Wednesday, 20 March 2019

HIKIMAR IYA MULKI

HIKIMAR IYA MULKI: LABARIN MADAKIN KANO MAHMUDU

Marigayi Mallam Aminu Kano ya ruwaito a littafinsa 'Hikayoyin Kaifafa Zukata' cewa:
   An bamu labari cewa a zamanin marigayi madakin Kano Mahmudu, talakawan wani ƙauye a ƙasar Bichi sun yi bore  bisa biyan haraji.
Bayan sun ƙi biyan harajin, har ma dagacin ƙauyen suka kora da jifa.
Lokacin da dagacin ya isa ga Hakimin Bichi, sai nan da nan Hakimi ya aike dogari da yaran hakimi don a binciko masa lamarin.
Ai kuwa dogari da yaran hakimi suma basu tsira ba, domin da zuwan su sai suka tarar mutanen garin sunyi shirin yaƙi mazansu da matansu, sun fito da karnukan su na farauta, suna masu riƙe da masu, kwari da baka da gatura. Don haka ba jimawa suka ranta a na kare zuwa gaban Hakimi.
Ganin abu ya kai haka sai hakimi ya aika zuwa ga Sarkin Kano. Daga nan kuwa aka sanar wa Razdan na kano.
  Shi Razdan bai yi wata-wata ba sai ya gayawa baturen ƴansanda cewa a tafi da shiri zuwa ƙauyen a kamo masu boren.
Amma da wannan magana ta dawo gaban Sarki, sai Madakin Kano Mahmudu ya yi wuf ya ce yana roƙon Sarki ya bashi dama ya soma zuwa da kansa kafin a je da ƴan sanda.
Da turawa suka ji wannan sai suka ce fau-fau haka ba zata yiwu ba. Tun da har mutanen sun ɗauko makamai, maganin su ƴan sanda masu bindiga.
Duk da haka, Madaki ya dage cewa yana roƙo a bari ya fara zuwa tun da shine Kansila mai kula da hakimai, haraji da sauran irin su. Kuma mutanen ƙauyen suna tare ne da matansu da ƴaƴansu duk a garin.
Da ƙyar dai turawa suka yarda ya je.
Ai kuwa da zuwan sa garin Bichi, sai ya aika ƙauyen da saƙo cewa Sarki ya aiko shi gare su, don haka yana so su taru dukkansu a cikin shirinsu, kada a rage kowa.
Kafin a ce mene ne wannan, mutanen sunyi cincirindo a bakin kasuwar ƙauyensu mazansu da matansu. Suna cike da fushin komai zai faru sai dai ya faru.
  Ba jimawa sai ga Madaki tare da Hakimin Bichi, da dagacin ƙauyen, da malaman hakimi sun ƙaraso wurin. Wuri yayi tsit ana sauraron aji saƙon Sarki.
   Sai Madaki yace "Jama'a Sarki ya gaishe ku, ya kuma ya gaishe ku. Ya ce in gaya muku cewa ya sami labarin abinda ya faru tsakanin ku da mai garinku wanda har abu ya kai da tashin hankali.
To kuyi sani, abinda Sarki yace in faɗa muku shine Sam bai taɓa cewa ku biya haraji ba. Saboda haka kun yi gaskiya da kuka ƙi biya."
Nan take wuri ya ɓarke da sowa ta godiya da cewa 'Allah ya bar Sarki, Allah ya bar Sarki'.
Sai Madaki ya cigaba da cewa "Amma abinda Sarki ya gaya wa mai garinku ya karɓa gare ku shine kuɗin arziƙi. Don haka ya turo ni in ware masu arziƙin cikin ku da matsiyatanku don mu sallami matsiyatan, masu arzikin su biya".
  Nan fa wuri yayi tsit. Sai wannan ya dubi wannan yace "yo waye zai yarda a kira shi matsiyaci?".
Daga can sai wani dattijo yace "Ranka ya daɗe duk cikin mu ba matsiyaci, saboda haka muna so mu je mu kawo".
Madaki ya basu lokaci aka tattaro harajin ƙauyen tsaf ba tare da anje da bindiga ba, wanda a wancan lokacin yawan harajin bai kai ya kawo ba.
Don haka Sahabi Mu'awiyya ya taɓa faɗawa ɗansa Yazidu cewa "Idan za ka biya buƙata da harshe, kada ka sa alƙalami. Idan kuwa da alƙalami ne, to kada ka sa takobi".

