Wednesday, 11 December 2019

TARIHIN GARIN WUDIL

TARIHIN GARIN WUDIL

Sadiq Tukur Gwarzo
Garin Wudil na ɗaya daga manyan garuruwa a jihar kano kuma gari ne mai ɗauke da tarihi, don haka muka ga dacewar taskance kaɗan daga ɗumbin tarihin wannan gari.
  Ance wani maharbi ne ya sari garin, shikuwa daga Katsina ya taso. Tana iya yiwuwa Muhammadu sunansa, ko kuma Daudu, amma dai an tabbatar shine na farko da yazo ya zauna a wannan wuri inda garin wudil yake a halin yanzu.
   Ko da yake, da fari ance acan tsallaken ruwa ya soma zama, amma sai yayi tunanin yin amfani da ruwa wajen kare kansa da garin da zai kafa daga mahara kasancewar wancan lokaci ana cike da yake-yake da kamen bayi, don haka ya tsallaka ruwa sannan ya kafa Bukkar sa yana mai cigaba da sana'ar sa ta farauta a dajin dake kewayen kogin wudil.
  Sannu a hankali mutane matafiya masu zuwa neman ruwa suka rinka sauka a kusa dashi. Tun wasu na sauka su ɗanyi kwanaki sannan su tashi izuwa inda suka dosa, har kuma aka samu waɗanda suka mayar da wajen kachokan wajen zama tamkar shi. Akan haka akace gungun wasu fulan Joɓawa suka riski wannan maharbin tare da zama kusa dashi. Daga baya kuma sai shugabancin garin ma ya koma hannun su.
Sunan wudil ya samo asali ne daga wata Aljanna da aka tabbatar tana zaune a gidanta dake cikin tsakiyar wannan ruwa na Wudil. Ana kiranta da suna 'Uwar Wudil'.
Babu tabbacin lokacin da aljannar ta soma zama acikin ruwan, amma dai an tabbatar da cewa har yanzu tana nan tare da ahalinta.
  Ance ita fara ce doguwa mai siffar balarabiya, gashinta har gadon baya yake, kuma bata cutar da mutane, domin abaya takan shiga cikin garin Wudil ta yadda har mutane kanci karo da ita ba tare da ta razanar dasu ba. Ansha kuma ganinta a sauran garuruwa dake jikin wannan kogi na wudil.
Aljannar Wudil tana da tsohuwar alaka da mutanen garin wudil. Domin an samu cewar tana taimakon garin wajen samun kariya daga dukkan sharri tare kuma da yin galaba a yakunan da duk garin zai tunkara. Ance abaya, manyan gari na zuwa bakin kogi su yanka shanu, raguna ko tumaki sannan su sanar mata da abinda ya tasowa garin misalin yaƙi sannan sai azo a tafi. Ita kuma aikinta ne tayi duk mai yiwuwa wajen ganin buƙata ta biya.
  Wannan abu yana daga abinda Mallam Bakatsine ya ƙyamata tare da riƙa a matsayin hujjar yin jihadi a  zamanin Shehu Usman Danfodio. Don haka ance da lokacin hijira yayi, sai mabiya Shehu Usmanu dake kano suka tafi wani waje da ake kira Kwazazzabon Ƴarkwando, amma shi Mallam Bakatsine sai ya fita kano ta gabas yaje garinsu Utai ya ɗauki iyalinsa sannan ya ƙarasa garin wudil, inda ya yada zango a wani wuri da ake kira Nagge, anan ya tara runduna tare da zuwa buga yaƙi da garin Gaya inda ya ƙwace iko dashi.
 Duk da kasancewar a lokacin Garin Wudil zagaye yake da ganuwa da kuma ɗumbin jarumai, kuma karkashi Sarkin Kano Alwali amma babu labari mai nuna cewa sarakunan wudil sun yaƙi Mallam Bakatsine, ance hakan baya rasa nasaba da kasancewar a zamanin Fulani ke mulkin garin kuma suna da alaƙa dashi, don haka suka mara masa baya har ya cimma burinsa.
  Ana kiran sarautar wudil da suna Ɗan Daudu, kuma garin yana can gabas da garin kano da misalin tazarar mil talatin. 

Wednesday, 9 October 2019

TARIHIN TSOHON BIRNIN HAUSAWA; KAFIN DABGA

TARIHIN TSOHON BIRNIN HAUSAWA; KAFIN DABGA

SADIQ TUKUR GWARZO, GGA

  Daga cikin tsoffin biranen da Maguzawa suka kafa waɗanda kuma suka shahara a ƙasar Kano tun kafin zuwan jihadin Fulani akwai wannan tsohon garin mai suna 'Kafin Dabga'.
   Wani mashahurin mayaƙi bamaguje mai Suna 'Dabga' ne ya sari garin, shine kuma yayi masa kafi gagarumi domin kuɓuta daga dukkan harin mayaƙan wancan zamani, don haka ake kiran garin da suna Kafin Dabga.
   Garin ya haɓaka, ya shahara, kuma ya samu ɗaukaka. A baya ance zagaye yake da ganuwa, wadda aka yiwa ƙofofi guda huɗu. A kowacce kofa mace da namiji ne suka tsaya aka yaɓe su da ransu saboda surkulle, sannan da wata ƙaya sarƙaƙiya ake rufe kofar shiga birnin ba da ƙofa ba. Don hakangarin ya kasanxe mai tsananin uytsaro.
Idan yaƙi yazo, daka ake sanyawa ayi da dare, sai mayaƙa su shirya da hanzari. Masu kwari da baka su hau saman ganuwa, masu masu da takubba su shige surƙuƙi suna sauraron ko-ta-kwana.
Daga cikin sarakunan da ake iya tuna sunayen su a wannan gari, ance sunan Sarkin Kafin Dabga na farko Dugaji, Bamaguje ne, yayi wannan sarauta kimanin shekaru 400 da suka gabata, ko da yake tsufan kukokin garin da marinar garin na iya kaiwa sama da waɗannan shekarun. Amma dai kwatancin shekarun da ake tsammanin an soma sarauta a garin kenan.
Bayan mutuwar sa sai shi Dabga yayi mulki, wanda asali ance ya zamo tamkar uba ne mai ɗora wanda yake so shugabanci a garin.
 Daga shi sai Also, sannan sai Abdullahi ya fara mulki a zamanin da Fulani suka karɓe sarauta.
Akwai manyan gidajen da har yanzu ake ambata a garin, waɗanda sukayi gadon shugabancin garin, da kuma jarumta tun kafin jihadin fulani, misalin su shine; Gidan Nazundumi, Gidan Dankali, Gidan Butsatsa, da Gidan Gigo.
KUKAR ƳAR FULANI
Akwai wata kuka mai tarihi a wannan gari mai suna kukar ƴarfulani. Ita ƴar fulanin aljanna ce wadda ake da yaƙinin akan wannan kuka gidan ta yake.
Ance a zamanin baya, tana taimakon garin lokacin da yaƙi ya taso, ko kuma wani mugun abu ya nufo garin, inda take sanya sarƙa ta kanan-naɗe mahara.
Ance kuma a zamanin mulkin sarki Abdullahi na garin, yana sanyawa a kai mata ƙwaryar nono da farin goro duk ranar juma'a, ita kuma takan yin shewa da godiya yadda duk wanda ke garin sai ya ji.
TARWATSEWAR KAFIN DABGA
Kafin garin kafin Dabga ya samu raguwar mazauna, ya kasance shahararre mai cike da mutane wanda ya kasance daga gari-gari akan zo masa don yin fatauci.
Sannan garin yayi yaƙe-yaƙe da biranen dake kusanci da ma na nesa misalin Gammo da Ƙiru, har ma ana cewa ba a taɓa cin garin da yaƙi ba.
Sai dai wata annoba da ta faɗawa garin ce tayi sanadiyyar ɗaiɗaicewar sa.
Ance wata baƙar aljana ce ta rinƙa halaka mutane.
Idan dare yayi sai tayi shewa, tace 'Kun Taru?', to fa duk wanda yayi ko da gyaran murya a wannan daren ba zai wayi gari ba. Daga nan aka sanyawa annobar suna 'Kun-Taru'.
Don haka aka rinƙa wayar gari da gawarwakin mutane burjik waɗanda ta halaka, hakan yasa mutanen garin da dama suka ƙaurace masa.
A yanzu dai, garin Kafin Dabga yana nan ƙarƙashin garin Karaye, a jihar kano.

