Sunday, 1 November 2020

TARIHIN JAGABAN, CHIF BOLA AHMED TINUBU

 ikakken sunan sa shine Bolanle Ahmed Adekunle Tinubu

Bolanle; a yarbanci na nufin, "wanda aka haifa cikin arziƙi," Adekunle kuma na nufin ; "Ƙari akan adadin yalwa da arziƙin iyali''. Sunan Ahmed kuwa  daga sunan shugaba ne Annabi Muhammad, S.A.W, wanda yake shine Muhammad Ahmad, cikamakin annabawa, abin godiya.

Shine mai rike da sarautun 'Asiwaju' na Lagos da kuma 'Jagaban' na masarautar Borgu dake jihar Niger.

An haife shi a ranar 29 ga watan Maris na shekarar 1952 a mafi inganci, a cikin birnin Ikko (Lagos). Shi musulmi ne.  Ya halarci makarantar firamare mai suna St. John's Primary School, dake Aroloya a Lagos, sai sakandiren Children's Home School dake Ibadan. Tinubu ya samu tafiya kasar Amurka domin karo karatu a shekarar 1975, inda ya soma karatu a kwalejin Richard J. Daley College dake Chicago, Illinois kafin daga bisani ya koma jami'ar jihar Chicago mai suna Chicago State University. Ya samu kammala digirin sa a shekarar 1979 daga wannan jamiar inda ya karanci Ilimin gudanarwar kuɗi da ake kira "Accounting".


Tinubu yayi aiki da kamfanin Amurka mai suna Arthur Andersen, da kuma wasu kamfanonin irin su Deloitte, Haskins, & Sells, da GTE Services Corporation duk a can Amurka. Bayan komowar sa gida Nigeria a cikin shekarar 1983, Bola Tinubu ya soma aiki da kamfanin Mobil Oil Nigeria, kafin daga bisani ya zamo cikin jagororin kamfanin.

 Ya soma shiga harkokin siyasa ne a shekarar 1992, lokacin da ya shiga jamiyyar Social Democratic Party (SDP) inda ya zamo mamba na ɗariƙar  'Peoples Front' wanda marigayi Shehu Musa Yar'Adua ke jagoranta, ɗarikar da ta ƙunshi manyan ƴan siyasu irin su marigayi shugaba Umaru Yar'Adua, Atiku Abubakar, Baba Gana Kingibe, Rabiu Kwankwaso, Abdullahi Aliyu Sumaila, Magaji Abdullahi, Dapo Sarumi da Yomi Edu da wasunsu. 

  An zaɓi Bola Tinubu a matsayin sanata mai wakiltar sanatoriyar Lagos ta yamma a jamhuriya ta uku wadda bata yi nisan zango ba sojoji suka yi juyin mulki tare da rushe mulkin dimokraɗiyya baki ɗaya.


 Bayan soke zaɓen shugaban ƙasa na kwanan watan '12 June' na shekarar 1993, sai Tinubu ya zamo ɗaya daga iyayen da suka kafa gungun kungiyoyin rajin dawo da mulkin dimokraɗiyya a Nigeria, kungiyar da ta shiga wayar da kan ƴan ƙasa akan nuna rashin goyon bayan mulkin soja da kuma ayyana marigayi Moshood Abiola a matsayin wanda yaci zaɓen shugaban ƙasa da aka soke na ranar 12 ga watan yunin 1993. 

Don haka, juyin mulkin da marigayi Shugaban ƙasa a wancan lokaci Abacha yayi na zamowa shugaban ƙasa da kuma yunkurin da yayi na ɗaukar tsauraran matakai akan masu niyyar bashi matsala a mulkin sa, sai Tinubu ya ƙetare ya bar Nigeria, bai sake dawowa ba sai bayan rasuwar Abacha a shekarar 1998, inda aka soma kafa tubalin ginin jamhuriya ta huɗu. 


A zaɓen shekarar 1999, Bola Tinubu ɗaya ne daga shugabannin jamiyyar Alliance for Democracy (AD), tare dasu Abraham Adesanya da Ayo Adebanjo. Ya shiga zaɓen firamare na jamiyyar ta AD a matsayin ɗan takarar ta na Gwamnan jihar Lagos, kuma ya samu nasara, inda ya doke abokan takarar sa na lokacin  Funsho Williams da Wahab Dosunmu, tsohon ministan ayyuka a Nigeria. Don haka a zaɓen shekarar 1999, Bola Tinubu ya samu tsayawa takarar gwamnan jihar Lagos a karkashin tutar jamiyyar AD, tare da samun nasarar lashe zaɓen cikin kwanciyar hankali.

A zaɓen shekarar 2015 kuwa, Tinubu shine jagoran gamin gambizar jamiyyan AC, ANPP, da CPC waɗanda suka dunƙule tare da komawa inuwar jamiyyar APC. Shine kuma ya jagoranci marawa shugaban ƙasa Buhari baya har ya samu tikitin takara a jamiyyar ta APC, har kuma daga bisani ya samu nasarar lashe zaɓen shugabancin ƙasar baki ɗaya.

Tuesday, 6 October 2020

2. HIKAYAR SAIFUL MULUKI DA BADI'ATUL JAMALI

 HIKAYAR SAIFUL MULUKI DA ALJANNA BADI'ATUL JAMALI

NA BIYU

Bayana wata huɗu, mutane huɗu suka dawo, ba su samo kome ba, suka ba shi labarin  binchiken su da isa matuƙa ga kokarin su. Allah bai rabbatar da wannan nufi da suka tasamma ba, sai ran attajiri ya dugunzuma matuƙa ainun.

   Na biyar ɗin su shine wanda ya nufi ƙasar Sham, watau shine na huɗu a lissafi, bai zame ba sai Dimashƙu.

   Ya same ta babbar alƙarya ce mani'imchiya, ya zamna nan yana tambaya, babu wanda ya ce masa ci kanka.

  Yayi haramar fita ya sake tafiya zuwa ga wani garin sai ya hangi wani yaro yana famfala gudu, yana tuntuɓe da ƙafarsa.

  Yace masa "kai samari, me ya faru kake gaggawa haka? ina zaka?."

  Sai yaro yace "zani majalisar wa'azin wani tsohon Malami ne wanda yake zama rana mai kamar ta yau, yana bada labaru da daɗaɗan hikayoyi waɗanda daɗai mutum bai taɓa jinsu ba; don haka nike gaggawar in samu zuwa wurin da wuri don kada na rasa wurin zama, ina tsoron matsatsi."

   Yace masa "in biyo ka?" Yaro yace ''in kana iya gudu zo mu je".

   Sai kuwa ya ja ƙyauren ɗakinsa ya kulle, ya bi saurayin nan a guje. Da suka isa sai suka tarar da dattijo zaune bisa kujerar sa, bai soma ko Basmallah ba. Suka zauna kusa dashi, suka kasa kunnuwan su gare shi.

  Zuwa jimawa, sai Malamin ya shiga bada labarai, bai tashi ba sai da rana ta kusa faɗuwa. 

Da gamawar sa, jama'a suka watse, sai magudancin nan ya kusance shi, yayi masa sallama; ya amsa masa suka gaisa da juna sannan yace "Allah ya bamu albarkacin Mallam, idan ka yarda ina so nayi tambaya". Mallam yace "Allah ya sanasshe mu, tambayi abinda kake so ya ɗana". 

  Sai yace "Ko Allah ya sa kana da labarin Saiful Muluki da Badiatul Jamali?" 

Tsoho yace "kai kuwa a ina ka samu wannan zanche? wa ya gaya maka wannan labari?"

  Yace "ji nayi, neman sa kuwa na fito, kuma shi ya taso dani daga nisan duniya zuwa nan. Idan kana dashi ina bara ka sanad dani don Allah da Annabin sa domin alherin ka. Abinda ka nema kuwa duk zan baka, da dai raina a hannu yake, in kache shi ka ke so wallahi da na baka."

  Ɗan Tsoho yace " Yi farin ciki, buƙatar ka ta biya: amma bani faɗawa kowa bisa tafarki, ban kuwa taɓa faɗawa kowa shi ba daɗai. Idan kana son sa kazo gidana tare da dinari ɗari, zan gaya maka shi bisa sharaɗi biyar".

  Yace "Zan baka dinare ɗarin da ka ambata, zan kuma baka goma kafin alƙalami,  zan amshi wannan hikaya da dukkan sharaɗin da zaka ambata akanta."

  Tsoho yace "tafi gobe da safe kazo da su ka riƙi buƙatar ka".

  Ya tashi ya sunkuya yayi godiya gun tsoho ya tafi makwancin sa yana cike da murna, ya zuba dinari ɗari da goma a cikin rarita, da fitowar alfijir ya tashi yayi wanka ya sa tufafin sa ya ɗauki mayani ya tafi gidan malami yayi sallama, da fitowar sa sai ya gaishe shi sannan ya miƙa masa jaka.

  Tsoho ya amsa yayi godiya ya shiga tare dashi zuwa shamakin sa, ya shiga ya fito masa da da tawada da alkalami da takardun rubutu, ya mika masa wani  littafi  yace "shine wannan littafi mai ɗauke da wannan hikayar". 

Ya amsa ya duba ya rubuce shi, ya karance shi ga malamin, sannan tsoho yace masa 

"Ya ɗana, farkon sharaɗin  da zan gaya maka shine kada ka bayar da wannan labari akan tafarki, na biyu kada ka gayawa mata shi, na uku kada ka gayawa wawayen mutane shi, na huɗu kada ka gayawa yara, na biyar karatun sa sai a gun sarakuna."   Bawan Attajiri Hassan Yace "to naji na karɓa", ya durkusa yayi godiya sannan ya tafi.

   A wannan lokacin saura kwanaki goma wa'adin sarki ga ubangijin sa Hassan ya cika, don haka yayi saurin aikewa da mai bushara zuwa gareshi, sannan cikin hanzari ya haɗa kayan sa ya nufi komawa gida.

