmad Ibrahim Bamba. Gashi kuma ya samu cikawa irin tasa.. da fatan Allah ya rahamshe su duka amin.

Abdullah bin ‘Amr Ibnul ‘Ash ya ruwaito daga Annabi Muhammad s.a.w cewa "Lalle, Allah baya ɗauke ilimi daga hanawar sa ga bayin sa. Sai dai yana ɗauke ilimi ne daga mutuwar malamai ta yadda tsarkakan mutane zasu gushe, sai mutane su naɗa wawayen mutane a shugabanci. Sannan idan aka tambaye su, sai suyi magana ba da ilimi ba. Sai su taɓe kuma suyi asara.” ( Al-Bukhari da Muslim suka ruwaito).

    Kaicho da rashin babban masani Dr Ahmad Bamba, to amma ya kamata kowa ya sani wannan duniya ba abar dawwama bace. Tabbas, kowanne mai rai zai ɗanɗana mutuwa. Kuma tabbas, yadda Dr Ahmad ya koma ga mahaliccin sa, kowannen mu lokaci yake jira domin komawa zuwa ga Allah. Don haka ya kamata mu shagaltu wajen aiki da koyarwarsa, da neman ilimi, da bin Allah da kuma neman dacewar Allah da samun Aljanna.

  Dafatan Allah ya gafartawa Dr Ahmad Ibrahim Bamba, Allah ya tallafi bayan sa amin.

Monday, 3 January 2022

ASALIN KISHI

 ASALIN KISHI


Daga Sadiq Tukur Gwarzo


GABATARWA

  A shekarar 2013, wani rahoton binciken masana da Farfesa Daniel Freeman na Jamiar Oxford tare da marubuci Jason Freeman suka wallafa a jaridar 'The Guardian' ta ƙasar Amurka, mai taken 'Jeolousy: It's in your gene', ya nuna cewa kishi gadajjen abu ne wanda kowanne ɗan adam ke tare da shi a cikin ƙwayoyin halittar sa. Binciken da masana suka gudanar  ya nuna cewa mata sun fi bayyana kishi sama da maza, wannan kuwa a kimiyyance muna iya danganta shi da yanayin mutumtakar jinsinan biyu wajen jure yanayai na zuciya da ɗaukar matakai a game dasu.

Mujallar BBC Science Focus ta taɓa yin nazari game da dambarwar masana akan 'shin kishi abu ne da ɗan adam yayo gadon sa ko wanda ya koya bisa zamantakewar sa a muhallin sa?'. Shine har suka kawo hujjojin kowanne ɓangare, ciki har da masu kallon yadda wasu sarakuna a zamanin baya su ke baiwa baƙinsu matayen su don su tara da su, da yadda wasu ke faɗin cewa basu taɓa jin kishi game da abokan tarayyar jima'in su ba, sai dai bisa la'akari da hujjojin masu cewa 'gadon kishi ɗan adam yayi', waɗanda suka haɗa da yadda maza a mafi yawan lokuta suke son kyakkyawar mace (satirical theory) mai jiki sama da sauran mata, da yadda wannan soyayyar ta maza kan haifarwa da mata daraja musamman daga ƴaƴayen da dangantakar ta samar musu saboda tarawar jima'i, sai ya zamana wajibi ga mata su fi buƙatuwar samun kaɗaitacciyar dangantaka wadda zata basu ƴaƴaye, wanda hakan kan tilasta jikkunan su samar da ƙwayoyin halittun da zasu fi son wanzuwar su kaɗaitattu ababen so a wurin abokanan zaman su (maza).  Wannan ne silar samuwar kishi a ɓangaren mata, wanda kan faru da zarar mace ta hangi yiwuwar faruwar wani abu wanda zai iya dakushe mata wancan muradi nata da tayi gado daga ƙwayoyin halittu. 

Sai kuma yadda aka lura da samun ɓurɓushin kishi daga wasu dabbobi misalin Gibbon waɗanda dangantakar su ta ƙwayoyin halittu ke tuƙewa da ɗan adam, don haka aka fi danganta kishi ga 'Natural Selection', watau watsuwar ƙwayoyin halittu.

  Ƙarin hujja akan haka shine yadda a baya-bayan nan wani rahoton bincike ya tabbatar da cewa kishi shine silar da yara ƙananu ke yawan kuka/rikici da dare domin kange mahaifansu daga tarawa wadda zata kai su ga samar musu da ƙani ko ƙanwa, da kuma yadda yara ke ƙara yawaita rikici bayan mahaifiyar su ta sake haihuwa.

Mutane da yawa da zarar an ambaci kishi sun fi danganta shi a tsakanin ma'aurata, musamman tsakanin kishiyoyi, amma a zahiri kishi ya wuce haka. Don haka a taƙaice, wannan ɗan rubutu zai kalli wasu daga taƙaitattun zantuka game da asalin kishi a kimiyyance da tasirin sa gami da yadda ya kamata a tunkare shi.