BARKWANCIN HAUSAWA

BARKWANCIN HAUSAWA

Acikin kowacce ƙabila a duniya, bayan tatsuniyoyi da karin magana da zambo da habaici, ana samun abubuwan da ake kira 'barkwanci'.
Shi Barkwanci ba batsa bane, ko ɓatanci ga wani. Ba kuma karin magana bane, kawai dai wata hikima ce mai ban sha'awa a tsakanin mutane.
Misali, idan mace tana da jika ɗa namiji, takan kira shi da suna 'mijina', shikuma yace 'matata'. Wannan barkwanci ne.
Ɗan mace da ɗan Namiji suna baiwa juna kuɗin shara a watan Muharram, wato watan cika ciki ko ace watan farkon shekarar hijiriyya. Wannan ma barkwanci ne.
Idan yaro ba ya jin magana, sai a kira shi da suna 'mai kunnen ƙashi'. Idan matar aure ta gamu da wani mai suna irin na mijinta ko ɗanta na fari, ba zata kira shi da sunan ba sai dai ta sakaya da wani sunan. Waɗannan duk barkwanci ne.
Haka ma ƴaƴaye basa faɗin sunan iyayensu saboda barkwanci.
Sannan idan mutum yaje baƙunta wuri, zaka ga baya cinye duk abinda aka kawo masa saboda barkwanci. Amma bayan ya kwana biyu a wajen sai ya rinƙa share abincin da aka kawo masa Kaf saboda barkwanci.
   Idan an tambayi marar lafiya 'yaya kaji da jiki?', sai kaji yace 'Mun gode Allah', ko yace 'da sauƙi', koda kuwa yana cikin tsananin ciwo ne. Wannan fa duk barkwanci ne.
Idan kuwa mutum ya samu wani abin alheri sai kaji yace 'kaga gamu dai' saboda barkwanci.
Watau dai, barkwanci a taƙaice hanya ce ta kyakkyawar tarbiyya mai sanya mutum yin dogaro ga Allah wajen faɗar abinda yake ciki, ko kuma ya nuna kunya da ladabi ga jama'a.
Haka kuma abu ne da yake koyar da jurewa wani abu kamar misali ciwo.
Don haka marigayi Mallam Aminu Kano (Allah yajiƙansa amin) yace ya kyautu a rinƙa koyar da barkwanci da sauran ɗabiu kyawawa na Hausawa a gida da makarantu don ɗorar da tarbiyya kyakkyawa ga yara masu tasowa. Rashin yin hakan kuwa shine zai sanya yara su tashi da son kallon sinimar iya sata ko kashe mutane ko wulaƙanta iyaye ko malamai ko sarakuna da dattijai da rashin tausayi, har kuma kaga sunyi zurfi wajen kwaikwayon raye-rayen batsa da ashariya da raina haƙƙi.

TARIHIN NUFE: KAFUWAR ƘASAR NUFE 4

TARIHIN NUFE: KAFUWAR ƘASAR NUFE
Kashi na huɗu
SADIQ TUKUR GWARZO
    Marubuci Buhari Daure ya ruwaito a littafinsa 'Tarihi da Al'adun Mutanen Najeriya' cewa kafuwar ƙasar Nufe ya wanzu a wajajen ƙarni na goma sha shidda ne. Inda yace asalin Nufe dana Igala ɗaya ne, sai wani ɗan sarkin masarautar Idah mai suna Tsoede yayi gudun hijira tare da kafa masarautar Nupe wadda ta haɗe ƙauyukan Beni, Bidda, Benu, Debo, Tafiya, Doka, Gaba, Dibo da Kupa.
Amma binciken Dr. Sidi Tiwugu Shehi ya kawo ra'ayoyin masana da yawa  saɓani da wannan.
Daga ciki akwai masu cewa asalin Nufawa zuriyar wani balarabe ne mai suna Uqba bn Nafiu wanda ya baro ƙasar su ta larabci tare da zama a ƙasar Nupe.
Wasu kuma suka ce Nufawa sun fito ne daga wani Mafarauci balaraben Misira mai suna Abdulaziz wanda ya gudo daga ƙasar sa ya sauka a Doko Dazi cikin ƙasar Nufe dashi da ahalinsa. Daga nan aka sanya musu suna 'Nefiu' da yaren ƙabilar Beni daya tarar, wanda ke nufin 'wanda ya gudo daga wani wuri' .
Sannu a hankali sai sunan ya sauya zuwa Nufe ko Nupe.
Wasu kuma sunce Asalin Nufawa daga ƙasashen Katsina, Kano da wasu makusanta suke. Har ma Clapperton yace sunan Sarkin su Tsoede, kuma sun zo ƙasar Nupe ne daga wani birni da ake kira Attah Gara.
   Shikuwa Ndagi Abdullahi ya tafi akan cewa Nufawa suna kakannin Hausawa, Yarabawa da Inyamirai. Inda yace zuriyar Nufawan ce ta fantsama tare da samar da waɗannan yaruka (ko ace ƙabilu)
Amma dai masani S.F Nadel ya raba Nufawa gida huɗu daga abinda ya kawo a littafinsa mai suna 'Social Symbiosis and Tribal Organisation'. Ga rukunan kamar haka:-
Rukuni na ɗaya sune Ndachezhi, watau Mafarauta kuma asalin mazauna ƙasar Nupe waɗanda akace suna zazzaune a ƙauyuka sama da shekaru dubu da suka gabata.
Rukuni na biyu sune Esozhi, suma asalin Nufawa ne waɗanda suka jima a ƙasar Nufe har ma suka  kafa birnin Kutigi.
Rukuni na uku sune Benu, waɗanda suka yo hijira daga ƙasar Bornu. Su kuwa da yawansu malaman addinin Islama ne da masu fatauci, daga baya ne suka samu ikon wasu yankunan Kutigi.
Sai Rukuni na huɗu waɗanda ake kira Konu, waɗanda asalinsu bayi ne da aka kamo wurin yaƙi daga ƙasashen Yarabawa, daga baya aka ƴantar dasu tare da basu mazaunai a ƙasar Nupe.
Sannan binciken masana kimiyya da aka gudanar a yankunan Jebba, Giragu, Tada, Oyo-ile, Esie-oba da wasun su ya nuna cewar ƙasar Nupe tana ɗauke da mutane tun sama da shekaru 3000 zuwa dubu 10,000 kafin haihuwar Annabi Isah A.S.
Wannan yasa ake hasashen cewar asalin ƙabilun da suka rayu a wannan yanki wanda ya mamaye yankin Abuja da wasu yankunan tsakiyar Nigeria, sune suka haifar da ƙabilun Yarabawa, Inyamirai, Nupawa, Igala, Idoma, Ebira da Gbayi.