  Sannu a hankali ya isa gida, koda attajiri yayi arba dashi sai ya rungume shi don murna, ya cire tufafin jikinsa na alfarma ya danƙa masa su, ya bashi ingarmun dawakai goma, taguwowi goma, alfadarai goma, bayi goma, waɗannan fa duk a matsayin barka da sauka ne ba a cikin ladan aikin sa ba.

 Bayan haka, Hassan attajiri ya sake rubuta wannan hikaya da hannun sa, sannan ya tafi ya yiwa Sarki albishir da ita a ranar da wa'adin su ya cika.

 Sarki ya cika da farin ciki, sannan ya aike a tara masa dukkan sarakunan sa, da malamai da mahankalta da masu duban tamrari duk na ƙasar sa, da suka gama taruwa sai Hassan attajiri ya labarta wannan hikaya a garesu.

   Ɗaukacin jama'ar suka cika da mamaki, babu wanda ya taɓa jin wannan hikaya mai daɗin gaske daɗai, babu zato sai dinare da azurfa da jauharori ke ta zuba akan Hassan Attajiri, ana yi masa kyauta dasu.. 

  Sarki ya shiga gida ya tuɓe tufafin jikin sa ya kawo masa su kyauta, ya mallaka masa yankin ƙasa guda, ya sanya shi wazirin dama. Yayi umarni a rubuta masa wannan labarin da ruwan dinari a taskance masa shi a taskar sa, a duk lokacin da ransa ya ɓaci sai Waziri Hassan ya karanta masa shi, kafin ya ƙare sai kaga farin ciki da annushuwa ya dabaibaye shi.

 Ga yadda wannan hikaya take:-

  A zamanin da anyi wani sarki a Masar, sunan sa Asimu ɗan Safwana...

  

  

Wednesday, 30 September 2020

TARIHIN KANO

 ASALIN KANO

(Fassarar Tarihin asalin Kano kamar yadda ya fito daga tsohon kundi mai suna 'TARIYK ARBAB BALADIL LAZIY MUSAMMA KANO' watau 'KANO CHRONICLE' da turanci, wanda aka gutsura shi a littafin 'HAUSAWA DA MAKWABTAN SU' littafi na biyu' )

SADIQ TUKUR GWARZO

Littafin ya soma kamar haka:-

Wannan tarihi ne na ma'abotan wannan gari wanda ake kira Kano. Shugaban su shi ne Barbushe, shi kuwa daga ƙabilar Dala yake. Shi Dala mutum ne baƙi, kakkaura, ƙaƙƙarfa, mafarauci ƙwarai. Ya kasance ya kan kashe giwa da sandar sa, ya saɓo ta a kansa, yayi tafiya da ita kamar mil tara.

  Ya zo garin nan, ba a san asalin sa ba. Da zuwan sa sai ya gina gidansa a saman dutsen Dala, ya zauna akan sa, shi kaɗai tare da matan sa da ƴaƴansa bakwai, huɗu maza uku mata.

   Sunan babban ɗansa Gargaji, shine kakan Buzami. 

Buzami kuwa shine uban Barbushe. Shikuwa Barbushe, shine ya gaji dukkan halayen Dala tun daga sanin tsafi har zuwa ƙarfi da sihirinsa da rinjaye ga ƴanuwansa, domin haka sai ya zamo shugaba a zamanin sa.

  Ga sunayen fadawan Barbushe; 

-Gunzago: gidan sa yana a ƙarƙashin Gwauron dutse daga gabas.

- Gagiwa uban Rubu wanda yake kama giwa da igiya saboda tsabar ƙarfin sa.

-Gubanasu

-Ibrahimu

-Bardoje

-Nisau (wanda garin Panisau ya samu daga sunan sa)

- Kamfatau

- Duje

-Janberi

-Gamakora

-Safataro

-Hangugu

-Gardangi.

- Ɗan buru: wanda gidan sa yake a jigirya.

-Jan Damisa: wanda gidan sa yake a magwan. Sunan sa Ruma, kuma shine kakan Rumawa. Tun daga Guga har zuwa Salanta ana danganta su da shi, ana ce musu rumawa, su jama'a ne masu yawa.

- Hamɓarau: gidan sa yana Tanagar.

-Gunbarjado: gidan sa yana Panisau, kuma shi ɗa ne ga Nisau.

  A wancan zamani na Barbushe, mutane kan taso tun daga Tuda zuwa Ɗan-baƙoshi, haka kuma tun daga Duji har zuwa Ɗankwai, dukkan su suna taruwa a wurin Barbushe a daren salla biyu,  domin shine babban su cikin tsafi.

  Sunan inda gunkin su yake ajiye 'Kakuwa', sunan gunkin kuwa 'Tsumburbura', domin itaciya ce da ake ambatonta 'Shamus', sunan mutumin da yake zaune a ƙarƙashin ta dare da rana 'Mai Tsumbura'. 

  An kewaye itaciyar da gini ne, babu mai shiga cikin ginin sai Barbushe, duk kuwa wanda ya shiga sai ya mutu nan take.

  Barbushe kuwa baya saukowa daga saman dutsen Dala sai idan ranakun idi biyu sun gabato. A lokacin ne mutane ke zuwar masa da ga gabas da yamma, kudu da arewa, waɗansu da baƙar kaza, waɗansu da baƙin bunsuru.

  Idan sun gama taruwa a ƙarƙashin dutsen Dala a ranar jajibere kenan bayan la'asar, sai Barbushe ya fito daga gidansa da dare tare da makaɗansa. Ya na mai kururuwa da ƙarfi yana cewa "Babban jimina aka sa mun gama kara-gaga laya Tsumburbura"

  Mutane kuma sai su amsa masa da cewa "Ga Tsumburbura, Kanawa, ga wajen Dala".

   Daga nan sai su ɗunguma tare dashi zuwa saman tsauni wurin gunki. Da isar su gurin gunkin sai kowa ya yanka abin da yazo da shi.

   Sa'an nan sai Barbushe ya shiga cikin ginin shi kaɗai, yana mai cewa "Ni magajin Dala da kun ƙi da kun so ku bini ba ra'ayi ba"

  Su kuma mabiyan suna kewaye ginin da gunki Tsumburbura take tsirara suna masu cewa " Mai gida bisa kan dutse, Ubangijin Mama, bi mun bi ka ba ra'ayi", a haka zasu wakana har huduwor alfijir sa'annan su tsaya suci abinci.

  Daga nan sai Barbushe ya fito ya basu labarin dukkan abinda zai faru acikin shekarar da zasu shiga, har ma da baƙon da zai shigo ƙasar su na alheri ko na sharri.

  Shine ma ya basu labarin gushewar mulkin su, da sarewar itaciyar shamus da suke yiwa bauta har ma da ƙonewar ta, da kuma gina wani masallaci a jikin dutsen Dala.

  Kuma yace musu "Wani mutum zai zo wannan gari tare da rundunarsa, ya mallakemu". 

Sai suka ce masa "Don me ka faɗi haka? wannan magana ce fa mummuna".

  Sai yayi shiru, sannan yace "da sannu zaku ganshi da alfarmar Tsumburbura! idan bai zo a zamanin ku ba, zai zo a zamanin ƴaƴanku, ya mallaki dukkan wanda ya samu a cikin wannan ƙasa dukkan ta, ya sa a manta daku duk da jama'ar ku, zai bayyana da ƙabilar sa zamani mai tsawo".

  Jama'ar Barbushe suka yi baƙin ciki ƙwarrai, suka gaskata abinda ya faɗa domin sun san baya musu ƙarya. Har ma suka ce "yaya za muyi mu kawad da wannan lamari?"

  Sai yace dasu " Babu yadda za ku yi sai haƙuri!".

   A haka suka wanzu cikin nadama bisa gushewar da mulkin su zaiyi mai tsawo har sa'ar da Bagauda yazo kano tare da runduna tasa a zamanin ƴaƴan waɗancan mutane na lokacin Barbushe, (amma wasu sunce zamanin jikoki ne), bai samu kowa ba daga makusantan Barbushe sai Janberi, da Hamɓarau, da Gardangi, da Jandamisa, da Kamfatau.

  Da waɗannan mutanen suka ga lamarin Bagauda sai suka ce "wannan mutumin shine wanda Barbushe ya bamu labari".

  Jamberi yace " Na rantse da Tsumburbura idan aka bar su a cikin wannan ƙasa, da sannu zasu mallake mu har mu zama kamar ba kome ba".

Mutane suka ƙi jin maganar sa, suka bar su suka zauna, suka ce "A ina Bagauda zai samu ƙarfin da zai rinjaye mu?"

     Bagauda ya zauna da rundunar sa a Gazarzawa, suka gina gidaje a cikin ta, suka zauna watanni bakwai, sannan suka tafi Sheme.

  A wancan zamani, daga Jakara zuwa Damargu, ana giran sa da suna Gazarzawa. 

  Daga Jakara zuwa Santolo, ana kiran sa da suna Zadawa.

  Daga Santolo zuwa Barku, sunan sa Fankui.

  Daga Bampai zuwa Wasai ana kiran sa da Raura.

  Daga Watari zuwa dutsin karya sunan sa Dundunzuru.

  Daga Santolo zuwa shike sunan sa Sheriye.

 Daga Damargu zuwa Kazaure sunan sa Sheme.

Daga Barku zuwa Kara sunan sa Gauɗe.

Daga Kara zuwa Amnago shine Gaji.

Sai kuma daga Mashi zuwa Ringim da ake kira Tokawa.

  Ma'abotan wannan ƙasa wanda Bagauda ya same su a cikinta suna mulkin garinsu, ba su bin kowa sai Tsumburbura da duhuwar sa Jakara.

Ana ambaton ta (jakara) da suna Kurmin baƙin ruwa, domin shi ruwa ne baƙi, duhuwa ta kewaye shi, ana kiyaye dukkan musiba da ita da gunkin su. Ta faro ne tun daga Gurgumasa har zuwa Dausara.