MA'ANAR KISHI

Masana da dama sun fassara ma'anar kalmar kishi gwargwadon fahimtar su, amma bisa tamu fahimtar, kishi na nufin wani yanayi na zuciya wanda yake cike da tsoro da firgici da tsana da ƙyamata, wanda ya ke bijirowa a duk sa'ar da wani ya fahimci samuwar wani abu mai barazana ga darajar sa ko matsayin sa, ko damar sa, ko mabiyan sa ko wani abu muhimmi da yake tutiya da shi.

ASALIN KISHI

Ko da yake, masani mai bincike Emanuel Eisner ya faɗi cewa ƙwayoyin halittar mu kusan ɗaya suke da na kakannin mu waɗanda suka rayu kimanin shekaru 600 da suka gabata, amma haɓakar yanayin kishi a zuciyoyin mu yana da alaƙa da sauyawar abubuwan da suka rinƙa faruwa ga ɗaukacin jikkunan mu na tsawon waɗancan shekaru, wanda hakan ke nufin cewa akwai ɗaukacin banbanci a tsakanin abinda mutumin yanzu zai yi kishi akansa da na mutumin da ya rayu shekaru 600 baya, wannan ya samu ne daga sauyawar muhallai, da buƙatu da muradun mu ne, amma kuma ɗaukacin jigon kishin sam-sam bai sauya ba.

Masani Aaron Sell na jamiar Griffith da ke Australia, ya yi nazari akan asalin kishi, inda har ya gano kishi ne silar aikatuwar wasu munanan laifuka da rashin zama lafiya irin wanda ake fama da su a halin yanzu. 

Misali akan haka shine KISA. 

Kimanin kashi 90% na kashe-kashe da ake yi a wannan duniyar maza ke aikata su, amma an lura da cewa mata ne akan gaba wajen kashe ƙananun yara (Infanticide) da kuma abokanan auratayyar su (spousal homicide).

Mu kalli Spousal Homicide: Wananan kalma na nufin yanayin kisan kai da kan faru tsakanin ma'aurata, walau miji ya kashe matar sa, ko mata ta kashe mijinta. 

Bincike ya tabbatar da cewa mata aka fi samu da kashe mazajen su.

Haka nan, Bincike ya nuna cewa sama da dubunnan shekaru, mazajen da suka rayu a wannan duniyar suna cike da kishin matayen su, don haka sun kasance cike da kokari wajen ganin sun mallaki akalar matayen su, watau sun kange su daga tarayyar da basa so. Wasu mazan kan yi haka ta hanyar tsoratarwa, ko nuna ƙarfi ga mata waɗanda akasari sune a ƙarƙashin su, wannan ya sa har zuwa yanzu akan samu yanayan da namiji zai saki mace, sannan ya bi sabon mijin da ta aura ya kashe ko ya yiwa lahani, saboda ya sake ta ne cikin fushi, yana mai burin ta shiga wani yanayi wanda zai sa ta yin nadamar rabuwa da shi ba don baya son ta ba, amma da zarar ya ganta cikin yanayi mai daɗi saɓanin yadda yayi muradi, sai kishi ya taso masa, wanda a wasu lokutan ya kan zama silar aikata munanan ayyuka.

 Su kuwa mata kasancewar su raunana ga maza, sai suka fi amfani da kisa a ɓangaren su wajen gudanar da nasu kishin na kange mazajen su daga tarayyar jima'in da ba sa so. Duk da cewa an lura da cewar mata masu ƙarancin shekaru kuma waɗanda basu haihu da yawa ba ne suka fi aikata hakan, amma sau tari ɓacin ran da ke tunkuɗa su aikata wannan mummunan aiki daga gundarin kishi ya ke.

Mai bincike Anne Campbel ta gudanar da cikkaken bincike game da silar rikicin mata, abinda ta tafi akai shine mata sun ɗora rayuwar su kachokan ne akan maza (uba, ɗan uwa, miji da sauran su), don haka matsawar mace tana da namijin da zai mata yaƙi, ba za a ganta cikin rikici ba. Saboda haka ana iya cewa babban abinda ke tunkuɗa mata aikata wancan ta'addancin na kashe mazajensu bai wuce yadda suke ɗaukar tozarci ne a gare su idan har suka samu raguwar daraja ko kawar da kai daga wanda suka ɗorawa so da aminci a garesu, don haka sukan gwammace halaka mazajen su duk a cikin kishi.