Monday, 12 August 2019

TARIHIN NUFE: KAFUWAR ƘASAR NUFE Kashi na huɗu

TARIHIN NUFE: KAFUWAR ƘASAR NUFE
Kashi na huɗu
SADIQ TUKUR GWARZO
    Marubuci Buhari Daure ya ruwaito a littafinsa 'Tarihi da Al'adun Mutanen Najeriya' cewa kafuwar ƙasar Nufe ya wanzu a wajajen ƙarni na goma sha shidda ne. Inda yace asalin Nufe dana Igala ɗaya ne, sai wani ɗan sarkin masarautar Idah mai suna Tsoede yayi gudun hijira tare da kafa masarautar Nupe wadda ta haɗe ƙauyukan Beni, Bidda, Benu, Debo, Tafiya, Doka, Gaba, Dibo da Kupa.
Amma binciken Dr. Sidi Tiwugu Shehi ya kawo ra'ayoyin masana da yawa  saɓani da wannan.
Daga ciki akwai masu cewa asalin Nufawa zuriyar wani balarabe ne mai suna Uqba bn Nafiu wanda ya baro ƙasar su ta larabci tare da zama a ƙasar Nupe.
Wasu kuma suka ce Nufawa sun fito ne daga wani Mafarauci balaraben Misira mai suna Abdulaziz wanda ya gudo daga ƙasar sa ya sauka a Doko Dazi cikin ƙasar Nufe dashi da ahalinsa. Daga nan aka sanya musu suna 'Nefiu' da yaren ƙabilar Beni daya tarar, wanda ke nufin 'wanda ya gudo daga wani wuri' .
Sannu a hankali sai sunan ya sauya zuwa Nufe ko Nupe.
Wasu kuma sunce Asalin Nufawa daga ƙasashen Katsina, Kano da wasu makusanta suke. Har ma Clapperton yace sunan Sarkin su Tsoede, kuma sun zo ƙasar Nupe ne daga wani birni da ake kira Attah Gara.
   Shikuwa Ndagi Abdullahi ya tafi akan cewa Nufawa suna kakannin Hausawa, Yarabawa da Inyamirai. Inda yace zuriyar Nufawan ce ta fantsama tare da samar da waɗannan yaruka (ko ace ƙabilu)
Amma dai masani S.F Nadel ya raba Nufawa gida huɗu daga abinda ya kawo a littafinsa mai suna 'Social Symbiosis and Tribal Organisation'. Ga rukunan kamar haka:-
Rukuni na ɗaya sune Ndachezhi, watau Mafarauta kuma asalin mazauna ƙasar Nupe waɗanda akace suna zazzaune a ƙauyuka sama da shekaru dubu da suka gabata.
Rukuni na biyu sune Esozhi, suma asalin Nufawa ne waɗanda suka jima a ƙasar Nufe har ma suka  kafa birnin Kutigi.
Rukuni na uku sune Benu, waɗanda suka yo hijira daga ƙasar Bornu. Su kuwa da yawansu malaman addinin Islama ne da masu fatauci, daga baya ne suka samu ikon wasu yankunan Kutigi.
Sai Rukuni na huɗu waɗanda ake kira Konu, waɗanda asalinsu bayi ne da aka kamo wurin yaƙi daga ƙasashen Yarabawa, daga baya aka ƴantar dasu tare da basu mazaunai a ƙasar Nupe.
Sannan binciken masana kimiyya da aka gudanar a yankunan Jebba, Giragu, Tada, Oyo-ile, Esie-oba da wasun su ya nuna cewar ƙasar Nupe tana ɗauke da mutane tun sama da shekaru 3000 zuwa dubu 10,000 kafin haihuwar Annabi Isah A.S.
Wannan yasa ake hasashen cewar asalin ƙabilun da suka rayu a wannan yanki wanda ya mamaye yankin Abuja da wasu yankunan tsakiyar Nigeria, sune suka haifar da ƙabilun Yarabawa, Inyamirai, Nupawa, Igala, Idoma, Ebira da Gbayi.

Saturday, 13 July 2019

TARIHIN HAUSANDA HAUSAWA: MAHANGA TA 7

TARIHIN HAUSA DA HAUSAWA: MAHANGA TA 7
Sadiq Tukur Gwarzo

Littafin 'Hausawa da Maƙwabtan su' wanda turawan mulkin mallaka da haɗin guiwar wasu hausawa suka samar mai ƙunshe da tarin zantuka  game da tarihin Hausawa da maƙwabtan su ya danganta asalin Hausawa ga Borno.
   Aka ce Sarkin Borno na da wani bawa mai suna Bawo, babu wanda ya san asalin sa, ko dangin sa. Amma abinda aka sani shine Sarkin Borno ya jiɓanta shi a kan biranen Hausa guda bakwai da ake kira Hausa bakwai yana mai riƙe dasu yana tattara haraji tare da kula da lamurorin su, har ya haifi ƴaƴa bakwai.
   A zamanin da ya ga alamun mutuwa sai ya sarautar da waɗannan garuruwa ga ƴaƴayen nasa. Kowannen su ya bashi birni guda.
  Har aka ce wanda ya sa a Daura ba namiji bane, mace ce mai suna Daura. Saboda haka ake ambaton garin da sunanta.
   Haka kuwa itace babba a cikin ƴaƴansa, itace ƴaruwar sarkin katsina da sarkin Kano da sarkin Gobir, domin dukkan su uwarsu ɗaya.
   Kuma sarkin Burmi da Sarkin Zazzau uwarsu ɗaya. Sarkin Rano kuwa shi kaɗai ne wurin uwarsa.
Saboda haka sai ya zamana ƴaƴayen sun cigaba da bayar da harajin ƙasashen su zuwa Daura, daga nan kuma ana aikawa Borno zuwa ga Sarkin ta.
Sarkin Gobir Bawa kaɗai ne ya ƙi bada harajin nan, sai kuwa yaƙoƙi suka rinƙa aukuwa tsakanin garuruwan da Borno, daga bisani ya ƴamtar da ƙasashen Hausa daga Borno.
Wannan abu tabbatacce ne a cikin labarun da aka faɗe su, haƙiƙa asalin su ƴaƴa ne, su ne ragowar Kibɗawa. Su kuma Kibɗawa sune jama'ar Fir'auna da suka tafo daga Misira suka cika garuruwan Ahira har suka tafi Gobir suka fitad da waɗanda suke cikinta, sune waɗanda suka mallake ta daga ƴaƴan Bawo suka karɓe sarauta daga hannun mutanen wajen. Suka rinƙa yin aiki daga abinda suka iske ƴaƴan Bawo suna yi, suna masu biyan haraji har zuwa lokacin da Bawo ya hana biya.

Monday, 10 June 2019

MAHANGA TA 8: HAUSA DAGA YANKIN ASIA

MAHANGA TA 8: HAUSA DAGA YANKIN ASIA
SADIQ TUKUR GWARZO

Wannan mahanga ta kalli kachokan ɗin harshen Hausa ne wanda Hausawa ke amfani dashi tare da yanke hukuncin cewa asalin Hausawa daga yankin Asia suke.
  Harshen Hausa dai ɗaya ne daga rukunin harsuna kimanin 250 masu suna 'Afro-Asiatic languages',  (Semito-Hamitic), waɗanda aka fi samu  a Arewaci da yammacin Afirka, Kasashen Larabawa da wasu tsibirai na yankunan Yammacin Asia.
  Asalin wannan suna dai na 'AFRO-ASIA' wanda ya haɗa kalmomin Africa da Asia watau ya fito ne daga wani   Ba Amurke masanin Harsuna  mai sunaJoseph H. Greenberg.
  Sannam dashi da wasu Masanan  sun yi hasashen cewa dukkan waɗannan harsuna kimanin 250 sun fito ne daga wani harshe guda ɗaya wanda akayi hasashen ya wanzu a duniya kimanin shekaru 15,000 kafin haihuwar Annabi Isah A.S.
  Ance mutanen yankin Urheimat da suke zaune a Asia tun a wancan taohon zamami ne suke amfami da harshen, kafin daga bisani wasu dalilai suka rinka sanya mutanen yin hijira gami da bazama cikin duniya, ta yadda har bayan shekaru kimanin dubu 17 harsuna 250 sun fita daga jikin yaren nasu.
Masana sun yi hasashen cakuɗuwar ƙabilu da harasa a kusan ɗaukacin yankunan duniya, don haka aka tsammaci wasu daga waɗancan zuriya ne suka keto bahar Maliya zuwa yankin Afirka da zama tare da barbazuwa a tsawon lokaci, inda zuwa yau harshen ya rarrabu zuwa gidaje 5.
 1. Egyptian ( Yankin Tekun Nilu)
2. Amazigh (Berber; Arewacin Africa da Tsakiyar Sahara)
3. Chadic (Tsakiyar Africa, da yankin Tafkin Chadi. Harshen Hausa na ciki).
4. Cushitic (Yankin da ake kira Horn of Africa), da
5. Omotic (Kudu maso yammacin kasar Ethiopia).
  Daga abubuwan da masana suka kalla wajen danganta waɗannan harsuna da juna akwai yanayin fatar masu amfani da harsunan, da kuma falsafar harasan kansu, ko ace wasu jigogi dake tattare da harussan baki ɗaya.
   Misali, harshen Hausa daya fito daga gidan Chadic, an kalli abubuwa da dama kamar kalmar 'Mashi', da yadda jam'in ta ke komawa zuwa  'Masu' wajen sauyawar 'h' da 'i' zuwa 's' da 'u'. Haka kuma an kalli yadda a harshen ake amfani da kalmar 'ka' wajen danganta mallakin Namiji da kuma kalmar 'Ki' wajen danganta mallakin mace, abinda kusan yazo ɗaya a dukkan rukunin harussa aka sanya su a gida ɗaya.
  A karshe, mahangar tana nuni da cewa Asalin masu harshen Hausa mutane ne jikokin wasu ƙabilu da suka rayu a yankin Asia dubunnan shekaru da suka gabata.
Farfesa Ibrahim Malumfashi, da Marubuci Ado Ahmad gidan Dabino MON na daga marubutan da suka yi rubutu akan mahangar.