  Ƙiraranta da zartakenta basa yin motsi har sai idan musiba ta gabato garin kano, sai aji tayi kururuwa sau uku, hayaƙi ya rinƙa fitowa daga cikin Tsumburbura, wanda ke cikin tsakiyar ruwa. 

Daga nan sai su nemi baƙin kare su yanka a ƙarƙashin Tsumburbura, kuma su yanka baƙin bunsuru a cikin duhuwar.

  Idan har hayaƙin da kururuwar suka ƙaru to tabbas sai wannan musibar ta sadu dasu, idan kuwa basu daɗu ba to musibar ta kau kenan. Sunan wannan duhuwar 'Madama', kuma sunan Tsumburbura Randaya.

  Ga sunayen waɗanda suka soma riƙe sarautar kano tun a zamanin farko:-

- Mazauda, shine babbansu, shine kuma kakan sarkin Makafi.

- Giji-giji shine sarkin Maƙera.

- Bugazau sarautar sa dafa giya.

- Hamburki sarkin magani kenan mai warkar da dukkan cututtuka.

- Ɗan ɓuntiya shine mai yawan tafiya cikin garuruwa da daddare, shine kakan kurmawa (sarautar kama masu laifi kenan) 

- Doron-maje shine sarkin Samari.

- Jandodo shine sarkin makaɗan gunduwa da kuru.

-Magaji shine kakan Maguzawa, shine mai fitar da ƙarfe daga ƙasa ya narka shi.

- Asanne shine kakan mawaƙa, shine sarkin Rawa.

- Bakwanyaƙi shine sarkin Maharba.

- Awar shine kakan Awarawa, shine mai yin gishirin Awar, kuma sarkin Ruwan dukkan ƙasar.

Dukkan waɗannan su goma sha ɗaya, kowannen su yana da ƙabila tasa  daban da jama'a mabiyan sa masu yawa, kuma dukkan su sune asalin KANO..

TARIHIN GARIN GWARZO

 TARIHIN SAMUWAR K'ASAR GWARZO


Gabatarwa


Littafin 'Mazan Kwarrai' shine wanda Marubuci IBRAHIM BALA GWARZO ya k'addamar dashi a wajajen shekara ta 2000, wanda ya tattaro tarihin kafuwar garuruwa kimanin talatin da suke a tsohuwar K'asar Gwarzo. Bisa bukatuwar wannan tarihi da muke dashi, kuma bisa bukatar yad'a Ilimi, yasa na nemi (Sadiq Tukur Gwarzo) sahalewar Marubucin (wanda yake Uba gareni) domin rubuta wani yanki gami da yadashi ga al'umma. Hakika marubucin yaji dadin haka, ya kuma sahale min izinin yin hakan. Godiya da fatan alheri a gareshi. 


TARIHIN SAMUWAR GARIN GWARZO


Kamar yadda tarihi ya nuna mana, akasarin garuruwan Kano Maguzawa ne suka Kafasu. Wannan gari na Gwarzo mai tsohon tarihi ya samu kafuwa ta hannun wani Bamaguje wanda ake kira 'GWARZO'. 

A zamanin da, zakaga mutum ya samu guri ya kafa gida shi kadai, wanda daga baya idan mutane suka fuskanci wurin yana da yalwa sai kaga suna zuwa da kadan_da_kadan domin zama. 

Ga al'adar mutanen da, wanda ya fara zuwa guri ya kafa gari shine sarkin garin. 

Bayan wannan Bamaguje mai suna Gwarzo (wanda akace yazo ne daga arewa a wuraren K'arni na Sha shidda zuwa na sha Bakwai) Ya kafa 'yan tsangayunsa ya zauna a wannan guri, sai wani Malami yazo daga kasar Sakkwato wanda ake kira Malam Rashidu ya sauka a gurin shima. Sai Mallam Rashidu ya shiga rokon Allah subhanahu wata'ala ya albarkaci wannan guri da suke zaune, ya kuma kareshi. Ai kuwa hakan ya samu, domin har lokacin yake-yake yayi k'aura ba'a taba cin k'asar Gwarzo da yaki ba. 

Bayan wani lokaci sai wani mutum da ake kira Isau yazo shima ya kafa bukkarsa ya zauna tare da Bamaguje Gwarzo da kuma Mallam Rashidu. Suna nan zaune abinsu sai ga wani Bamaguje ya risko wajen, sunan sa Kutunku, amma anfi kiransa da Riji. 

Ganin haka sai Bamaguje Gwarzo yayi murna, ya samu danuwa. Wannan yasa yayi tunanin raba wannan wuri da suke zaune biyu b'angaren gabas da yamma masu kudu, sannan ya baiwa Bamaguje Riji mulkin barin gabas, shikuma yaci gaba da mulkin b'angarensa. Sai ya kasance duk bak'on da yazo ya zauna a b'angaren yamma maso kudu (wanda daga bisani ake kiran wurin da suna Gwarzo), to ya zama talakan Gwarzo, wanda kuma ya zauna a barin gabas (shima daga bisani Riji ake kiran wurin), Riji ne shugabansa. 

A iya wannan lokaci, mutane sun rinka zuwa suna zama a wannan yanki. Akwai misalin wani hab'en mutum mai suna Katamba, wanda Gwarzo ya bashi wuri a inda ake kira Katambawa a yanzu, sannan da misalin wasu mutane da suma suka zo shigewa suka nemi a basu matsuguni, sai Gwarzo ya basu wani wuri a gabas dashi, inda a yanzu ake kira da Tsohon Garu. A wancan lokaci, ba iya wurin da mutum zaiyi gida kadai ake baiwa bako ba, A'a, ana bashi ne har ma da inda zai noma domin ya ciyar da kansa da kuma iyalinsa. 

A kwana-a-tashi, sai Allah ya kawo wani dan-fulani mai suna Baba. Daya zo sai ya sauka a yankin da Gwarzo yake iko dashi. Shikuwa wannan bafullatani ance yazo ne daga Musawa ta k'asar Katsina, kiwon shanu da dabbobi itace sana'ar sa. 

Ance wata rana sai dabbobin Bafullatani Baba suka shiga cikin gonar wani Bamaguje mai suna Rijau tare da tafka masa b'arnar amfanin gona, wannan yasa ya kai k'ara ga Sarkin wurin watau Gwarzo. Da aka kira Baba dan fulani sai aka tsareshi sai daya biya kimanin b'arnar da dabbobinsa sukayi, sannan aka yanka masa tara ya biya. 

Ganin haka sai wannan bafullatani Baba ya sayar da dabbobinsa ya k'ulle kudinsa ya tafi kano wajen d'an iyan Kano domin lokacin shine mai kula da yammacin kano, inda ya nemi sarautar Gwarzo, wadda akewa lak'abi da 'd'an Gwarzo'. Sai kuwa yayi dace aka bashi. Aka tanaji dawakai daga kano bayan nad'insa, aka rakoshi zuwa garin Gwarzo ana kad'e-kad'e da bushe-bushe. 

Koda Bamaguje Gwarzo, wanda yake sarkin Gwarzo (d'an Gwarzo mai ci) yaji kade-kade da bushe-bushe, sai ya aika aje a gano masa menene ke faruwa. Inda aka zo aka sanar masa cewa bafullatanin nan Baba da aka yiwa tara aka nad'o daga kano a matsayin sabon d'an Gwarzo. Jin haka keda wuya sai Bamaguje Gwarzo da Mallam Rashidu suka shiga gidajen su, tun daga nan ba a sake jin ɗuriyar su ba.

Friday, 4 September 2020

YADDA AKE KITSO A KASAR HAUSA A ZAMANIN DA

 YADDA AKE YIWA MATA KITSONA ZAMANIN BAYA

Yazo a cikin littafin 'Labarun da dana yanzu', babin farko mai suna 'Labarin sana'o'in Hausa' cewa :- Idan mace za tayi kitso (a zamanin da), sai ta nemi rama, da mai, da shuni.

   Sa'an nan sai ta tafi gidan makitsiya, ta ba ta tsinke ta kwance kanta, watau ta tsefe gashin ta ya tashi. San nan sai ta kwanta rub da ciki a gaban makitsiya. Makitsiya zata sharce gashi da tsinkenta ta rarraba shi kashi-kashi; wajen doka daga tsakiyar kai, wajen kaikainu daga sashen kai, kai-kainiya ta dama data hagu, da wajen ɗan ƙeya daga can wajen ƙeya.

  Idan ta gama karkasa kan haka, sai ta shafe shi da man shanu, sai kuma ta soma kitse wajen kaikainu, sannan ta kitse wajen ɗan keya. San nan sai ta faɗa tsakar ka, ta sanya doka (wani tsumma ne ko kaɗi da ake nannaɗewa da zare sai a cusa) sai a kitse duka, tana mai sanya rama tare da gashin. 

  Daga nan sai ayi fishi ko roriya; watau abi sauran ƙananun gashin gefen kaikainu dana tsakankanin kaikainu dana doka a gama da rama a kitse, duka da ƙayar bushiya ake tattara gasun nan. 

  Daga nan kuma sai a kawo mai a labta ga kan, sa'annan a kuma shafe shi da shuni. 

  Kitso ba doka akan ce masa 'juye', kitso wanda aka jera ƙananan kaikainu a tsakar kai har ga ƙeya maimakon doka ana ce masa 'kumbuche'. Kitso mai ɗan ƙeyi biyu ana ce masa 'mace-da-goyo'. Akwai kitso mai suna 'barikanchi' wanda ake yinsa yayi tuk-kaye. Bayan waɗannan, akwai kitson Yorubawa da kitson fulani da ake ce masa 'bijaji'. 

Saturday, 22 August 2020

ILIMIN SANIN RUBUTACCIYAR WAƘA

 ILIMIN SANIN RUBUTACCIYAR WAƘA

  Ita dai rubutacciyar waƙar hausa ta samu tasiri ne daga waƙoƙin larabci, domin kuwa ba a san ta ba sai da musulunci da ilimin larabci suka shigo ƙasar nan, watau musamman lokacin jihadin Shehu Usmanu.