Amma a game da kisan ƙananun yara da mata kan yi (infanticide), shahararrun masanan nan Martin Daly da Margo Wilson sun yi bincike akai, inda suka bayyana cewa samuwar kishiyar uwa a gida na sanya yaro cikin haɗarin fuskantar kisa a ƙalla da kashi saba'in, da kuma haɗarin fuskantar cin zarafi da kashi 40. Wannan ma duk kai tsaye ana iya cewa daga kishi ne wanda ke faruwa a tsakanin matan gida wanda kuma yake shafar yaran.

Don haka, a ƙarshen binciken Masani Aaron ya tafi akan cewa ɗan adam bai ginu da ƙwayoyin halittun yin kisa don kange wanda yake so daga wata tarayya da ta saɓawa son zuciyar sa ba, sai dai kisan ya kasance a matsayin makami da wasu yanayai munana na zuciya kan tunkuɗa wasu mutane su yi riƙo da shi gwargwadon juriyar su ga wutar kishin da ke ruruwa a zukatan su. Wannan kuwa yanayi akan same shi a sauran sassan rayuwa ba ga auratayya ba kaɗai.

Haka nan, masana sun kalli yawaitar tashe-tashen hankula tare da danganta su da kishi, wanda yake faruwa sabili da tarayya akan abu guda da wasu mutane ke son mallaka, ko kaɗaituwa da shi da makamantan irin haka, don haka duk wanda ya ga akwai yiwuwar ya rasa wata martaba da yake tinƙaho da ita ko wani na son tarayya da shi ko kuma wani ya hau turbar fifita a wani lamari sama da nashi, sai kawai yayi martani da ayyuka waɗanda suka saɓawa hankali. Akwai irin waɗannan abubuwa da yawa a cikin kasuwanci, siyasa, malantaka da sauran lamurori na zamantakewar al'umma.

  Akwai ƙarin hujjoji masu nuni da cewa kishi daɗaɗɗen abu ne da ke cikin jini wanda yake yawatawa a jijiyoyin ɗan adam, daga misali shine kisan farko da ɗan adam ya soma aikatawa a duniya, watau tsakanin Ƙabila da Habila (Cain da Able), da kuma yadda yazo a tarihi wurare daban daban inda ɗanuwa ya kashe ɗanuwansa bisa wani dalili mai tuƙewa da kishi.

  Susan Dudley, masaniya ce mai bincike, ta gudanar da wani bincike dangane da wasu tsirrai (American sea rocket) wanda ya ƙara mana fahimra a game da asalin kishi.

  Susan ta ware wasu tukwane guda biyu ne, sannan a tukunya ta ɗaya ta shuka jinsin tsirrai guda guda biyu ƴan uwan juna, a tukunya ta biyu kuwa sai ta shuka mabanbantan jinsinan tsirrai. Bayan tsawon lokaci sai ta samu cewa tsirran da aka shuka a tukunyar da ke ɗauke da mabanbantan tsirrai sunfi saurin girma fiye da ɗayar. Wannan na nuna cewa akwai kishi har a tsakanin tsirrai, domin gashi tsirran da suke da alaƙa da juna sun hana junan su girma yadda ya kamata. Wannan fa ya faru ne a tsakanin tsirrai wanda kowa ya sani kashi 25 zuwa 30 na ƙwayoyin halittar su ɗaya yake da na bil'adama. Ina ga shi jansa ɗan adam? 

Don haka fahimtar ainihin yadda kishi ya samo asali na da buƙatar dogon nazari mai tuƙewa da asalin samuwar ɗan adam, amma dai a mafi rinjaye, ƙwayoyin halittar ɗan adam ne ke ɗauke da shi.

A INA AKE SAMUN KISHI

An fi samun kishi a tsakanin abubuwa biyu masu alaƙa da juna.

 Misali, mutum ya fi kishi da mutum, dabba ta fi kishi da dabba, haka ma tsirrai sun fi yi a tsakanin su.

  Haka kuma, ko a cikin mutane, yawan zurfin alaƙa ke nuni da yiwuwar samun zuzzurfan kishi. Ko kuma ace, kishi ya fi samuwa a tsakanin wasu mutane da suke tarayya da wani abu, misalin jinsi, ƙabila, harshe, gari ɗaya ko ƙasa ɗaya, ko ƴanuwa da abokanai, ko a tsakanin wasu rukunin al'umma masu aiki ko sana'a iri ɗaya, da dai makamantan su.

Don haka za a ga cewa mace ta fi kishi da mace ƴaruwarta sama da namiji. Haka kuma sau tari, Bahaushe ya fi jin kishi ga abinda ya shafi ɗanuwan sa Bahaushe. A wani yanayin ma akan samu cewa mutum ya fi samun maƙiya daga ƴanuwan sa na jini . 