Sunday, 26 May 2019

TARIHIN FULANI A WATA MAHANGAR

TARIHIN FULANI

SADIQ TUKUR GWARZO

  ASALIN KALMAR FULANI


Mal Ahmad Usman Bello, shugaban kungiyar Fulani ta kasa mai suna FULDAN, bafullatani ne Batoranke, kuma masani akan tarihin jinsin sa, a wata zantawa da mu kayi dashi ya faɗa mana wasu ƙarin mahangai game da tarihin Fulani.
   Da fari dai, masanin ya faɗa cewar tabbataccen tarihi shine wanda yazo a Alkur'ani da Hadisai, amma duk wani abu wanda ba shiba kan iya zamowa gurɓatacce, don haka bai ɗoru akan cewa wajibin duk abinda ya faɗa shine na gaskiya ba.
   A cewar sa asalin sunan Fulani shine Tuta (Futa Toro), kuma suna cikin tsoffin kabilun duniya ne. Shi sunan Futa din sun samo shine daga kakansu/uban su da ake kira Futa, kuma shi jika ne ga Annabi Nuhu. Ta wajensa aka samar da Samudawa da Adawa, don haka faɗin Ta Ala a Alkurani (IRAMA ZA TUL IMAAD) da kabilar su yake, domin an samu cewa an taɓa kiran su da suna Iramawa.
  Daga bisanin saboda yawaitar su ga yake-yake, sai aka rinka kiransu da suna Fatah, ma'ana Jarumai. Sannu a hankali kuma aka koma ambaton su da suna Futa.
Yanayin zaman su a wurare kuwa shine silar sauyawar sunayen su, ta yadda ake kiran wasu Futa Toro, ma'ana Futawa mazaunan Toro, da Futa Masina, Futa Jallo, Futa Falgo da sauran su
   A cewar masanin, shi wannan sunan na FULANI, ya samo asali ne a yammacin afirka, sanda suka haɗu da kabilar MANDINKA wajen zama, waɗanda suma kusan fulani ne a halaye da ɗabiu.
Mallam Ahmad ya tafi akan cewa Fulani kabilar farko ce da suka soma zaman Afirka, kuma sune suka zo da addini yammacin Afirka, amma fa addinin Yahudanci. Shikuwa kowa ya sani addini ne na jinsi, ba na kowa da kowa ba.
Don haka idan fulanin sun tara ƴaƴan su, su kan sanar musu da cewa 'Ana Hulɓe (Fulɓe) Allah'. Ma'ana mu masu tsoron Allah ne, kada kuyi abinda Mandinkawa abokan zaman mu suke aikatawa. Daga nan sai mandinkawa masu zuwa ganin su suka rinka kiransu da suna Fulah, kafin daga bisani sunan ya rinka sauyawa zuwa Fullata, da Fulɓe.
ASALIN BAFILLATANI
  MAHANGA TA ƊAYA
Mallam Ahmad ya sanar mana da cewa Bafillatani ya samu ne daga jikin Annabi Nuhu A S.
 Asalin zuriyar sa kuma a yankin Ɗurun Sinin take da zama. Anan ne har Annabi Musa A.S ya riske su a zamanin sa lokacin da aka saukar masa da Attaurah. A lokacin suna masu bautar shanu, don haka sai ya kira iya kabilar sa Bani Israila zuwa bautar Allah makaɗaici.
Shiyasa sai Bani Isra'ila suka yi kwaɗayin a sanya musu abin bauta kamar yadda futawa suke yi, har kuma Musa Samiri ya shagaltar dasu tare da sanya musu ɗan mariki a matsayin abin bautar Annabi Musa A .S.
 Sai daga baya Annabin Allah Musa ya gane lamarin, sannan ya kira shugaban su mai suna Tori ya karbi addini, shine har akayi bikin karɓar sa ranar asabar a jikin dutsen Ɗuri Sina. Fulani na kiran bikin 'Larki'. Har kuma sukan ce "RaduTori Sinin", watau ga Inda Tori ya musulunta wajen nuni da Ɗuri Sinin.
A wannan zamanin, sai kabilar Futah ta kasu. Wasu suka karbi addinin Annabi Musa bisa biyayya da shugaban su Tori, wasu kuma suka bijere, inda sukayi Hijira zuwa Afirka ta Kudu, daga jikin su kabilun Chusi da ake kira Totsi yanzu suka fita, da sauran kabilun da suka mamaye yankunan.
ASALIN BAFILLATANI: MAHANGA TA BIYU
  Akace asalin Fulani tare da Yahudawa suke da zama. Don haka kusancin su ke sanyawa ake kiransu da sunan Yahudawa. Kuma su mayaƙa ne mara sa tsoro waɗanda basa rabo da makami, sannan suna matukar ɗaukaka ranar asabar sama da sauran ranaku saboda tarayyar su da yahudawa. Sannu a hankali suka famtsama yankin Afirka ta Yamma.
ASALIN FULANI: MAHANGA TA UKU
Wannan mahangar kuma ta nuna cewa Fulani tsatso ne daga zuriyar Annabi Ayyuba A.S..
Akace a lokacin da ya zama dattijo yana wa'azi a gefen tekun Indiya, sai aka bashi wata mace aure wadda bata son sa. Don hakan idan dare yayi sai ta guje masa zuwa bayan ɗaki, acan kuma sai sheɗan ya rinka zuwar mata yana tarawa da ita. A haka har ta samu rabon yaro namiji wanda baya magana da kowa.
Akayi magana akan yadda ta samu wannan yaro dube da rashin tarayyar ta da maigidanta, amma Annabi Nuhu yace a kyale ta a matsayin matar sa, daga bisani hakan ya cigaba da faruwa har ta sake haifar yarinya mace.
 Don haka waɗannan mace da namijin da suka girma sune suka fara amfani da yaren su sabo na Fulatanci.
  MAHANGA TA 4
A kwai kuma mahanga ta huduhar ila yau daga Mallam Ahmad Usman mai cewa asalin Fulani Rumawa ne. Kabilun Rum (Romans) ne makiyaya da suke zaune a karkara. Lokacin basasar Rum bayan kisan Julius Caesar sai ya zamana babu tsaro a kasar ta Rum. A dalilin haka da yawansu su ka rika kwararowa cikin Africa don kubutar da dukiyoyinsu. Cudanyarsu da wasu kabilun Africa ne ya samar da yaren fulatanci. Lokacin wannan kaura tare suka shigo Africa da mazauna yankin Sisley makiyaya. Wadannan kabilun mazauna Sisley su Fulani ke Kira Sissilɓo wato mutanen Sisley, da Hausa muna kiransu sulluɓawa. Har a yau dinnan da yawa daga cikin sulluɓawa ba sa amsa sunan Fulani.

Saturday, 25 May 2019

MAHANGAR MU AKAN TALAUCI DA MATSALAR TATTALIN ARZIKI

MAHANGAR MU AKAN TALAUCI DA MATSALAR TATTALIN ARZIKI A NIGERIA.
(Gaskiya ɗaci gareta)

24-janairu-2016

    Tare da SADIQ TUKUR GWARZO

Assalamu alaikum
    Duba da matsanancin halin da talakawan ƙasa ke ciki, gami da tsare-tsare wadanda hukumomi ke dauka don saisaita lamurori a ƙasar nan, ya sanya mu yin duba gami da yin wannan rubutu.