   Tun daga nan har zuwa yau, idan aka bincika marubuta waƙoƙin hausa za a tarar ba zasu rasa wani tasiri na harshen larabci ko addinin musulunci ba.

   Wani abin ban sha'awa kuma shine, harshen Hausa harshe ne mai iya karɓar kowanne irin salo da harshen larabci yazo dashi, ya zauna daram kamar dama anan aka halicce shi.

   Bugu da ƙari, ma'aunin waƙar hausa rubutacciya da amsa amon ta duka irin na waƙoƙin larabawa ne, sai fa daga bisani ne mawaƙan hausa suka saɓa da irin waƙoƙin larabci, har ma aka samu sabbin jigogi waɗanda suka shafi lamuran yau da kullum.

    Abubuwan da ake sa rai aga sun tabbata kafin a hukunta cewa rubutacciyar waƙar hausa tayi yadda ake sonta guda 9 ne, amma na ƙarhen bai zama tilas ba. 

Ga abubuwan kamar haka:-

1. Buɗewa da rufewa da yabon Ubangiji da Salatin Annabi (S.A.W).

 Misali: Na fara da sunan Zuljalali maƙagin duniya,

   Ina salati ga Khairul Anami hasken idaniya.

2. Ma'auni; ta yadda za a iya yanyanke ta kuma baitocinta su zamo kai-da-kai.

  Misali: 

*Dawil:

 Mutum haka ma in yaga bashi da ko zare,

Ya kan roƙi Allah safe da daddare.

*Madid:

Ko ina, duk an sani kai ka mulki,

Duk ƙasar nan babu mai arziƙin ka.

*Da sauran su; kamar su Basiɗ, Watir, Kamil, Hazaj, Rajaz, Ramal, Mumsarih, Hafit, Muƙtabib, Mutaƙarrab, Muɗarid.

3. Waƙa ta kasance tana amsa amo, tana kuma da ƙafiya.

4. A shirya baitocin waƙa dai-dai da ɗangogin waƙa guda bakwai.

   Misali: Gwauruwa itace mai baiti ɗango ɗaya.

Ƴar tagwai mai ɗango biyu,

Ƴar uku mai uku,

Ƴar huɗu mai guda huɗu,

Ƴar biyar mai biyar,

Tahamsi mai shidda,

Sai Tarbi'i mai guda bakwai.

5. Ambaton jigon waƙa tun daga farkon ta.

  Misali: "Nayi shiri tsaf zan ja hankali,

                Akan mata masu yawon dandali".

6. Warwarar jigon waƙa

Watau a kawo ɗangogi waɗanda suka tafi dai-dai da jigon da ake waƙar akan sa.

7. Ambaton sunan mawaƙi da tarihin yin waƙar a ƙarshen ta.

8. Salon mawaƙin ya kasance yana da ƙarfi, watau yana yin bayani mai gamsarwa.

9. Gwanin ta da iya sarrafa harshe.

Sadiq Tukur Gwarzo ya ciro wannan bayanin daga littafin 'WAƘA A BAKIN MAI ITA' wanda kamfanim ɗab'i na NNPC ya wallafa a shekarar 1979.


Monday, 13 July 2020

ƘABILAR MAASAI: DALILIN SHAN JINI DA KIWON SHANU

ƘABILAR MAASAI: DALILIN SHAN JINI DA KIWON SHANU
Sadiq Tukur Gwarzo, GGA
Maasinta,  shine ake ɗauka Uba kuma wanda ya samar da tsatson ƙabilar Maasai, ance ya samu kyautar shanu ne daga Ngai – Ubangijin sama- wanda ya sauko da shanun daga sama zuwa ƙasa acikin salkar fata.
  Tun daga wannan lokacin suke kallon shanu a matsayin tsarkakku,  kuma darajar su tana kaiwa kafaɗa da kafaɗa data ƴaƴansu. Hakika yawan yara da yawan shanu ke nuni da tumbatsar mutumin ƙabilar Maasai.
Dajin da ya ratsa shahararrun yankunan Ngorongoro, Amboseli, Serengeti, Masai Mara da Tsavo dukkan su nan ne wuraren kiwon alummar Maasai. Kabilar Maasai na amfani da yaren Maa ne, kuma ana samun su a yankunan kasashen Kenya da Tanzania.
Haka Kuma duk da yadda sauyin zamani ke tunkuɗe al'adu ga ƙabilun duniya, amma kabilar Maasai suna yaƙi tukuru wajen kere al'adun su na kaka da kakanni, don haka suka yi shura a cikin ƙabilun kudancin afirka musamman wajen kiwon shanun su, tafiya bisa tituna ko rawar adumu.
Daga cikin shahararrun al'adun gargajiya na ƙabilar Maasai akwai rawar tsalle ta adumu, sanya tufar 'shuka' mai kaloli, da yin kaki ko kuma kwankwaɗar jini.
Adamu shine sunan rawar tsalle-tsalle da akeyi a matsayin biki yayin da yara matasa suka zama mahankalta waɗanda suka isa aure. Ana rera wakoki  nangargajiya yayin bikin, sannan wanda tsallen sa yafi na kowa shine yayi nasara, kuma shi ke samun macen aure da tafi ta saura.
Kalar tufafin shuka da suka fi sanyawa itace Ja, wadda take wakiltar jini, kuma take a matsayin kariya a garesu ga namun daji. Yayin da shuɗiya ke nufin sararin sama wadda ke samar da ruwan sama ga shanu. Kalar rawaya kuwa na nufin haihuwa da girma. Baki ɗayan waɗannan tufafi na su ke ƙara musu keɓantaka a cikin ƙabilun afirka.
Kasancewar a cikin wasu ƙabilun ana ƙyamar kaki, amma a Maasai shi abin so ne, domin babban abin girmamawa ne idan zaka gaisa da mutumin da kake girmamawa sai kayi kaki ka tofa a tafin hannu sannan ka miƙa masa hannun ku gaisa. Hakan na nufin share dukkan wani sharri daga tafin hannun, haka kuma idan kaje barka sai ka tofa kakin ka a goshin yaron sannan ka nuna soyayyar ka a gare shi. Shan jini kuwa wani abu ne da ya zama ruwan dare a garesu.
 Don haka alummar ƙabilar Maasai na shan jini ne a matsayin sinadarin ƙara lafiya da kuzari. Jinin da suka fi sha kuwa shine na saniya, wanda har sukan gauraya shi da madara su kwankwaɗa abinsu a duk sanda suke so.
   Zuwa yanzu kabilar ta rarrabu zuwa 21 kamar haka, kuma kowacce na da ɗan sirkin al'adu da saura:- Keekonyokie, Damat, Purko, Wuasinkishu, Siria, Laitayiok, Loitai, Kisonko, Matapato, Dalalekutuk, Loodokolani, Kaputiei, Moitanik, Ilkirasha, Samburu, Lchamus, Laikipia, Loitokitoki, Larusa, Salei, Sirinket and Parakuyo

Sunday, 5 July 2020



AL'ADA MAI BAN MAMAKI:  DALILIN RASHIN WANKA A KABILAR HIMBA 
Sadiq Tukur Gwarzo, GGA
08060869978
  Kabilar Himba da ke kasar Namibia rukunin wasu kaɗaitattun mutane ne waɗanda ɗabi'an su suka zamo bare, ko ace ababen mamaki ga sauran mutanen duniya.
 Akan kira su da suna Ovahimba ko Omhimba, suna rayuwa ne a yankin Kunene cikin kasar Namibia.
Daga cikin al'adun su da suka sha banban da mafi yawan sauran al'adu, akwai al'adar su ta tarbar baƙo da mata domin yin jima'i da su, da kuma sanyawa jarirai tsakiya a wuya tun suna zanin goyo. 
 Sannan basu cika cuɗeɗeniya da sauran kabilu ba balle har a samu sauyin al'adun da suka yi gado kaka da kakanni, waɗannan mutanen suna matukar kokari wajen ganin basu yi aron wata baƙuwar al'ada ba komai kyawunta, don haka muna iya cewa mafi yawan ababen da suka yi riko tun na kaka da kakanni ne.  
Sana'o'in da mazajen kabilar suka fi riko dasu  sune kiwo da noma, matan su kuwa sunfi damuwa da shiga daji samo itacen hura wuta don girka abinci da kuma jigilar samar da ruwan sha ga ahalin su.
  Suna bauta ne ga allolin iyayen su, sannan mazaje na auren mace sama da ɗaya, suna kuma yiwa yara mata aure tun da kuruciyar su.
Babban abin mamaki dangane dasu shine rashin yin wanka da ruwa. Yana daga al'adar da suka yi gado ta rashin wanka da ruwa kwata-kwata a rayuwar su, dalilin haka kuwa ance baya rasa nasaba da rashin kyawun yanayin yankin da suke raye. Yankin su ya shafi sahara ne, samun ruwa na da matukar wahala a tattare dasu. Don haka darajar sa ya sanya suke ganin tamkar asara ne a kwarar dashi wajen wanke gangar jiki.
  Sai dai kuma hakan bai sanya sun zama ƙazamai munana ba, ta yadda suka bullo da wata dabara wajen tsaftace jikin su wajen amfani da albarkatun dake zube a yankin nasu.
   Dabarun sune;  goge jikkunnan su da wata irin kuɓewa ja dake fito musu, sai kuma yin sirace a kullum don tsaftace jikkunan su.
   Yadda suke siracen shine, ana zuba garwashi a rufaffen mazubi mai cike da garin magani da kofa a sama, don haka da zarar hayaki ya soma tashi sai mutum ya durƙusa yana mai kara jikin sa ga tururin wanda zai rinƙa shiga sassa daban daban na jikin yana tsaftace shi. 
Ƙabilar Himba na da matukar son baƙo, tare da kyautata masa, amma fa basa bari baƙuwar al'ada ta gauraya da tasu.