Friday, 8 March 2019

IKON ALLAH: HALITTAR ZANZARO

IKON ALLAH: HALITTUN GIDA DA NA DAJI
1. ZANZARO, ISHARA GA MAI LURA
  Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai.
A wannan makon cikin ikon Allah zamu buɗe wannan fili ne da nazarin hikimomin da Allah Ta'ala ya ajiye wa zanzaro.
  Babban abin mamaki ga zanzaro shine, kullum za ka ganshi su biyu tare da matarsa.
   Lokacin da matar ta kusa yin ƙwai, shi mijin ya sani, don haka za ka gan shi yana ta zirga-zirga.
Da farkon farawa sai ya sami wani wuri cikin ɗaki ya ɗebo ɗanyar ƙasa a ko'ina ne ya same ta, domin gina gida.
    To a cikin bakinsa akwai wani ruwa mai danƙo da yake shafawa ƙasar a lokacin da yake ginin.
   Za ka ga ya yi ginin nasa hawa-hawa har ya ƙare dai-dai yawan ƙwayayen da mai ɗakinsa za ta yi. Kuma daga cikin ɗakunan yana yin wata farar shimfiɗa mai taushi.
Daga yin wannan, sai ya sanar da matarsa. Ita kuma babu wata wata sai aga ta shiga zuba ƙwai.
Da zarar ta ƙare, sai ya je ya samo tsutsotsi masu rai ya zuba cikin ɗakunan.
 Wani babban abin mamakin ma shine, a bayan sa akwai wani abu mai tsini kwatankwacin allurar likita ɗan tsirit da shi.  Wanda acikin sa akwai wani ruwa daidai da ruwan allurar da likitoci ke yiwa marar lafiya yayin da za a gudanar masa da aikin tiyata, wadda take ɗauke masa raɗaɗi gami da sanya shi bacci.
Sai zanzaron yabi duk tsutsotsin nan yayi musu waɗannan allurori, sannan sai ya cusa su ɗakunan da matarsa ta zuba ƙwayayen ta.
Daga nan sai ya ɗebo sabuwar ƙasa ya liƙe ƙofar ɗakin ya yi tafiyar sa tare da matarsa.
Bayan wasu kwanaki kaɗan sai ƙwayayen nan su ƙyanƙyashe kansu, sannan su cinye naman tsutsotsin nan domin da ma ba su mutu ba balle su ruɓe su zamar musu cuta.
Ba da jimawa ba sai kaga jira-jiran zanzaro sun girma a wannan ɗaki mai matsatsi, sannan su yunƙura da ƙarfi wadda zata sa ɗakin ya fashe tare da ficewa daga cikin sa.
Wani abin ta'ajibin a nan shine, su waɗannan ƴaƴan zanzaro idan lokacin yin ƙwansu ya zo haka suma zasu yi duk kuwa da cewar ba su tarar da iyayen su ba balle ace a wajen su suka koya.
Sannan, yadda namijin zanzaro ke yiwa matarsa hidima shima abin koyi ne matuƙa ga dukkan ɗan Adam.
Don haka lalle akwai hikimomi a tattare da wannan halitta ta ubangiji wadda idan mutum ya natsu ya gane, zai ƙara jin tsoron Allah gami da kiyaye haddodin sa, domin shi mai iko ne a kan komai.
An ciro ne daga Littafin HIKAYOYIN KAIFAFA ZUKATA NA 2 Wanda Mallam Aminu Kano ya rubuta.
Insha Allah, a wani makon zamu taɓa wata halittar ta da ban. 