   DALILAN DA KE SANYA TALAKA CIGABA DA ZAMOWA CIKIN TALAUCI, ATTAJIRI KUMA YA CIGABA DA ZAMOWA CIKIN ARZIKI
   A shekarar 2007, wani hasashe da ofishin mai kula da hada-hadar  kudi na al'ummar ƙasar Amurka (Congressional Budget office) yayi, ya nuna cewar duk wasu tsare-tsare da gwamnatoci ke aiwatar wa ga 'yan ƙasa, attajirai kurum yafi amfana, domin kuwa talakawa na ƙara cigaba da zamowar su cikin talauci ne.
   Ga kadan daga abinda bincikensu ya nuna;
TALAKAWA: A tsawon shekaru talatin, samun kudin su ya haɓaka ne da kaso goma sha takwas kacal. (Ma'ana talakan da yake samun dalar Amurka ɗaya a tsawon wancan lokaci, har yanzu baya samun dala biyu)
MATSAKAITA: A tsawon shekaru talatin, samun kudin matsakaitan mutane ya ƙaru ne da kashi 40 kacal.
ATTAJIRAI: A tsawon shekaru talatin, samun kudin attajirai ya haɓaka ninkin-ba-ninkin da kashi 275. ( wannan labari yana da matuƙar kyau idan aka haɗa shi da yanayin da talakawan nigeria suke daga shekaru talatin zuwa yau)
   Haka kuma a shekarar 2010-zuwa-2011, lokacin da tattalin arzikin Amurka ya fadi warwas, hasashe ya nuna cewa rashin aikin yi da talauci sun ƙaru sosai, har ma akace Amurkawa miliyan arba'in da shidda, wadanda a baya suke da rufin asiri ne (matsakaitan mutane) suka fada sahun talakawa. Hakan ne ya nuna cewa a duk Amurkawa guda shidda, biyar talakawa ne, ɗaya ne attajiri. Mutanen da a baya suke daukar dawainiyar wasu, ya zama sun koma ta kansu sukeyi. Wannan kuma sai ya haifar da ƙaruwar munanan laifuka gami da rashin kwanciyar hankali a ƙasar ta Amurka. 
   Har ila yau, a wani bincike da masana siyasar duniya suka gabatar, sun lura da cewa manyan shugabannin duniya masu farin jinin mabiya, suna haduwa da baƙin jini, ko dusashewar farin jini yayin da suka hau karagar mulki, saboda yadda suke gaza aiwatar da ainihin muradun da mabiyan nasu suka zabe su akai. 
Misali; Franklin Delano Roosevelt da Adolf Hitler, dukkansu shugabanni ne da tarihi ba zai mance farin jinin su a wurin mabiyan su ba, har ma sun hau karagar mulki cikin soyayyar al'umma madaukakiya, amma kuma sun bar mulki cikin baƙin jinin jama'a.
   Amurkawa sun zaɓi Franklin Roosevelt ne a lokacin da suke mawuyacin talauci, tsammanin su da zarar ya hau mulki zaiyi ƙoƙarin magance wannan matsala, amma sai akayi rashin sa'a, jim kaɗan da hawan sa mulki sai ya tunkari yaƙi tare da ƙara tsunduma Amurka cikin Ƙangin karyewar tattalin arziki. 
Haka ma Adolf Hitler, jamusawa sun lamunce masa ya hau kan mulki cikin gagarumar soyayya saboda suna tsammanin shine kadai ɗan kishin ƴasa, wanda zai iya warkar da annobar talauci da ta biyo bayan yaƙin duniya na ɗaya da Jamus ta gwabza, amma da hawan sa karagar mulki sai ya ƙara cusa ƙasar Jamus a cikin yaƙin da yafi na baya tsamari.
 Makamancin haka ne ya auku ga shugaba obama, wanda ya hau mulki cikin farin jini sosai a karo na farko, amma a karo na biyu ya gamu da raguwar masoya, domin ya gaza warkar da ƙishirwar mabiyansa (daga baya ma sai gashi jamiyyar sa ta faɗi warwas a mulki).
   Wadannan duk abubuwa ne da zasu haska mana abinda zai iya faruwa a ƙasar mu Nigeria dai-dai da abinda yake faruwa ayau. Tunda dai munji Imam ibn khaldun na cewa "abinda ya faru a jiya, shine ke bada labarin abinda ke faruwa ayau. Abinda ke faruwa a yau kuwa, shine ke haska abinda zai auku a gobe".
   A ƙasar nan, muna iya cewa mutane biyu ne attajirai. Ɗaya sunan sa Dan siyasa, dayan kuwa Dan kasuwa ake yi masa laƙabi. Kusan dukkan su, suna amfanuwa ne da gwamnati, suna kuma taka doron bayan talaka ne don samun arziƙi. Dan siyasa, sai jama'ar talakawa sun zabe shi zaici mulki sannan ya samu zarafin juya lalitar al'umma, haka ɗan kasuwa wanda  yake samun arziki ta hanyar sayarwa da al'umma hajojinsa.
   Maganar gaskiya itace, dukkan wani tsare-tsare da gwamnati ke ɗauka domin sauƙaƙawa talakawa sau tari, wadancan mutanen biyu take taimakawa. Sauran talakawa kuma take ƙara ƙuntatawa.  Yawansu kuwa dai-dai yake da biyu bisa goma, ma'ana ayanzu, muna iya cewa acikin mutanen Najeriya goma, mutane takwas talakawa ne masu neman na abinci, mutum biyu ne attajirai. Ita kuwa gwamnati, wasu mutane da ake kira 'Bureaucrats' ne ke tafiyar da ita.. mutane ne 'yan jari hujja wadanda basu san zafin talauci ba, idan za'a siyar da shinkafa buhu daya akan naira dubu dari, litar man fetur akan naira dubu, ba zasu damu ba.
   Ku duba ma'anar kalmar 'Pain' a dikshinari, talaka shi kaɗai yasan zafin talauci, tunda a cikin sa yake. Talakan nan kuma ya zaɓi wannan gwamnati ne don ta yi masa maganin matsalar tsaro da talauci da suka addabeshi. Kamar misalin mutum ne yana tsananin jin ƙishirwa, sai ya aiki wani ya kawo masa ruwa, idan ɗan aiken yayi jinkiri, dole wannan mutumi ya ƙara tura wani dan aiken domin samun biyan buƙatar sa. Don haka matsawar wannan gwamnati zata yi nuƙusani wajen sassauta tsadar rayuwa, ko warware matsalolin tsaro, dole ne farin jinin shugabanta ya ragu kamar yadda abin ya faru a Amurka da Jamus.     
   Masana ilimin tsimi da tanaji, sunyi mana bayanin yadda abubuwa ke yin tsada ko arha, ga abinda suke cewa "idan kayayyaki suka yawaita a kasuwa, dole farashin su ya karye. Idan kuwa sukayi ƙaranci, dole darajar su ta hau". Don haka, idan har dagaske gwamnati tayi shirin sauƙaɗawa talakawa, muna iya cewa bata kyauta ba yadda ta samar da ƙarancin kayan abinci a ƙasar nan (gwamnati ta hana shigowa dasu) domin ba tayi wani tanaji na azo a gani ba. Ya kamata ta fara baiwa 'yan ƙasa taki da iri na nomanta, sannan ta baiwa 'yan kasuwa damar kafa kamfanoni, in yaso idan aka yi noma sai tace ta hana shigowa da hatsi yadda tilas ayi amfani da kayan gida, amma wallahi abinda tayi a yanzu ya sanya al'umma cikin tsanani, kuma hakan kuskure ne.
   Batu na gaskiya, tilas ne mu fadawa shugaban mu kuma masoyin mu gaskiya. Idan har ya samu matsala a mulkinsa, dukkan mu ne muka samu matsala. 
Abinda zai yi maganin karyewar tattalin arzikin ƙasa shine gwamnati ta bada agajinta wajen ganin an bude ƙananun masana'antu, ta sauƙaƙa haraji, sannan tayi tanajin duk abinda take tunanin ana buƙatar sa a cikin gida, daga bisani sai a tilastawa 'yan ƙasa dogaro da wadannan masana'antun. Wannan ne kurum zai habaka dogaro da kai, gami da samar da dumbin ayyukan yi a ƙasa. 
 Idan da zamu bibiyi tarihin ƙasahen china, Indiya da Iran, da mun tabbatar da wadannan abubuwa. Amma a yanzu, tsarin da gwamnati ta dauka na nuna cewar talauci zai cigaba da wanzuwa a ƙasar nan har nan da shekaru biyu da rabi, babbar matsalar shine, dole ne rashin zaman lafiya ya ƙaru a ƙasar saboda talaucin da yawa-yawan 'yan ƙasa ke fama dashi, sai dai idan gwamnatin zata ƙaro makamai ne yadda zata rinƙa kashe 'yan ƙasarta da kanta. 
   Shi fa mulki dan Hikima ne, shi yasa Hausawa ke cewa idan aka ciza, sai a hura. Idan bala'I yayi bala'I, sai ka ga talaka ya dai na tsoron mutuwa, daga nan sai ya fara fito-na-fito da gwamnati. Wannan ne yasa Marigayi Umar 'Yar aduwa yaci nasarar mulkinsa (Allah yajiƘansa) domin yayi hikimar sulhu da 'yan tawayen Naija Delta wadanda talauci yasa basa tsoron mutuwa. Shi kuwa talakan ƙasar nan, ya kamata ya mayar da kai wajen neman ilimin neman  dukiya gami da sarrafa ta, ta yadda zai matsa daga halin da yake ciki zuwa na gaba, sannan kuma ya sani, duk abinda gwamnati za tayi, attajirai zata ƙarawa arziƙi. Kuma ba zata iya karya su ba. Idan aka cire tallafin mai, attajirai aka taimakawa domin zasu siyo a waje da sauƙi, suzo su siyar da tsada a gida. Haka kuma idan an hana shigowa da shinkafa, attajiran dai aka ƙara taimakawa, domin sune ke da kudin yin gagarumin noma, wasunsu kuwa tuni sunyi hasashen aukuwar hakan, kuma sunyi tanajin kayan abinci daro-daro, don haka a hankali zasu rinƙa fitowa dasu suna siyarwa al'umma da tsada.
   Madalla da  Abraham Lincoln (tsohon shugaban amurka) wanda yake cewa.        "You cannot strengthen the week by weakening the strong.
  You cannot help the wage earner by pulling down the wage payer"
  A ƙarshe, muna fatan Allah ya ganar da shugannin mu, Allah ya dora su bisa tafarki na gaskiya. Amin
  Dg Sadiq Tukur Gwarzo