Saturday, 30 May 2020

LABARIN DAN SANDAN CIKI NA INGILA

LABARIN WANI FASIHIN ƊAN SANDAN CIKI WANDA YA CIRI TUTA A YAƘIN DUNIYA NA BIYU

  Daga littafin Hikayoyin Kaifafa Zukata wallafar Marigayi Mallam Aminu Kano.

 A zamanin yaƙin duniya na biyu, anyi abubuwan bajinta, ƙwazo da ƙuru marasa iyaka. Irin waɗannan abubuwa ya kyautu yara su sani don gaba. Saboda haka ne zamu ba da labarin bajinta, ƙwazo da basirar wani ɗan sandan ciki na Ingila.
  Lokacin da jamus suka cinye ƙasar sa suka mamaye ƙasar Turai, sai ya zamana aika saƙon hannu zuwa ga Rashawa abu ne marar yiwo domin duk hanyar da za a ratsa zuwa Rasha Jamusawa suna nan sun kuma sanya ido su ga wani baƙon abu.
Ƙasar Ingila na son aikawa da saƙon hannu zuwa ga kwamandan yaƙi na Rasha, amma kafin aje sai an bi ta ƙasar Faransa, an ƙetare Switzerland an ɓulla ta Yugoslavia kafin a tarar da Rashawa.
Akan haka sai hedikwatar ƴan sandan ciki ta Ingila ta zaɓi wani gwarzo a cikin jami'anta. Ranar da zai tashi sai shugaban hedikwatar ya kira shi yace da shi, "Gwamnati ta zaɓe ka ka kai saƙo wurin Marshal Timoshenko. Za a sanya ka a jirgin sama mai laima a kai ka kusa da Faris a jefa ka. Za ka sauka a wani daji mil goma daga Faris da ƙarfe ɗaya na dare. Da zarar ka sauka in ka duba na'urar gane kusurwa 'kanfas' ka ga gabas, sai kayi ta tafiya har zuwa yadi ɗari ko fin haka da kaɗan, a hagun ka zaka tarar da tsohon basukur. Akwai fitilar kalanzir ka kunna ka tura har kazo babbar hanya. Daga nan ka bi hanyar zuwa otal mai suna Edward Set. Ka jingine basukur ɗin ka shiga dai-dai ƙarfe biyu saura kwata. Idan ka kuskure abu ɗaya zaka shiga halaka.
Da zarar ka shiga, wanda yake aiki a lokacin zai kunna taba sigari da zarar ya ganka. Daga nan zai baka ɗaki. Bayan ƙarfe uku da kwata ka fito daga ɗakinka ka je cikin lambun otal ɗin kana shawagi. Wani mutum zai zo da jarida a hammatar sa ya zauna a kujera mai fitila. Bayan yayi karatu zai bar jaridar a nan ya tafi nasa zarafi. Kai sai ka ɗauki wannan jaridar kaje ɗakin ka ka duba shafin talla. Anan za ka ga abinda za ka yi. A dawo lafiya, Allah ya kiyaye. Kada ka mance da cewa sirrin aikin ƴan sandan ciki shine aiki da hankali".
Nan da nan aka ɗauki ɗan sandan, aka ya dashi a gefen Faris, ya tarar da komai yadda aka gaya masa, ya kuma yi duk abin da aka ce yayi.
Da ya duba shafin talla ya fassara saƙon dake ciki, sai ya ga ance dashi nan take ya je ƙofar otal zai tarar da mota sabuwa mai lamba kaza, a cikin ta akwai ƙatuwar jaka cike da kuɗin Ingila fam dubu ashirin. A cikin su guda ɗaya ce tak ke ɗauke da saƙon da ake so Marshal Timoshenko na Rasha ya samu.
Nan take ya fito da gaggawa, ya ɗauki mota ya kama hanya. Ya yi kamar awa ɗaya yana tafiya har ya zo wata kwana, sai ya ga mutum a kwance jina-jina. Ya ja birki don kada ya taka shi. Kuma ya tabbata an kaɗe shine aka bar gawar sa anan. Sai kawai ta fito ya kama ƙafar sa don ya janye shi ya samu hanya.
Ai kuwa sai wuf yaga mutumi ya miƙe ya zaro labarbar, ya auna shi da ita, sannan yace "Ni ɗan sandan ciki ne na Jamus. Sunan ka Robinson. Yau ka sauka daga Ingila. A motar ka akwai saƙo zuwa Marshal Timoshenko. Yanzu ba wata magana sai ka ba ni mota da kayan cikin ta ko in kashe ka".
Nan da nan ta ya sakar masa mota. Ya shige kenan zai tashe ta sai Robinson yace da shi, "Ina so ka taimake ni da abu guda". Wato zan buɗe hannayen kwat ɗita ka harba wurare daban daban don in koma gida a sani sai da tsiya tsiya aka karɓi kayan nan. In ba haka ba sai a zaci ƙarya nake".
Ɗan sandan cikin Jamus ya yi masa yadda yace. Daga gamawa sai Robinson ya zaro tasa labarbar ɗin yace "Harsashin ka ya ƙare, bani motata. Amma ni ba zan yi wauta in bar ka a raye ba". Sai ji ka ke fa! fa! fa! fa! ya harbe shi.
Ɗansandan Jamus ya mutu, Robinson ya shiga motar sa ya kai saƙo inda aka tura shi ko tsartse bai yi ba.

Sadiq Tukur Gwarzo

Monday, 3 February 2020

KASUWANCIN YANAR GIZO 1



Assalamu alaikum.
    Wannan wani sirri ne wanda na rubutashi da harshen turanci don siyarwa a kasuwa, amma yanzu saboda rashin yiwuwar hakan na yanke shawarar fassara shi da hausa tare da yada shi gay an uwana musulmai hausawa. Ina fata wasu za suci gajiyar wannan sirri.
       Da fari dai wannan tsarin kasuwanci da zanyi bayani akansa sunansa a turance ``ONLINE BUSINESS``. Idan akace online, a hausance ana nufin duk wani tsari wanda aka maqala naura mai kwakwalwa ta kwamfuta ko wayar sadarwa ta handset, ko kuma wasu na`urori, aka maqala su da yanar gizo wato internet. Business kuwa kowa ya sani, ma`anar sa kasuwanci.
         Wannan kasuwanci, mutanen duniya a qasashen da suka ci gaba tuni sun dade da dulmiya a cikin sa, domin suna yin siye da siyarwa na motoci, ticket na sinima ko na jiragen sama, tare da dubban abubuwa wadanda daga daki ma zaka siya, kafin wani lokaci abin zaizo qofar gidanka. Sai dai kada mai karatu yayi tunanin zan sanar dashi hanyar da zai zama attajiri na dare daya domin mafiya yawan masu kawo irin wadannan hanyoyin ga mutane a zahiri ko a yanar gizo zaka samu cewa yan damfara ne, amma dai na tabbata cewa zan kawo ingattattun hanyoyi wadanda idan mutum ya dage, yayi juriya kuma zaici moriyar kasuwancin.
           MUHIMMANCIN KASUWANCIN YANAR GIZO-GIZO
Ba a buqatar wani babban jari, ko ofishi kafin afara wannan kasuwanci. Dakin ka/ki zai iya zama babbabn ofishin ka/ki. Babban abin buqata kawai shine na`urar kwamfuta sai modem wanda zai sada ka da yanar gizo. Ko kuma wayar sadarwa wadda ake shiga  yanar gizo da ita.
  Kowa da kowa zai iya yin wannan kasuwancin mace ko namiji, babba ko yaro. A wannan kasuwancin, ba`a buqatar kwalin digiri, difloma ko NCE, abin nema kawai wanda zai fara kasuwancin yasan yadda zai karanta ya fahimta da yadda zai rubuta, sai kuma yadda zai sarrafa na`urarsa mai kwakwalwa ko wayar sadarwarsa.
wanda zaiyi wannan kasuwanci yana da yancin gudanar da kasuwancinsa a duk sanda yaso, da safe ko da rana ko kuma da dare, domin ba kamfani bane da zasu ce maka lokaci kaza lalle ka fito wajen aiki.
a wannan kasuwancin akwai kwastomomi masu tarin yawa wadanda a kullum suke jiran ka/ki kawo musu wani abu sabo wanda ya hadar dana ilimi, labari, hoto, hoto mai motsi wato video, ko wani ra`ayin ka akan wani abu su kuma su biya ka kudi.
haka kuma kasuwancin baya baqatar ace jiddin walahairan kana/kina kasuwa, kawai matsawar ka kasa abubuwa masu amfani wadanda mutane sukeso, to kana iya kwanciya bacci ma, domin kudade ne zasu ta kwankwasa maka qofa ta hanyar alatin waya daga asusun bankin da kake ajiya.

MATSALAR KASUWANCIN YANAR GIZO
  Kamar yadda aka sani, duk abin da yake da amfani, to yana da rashin amfani ko da kadan ne. Daga cikin matsalolin wannan kasuwanci, akwai rashin tabbas na cewa inda zaka saka kudin ka ingattacce ne ko kuma guri ne nay an damfara. Domin akwai tarin yan damfara a yanar gizo wadanda ake kira scammers, ko crackers, amma cikin rashin sani wasu sunfi kiransu da hackers wadanda qiris suke jira kayi kuskure su kuma suyi awon gaba da kudinka.
    Hanyar kariya kuwa itace mutum yayi taka tsan-tsan, duk shafin daya shiga, na`urarsa tace bata gamsu da ingancin wannan shafin ba to zai fi kyau mutum ya hakura don kaucewa yan damfara dama cutuka masu yaduwa na yanar gizo wato virus. Haka kuma duk wani shiri da akaiy maka/miki talla a yanar gizo wanda akace zakayi/zakiyi arziqi na dare daya, to mutum ya guji shiga, domin yan damfara sunfi amfani da wadannan shirin don su jawo hankalin masu idon cin naira.