TARIHIN NUFE: LABARIN SHEHU ABDURRAHMAN 3

TARIHIN NUFE: LABARIN SHEHU ABDURRAHMAN SHERIF
Kashi na uku
SADIQ TUKUR GWARZO
  Ko da Manmachu (Etsun Nufe Ikaku) yaji labarin yaƙin Shehu Abdurrahman, sai ya ɗaura yaƙi da dawaki dubu talatin da biyu da ɗari biyu ya tunkare shi, suka buga yaƙi, nan ma Shehu Abdurrahman yaci galaba akansa.
   Sa'an nan yaƙi ya sake aukuwa tsakanin su misalin wata biyu ba tare da sunyi galaba akan sa ba.
 Shaihu Abdurrahman ya sauka da sansaninsa a ƙofar Daba, yace musu "Ku bi Allah, ku bi manzon Allah, ku bi ni". Suka bi shi zamani ƙanƙane. Sannan suka sake tayar da ƙayar baya, inda suka ce "Mu bamu bin Sarki mai zane da yawa a fuska tasa"
   Shaihu ya taso da sansanin sa a Daba, ya tafi garin da ake kira Kere ya zauna acan. Yayi sarauta kamar shekaru uku, sannan ya ƙuduri gina gari.
   Yana cikin wannan shawara sai Sarki Majiya ya amshi sarauta bayan mutuwar Etsu Ikaku. Ai kuwa ya taho da jama'a mai yawa don ya yaƙi Shaihu Abdurrahman.
   Jama'ar Shehu Abdurrahman suka ce masa "Haƙiƙa Sarki Majiya ya zo da mutane masu yawa don su yaƙe mu". Sai ya ce musu "Ku rabu dashi"
  Shaihu Abdurrahman ya zauna daga shi sai rigarsa a bisa tudu, cikin kasuwar Kere, yana karanta wasu takardu. Yaƙi ya auko Kere har ya shigo cikin gari, dakarun Majiya suka ƙwace ikon garin duka.
   Sa'an nan sai Shehu Abdurrahman ya tashi daga kan tudun ya kwashe iyalin sa da dukkan dukiyar dake damfamin sa, ya fita izuwa wata fadama a wajen gari kusa da Kere wadda ake ce mata Jigi, ya ajiye iyalin nasa acan sannan ya koma gari.
  Yace "Ba na son jama'ar musulmi masu yawa su halaka domina. Ina tsoron Ka da zunubinsu ya taru a wuyana, wannan al'amari dai daga ikon Allah  ne maɗaukakin Sarki. Amma abinda nake roƙo a wurin Allah shine wani mutum ya kashe ni. In mutu dalilinsa."
   Shaihu ya zauna har dakarun Majiya suka kewaye shi, amma babu wanda ya matsa kusa dashi saboda tsoro, bashi da wani makami sai takardun sa da yake karantawa. Kafin nan dama sai da yayi taimama yayi sallah raka'ah biyu ta fuskar gabas, yayi raka'o'i biyu a fuskokin yamma, kudu da arewa, sannan bayan sallama ya kwanta, ba riga jikinsa sai mayafi, yace musu "Ku zo ku kashe ni domin Allah".
  Wani mutum da ake cewa dashi Chado shine ma'abocin magani, shine dogarin Sarkin Nufe Majiya, ya kusanci shehu Abdurrahman ya yanka shi, har ya datse kansa. A wannan lokaci ciwo ya sami hannunsa domin kisansa, idanuwansa sukayi cizara.
   A wata maganar ance wanda ya ɗauko kan Shehu Abdurahman ya kaiwa Sarki Majiya albaras ta ɓata hannuwansa.
   Shikuwa Sarki Majiya sai ya sanya Kan cikin farin bargo mai geza, ya tafi ya ajiye shi ajiya mai kyau, daga baya ya umarci mutanen sa su jefa shi a kogin kaduna.
  An kashe Shehu Abdurrahman ranar alhamis, da hantsi, shekarar hijirar Annabi Muhammadu s.a.w dubu da metan da talatin da huɗu. Shi yana cikin turbar ƙadiriyya ne, ya zama sarki waliyyi maɗaukaki.
   Daga nan sai Sarki Majiya ya rinƙa ɗaukaka kansa, yana hura hanci, yana baiyana girman kai domin kisan sa ga Shehu Abdurrahman. A lokacin kuwa Mallam Dando (wanda za a ji labarin sa nan gaba kaɗan) yana cikin tawagar sarkin. Don haka da yaga abinda aka yiwa Shaihu Abdurrahman, sai ya gudu ya tafi cikin Juguma ya zauna acan. A zamanin girman waliyyantakarsa bai bayyana ba a ƙasar Nufe".
 