AMFANIN KISHI

  Masana sun kalli tasirin kishi, sun kuma tabbatar da cewa abu kamar sa wanda ya daɗe a duniya yana ta bibiyar ƙwayoyin halittar ɗan adam ba zai taɓa kasancewa mara amfani ba. Babban amfanin da aka fi dangantawa kishi shine; ankararwa da kuma zaburarwa domin tashi tsaye bisa naƙasun da akan iya haɗuwa da shi a lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Don haka, ɗan kasuwar da ya fahimci yiwuwar wani abokin kasuwancin sa zai danne shi a fannin kasuwanci, zai ji kishi a zuciyar sa, wanda hakan na nufin ya zaburar da shi domin fahimta gami da gyara abubuwa na kuskure da yake aikatawa gami da ɗorarwa akan ayyukan da zasu ƙara riƙe masa martaba a kasuwancin sa. Irin haka ne ga kishiya ta aure, ko malanta, ko ta duk wani abu da kishi kan iya bijirowa a cikin sa.

  Saboda haka kyakkyawan kishi abu ne da aka lura da cewa zai iya samar da cigaba ga mutane ko ga yankuna ko ga duk wani abu da ake kishi akan sa matsawar an yi amfani da shi bisa tsari kyakkyawa yadda ya kamata.

ILLAR KISHI

Mutane da yawa suna faɗawa cikin munanan ayyuka sabili da kishi. Wani kan kashe wanda yake kishi dashi, ko ya bi wasu hanyoyi da yake gani zai iya  wargaza lamurran abokin kishin sa. Wanda akan haka, wasu kan rasa rayuwar su, ko matsayi ko darajar su ko imanin su da Allah maɗaukakin sarki. Wasu ma na tsintar kawunan su a kurkuku ko a wani yanayi mara daɗi tun anan duniya duk bisa mummunan aikin da aka aikata saboda kishi.

  Babban illar kishi ga ɗan adam shine; hana girma ko haɓaka.

   Sau tari, mummunan kishi ne silar durƙushewa da rashin cigaban al'umma. Shine kuma kan zama silar yawaitar munanan ayyuka da rashin zama lafiya.

MAFITA GAME DA KISHI

Yana da kyau a sani cewa babu wani ɗan adam da ba ya jin kishi matsawar yana da lafiyar ƙwaƙwalwa. Sannan babu wata ni'ima ko fifiko da Allah zai yi ga wani ko wata wadda ba zata sanya kishi a zukatan mutane musamman masu wani abu iri ɗaya da shi ba. Mafitar ɗaya ce; a mayar da dukkan lamurra ga Allah.

Masani Berit Brogard yana da dabarar  'normalism the feelings' wajen kashe mummunan kishi, watau ɗaukar irin waɗannan yanayai a matsayin abu gama gari wanda bai kamata a tayar da hankali akan sa ba. 

Don haka da zarar tunanin sa ya bijirar masa da wani abu na kishi, sai ya kwantarwa da zuciyar sa hankali, ya faɗa mata wannan abin fa 'is normal' ba abu ne mai buƙatar ɗaga hankali ba.

 Sanin kowa ne cewa kowanne ɗan adam yana da ƙaddarar sa, wani mai kyau wani mara kyau. Don haka, sunnar rayuwa ce irin abin nan da ake cewa 'yau gareka gobe ga wanin ka'. Watau komai na tafiya da lokaci. Idan yanzu kai ne ke sharafi, to ai a baya ba kai bane, don haka nan gaba ma wani ne zai yi ba kai ba.

Abu na gaba shine buƙatar rage abinda masana ke kira 'endowment effect', watau yanayai da kan sa mutum ya ji cewa shi kaɗai ya isa da abu kaza ko jin cewa abu kaza mallakin sa ne shi kaɗai tilo, kamar yadda aka fi samu a tsakanin ma'aurata. 

Ya kamata mace ta sani cewar an halartawa namiji ƙarin aure a duk sanda ya samu sukuni, haka shima namiji ya sani cewar mace na da damar samun annushuwa da wanin sa idan ƙaddarar rabuwa ta auku a auratayyar su.

Kuma ya kamata kishi ya zamo silar zaburar da mutane aikata kyakkyawan ayyuka ba munana ba.

Sannan mutum ya ɗora faruwar lamurra dukkan su ga Allah maɗaukakin sarki, walau ga kansa ko ga wanin sa.

Ƙarshen wannan muƙala kenan.

Ina mai adduar Allah ya jikan babban marubuci Alh Bashir Usman Tofa wanda aka yi jana'izar sa ayau litinin 2/1/2022.

Ga masu buƙatar ƙara samun sani gaɓe da wannan muƙala, akwai kwas mai taken 'Introduction to Mental Health' wanda muka samar kyauta a kwalejin Hausa ta yanar gizo mai suna AAGHOLI akan adireshin (https://www.aagli.com.ng)

Nine naku Sadiq Tukur Gwarzo (Public Health Nurse, mamba Global Goodwill Ambassadors)


  



I