WATA RANA A KASAR HAUSA 2

Ishaqa yayi murmushi. Yace "wataqila ma na rigaki sanin wannan labarin. Kinsan mu matafiya ne, muna bada kyauta don a bamu labari, wannan labarin kuwa ya shahara a qasar hausa" Daga nan dai suka ci gaba da firar su ta arziki.
A wani lokaci suna cikin tafiya, sai suka jiwo ihu da hargowa. Daga can kuma suka ga hayaqi na tashi, ashe mahara ne masu dibar bayi suka tasamma wani dan qauye.
Akan idon su ishaqa maharan nan suka rinqa rashin mutumci, su kashe na kashewa, su kama na kamawa a matsayin bayi. Mata da yara kuwa me sukeyi idan ba kuka ba. Gashi kuma duk sun cinnawa qauyen wuta.
Ishaqa ya matsa da dokinsa kusa dadokin Randiyya, ya saitu da ita sannan ba ya fara magana da cewa "Tarihi na ya soma ne da misalin wannan abinda kike gani. An bani labarin cewa tun ina yaro akayi wa kauyen mu irin wannan zaluncin, ahaka aka daukeni daga wurin mahaifana tare da siyar dani bawa ga Mehmet. Don haka a hannun sa na girma, a yanzu haka na mance siffar garin mu data mahaifana, ban san komi ba kuma sai bauta..
 
   Jikin Randiyya yayi sanyi, duk ta kamu da tausayin sa gami da tsantsar kauna. A hakika a yanzu tana jin babu wanda ya dace da ita sai Ishaqa.
    A yanzu ta kamu da tausayin kanta gami da tausayin sauran al'umma marasa qarfi. Kuna ji kuna gani, za'a maishe da gidaden ku kufai, amaidaku bayi ba tare da kunyi laifin komai ba. A gabanta Uwa ke rabuwa da danta kowa na kuka, uwar  sadauki kaza ya kamata, 'ya'yan kuma wani sadaukin ya kame su, kuma wataqila suda haduwa har abada. Wannan wacce irin rayuwa ce? Randiyya ta raya a zuciyar ta.
    Hargowar dawakan dataji yana tunkaro su ne ya katseta daga halin tunanin da take ciki, da ita da sauran 'yan tawaga gaba daya suka karkata hankulansu izuwa ga abinda ke tahowa garesu.
    Runduna ce ta mayaka suka durfafo su, ba abinda kake ji sai ihu da kade-kade. Tun daga nesa suka hango jagoran tafiyar a gaba, yana ta azama ya tarar dasu. Wani makidi kuma sai zuga shi yake da baitoci. Yana cewa;
      Ja gaba, kaine a gaba
     Gimbau aljanin dare
      Na burungu tsoranku ake
      Take mutum Sare mutum
      Ja gaba, kaine a gaba
 