TARIHIN NUFE: LABARIN SHEHU ABDURRAHMAN SHARIFI 1

TARIHIN NUFE: LABARIN SHEHU ABDURRAHMAN SHERIF
Kashi na ɗaya
SADIQ TUKUR GWARZO
Kafin muji labarin asalin Nufe da tarihin ta, zamu fara jin labarin Shehu Abdurrahman al Sherifi ne, shahararren masani kuma mayaƙi ɗan ƙasar Nufe.
Alƙalin Nufe Ummaru ɗan Muhammadu  Allah ya rahamsheshi ya bamu labarin da mahaifin sa ya sanar dashi game da Shaihu Abdurrahman ɗan Muhammadu Sharifi bawan Allah.
  Yace " Mahaifinsa Muhammadu Sharifi balarabe ne, zamanin da faɗa ya auku tsakanin larabawa da turkawa a wajajen ƙarni na goma sha takwas, sai Muhammadu Sharifi ya gudu tare da ƙetare kogi mai zartsi ya shiga ƙasar Nufe, ya zauna a cikinta lokaci mai tsawo.
   Sa'an nan sai ya zauna a ƙasar Abaji ya daɗe.
Akwai wani malami a ƙasar Abaji yana da ƴa Mace kyakkyawa, sai ya ba da ta sadaka ga Muhammadu Sharifi domin neman ladan Allah.
  Bayan Muhammadu Sharifi ya tara da amaryarsa, sai ta samu ciki, daga nan kuma sai ya bar wannan gari zuwa wani wuri daban, ya zauna lokaci mai tsawo acan har matar sa ta haihu yaro ya girma. Aka sanya masa suna Abdurrahman.
 Rannan sai kakan sa yake tambayar sa "kai ina uban ka ne?"
Sai yaro yace "ai ni ban taɓa ganin ubana ba, amma In Allah yaso, kana ganin sa gobe da hantsi".
 Sai kakan yace " idan ubanka yazo ka ganshi zaka gane shi?". Yaro yace "in yazo, na san shi in Allah yaso". Kakan yace ''su wanene dangin ubanka, Bahaushe ne ko Banufe?" Yaro yace ''Haƙiƙa ubana Balarabe ne, sharifi, kakansa kuwa Alassan ne ɗan Ali ɗan Abi Dalibi, Allah ya girmama fuska tasa"
Ai kuwa abinda yaro ya faɗa ne ya auku, sa'ad da yaro ya ga ubansa sai yace " Marhaba da ubana! Barka da komowa daga ziyara! Ka sani ƙasarmu ba irin ƙasar ku bace: ƙasar ku ta larabawa ce"
 Sai kuwa mahaifinsa yayi mamakin abinda yaji daga gare shi. Yace masa " wa ya sanad dakai ni ba mutumin nan ƙasar bane?"
 Yaro yace masa " Wanda ya halicce ni ya sa ni acikin tsatsonka ya goye ni, shine ya sanad da ni maganar nan da na faɗa maka"
  Sa'an nan ubansa yace" wa ya sanad dakai karatu?" Sai yaro yace "Wanda ya halicce ni ya shiryad dani madaidaiciyar turba, shi ne ya sanad dani"
Daga nan sai Uban ya zauna tare dasu tsawon watanni uku, sannan yace wa ɗan nasa " Ina son in koma wurin da na fito, watau ƙasar larabawa".
Ɗansa Abdurrahman yace " In Allah ya yarda ba mu ƙara gamuwa bayan wannan rana har zuwa ranar ƙiyama"
 Ubanshi ya bar shi a wurin uwa tasa ya tafi. Ɗan uwanta shine wanda ya kai shi makaranta a cikin Ebugi.
  Da ya tafi makaranta sai yaƙi yin karatu, idan malamin sa yace masa "Yi karatu", sai shima yace "Kai ma kayi karatu".
A zamanin da yaro ya nufi nunawa malamin sa yana da karatu, sai yace masa "Ina son ka tara malamai a gidanka"
Ai kuwa malami ya tara malamai kamar yadda yaro ya buƙata. Dukkan su suna ɗauke da takardun Alƙur'ani maigirma. Sannan yaro ya soma karatu tiryan-tiryan da ka.
  Daga wannan rana malaman garin duk suka gane yaron yana da karatu, kuma suka san cewa shi waliyyi ne daga waliyyan Allah maɗaukakin sarki.
Akwai wani zane mai yawa a kunduƙuƙinsa na hagu, Nufawa na kiran zanen da suna 'Benuwa'. Akwai kuma wani a kundukukin sa na dama, ana ce masa 'Banguba' da Nufanci. Sai kuma wani tukku a tsakiyar kansa da Nufawa ke kiransa da suna 'Kuturma'.
  Malam Abdurrahman yayi addua cewa 'Na roƙi Allah ya shafe dukkan zanuka da yake fuskokin mutane ranar alƙiyama, ban da zanen fuskata, domin itace alama ta a ranar alƙiyama'.
A zamanin da ya nufi mulkin duniya, ya kan hau jaki ya tafi ya dakace turbar kafirai waɗanda suke dawowa daga kasuwa yayi musu fashi. Idan kafirai sun biyo shi, suka iske shi a turba, idan yayi musu tsawa sai wuta ta riƙa fita daga cikin bakinsa tana binsu tana kora su suna guje mata.
A zamanin da shekarun sa suka yi yawa har ya balaga, sai yayi nufin tafiya ƙasar Hausa bayan ya kai hari ƙasar Bida dake cikin ƙasar Nufe.
A duk inda ya samu kafirai a hanya sai ya yaƙe su, har ma ance yayi yaƙi da garuruwa bakwai bakwai na kafirai, sannan ya zarce ya tafi Sakkwato domin ziyarar Shaihu Usmanu, hasken zamani, fitilar addini, kambin yamma, babban waliyyi.
  Ko da isar sa Sakkwato sai yace wa Shehu Usmanu "Ni nazo karatu ne gareka ya Shaihun mu, malamin addini".
   Sai Shehu Usmanu yace masa "Tafi wurin Abdullahi kayi karatu a wurin sa".
  Daga nan sai ya cira ya tafi Gwandu, ya sauka wurin shehu Abdullahi wanda ya girmama shi tare da saukar dashi a masauki mai kyau.
Bayan wannan, sai Shehu Abdurrahman yace da Shehu Abdullahi "Ni ina so in yi karatu ne a wurin limamin mu, shehu Usmanu mai sabunta addini. Amma yace ba shi da sukuni, ya maishe ni gareka".
  Sai Shehu Abdullahi yace masa "Ko kasan Balaga da Ma'ani da Badi'i?"
  Abdurrahman yace "duka waɗannan fannonin na sansu.
Sai Abdullahi Gwandu yace masa "Ko kasan Tasifi da Tauhidi da Tafsirin Alƙur'ani?"
Abdurrahman yace "duka na san waɗannan turbobin da ka faɗa"
  Sai ya sake tambayar sa da cewa "Shin kasan Aya mai shafe Aya, da wadda aka shafe, da ma'anonin su da kuma wuri wanda yake da fassarori da yawa?"
Nan ma sai Abdurrahmanu yace "duk na sansu, har ma na san Tafsirin Alif Lamin, da Yasin, da Nun, da Sad, da Ƙaf da sauran su duka"
Daga nan sai Shehu Abdullahi Gwandu yayi shiru ya ƙyale shi.