   Kafin na fara bada hanyoyin da zaa iya samun kudi a yanar gizo, akwai muhimmin abu da mutane ya kamata su sani, wannan abu kuwa shine hanyar da kudi zasu shiga aljihun wanda zaiyi kasuwancin kuma hanyar da zai tura da kudinsa don siyen abin da yake so.
    Duk abinda kake son siya ko siyarwa a yanar gizo, ba zaka sami dama ba har sai ka nemi daya daga cikin wadannan katuna dazan kawo, katunan sune; debit card, master card, visa card ko paypal. Ana iya samun wadn nan katuna masu kama da katin ATA a bankuna irinsu GT bank, zenith bank, sterling bank da sauransu.
Don naka kamar yadda ake siyen katin waya ko biyan kudin wuta da ATM, haka ake siyan abubuwa a yanar gizo da daya daga cikin wadancan katuna, sai dai idan abin irin su mota ne ko wayar sadarwa, za`a caje ka wasu kudi da ake kira shipping domin a kawo maka wani waje mafi kusa dakai yadda zakaje ka amshi kayanka.

HANYOYIN DA ZA`A IYA SAMUN KUDI TA HANYAR YANAR GIZO
    Hanyoyin suna da tarin yawa, amma da yake sun kasu gida-gida ne, ina sa ran in sha Allah zan kawo kadan daga ciki, nayi bayanin su tare da bada misalai dai-dai gwargwado.
1.   Affiliate marketing
         Wannan hanya tana daga cikin mafiya yawan hanyoyin samun kudi a yanar gizo, domin akan samu sama da naira dubu dari hudu a wannan fanning.
    Ma`anar wannan hanyar itace dillanci, wato zaka zama dillali ne, ka amso dillancin sayar da hajar wani kamfani kazoo ka kasa a shafin ka na yanar gizo ko kuma a shahararrun shafukan duniya irinsu facebook, yahoo ko google.
     Idan mutum ya lura sosai, idan ya bude shafin yanar gizo, yakan ga wasu hotuna a gefe da gefen shafukan wadanda suke dauke da talloli, wadan nan talloli su ake kira Adsense, ko kuma ace Ads.
     Yadda ake samun kudin kuwa shine, za kayi yarjejeniya da masu kayan, zaka zabi yadda kake so su biya ka aduk sanda wani yayi maka kilik akan tallar, kai kuma zaka fayyace musu cewa acikin mutane kaza da zasuyi kilik akan tallar, kana sa ran mutane kaza zasu sayi hajar taka. Idan har abin da ka saita yayi dai-dai, zaka samu kudi, idan kuwa aka samu mishkila, to zasu zaftare maka kudi, don haka ana buqatar ayi taka tsan-tsan.
YADDA AKE SA TALLA (ADS) A SHAFIN FACEBOOK
Idan zaka sa talla, wajibi ne mutum yayi la`akari da abin da mutanen wajen da zai kaiwa tallar suka fi so domin samun kasuwa, kuma kamar yadda aka sani shafin facebook yana daga cikin shahararrun shafuka na duniya da miliyoyin mutane ke amfani dashi a kullum, shi yasa maimakon ace sai ka qirqiri shafinka na kanka, kana iya amfani da facebook don samun kudi, inda zasu dauki harajin amfani da shafin su da kayi sub aka ragowar kudinka.

Tallar da tafi garawa a yanar gizo sune:-
singlesnet. Adireshinsu; www.publishers.single.com/register
mate1          ,,     ,,          mate1.com/affiliates
true             ,,      ,,,          true-affiliates/sign.asp
clickbank    ,,      ,,           www.clickbank.com   (amma basa amsar yan najeriya)
eye ern       ,,       ,,          www.eyeearn.com-signup

MATAKAN DA ZA,ABI DON YIN RIJISTA
ka ziyarci daya daga wadannan adireshin da na kawo
ka cike fam din da aka kawo, a ciki zaka zabi qasa, shekaru ko jinsin mutanen da kake son a kafawa tallar taka.
kayi rubutu wanda zai jawo hankalin mutane suyi maka kilik ko su sayi kayan, ka sanya hoto main an sha`awa wanda zai jawo hankali.
sai ka sai ta yadda kake so a baka a duk kilik daya, da yadda kake tsammani za`a siyi kayan a iya adadin kilik da zaka ware.
        A rubutu na gaba insha Allah zan cigaba da qarin bayani.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
    08060869978

KASUWANCIN YANAR GIZO 2




Assalamu alaikum.

Hanyoyin da ake samun kudi a yanar gizo;-
Article writer
A wannan fannin, mutum yana iya zama mai rubuce-rubuce ga jaridu, qasidu ko wasu gurare na dab`I na duniya, inda zasu nemi ka rinqa rubuta musu sharshi kan al`amuran yau da kullum da suka shafi siyasar duniya ko ta qasashe, ko kuma rubutu kan kasuwanci da yadda za`a habaka kasuwanci, ko rubutun daya kebanci soyayya, ma`aurata da yarda za`a zauna lafiya da juna, dama sauran dumbin fannoni wadanda mutane suke zumudin karantawa idan sun ganshi.
Mai sha`awar wannin fannin, babu wata wahala, kawai abinda zaiyi shine, yayi tunani a karan kansa wane fanni yake da gogewa, inda zai rinqa yin rubuce-rubuce mai qayatarwa da jan hankali, zai kuma  tabbata zaiy iya kiyayewa da qa`idojin rubutu na harshen turanci, daga nan sai ya ziyarci search engine kamar google a adireshinsu www.google.com, idan shafin ya bude, sai ya binciko qasida, ko jaridar da suka kebanci irin abinda yake da kwarewa akansa. Idan yafi kwarancewa akan rubutun daya shafi siyasa, kai tsaye qasidun siyasa zai bincika.
Idan har kayi haka, zai samu shafuka masu tarin yawa na qasidu(magazines), da jaridu na dunya, daga nan sai ka zabi wadda ta kwanta masa, ka ziyarci shafin jaridar ta hanyar kilikin akan adireshinta, sai ka karanta irin abubuwan da jaridar ko qasidar suke bugawa wadanda mutane irinka ke turo musu, daga nan sai ka tuntubi editan jaridar ko qasidar. A wannan gabar ne editan zai so yasan wanene kai, yasan kwalin rubutun ka da kuma abinda kake ganin zaka iya yi musu rubutu akai tare da tura wani samfuri na rubutun da ka tabayi. Indai mutum yabi qa`idoji daki-daki, zai samu gurbin yin rubuce-rubuce, inda za`a rinqa biyansa a mako ko a sati ko kuma duk rubutun daya gudanar.

YADDA MUTUM ZAI IYA YIN RUBUTU GA SHAFUKAN YANAR GIZO A BIYA SHI
Kamar yadda nake tunanin wasu suna da masaniya, yanar gizo ba ma`asumiya bace wadda ake yi mata wahayi daga sama, duk tulin bayanan da muke gani yau da kullum da suka shafi fannoni da dama na rayuwa da har wasu ke ikirarin duk abin da ka nema a yanar gizo zaka samu, to mutane ne mahaluqai suka dauki gabarar rubutawa. Wasu sun rubuta ne a matsayin (blog) kuma a kyauta, wasu kuma sun rubuta an biyasu. Don haka kai ma kana iya yin irin wadannan rubuce-rubuce a shafukan yanar gizo a fannin da ka sani. Domin yin haka, zaka iya ziyartar:-
www.getafreelancer.com
www.freelancewriting.com
wadannan adireshoshi suna da ban mamaki, aikin su kamar yankan wuqa( ta bakin mata) haka yake. Kawai abin da zakayi shine, ka ziyarci daya daga adireshin sannan kayi sign up, zasu nemi ka fada musu fanning da kake rubutu akai tare da tura musu samfurin rubutun da ka taba yi.

www.debthelp.tu
wannan shafin yana da wuya kafin su amince zaka rinqa yi musu rubutu, amma da zarar sun amince da ingancin ka, zasu baka dama ka rinqa yi musu rubutu suna biyanka $20 dala ashirin a duk rubutu. Idan kullum zaka rinqa yi ba zasu damu ba wajen baka kudin ka a kullum.
www.epinions.com
wannan ma wani shafi ne mai ban mamaki, ana samun kudi matuqa ga masu wayo. Yuadda akeyi shine idan kayi rijista dasu, zaka rinqa rubuta musu ra`ayinka ne akan kayayyakin su (products), duk wanda yayi kilik akan wannan ra`ayin naka, zaka samu kudi. Don haka anan ana yin ramuwar kura, idan kayi wa wani kilik, shima sai yayi maka, amma idan kana tunanin zaka rinqa yiwa kanka kilik, tofa wayon su ya isa, duk kilik da kayiwa kanka da kanka sai sun zaftare maka kudin da ka samu. Adsence ma haka yake.

www.articlemarket.com
www.ehow.com
da sauransu.

YADDA MUTUM ZAI SAYAR DA HOTUNA A YANAR GIZO-GIZO
Wataqila wannan ya bawa wasu mamaki, amma a yanzu yanar gizo tayi bunqasar da kome kake dashi, kome ka sani kuma koda ilimin kora jaki ne, zaka iya samun kudi dashi domin wani yana can yana neman irin wannan abinda kai ka sani din. Don haka zaka iya zama mai daukar hoto na mutane, dabbobi, fulawowi da sauransu, ka sayar a yanar fizo.
Shafukan da ake sayan hoto ko a siyar sun hadar da:-
www.photoprofit.com
www.dreamtime.com
www.stockphoto.com
www.fotolia.com
www.freeimages.com

Idan kuma mutum yana sha`awar siye-siye ne a yanar gizo, indai ya mallaki daya daga cikin katuna masu kama da katin ATM, sai ya ziyarci daya daga cikin manyan shagunan yanar gizo, inda zai siyi kaya a kawo masa har gida cikin  rahusa. Adireshin shagunan sune:-
www.amazon.com
www.ebay.com

Anan nake ganin zan jingine wannan fanning, amma cikin ikon Allah a gab azan tabo wasu bangarorin. Ina fata yan uwana zasuci moriyarsa.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo.
08060869978

Thursday, 30 January 2020

WANENE SADIQ TUKUR GWARZO?