Sarkin yaki ya daga murya yana cewa "Ku fito mana da macen data shiga cikin ku, ko kuma yanzu zaku hadu da fushi na"
   ya cigaba da cewa "Ku fito da macen nan da gaggawa. Haqiqa an tabbatar mana da cewa tana cikin ku. Ku fito mana da macen nan da gaggawa" yana maimaitawa har sai da yazo dab da ishaqa, rundunar sa kuma tana baya.
   Ishaqa ya dubi rundunar Sarkin yaqi wadda ta ninka su ninkin ba ninkin, ya kuma kalli tawagarsa wanda da alamar sun tsorata matuka, ya tabbatar da cewa idan fada zasuyi bazaisha Lalai ba, sai kawai ya fara kwallawa Randiyya kira.
"Randiyya! Randiyya!! Randiyya!!!" Har sau uku.
   Daga baya sai gata ta matso kusa dashi ba tare da ta amsa kiran ba, fuskarta na rufe cikin bakin mayafi kamar yadda ta saba.
     Shima Ishaqan bai kalle taba, ya fara bata umarni da cewa "wadannan mutanen na son daukar ki, don haka kiyi saurin shiga cikinsu"
    Ya dubi sarkin yaqi yace "gata nan, kuna iya daukar ta"
   Sarkin yaki yayi ihu gagarumi, ya kuma bushe da dariya, yace "yaro kayi arziki, da yanzunnan zan cire makogwaran kowanne daga cikin ku. Ka ganmu nan, koda girka muna iya buga fada ballantana ku dinnan 'yan tsirari. Kuma sa'ar ku daya bada izininku ta shiga cikin kuba, amma haqiqa da sai mun hukunta ku"
   Daga nan sai ya matso da dokinsa kusa da Randiyya, ya sureta izuwa dokinsa, sannan ya juya akalar dokin ya fita aguje.        Randiyya na zullo da qoqarin kubucewa amma ya riketa katamau, kuka kawai takeyi tana neman taimakon Ishaqa tana cewa "kaji tausayina ishaqa, na shiga halaka, bani da kowa sai kai, kada kayi mini haka ishaqa.."
     Kwalla ta kwaranyowa Ishaqa, ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Sannan a sanyaye shima ya juya akalar dokinsa ya fincika a guje yayi hanyar damagaran tare da umartar 'yan tawaga subiyo shi.
   Ottoman yayi azamar saituwa da Ishaqa yana masa magana da cewa "ka ceci rayuwar mu da dukiyar mu, ban taba tunanin kana da basira haka ba"
   Ishaqa yayi murmushi yace" ai masu magana na cewa gudun da babu tsira kwanciya tafishi, don haka naga bai kamata na sanya rayukanku da dukiyoyinku cikin asara ba akan abinda a zahiri ni ya shafa ba kuba"
   Tun daga nan bai kara cewa uffan ba suna ta faman azama kamar wadanda aka biyo har saida getsin yammaci suna daf da shiga garin damagaran, sannan yaja akalar doki ya tsaya.
    Ya matso kusa da ottoman yace "anan zamu rabu daku, ina roqonka kayiwa maigidana bayanin nasarar fataucin da mukaci, ka kuma nemar mini gafara. Hakika zan sadaukar da raina wajen ganin na ceto ran waccan yarinya. Daman na fada maka dalilin dayasa ban tanka suba dazu, amma a yanzu inaganin kun tsira, don haka zan tari aradu daka.."
   Ottoman yace sam baza'ayi haka ba, ya bari su shiga damagaran sai su tattauna yadda za'ayi fadan. Tunda suna da bindigogi kuma akwai tsama tsakanin Sarkin damagaran dana kano, don haka yana ganin Sarkin damagaran zai iya basu rundunar sadaukai wadanda zasuje suci kano da yaki harma su rushe ta su kuma qwato macen. Amma yanzu Mehmet bazaiji dadi ba idan yaji cewa saboda mace ka tafi a kasheka kai kadai."
   Ishaqa dai ya qeqashe kasa yace sam bazai shiga damagaran ba, hakan kuma akayi. Ala tilas suka rabu, su suka shiga gari shi kuma ya juyo yana dauke da doguwar bindigarsa da kuma takobinsa. A rataye, yayi nadi irin na buzaye, babu mai iya gane shi.
    A dai wannan ranar wajajen dare Ishaqa ya cimmarwa rundunar Sarkin yaqi wadda take ta azama ta isa kano. Sai kace sun san wani abu zai biyo baya.
   Tun daga nesa ya sakar musu bindiga, ji kake daram. Dawakai suka firgice abinka da dare mai amsa qara, cikin mazaje ya duru ruwa saboda wutar da suka gani ta tashi daga bindigar. Dawakai suka fara ja da baya suna tirjiya. Ishaqa ya fuskance su yana mai daka musu tsawa, yace "Ku fito mini da macen cikin ku ko kuma yanzu naga bayanku"
    Sarkin yaqi yace ai mutuwa ce kadai zata sa ya rabu da yarinyar nan ba mutum mahaukaci kamar saba mai tarar mutuwa da dare. Don haka baya tsoron a gwabza yaqi a kanta.
Da fadin haka sai ishaqa ya sakar musu harbi, bindiga ta qara tashi daram, wannan yasa wasu dawakan suka ranta a na kare.
     Da ganin haka sai sarkin yaqi ya kurma ihu, sannan yace arna maza bisa kanka bari yanzu na sare kanka kowa ya huta, sai kawai ya tunkaro ishaqa a guje cikin azama yana mai rike da wani dogon mashi a hannunsa na hagu, takobi kuma a hannunsa na dama. Yana ta azama da dokin yiwa Ishaqa kwaf daya. 
   Ishaqa ya saici sarkin yaki da harbi amma bindigar taqi tashi, yayi yayi sai dai ina, wannan yasa sarkin yaqi ya qara azama yana ihun cewa sunci sunsha ba don qaramin qwaro irinsa ba. Shi kuma Ishaqa sai ya juyar da bindigar sa izuwa bayan sa tare da zare takobinsa sannan yayi kan Sarkin yaqi da sara.
    Arangamar tasu tana da ban tsoro, sara kowannen su yake kaiwa ba tare da yasamu inda yake kai sarar ba. Kowanne ya himmatu wajen cin nasara. Yayin da rundunar sarkin yaqi kuma ta tsaya tana kallon abinda zai faru.
    Ishaqa dai ya wanzu kai sara gami da gociya sai dai a haqiqa ya soma galabaita saboda jarumtar sarkin yaqi tasha bam-bam da tashi. Kafin ayi nisa ma sai da sarkin yaqi ya illata dokin Ishaqa, tilas ishaqa da dokin suka fadi qasa wanwar, sannan sarkin yaki ya qara binsa da niyyar soke shi da mashi, amma Ishaqa yayi gociya wadda duk da haka saida sarkin yaqi yayi nasarar sukar sa a qafa.
   Ishaqa yayi qara yana kiran sunan Allah, anan nema Randiyya ta jiyo muryar sa har ta gane shi, sai kuma tsoro ya qara rufe ta, da yake an kulle tane acikin wani qaton akwati na qarfe wanda bayi ke dauka, sai ta fara bubbuga akwatin bam-bam bam-bam tana kuka. Tsammanin ta an kashe Ishaqa.
   Ishaqa yaja jiki daqyar ya tashi yana jan qafa, yana ja da baya. Yayin da shikuma Sarkin yaqi ke murmushin qeta, tsammanin sa fadan yazo qarshe.
   Sarkin yaqi yayi azama ya tsikari dokinsa, yayi kan Ishaqa takobi zare da niyyar tsinke kansa, sai akayi sa'a ishaqa ya durkusa qasa tare dakai mahaukacin sara. Wanda yayi sa'ar sare qafafuwan gaba na dokin sarkin yaqi.
    Kafin kace kwabo doki ya fadi rica, shikuma sarkin yaqi fuskar sa ta tunkuyi qasa idonsa ya rufe sosai saboda yashi daya shiga ciki.
   Ya tashi fagam-fagam yana qoqarin goge qasar daga idon sa, ya dakawa rundunar sa tsawa  kuma da cewa suyi azamar halaka Ishaqa kafin wani abu ya same shi.
Ganin yuyar rundunar Sarkin yaqi ta taso kansa, yasa yayi saurin ciro bindigarsa dake maqale a bayan sa. Da fari dai bakin bindigar da akayi da qarfe ya samu ya cakawa sarkin yaqi a maqogwaro, tunda ya fuskanci takobi ma bata samun nasara akan sa, wanda nan take sarkin yaqi yayi rashe-rashe a qasa cikin jini, sannan ya fuskanci rundunar ya fara sakar musu harbi daram, amma tashin bindigar biyu harsashi ya qare, don haka sai jikinsa yayi sanyi  yasan tabbas bazai tsira ba. Kawai daya fuskanci sarkin yaqi ya mutu sai fara rayawa aransa cewar ko yanzu ya mutu Randiyya zata samu sassauci tunda ga makiyinta ya mutu. Don haka ya shiga sauraro da tsammanin mutuwarsa daga rundunar dake daf da aukar masa.
   Daf da isowar sune sai suka fara jiyo harbi daga baya tare da sautin kofatan dawakai, Ishaqa ya juya da sauri don ganin mutanen da suka iso wurin. Sai kuwa ya hango ubangijinsa Mehmet, da Ottoman da kuma gagarumar rundunar yaqi. Yayi murmushi, yaji wani farin ciki da qwarin guiwa ya lullebe shi, bai san sa'ar daya zare takobi yayi kan  rundunar da sara ba.
    Fada ya kaure sosai, runduna da runduna, sadaukai sai aiki sukeyi. Amma da yake mutuwar sarkin yaqi ta raunana rundunarsa, ba'a jima ana gwabzawa ba akaci nasara akansu, wadansu suka arce, wadansu kuma suka miqa wuya tare da gabato da Randiyya ga Ishaqa.
    Randiyya ta rungume Ishaqa tana kuka gami dayi masa godiya, ta rasa kalmomin da zata fada masa ma don murna.
    Ishaqa ya kama hannun ta sannan ya gabata ga Mehmet, suka duqursa agabansa duka suna masa godiya.
Ishaqa yace "ya shugabana, haqiqa zuwan ka wajen nan ya sani mamaki, kuma tabbas ka ceci rayuwata. Bani da abinda zance maka don yi maka godiya"
  Mehmet yace "Ishaqa kayi sani, na riqeka tamkar dana. Tunda na samu labarin abinda ya auku nace bazan dakata ba, tilas a darennan na biyo bayan ka domin inaji inagani mutuwa tayi awon gaba da Abdulkarem, ba zaiyiwu na bari kaima ka mutu ba alhali inada abinda zan iyayi. Wannan yasa muka nemi taimakon sarkin damagaran na sadaukai kuma shine ka ganmu anan. Don haka yanzu daukar ku zamuyi mu koma damagaran kawai"
 
(Bayan wani lokaci aka daura auren Ishaqa da Randiyya, anyi biki gagarumi. Ishaqa kuma ya cigaba da kula da dukiyar mehmet, suna fatauci daga ankara izuwa qasashen hausawa).

Muna adduar Allah ya mayarwa 'Yan kasuwar da sukayi asara sanadin gobara da alheri amin. 

WATA RANA A KASAR HAUSA 1

HIKAYAR HAUSA: WATA RANA A KASAR HAUSA!

Tare da SADIQ TUKUR GWARZO

Shekaru daruruwa da suka gabata, tarihi ya nuna cewa qasar hausa na karbar baquncin fararen fata wadanda akasarin su Larabawa ne, da kuma mutanen hadaddiyar daular Ottoman, wadanda ake kira da Turkawa, masu zuwa siye da siyarwa.
A wani lokaci irin haka, anyi wani shahararren Falke wanda yake tasowa daga Birnin Ankara izuwa kasashen hausa, sunan sa Mehmet. Sana'ar sa itace fatauci, don haka a wannan lokacin Mehmet yana zuwa kasashen hausa ya siyarwa da sarakuna kayan sawa na alfarma, kayan fada da kayyakin Alatu. Shi kuma yana siyen bayi daga wurin su ya taf da su kasashen larabawa ya siyar.
Mehmet yana da wani da matashi mai suna Abdulkarem, wanda yake matukar kauna. Har ma shi yake dorawa akan duk wani abu nadukiyarsa. Rannan kaddara Abdulkarem ya kamu da wata cuta, ashe cutar ajali ce, babu jimawa rai yayi halin sa.
Hakika, mutuwar Abdulkarem tayi matukar dugunzuma Mahmet, amma kasancewar sa musulmi, sai ya dangana ga Sarki Allah. Daga nan kuma sai ya jawo wani bawa mai suna Ishaqa wanda yake amini ne na qut da qut ga marigayi Abdulkarem ya maisheshi tamkar da. Duk wani abu da Abdulkarem yake yi masa, sai Ishaqa ya zamo yana kamantawa.
A Wata shekara, Mehmet kamar yadda ya saba, ya keto ta Libiya daga Ankara, ya sauka a Damagaran, sai dai jikin sa na masa nauyi, wannan yasa yaji tsoron qarasawa cikin kasar hausa, ya yanke shawarar zai tura Ishaqa ya wakilce shi a kasuwancin da suka saba, shi kuma zai huta anan damagaran, in yaso idan yaji dama-dama sai ya gangara Kukawa dake Masarautar borno ya taba kasuwanci ya dawo Damagaran ya jira su.
Haka kuwa akayi, Ishaqa ya zamo jagora, ya taso da tawaga suka biyo ta qasar sakkwato, yana tare da turkawa abokanan mehmet, da dakaru masu yi musu rakiya da kariya, wadanda suke dauke da bindigu, takubba da sauran kayan fada don gudun Mahara da 'yan fashi. Duk da dai suna da kyakkyawar alaqa da sarakunan kasar hausa, amma 'yan ta'adda na iya yi musu kwanta-kwanta su karbe dukiyoyin su.
A kwana a tashi, Ishaqa da tawagar sa ta Iso birnin Kano. Daman bisa al'adar su sukan tsaya a babban gari suci kasuwa su kuma baiwa sarkin garin kyauta. Amma da yake Mehmet yana da babbar alaka da Sarkin kano na lokacin, kyautar sa tana zamowa ta musamman, kuma sau tari, daga kano kukawa suke qarasawa, amma da yake sun raba tafiyar da mai gidansa, wannan na nuna cewa a bana iya kacin tafiyar su Kano.