TARIHIN NUFE: LABARIN SHEHU ABDURRAHMAN 2

TARIHIN NUFE: LABARIN SHEHU ABDURRAHMAN SHERIF
Kashi na biyu
SADIQ TUKUR GWARZO
  Daga nan sai Shehu Abdullahi ya sallami Shehu Abdurrahman don ya koma wurin Shehu Usmanu.
   Da ya ƙarasa wurin sa, sai yace masa "ban sami karatu ba a wurin ɗan uwanka".
Babu jimawa kuma akace sai ga Shehu Abdullahi Gwandu ya iso wurin Shehu Usmanu. Inda yace masa "Ya hasken zamani, ya shugaban addini, ka aika mini da baƙo Banufe, baubawa mai zane da yawa a fuskarsa domin ya wulaƙanta ni ne?"
  Sai Shehu Usmanu yace "Wannan magana ba haka bame kamar yadda ka faɗa"
   Ana haka sai Abdurrahman ya nufi shehu Usmanu domin ya zauna tare dashi akan gadon sa. Sai kuwa Abdullahi Gwandu ya janyo shi, domin hana shi zama tare da shehu.
Sai Shehu Abdullahi ya faɗi ga shehu Usmanu " Ya shugaban addini mai sabunta addini, hasken zamani, fitilar addini, kambin yamma, babban waliyyin yamma, wannan Banufe yana da wata karama ne ta masu girma har da ka girmama shi?"
Sai Shehu Abdurrahman ya umarci wani yaron sa ya kawo buzun rago. Ko da aka kawo masa sai nan take ya jefa shi sama a matsayin shimfiɗa, sannan ya hau kai ya zauna a kansa.
 Ganin haka sai Shehu Usmanu yace da ɗanuwansa Abdullahi "Ya ɗanuwana ko kaga girman da Allah ya bashi? Don haka nace maka ka bar magana dashi. Ni haƙiƙa na ganshi da malami na Mala'ika Jibrilu suna karatu cikin sama tare".
   Bayan wannan sai Shehu Abdurrahman yace "Ya Shaihu Usmanu, ko kana da wata ƙasa ta abokan gaba wadda ka yaƙe ta amma baka ci ta ba?"
   Sai Shehu yace masa "Ina da ita, na yaƙe ta har sau uku ban sami buɗinta ba har yanzu. Ita ce Gobir"
   Sai Abdurrahman yace masa "Ka yarda mini in tafi in yaƙe su?"
   Shehu Usmanu yace masa "na yardar maka"
   Sai kuwa Shehu Abdurrahman ya fidda yaƙi gareta, yaje ya yaƙeta, yaci nasara, ya sami ganima, kuma dukkan fulani ma suka sami ganima.
  Sa'an nan mutane suka cewa Shehu Usmanu "In ka bar Abdurrahman anan zai karɓe mulkin ƙasa duka daga hannun ka in baka maishe shi Nufe ba"
Sai kuwa Shaihu ya sallameshi bayan ya roƙi Allah, Allah kuwa ya amsa masa.
Sa'an nan Allah ya fishshe shi daga ƙasar Hausa ya maishe shi ƙasar Nufe, ya fita daga gareta ranar laraba.
   A zamanin da ya fita yana tare da dawaki saba'in, ya tasamma wani gari da ake ce masa Adusa. Ya gamu da jama'ar garin a Gabi ya yaƙe su, ya samu ganima dasu. Daga nan suka sake shiryawa suka tarbe shi gamuwa ta biyu a Adogudawa suka buga yaƙi, nan ma yaci su da yaƙi.
A wannan zamanin kuwa Sarkin Nufe da ake kira Etsu Ikaku bai fara sarauta ba, ana kiran sa da suna Manmachu. Kuma yana zaune a wani wuri da ake kira Kodagi bayan an tura shi yaƙi baici nasara ba yaƙi komawa gida, har ya gina babban gari a wajen ya zama sarki mai ƙarfin gaske.