TARIHIN SADIQ TUKUR GWARZO
(Global Goodwill Ambassador)
  Shi bafillatani ne, an haife shi a garin Gwarzo, ya fito ne daga zuriyar Mallam Isah wanda Ɗan Gwarzo Baba ya gaiyato daga Sokoto domin tseratar da garin bisa wani mummunan hari da Ɗan baskore, sarkin Maraɗi na zamanin ke shirin kawowa wannan gari a ƙarni na goma sha takwas.
  Sadiq Gwarzo ya yi karatun addini dana boko a garin Gwarzo, sai a shekarar 2005 ya bar garin zuwa kwalejin fasaha mai suna GTC BAGAUDA domin kammala karatun sakandare, inda ya karanci fannin 'Carpentry and Joinery'. ya kammala karatun a shekarar 2008.
  A shekarar 2009 Sadiq Gwarzo ya yi karamar Diploma akan 'Computer Networking and Maintenance' a cibiyar koyar da karatun Kwamfuta ta Himma dake Gadon kaya a garin Kano, daga nan sai ya koma Gwarzo ya sake yin karatun karamar Diploma a 'School of Environmetal Studies' wadda ke ƙarƙashin 'Kano state Polytechnique', inda ya karanci 'Painting and Decoration'.
  Bayan ya kammala a shekarar 2011, sai kuma ya samu shiga 'School of Nursing kano' a shekarar 2012, ya kammala kwalejin a shekarar 2015 a matsayin cikakken majinyaci.
   Sannan yabsake komawa makarantar School of Hygiene a shekarar 2017 tare da karantar babbar diploma watau 'HND Public Health Nursing', inda ya kammala a 2019.
  Haka kuma yayi kwasa-kwasai da yawa ta yanar gizo daga  jami'ar buɗe ta ƙasar Australia, daga ciki akwai:-
-Anthropology: Becoming Human
-Origin of Crime
-Asronomy: Discovering the Universe
- Midwifery Education
-World Music
Da wasun su.
  Sadiq Gwarzo ya soma rubuta littafi tun yana firamare, kasancewar sa ya tashi a matsayin makaranci. Amma dai littafin sa na farko shine 'Nasara a Tafin Hannu' wanda ya wallafa a shekarar 2010. Daga nan sai 'Hikimar Allah Na Da yawa' a 2012, da 'Ilimin Kasuwanci' a 2015, sai kuma ' The Art OF Talking cure' a 2016.
Sauran littattafan da ya wallafa sune:
-Sabuwar Fuskar Ilimin Falsafanci
-Sirrin Rayuwa a cikin ilimin Lambobi
-Tarihin Tsohuwar Daular Baƙin mutum
-Kula da Lafiyar Mata masu ciki da kananun yara
-Asalin Hausawa daga kaɗe-kaɗen su
-Tarihin Daulolin Musulunci
-Magana Hausa
-Madubin Sarakuna
-Tarihin Jihadin Danfodio a Kasar Hausa
 Sadiq Gwarzo ya fi karkata akan rubututtukan da suka shafi 'tarihi', shiyasa wasu marubutan kan yi masa laƙabi da suna 'Gwarzon Tarihi', amma duk da haka ya yayi rubututtuka da dama akan fannikan siyasa, kasuwanci da zamantakewar rayuwa. Akan haka, ya rubuta muƙalu sama da 250 waɗanda ya taskance a turakar sa ta yanar gizo  http://sadiqtukurgwarzo.blogspot.com. Haka kuma ya taya Mallam Salisu Durmin Iya gabatar da shirin 'Hausa Rigar Siliki' a gidan Radiyon Guarantee na kusan tsawon shekara ɗaya a inda suka rinƙa tattaunawa akan tarihi da kafuwar ƙasashen Hausa. Baya da haka, Sadiq Gwarzo da taimakon masana kuma marubuta irin su Farfesa Yusuf Adamu, da wasun sa, sun kafa wata cibiya mai rajin bincike akan tarihin hausa da hausawa wadda suka sanyawa suna 'Center for the study of Hausa Civilisation', Ƙari akan haka, Sadiq Gwarzo na gabatar da ayyukan fassara ga kamfanoni na gida dana waje, da rubututtuka na tarihin ɗai-ɗaikun al'umma da kuma jaridu irin su Leadership Hausa, Manuniya da wasun su na yanar gizo. 
   A shekarar 2019 kungiyar duniya mai rajin tallafawa al'umma mai suna 'Global Goodwill Ambassadors' suka baiwa Sadiq Tukur Gwarzo lamba da sahalewar zama mamban su bisa ayyukan alheri da yake yi a fannonin taimakon al'umma. Tun kafin wannan lokacin, ya kasance a gaba-gaba wajen yaƙi da cututtuka masu damun al'umma misalin HIV, da Malaria  ga ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa.
    Zuwa yanzu, Sadiq Gwarzo na gabatar da ayyukan sa na rubuce-rubuce, da na ƙungiyoyi tare kuma da kasuwanci. Sannan tare da haɗin guiwar marubuci Ɗanladi Haruna, ya kafa kwalejin farko ta yanar gizo wadda ake koyar da ilimai da harshen Hausa. Babban burin sa shine Hausawa su sami ilimi a sauƙaƙe, su kuma soma gogayya da sauran al'ummar duniya akan haka. Dalili kenan da ya samar da kwalejin domin share fage ga duk wani son koyo da koyarwa. Kuma ana sa ran kwalejin zata fassara manyan ilimai da ake taƙama dasu a zamance anan duniya domin koyar da al'ummar Hausawa.
   Zuwa yanzu, Sadiq Gwarzo na da mata ɗaya, da ɗa ɗaya.
   