Da isar su birnin kano, suka aika wani baran su domin yayi musu iso. Babu jimawa kuwa akace Sarki na maraba dasu, don haka suka dunguma izuwa cikin gari.
Tun daga kofar gari Ishaqa da mutanen sa suka lura da sauyi a garin. Gashi dai an qawata gari kamar ana wani qwarya-qwaryan biki, amma kuma gidaje da rumfunan kasuwa duk a rufe, ba kuma a ganin mutane a garin. A haka har suka isa fada.
Fadar ce suka gani cike da mutane. Ashe sarkin garin ne ya tara al'ummar sa duka yana musu jawabi.
Isar su keda wuya aka basu wuri a fadar, aka kuma shaida musu cewar su dan jira sarki ya kammala wani uzuri sannan ya saurare su.
Akan idon su Ishaqa Sarki keta zazzagawa al'ummar garin fada. Yana ta cika da batsewa. Su kuma al'ummar gari kowa yayi tsit, babu mai cewa kanzil. Ko da gyaran murya baka ji. Wanda hakan ke fayyace irin tsoron da jama'ar garin kewa sarkin nasu. Daga bisani bayan ya gama fadan, aka gabato da wani mutumi. Sarki ya umarci hauni ya sare kansa. Ai kuwa kafin kace kwabo sai ga jini yana tsartuwa, hauni ya raba kan mutumin da gangar jikin sa.
Wannan abu yayi matukar kidima turkawan dake tawagar ishaqa. Kasancewar basa jin hausa sosai, sai suke tambayar ishaqa abin dake faruwa. Sai shima ya kusanci wani bafade da wannan tambayar.
Bafaden cikin tsoro murya kasa-kasa ya baiwa Ishaqa amsa da cewa "Ranka ya dade, akwai sarkin yaki gashi can Azaune, shine yayiwa sarki bajinta ta cinye wani Gari da yaqi. Wannan yasa Sarki ya yaba masa kuma yace ya zabi duk abinda yakeso sarki zaiyi masa. Sai sarkin yaqi yace babu abinda yakeso sama da a aura masa diyar wannan mutumi da aka sare kansa. Ita kuwa wannan yarinya duk garinnan babu kyakkyawa irinta. Sarki kuwa yace tilas haka ta yiwu, don haka yaune ranar da akasa za'a daura aure, amma kuma sai aka nemi amarya qasa ko bisa aka rasa. Wannan yasa sarki yayi fushi yace ubanta ne ya boyeta, don haka ya yanke masa hukuncin kisa. Ita kuma gobe zai tura da rundunoni, yasha alwashin indai tana doron qasar nan sai an kamo ta"
Ishaqa ya girgiza kai alamar baiji dadin abin ba. Ya kalli mutumin da ake cewa shine sarkin yaqi, ya ganshi wani bijimi ne maras kyan gani. Gashi baki wuluk, da jajayen idanuwa sai muzurai yakeyi. Tabbas shima ya hango dalilan da zasu hana kyakkyawar budurwa ta auri wannan basumuden mummunan kato, ya tabbatar babu soyayya a lamarin, amma kasancewar tarbiyar da Mehmet ya basu itace kada su yarda su sanya baki cikin sha'anin mulkin wani sarki, sai kawai ya labartawa turkawan abinda ke faruwa sannan ya
gargade su da kada wanin su yace uffan.

Bayan sarki ya kammala ne, sai ya fuskanto su. Yayi musu lale marhabin yana mai tambayar ina abokin sa Mehmet ya shiga?
Ishaqa ya labarta masa halin daya baro Mehmet da kuma shawarar daya yanke. Daga nan kuma ya gabatarwa dasarki kayayyakin da mehmet din ya aiko su dashi wadanda suka hadar da manyan riguna da shimfidu na alfarma, da wasu dogayen bindigu tare da alburusan su, da tasoshi nacin abinci wadanda akayisu da azurfa, da dai makaman tansu. Sarki ya dube su cikin farin ciki yayi murna sosai. Sannan shima ya bada umarnin a hada musu bayi wadanda zasu tafidasu.
A wannan Rana dai 'yan tawagar ishaqa hutawa kurum sukayi. Kashe gari kuma suka shiga kasuwa. Anan ne kowa yake siyar da kayan dayake tafe dashi, tare da siyo abinda yake ganin yana da daraja a kasashen larabawa.
Bayan kwana biyu suka yi bankwana da Sarki, sannan suka hau dawakan su tare da yin haramar komawa Damagaran.
Basu jima suna tafiya ba sai wani baturke wanda yake aboki ne ga Mehmet mai suna Ottoman, ya matso kusa da Ishaqa yana cewa "Ishaqa Mujde, mujde ishaqa". Ma'ana "Inada wani kyakkyawan labari ishaqa" sai kuma ya gabatarwa da Ishaqa wata mace wadda ta lullube fuskarta da bakin mayafi.
Ishaqa ya tambayi Ottoman menene labarin? Kuma wacece haka? Shine ottoman din yake sanar dashi cewa ai wannan macen itace wadda ake nema a kano, kuma kawai ganinta sukayi acikin tawaga ba tare da sun san yadda akayi ta shigo ba. Don haka kasuwa tayi riba kenan, domin ya tabbatar da cewa ba qaramar daraja matar zatayi ba.
Nan take Ishaqa ya tsaida dokinsa, abinda ke nuni da kowa ma ya tsaya. Ransa a bace, ya kalli macen gami da daka mata tsawa, yace "yi maza ki fita daga ayari na, ba zaki janyo min masifa ba".
Matar nan ta rugo da gudu ta duqursa a gabansa tana magiya, ya taimaka ya kyale ta, yayi mata rai, saboda komawarta kano azaba ce. Har tana cewa "ya kai wannan shugaba mai adalci kaji tausayi na, kayi mini rai, bani da kowa a duniyar nan, sun kashe mini mahaifina, sun karbe duk abinda muka mallaka, idan na koma hannun su mutuwa zanyi.."
Ishaqa yace ai sam bazai yiwuba. Saboda matsawar Sarkin kano yaji labarin sun tafi da ita zai iya biyo sawu, ko kuma zai iya yanke duk wata alaqar kasuwanci dake tsakanin sa da maigidansa Mehmet, shikuma ba zai taba son ya batawa ubangijin saba. Don haka sai ya umarci wasu dakarunsa da suyi gaggawar ciccibarta su mayarkano.
Tana kuka da birgima haka suka fincike ta, suka dora bisa wani ingarman doki, suka fita aguje zasu kaita kano.