Tuesday, 5 March 2019

LABARIN ZUWAN KWARARRAFAWA BIRNIN KATSINA

LABARIN ZUWAN KWARARRAFAWA BIRNIN KATSINA

A ƙarni na goma sha shidda, zamanin mulkin Sarkin Katsina Jan Hazo, ance kwararrafawa sun kawo yaƙi birnin katsina.
  Sarkin su ya sauka a yammacin gari a Babbar Ruga, yayin da wazirin sa ya sauka a gabashin gari.
   Sarkin kwararrafawa ya kama mashin sa ya girgiza sannan ya jefa shi cikin gari, aikuwa sai mashin ya faɗa can tsohuwar Kasuwa kusa da kududdufin Tafkin Daule, inda wuta ta kama nan take.
   Daga nan sai sarakunan Katsina suka taru a wurin Sarkin Katsina Jan Hazo, sukayi shawarar su fita daga garin in yaso wanda zai samu tsira ya tsira.
     Bayan nan sai suka aikawa Mallam Ɗan Masani shawarar da suka yanke, shikuwa  sai ya gayawa matarsa ta yi shiri su fita daga gari.
Ita kuma sai tace 'ni da bani fita ko da dare, don haka ba zan fita da rana ba'.
 Sai yayi mata faɗa, sannan ya aikawa Sarkin Katsina da cewa kada su fita daga gari har sai sun ga abinda Allah zai yi dasu, ya shiga roƙon Allah ya ɗauke musu wannan bala'i.
  Da dare sai Sarkin Kwararrafawa ya tashi don ya duba dokinsa, sai kuwa doki ya shure shi a wajen cibiyarsa, ya faɗi yana shure-shure, kafin a jima ya mutu. Aka baiwa wazirin sa labarin abinda ya auku, sai ya hau dokin sa domin yaje ya gano, sai kuwa dokin ya kayar dashi, wuyan sa ya karye ya mutu.
 Haka kuma acikin daren nan manyan-manyan sarakunan su duk sai da suka mace. Yaƙin su ya ƙare, suka tashi.
   Sarkin Katsina Jan Hazo yazo gun Mallam Ɗan Masani yayi durƙushe yana godiya, yayi masa alƙawarin kowa yazo gidan sa don kamun ƙafa ya tsira, koda kuwa kisan kai yayi.

Saturday, 2 March 2019

NAƘULƘULAN GWAGGO MAI KARATU

ALEWA IRIN TA DA: NAƘULƘULAN GWAGGO MAI KARATU
DAGA
LITTAFIN HIKAYOYIN KARFAFA ZUKATA NA MALLAM AMINU KANO
Aure abu ne wanda yake da siffa daban da kowanne irin al'amari. Kuma yadda mata suke kallon sa ba kaɗan ne ba. Amma a duk sha'anin aure ba abu mai ciwo irin kishiya.
  A hakan ne har ake magance-magance, da tsubbace-tsubbace da sauran camfe-camfe. Har su matan sun ƙago malama mai koya musu karatu na zama da miji balle idan tana da kishiya.
   Irin wannan malama ana kiran ta da suna 'Gwaggo mai karatu'. Za ka gan ta tana shiga gidahe ta sadu da mata, shi mai gida yana can yana shirmensa.
   Galibin karatun da matan ke koyarwa bai shafi koya addini ba. Da yawan sa karatun samun miji ne a hannu.
  Ga misali:
   Bismillahi lomilo,
   Lomilo-milo cilo,
   Locilo Balarabe,
  Al-sahlu wali,
  Malandi, Malandi,
   Malandi, Malam Hassan,
   Gwaggo ce, jure,
    Matalulu, tayayye, almala kusar.
A camfin, an ce idan mace ta karanta wannan sau bakwai ta tofa akan matashin kan mijin, da zarar ya ɗora kan sa akai za ta malleshi.
Idan kuma sun yi faɗa ne wanda har ya kai ta ga yin yaji, akwai naƙalin da ake yi wanda zai sa miji da kansa ya dawo yana godo don ta dawo.
Ga misalin sa:
   Alhamdu Lillahi,
 Rabbi da alamina,
Yaushe ka je garinmu,
Domin me, domin me,
Domin karfata da cinya,
 Ba zan zauna ƙasar ɗiyan ba,
  Taken ɗiyan da ɗauri, galadiman,
  Ɗiyan nasara,
   Da tsohuwar gidanmu,
    Ta taushe ni kan giginya,
    In faɗo in karye,
    Ban faɗo ba ta ji kunya,
    Ku dubi kdo yana kashin dirka,
    Na awaki ba ma saniya ba,
    Da a gamo, da gamo,
    Wata buta ta ishi malam,
   Magurji bida.