TARIHIN ZUWAN TURAWA AFIRKA TA YAMMA

TARIHI ABIN TUNAWA: ASALIN YADDA TURAWA SUKA BINCIKO AFRIKA TA YAMMA
Daga SADIQ TUKUR GWARZO
Tun da jimawa, Labarai masu ƙayatarwa suka cika kasashen Yammacin Turai dangane da yankin Afirka ta yamma. Tatsuniyoyi sun shahara akan haka. Labarin Attajiri Mansa Musa mai kyautar gwala-gwalai ya zamo abin jimami a Ingila, haka kuma labarin shaharar Kogin Kwara ba zai misaltu ba.
A wancan lokacin dai, turawa na ɗaukar birnin Tambuktu a matsayin birnin Gwal, domin haka ma suke yiwa garin laƙabi da suna 'birnin gwal', suna kuma da ƙarancin sani game da kogin Kwara.
A kan hakane aka kafa wata kungiya a birnin landan mai suna 'Association for promoting the discovery of the interior parts of africa' a shekarar 1788, wadda a taƙaice ake ambatar ta da 'African association'. Kungiyar, wadda sir joseph Banks ke jagoranta, ta ƙunshi manyan mutane, masana da attajirai, kuma tana da burin binciko zance mafi gaskiya dangane da Birnin Tambuktu, da kuma kogin Kwara. Wannan yunkuri shine asalin fara laluben turawa a kasashen Afirka ta yamma.
Akan haka, an rinƙa sauraron matafiya da sauran masu binciken tarihin duniya dangane da abinda suka sani game da Tambuktu da kuma kogin kwara. Ga misalin abubuwan da aka samo;
I. Bayani yazo daga James Bruce dan Kasar scotland, wanda a shekarar 1769AD ya isa kasar Habasha cewa "daular Tambuktu karkashin mulkin Muhammadu Askia I, tayi matukar karfi a wajajen ƙarni na 13 zuwa na 15, kuma itace ta mamaye mafi yawan ƙasashen yammacin Africa, tun daga yankin Gambiya da senegal, har zuwa sokoto dake ƙasar Hausa. A gabashi kuma sai da ta dangane da kogin kwara. Garin Timbuktu kuwa, yana dauke da baƙi masu yawa, kuma gari ne mai cike da arzikin gwal.
ii. An samu labari daga wani masani mai suna Al Hassan Bin muhammad al-Wazziniz zayyati wanda akewa Laƙabi da Leo Africanus (ma'ana zakin Afrika) wanda kuma akace kakannin sa na cikin gungun musulman da sukayi gudun hijira izuwa sassan duniya daga birnin Andaluz a shekarar 1492 sa'ar da Sarki Ferdinand da Sarauniya Isabella suka cinye garin da yaki, ga abinda ya  faɗa bayan ya samu damar ziyartar Timbuktu "ana kawo hatsi, shanu, madara da man shanu mai tarin yawa izuwa garin Timbuktu duk kuwa da kasancewar garin cikin sahara inda babu ƙoramu da lambuna. Babban abinda mutanen garin ke musayar kasuwanci dashi shine gishiri''.
Ya ƙara da cewa ''Sarkin Timbuktu attajiri ne na gaske, wanda ya mallaki sulalla na zinare marasa adadi. A koda yaushe kuma idan yana tafiya zaka samu kimanin dawakai 3000 suna rufa masa baya. Sannan yana da tarin likitoci, alƙalai, malamai masu wa'azi da sauran masana zazzaune a fadar sa''.
Daga wajen Leo Africanus ne kuma turawan ingila suka fahimci cewa Gishiri yana da matuƙar daraja a Timbuktu, saboda ya ayyana cewa zuwa akeyi dashi daga wani gari mai suna Tangaza, wanda yake da nisan Mil ɗari biyar daga Timbuktun. Har ma yake cewa "na taɓa kasancewa a Timbuktu a lokacin da farashin mangalar gishiri yake dai-dai da farashin sisin gwal tamanin".
iii. Wani bayanin ma ya samu daga hannun wani mai suna Asseed El hage Abd Salam Shabeeniy, wanda akewa laƙabi da Shebani, a wajajen shekara ta 1788. Shebani ya rayu a timbuktu tsawon shekara uku, inda har ya leƙa kasar hausa, ga kuma abinda ya naƙalto " Adadin mutanen garin timbuktu zai cimma dubu 40, banda bayi da kuma baƙi mazauna garin. Duk al'ummar garin baƙaƙen fata ne, sannan kuma kusan duk baƙon da zaije garin sai ya auri 'yar garin saboda kyawun matayen su. Kallo daya tak zai sa ka faɗa so da ƙaunar su"
Ƙari akan haka shine labarin Attajirin Sarkin Timbuktu Mansa Musa wanda ya baza duniya. Ance yayi zamani a wajajen ƙarni na 12, shine kuma ya taɓa ziyartar Saudiyya da ɗumbin bayi gami da ɗumbin gwala-gwalai.
Sai dai duk labaran nan, babu abinda akeji game da Kogin Kwara, kuma har izuwa lokacin kafuwar kungiyar, ba a samu wani bature farar fata ba wanda yayi ikirarin yaga Kogin kwara da idanuwansa.
A shekarar 1790, wani tsohon soja mai suna Daniel Houghton ya tunkari wannan kungiya ta 'African Association', da nufin amsar kwantiragen zuwa Africa ta yamma da ƙafa don gani da ido.
  Nan take kuwa kungiyar ta amince masa, ta kuma ɗora masa nauyin ziyartar Tafkin Barra kunda (wani gari dake ƙasar Gambiya) da kuma ƙasar Hausa tare da binciko ainihin inda garin Timbuktu yake, sannan ya ƙarƙare tafiyar a gaɓar kogin Kwara.
 Da yin haka, sai ya shiga kokarin koyon harshen Larabci tare da wani yare na ƙasar senegal mai suna 'Mandingo' ta yadda zai samu damar mu'amala da mutane.
Sannan ya sanya ranar fara tafiya.
A watan Oktoba na shekarar 1790, Hougton ya shigo jirgin ruwa, inda bayan wasu kwanaki ya sauka a gabar Kogin Gambia a wani gari da ake kira Barra. Ya tafi tiryan-tiryan har wani gari mai suna Pisania, daga nan ya risƙi wani gari da ake kira Jonkakonda, daga bisani kuma ya ƙaraso masarautar Wuli a farkon shekarar 1791.
A wannan wuri, ance Sarkin Masarautar Wuli ya karɓi Houghton da girmamawa, har ma ya bashi mazauni a garin sa mai suna Medina. Sai dai ba a jima ba abokan hamayyar Sarkin suka kawowa garin hari, inda kuma sukaci nasarar kone garin, har ma kayyayakin Houghton na yaƙi da wasu abubuwa masu amfani suka ƙone ƙurmus. Wannan abu yayi masa ciwo matuƙa.
Duk da haka, Houghton baiyi ƙasa a guiwa ba, inda yaci gaba da tafiyar sa yana neman garin Timbuktu.
  Ance a wajajen watan Mayu na shekarar 1791, Houghton ya bar gaɓar tekun Barra, sannan ya kutsa kai don tunkarar Timbuktu. A lokacin ne kuma ya tura da saƙo zuwa Ingila mai ɗauke da labarin yadda tafiyar sa take kasancewa. Saƙon ya isa birnin Landan cikin nasara.
Daga nan, Houton ya samu damar gewayawa ta kogin Senegal, shine ma sarkin wani gari yaci mutuncinsa, da ƙyar ya samu kuɓuta ya isa masarautar Ferbanna dake yankin Bambu na ƙasar ta senegal acikin damuna ta wannan shekara.
Daga nan ne kuma ya hadu da wani Matafiyi mai suna Madegammo, wanda yayi alƙawarin zai yiwa Houghton jagoranci izuwa birnin Timbuktu a kyauta. Sun fara wannan tafiya ne a watan yulin 1791, shine har Houghton ya ƙara turawa da saƙo gida yana mai labarta yarjejeniyar da sukayi da matafiyin, ya aika saƙon ne ta hanyar matafiya, kuma sannu-a hankali ya isa birnin landan.
  Wannan saƙon shine ya zamo na ƙarshe, domin daga nan ba a ƙara jin ɗuriyar sa ba.
A shekara ta 1793, labari mai tushe ya riski Landan cewar Houghton ya samu kansa cikin mawuyacin hali yayin tafiyarsa zuwa Tambuktu, wannan ne yasa tafiyar ta sire masa, abokan tafiyar sa kuma suka ribace shi, inda suka sauya akalar tafiyar izuwa wani gari mai suna Tisheet (wanda yake a ƙasar Mouritania a yanzu). Amma kwana biyu da yin haka, sai Houghton ya fuskanci cewa abokan tafiyar sa na yunƙurin hallaka shi, wannan yasa ya tsere musu, ya shiga cikin sahara ba ruwa ba abinci a tare dashi, a daddafe ya isa wani gari mai suna Tarra, inda kuma cikin rashin sa'a, mutanen garin suka hanashi ruwa da abinci, wannan yasa yunwa ta halaka shi.
  Ance ko gawar Houghton mutanen garin ƙin binne ta sukayi, a ƙarshe tsuntsaye ne suka yagalgalata a banza.
Wannan labari yayi matuƙar ɓatawa Ingila Rai, sannan ya dakushe guiwar masu son jin labarin africa ta yamma da yawa.
   Amma ba'a fi shekaru biyu ba, sai ga takarda daga hannun wani baturen ƙasar scotland mai suna MUNGO PARK, yana neman sahalewar ƙarasa aikin da Houghton ya fara..
Tafiyar mungo park (wadda tarihin ta yazo a littafin Mungopark Mabuɗin Kwara) tana ƙunshe da darasi mai tarin yawa. A cikin ta ne mukaji yadda iyaye da kakanni suka rayu a wancan zamani, da kuma yadda Mungopark ya rinƙa bibiyar matsalolin da marigayi Houton ya fuskanta, har ma da laifuffukan da ya yiwa sarakunan africa ta yamma, dalilin dayasa suka tsaneshi kuma kenan har abin ya kai shi ga halaka!

TARIHIN MAHAIFIN MANI MAKWALLA DA YADDA YA KUƁUTAR DA GARIN GWARZO

TARIHIN MANIN MAKWALLA
Sunan Mahaifin Manin Makwalla Mallam Isah, shi Bafillatani ne Batoranke, kuma malami masanin asararu, a sokoto yake da zama.
  Wata rana a wuraren ƙarni na goma sha takwas kafin zuwan turawan mulkin mallaka, watau jim kaɗan da yin jihadin fulani a ƙasar Hausa, sai wani sarki ya aiko da goron yaƙi zuwa garin Gwarzo.
  Garin Gwarzo an sani cewa Bamaguje Gwarzo ne ya kafa shi, amma daga baya wani Bafillatani mai suna Baba ya karɓe iko da garin, har kuma ya kasance fulanin ke gadon mulkinsa, amma kuma ana kiran sarkin garin da suna 'Ɗan Gwarzo', don haka an samu cewa a lokacin jihadi, fulani basu yaƙi garin ba, har ma ana cewa Shehu Abdullahi Gwandu watau ƙani ga Mujaddadi Usman Ɗan Fodio, ya sauka a garin yayin da ya taho daga sokoto zai je Birnin Kano.
   Don haka, bisa labarin zuwan wannan yaƙi, sai ake ganin duk da kasancewar garin Gwarzo a lokacin zagaye yake da ganuwa domin kariya daga mahara, amma lalle an tabbatar zuwan wannan sarkin bala'i ne ga garin. Don haka sai Ɗan Gwarzo na lokacin ya shiga shawarwarin mafita.
   Akan haka wani bafaden sa ya bashi labarin wani malami mai suna Mallam Isah dake sokoto, tare da shawarar aje azo dashi domin samun kuɓuta daga wannan ƙangi.
  Ɗan Gwarzo ya amince da wannan shawara, sannan ya tashi fadawa da abin alheri zuwa sokoto da hanzari. Da isar su suka gabatar wa da Mallam Isah saƙon Ɗan Gwarzo tare da buƙatar su ta ya biyo su zuwa garin Gwarzo domin taimakawa da adduar samun kariyar musibar dake tunkaro garin.
Abun da akayi kenan, Mallam Isah ya taso tare da fadawa suka nufo Gwarzo. Kwanci tashi sai ga su a garin. Ɗan Gwarzo yayi masa marhaban lale tare da sake gabatar masa da halin ƙuncin dake gaban su.
Mallam Isah yace masa kada ya damu, insha Allahu Allah zai yi maganin wannan fargaba. Sannan ya nemi a samu wani da zai yi masa jagoranci wajen kewaya ganuwar garin Gwarzo.
Ance Mallam Isah carbi ya ɗauka a hannunsa yana ja, yana lazimi, yana bin ganuwar data zagaye garin Gwarzo yana addua, bai gushe ba har sai da ya kewaye garin baki ɗaya, sannan ya koma masaukin sa ya zauna.
Aikuwa Allah da ikonsa, koda waɗannan maharan suka zo, sai garin ya ɓace musu, ance daga cikin Gwarzo ana jiyo sautin kiɗe kiɗen su da haniniyar dawakansu, amma kuma Allah ya hana su ganin garin balle su durfafe shinda yaƙi. A haka sukaƙaraci zaman su suka koma inda suka fito.
Jim kaɗan da faruwar haka sai Mallam Isah yace da Ɗan Gwarzo zai koma gida wajen ahalinsa, sai kuwa Ɗan Gwarzo ya shiga lallami da magiyar kada ayi haka, domin yana fargabar kada bayan tafiyar sa maharan su sake dawowa.
Babu yadda Mallam Isah ya iya, sai ya aike aka taho masa da ahalin sa daga Sokoto zuwa Gwarzo.. Kunji asalin yadda Manin Makwalla ya tashi a Gwarzo.