Idan za a shiga ɗakin kishiya kuwa, ga addu'ar da matan ke koyarwa a rinƙa yi:
   Ramani
   Tatumani
    Abu-adani.

Karatun shiga banɗaki kuwa shine:
   Digirgishili,
    Digirgishila.

TSOFFIN AL'ADUN AURE NA HAUSAWA

ALEWA IRIN TA DA: WASU TSOFFIN AL'ADUN HAUSAWA
DAGA
LITTAFIN HIKAYOYIN KAIFAFA ZUKATA NA MALLAM AMINU KANO
1. AL'ADAR TSARUNCE
A da can, a ƙasar hausa ana yin wata al'ada.mai suna 'tsarunce'. Watau abota tsakanin tsara saurayi da budurwa.
Yadda ake yinta kuwa shine, budurwa za ta je gidan saurayin da take abota dashi ta kwana, ta dawo gida da safe a idon kowa saboda kowa ya aminta da cewa babu magamar baɗala a game da su ko ƙyas.
 Domin a wurin kwanciya ma juya wa juna baya suke yi.
Idan kuwa saurayin ya kuskura ya juya gabansa sai budurwar tayi wuf ta tsallake ta tafi gida komai dare.
 Daga nan kuwa sai an kai ruwa rana kafin a sami budurwar da zata aminta ta auri wannan saurayi, domin abinda yayi ya ɓata masa suna, ya baiwa kowa kunya.
2. AL'ADAR WANKAN AMARYA
A da can ana aurar da budurwa da zarar ta yi haila ta fara yin durwa . Shi yasa ake kiran ta da suna 'mai durwa' ko ace 'budurwa'.
Kuma ranar da za a kai ta sai ayi mata wanka a gaban danginta da dangin mijinta don a tabbatar yarinyarsu ƙalau take.
3. AL'ADAR BIKIN AURE
Ana kiran kiɗan ƙwaryar da akeyi ranar biki  da suna 'tirƙeƙe-tirƙeƙe'.
A yanzu tuni an mance dashi.
Sai kuma gaɗar da samari sukeyi a lokacin biki. Akwai rawar da akeyi mai suna 'tamalmala-tamalmalaye'. Da kuma wata mai suna 'ruwan jiran bawaita'.
Akwai kuma rawar da mata kanyi a dandali.


Sadiq Tukur Gwarzo

TARIHIN HAUSA DA HAUSAWA MAHANGA TA 7

TARIHIN HAUSA DA HAUSAWA: MAHANGA TA 7
Sadiq Tukur Gwarzo

Littafin 'Hausawa da Maƙwabtan su' wanda turawan mulkin mallaka da haɗin guiwar wasu hausawa suka samar mai ƙunshe da tarin zantuka  game da tarihin Hausawa da maƙwabtan su ya danganta asalin Hausawa ga Borno.
   Aka ce Sarkin Borno na da wani bawa mai suna Bawo, babu wanda ya san asalin sa, ko dangin sa. Amma abinda aka sani shine Sarkin Borno ya jiɓanta shi a kan biranen Hausa guda bakwai da ake kira Hausa bakwai yana mai riƙe dasu yana tattara haraji tare da kula da lamurorin su, har ya haifi ƴaƴa bakwai.
   A zamanin da ya ga alamun mutuwa sai ya sarautar da waɗannan garuruwa ga ƴaƴayen nasa. Kowannen su ya bashi birni guda.
  Har aka ce wanda ya sa a Daura ba namiji bane, mace ce mai suna Daura. Saboda haka ake ambaton garin da sunanta.
   Haka kuwa itace babba a cikin ƴaƴansa, itace ƴaruwar sarkin katsina da sarkin Kano da sarkin Gobir, domin dukkan su uwarsu ɗaya.
   Kuma sarkin Burmi da Sarkin Zazzau uwarsu ɗaya. Sarkin Rano kuwa shi kaɗai ne wurin uwarsa.
Saboda haka sai ya zamana ƴaƴayen sun cigaba da bayar da harajin ƙasashen su zuwa Daura, daga nan kuma ana aikawa Borno zuwa ga Sarkin ta.
Sarkin Gobir Bawa kaɗai ne ya ƙi bada harajin nan, sai kuwa yaƙoƙi suka rinƙa aukuwa tsakanin garuruwan da Borno, daga bisani ya ƴamtar da ƙasashen Hausa daga Borno.
Wannan abu tabbatacce ne a cikin labarun da aka faɗe su, haƙiƙa asalin su ƴaƴa ne, su ne ragowar Kibɗawa. Su kuma Kibɗawa sune jama'ar Fir'auna da suka tafo daga Misira suka cika garuruwan Ahira har suka tafi Gobir suka fitad da waɗanda suke cikinta, sune waɗanda suka mallake ta daga ƴaƴan Bawo suka karɓe sarauta daga hannun mutanen wajen. Suka rinƙa yin aiki daga abinda suka iske ƴaƴan Bawo suna yi, suna masu biyan haraji har zuwa lokacin da Bawo ya hana biya.