Ana haka kuma sai Ishaqa ya fahimci hukuncin da ya dauka bai yiwa 'yan tawaga dadi ba, saboda duk tausayinta ya kamasu. Yayi jim yana tunanin mafita, shima kansa tausayin nata ya kamashi, sai kuma ya yanke shawarar canzatunani.
Saboda haka da kansa yabi bayan dakarun yana kwalla musu kira har saida ya tsayar dasu, sannan ya umarci a kyaleta a tawagar, amma da sharadin zata rinqa boye kanta don gudun kada a ganta akaiwa Sarki labari ya biyo bayansu. Daga nan sai suka ci gaba da tafiya.
Tun daga wannan lokacin, wannan matar take ta yunkurin zantawa da ishaqa. Shi kuwa sam bata gabansa, har kar sa kawai yakeyi. Daman mutum ne wanda bai cika son surutu ba.
Rannan kuwa sai akayi sa'a, tawaga ta yada zango, Ishaqa da Ottoman sun kebe suna fira, sai yaji ottoman yana magana da harshen turkanci, yana cewa "Guzellik Guzellik, ya subhanallah" Ma'ana, 'Kyakkyawa kyakkyawa, tsarki ya tabbata ga Allah'.
Ashe matar nan ce ta yaye fuskarta ta tunkaro inda suke domin tayi magana da Ishaqa. Da isowar ta tagaishe da ottoman, sannan na roqeshi izinin ganawa da Ishaqa. Don haka sai ya tashi ya basu wuri.
Ta dubi ishaqa, suka hada ido, ta sakar masa wani murmushi lallausa, sannan ta dukar dakai ta fara magana cikin ladabi, tana mai cewa "Ya shugaba, ina maka godiya bisa tausayi na da kaji har ka kyaleni acikin tawagar ka, kuma idan ka amince, inason labarta maka halin da nake cikine"
Ishaqa ya kura mata ido, saboda ya tsinci kan sa ne a wani yanayi wanda har yanzu bai san sunan saba. Ya gyada kai, alamar ya amince. Ita kuma sai ta cigaba da cewa "Da fari dai sunana Randiyya, mahaifina attajirine babba abirnin kano, wanda babu attajiri irinsa. Ni kuma nice kadai 'yarsa, mahaifiyata ta rasu tun ina karama.
Rannan sai gaba ta hadosu da Sarki a dalilin haraji. Sarkin yaqi ke zuwa karbar haraji wajen mahaifina. Shi kuma kamar yadda ya saba,bayan ya biya harajin, yana yiwa Sarkin yaki alheri mai yawa. To lokacin da yazo sai akayi rashin sa'a ya hangoni, ai kuwa sai ya kamu daso na. Yace idan har mahaifina zai yarda ya aura masa ni, to ya bar kara biyan haraji, kuma sai yaga bayan makiyansa duka. Shi kuma mahaifina yace gaskiya lokacin dazai aurad dani bai karasa ba, kuma zumunci yake so ya hadani da dan-dan uwansa.
Daga nan fa Ran sarkin yaki ya baci, yayi rantsuwa da cewa sai ya bakantawa mahaifina, kuma ko bayaso sai ya aureni. Daga nansai ya tafi ga sarki, ya shirya qarairayi wadda ta sanya Sarki yaji ya tsani mahaifina.
Sarki ya aiko gidan mu da cewa baya son zaman mu a garinsa. Don haka ya bamu kwana daya, mu hanzarta bar masa gari.
Cikin tashin hankali mahaifina ya nufi fada, yayi juyin duniyar nan, sarki yace sam bazai saurareshi ba, dole ne ya bar gari. Tilas mahaifina ya shiga hada kayan sa don fita daga garin.
Abin bakin cikin ma shine, sarki ya hana kowa daga mutanen garin amsar ajiya ko tsaron wani abu na daga dukiyar mahaifina. Ya kuma ba da shelar cewa idan kwana daya ta cika, kowa na iya zuwa gidan mu duk abinda ya samu ya zama ganima.
Mahaifina ya hada abinda zai iya dauka bisa dawakai, ba shiri yasa ni agaba da wasu amintattun bayin sa muka bargarin muna kuka. Fitar mu keda wuya sai muka mufi wani gari Marke inda Sarkin garin aboki ne ga mahaifi na.
Bayan kwana biyu, sarkin yaki ya kara zuga sarki akan cewa dole abi bayan mahaifina a kamo shi a daure, idan ba haka ba zai tara sadaukai yazo daukar fansa ga sarki. Don haka sarki ya baiwa Sarkin yaqi izinin aiwatar da wannan aiki, da nudin idan har sarkin Marke yayi turjiya, ya qone garin duka da abinda ke cikinsa.
Hakan kuwa akayi, Sarkin Marke yace bazai sallama muba sai dai ayi duk wanda za'ayi. Sadaukan sarkin yaqi suka rufarwa garin da fada, suka shiga kisa ba babba ba yaro, suna kone gidaje. Akarshe sarkin Marke ya gudu mu kuma suka samu nasarar kama mugami da komar damu kano.

Ala dole mahaifina yace ya gamsu ayi aurena da sarkin yaqi domin a zauna lafiya. Sarki yace to zai yafe masa laifin sa idan har akayi auren lafiya, amma idan wani abu mummuna ya auku, to tilas sai ya halaka shi a gaban dumbin jama'a.
Daga baya mahaifina ya yanke shawarar daya hada jinin sa da azzalumi irin sarkin yaki, gara ya mutu. Don haka ya nemi wani bafade wanda ya shirya sace ni tare da shigar dani tawagar ku. Da ranar daurin auren kuma tazo sarki bai ganniba, shine yasa aka sare kan mahaifina.
Ta kare da cewa " a yanzu haka na mika wuya a gareka, ina rokon taimakonka. Ba ni da wani gata idan ba kaiba. Ka taimakeni na isa Damagaran, akwai dan uwan mahaifina da yake fatauci acan, wajensa nake son komawa.
Ishaqa yayi ajiyar zuciya yana mai tausawa Kyakkyawa Randiyya. Ya kalleta cike da jimami, yace "Hakika na tausaya halin da kika shiga. Kuma ina sanar miki da cewa a shirye nake na taimake ki dom ki tsira daga sharrin wadannan azzalumai. Amma fa ki sani, wannan lamri yana da matujar hatsari. Kinga dai ni yaron gida ne, wakilci nakeyi, don haka nake kaffa-kaffa da rayukan wadanda nake jagoranta gami da dukiyoyin su. A yanzu kuma muna cikin wani lokaci, sarakunan mu basu da tausayi. Akan ki yaki zai iya barkewa
tsakanin Damagaran da kano, duk da daman nasan sukan fafata jefi-jefi.. Gashi kuma labari baya buya, ina tsoron kada aje a sanar da Sarkin kano cewa kina cikin tawagar mu, nasan tabbas sai ya biyo bayan mu.."
"Ni dai ka zama gatana" Randiya ta fada. "Allah shine gatan mu Randiyya.." inji Ishaqa. Sai ya qara da cewa " Amma ki kwantar da hankalinki, da yardar mai duka zaki kubuta" itama Randiyya ta nemi sanin tarihin sa amma yace kada ta damu, zai sanar da ita.
Sannu a hankali tawaga na cigaba da tafiya tana kusantar Birnin damagaran,
Shaquwa ta fara aukuwa tsakanin Ishaqa da Randiyya, har ya kasance kusan koda wanne lokaci suna tare da juna. Ayi raha ayi firar duniya. Wannan ne ya fara daukewa Randiyya bacin ran da take ciki, hankalinta ya fara kwanciya.
Wata rana suna tare, sai Randiyya take cewa "Ya shugabana, naga kamar kai ba bahaushe bane, wataqila baka san rike zumunta ta hausawa ba.. Idan ka shirya, zan baka wani labari"
Ishaqa yayi murmushi, yace "na gane wayon ki ay, so kikeyi kibugi ciki na na baki tarihi na, ni kuma nace miki lokaci baiyi ba, kawaidai idan kina da labari mai dadi ki bani"
Randiyya ta kyalkyale da dariya tana mai rufe fuskarta don kunya, sannan ta soma bashi labarin da cewa " A wani gari, anyi wasu abokan juna su biyu, wadanda suka amince da juna. Sai suka yanke shawar tafiya wani gari neman kudi. Akayi sa'a kuwa, garin da sukaje suka sami 'yan kudinsu, har ma kowannen su yayi aure.
Rannan sai suka ce ai kuwa ya kamata muje garinmu da matayen mu domin suga iyayen mu. Ai kuwa sai suka yi shiri suka kama hanya. Tinkis tinkis suna tafiya, sai dare yayi musu cikin wani daji. Sai daya abokin yace ai kuwa ya kamata su tsaya ana shikuma ya nemo musu karyo musu itacen da zasu kunna wuta, in yaso idan ya samu 'ya'yan itatuwa ma zai hado musu dashi.
Tafiyar sa keda wuya sai ga Zaki ya qaraso wurin, yana gurnani, matan nan duk suka rude, shikuwa namijin yayi ta maza ya zare wuka ya durfafi zaki. Kaca-kaca har ya samu nasarar halaka zaki.
Yana cikin hutawa sai yajiwo tafiyar abokin nasa yana dawowa, sai kuwa yace da matan su kwanta kamar sun mutu shi kuma ya tsayar da zakin kamar mai rai, domin ganin yadda abokin zaiyi.
Isar abokin keda wuya yayi kuwa, yace aikuwa rayuwa ta bata da amfani, tilas na rufarwa zakin nan in yaso ya kashe ni kamar yadda ya kashe min 'yanuwa. Da fadar haka sai ya rarumi zaki, sai dai ga mamakin sa sai ya tarar da zaki a mace, anan ne abokin da matan suka tashi suna masa dariya gami da jinjina masa. Kaji kadan daga amincin hausawa"

MAZA GUMBAR DUTSE: AYYUKAN ASUSUN TALLAFIN MAN FETUR (PTF) NA GWAMNATIN JANAR SANI ABACHA, WANDA SHUGABA BUHARI YA JAGORANTA

MAZA GUMBAR DUTSE: AYYUKAN ASUSUN TALLAFIN MAN FETUR (PTF) NA GWAMNATIN JANAR SANI ABACHA, WANDA SHUGABA BUHARI YA JAGORANTA

    Daga Sadiq Tukur Gwarzo

A watan Oktoba na shekarar 1994, marigayi Shugaba Sani Abacha dake mulkar Nigeria a lokacin, ya bayyana Karin kudin man fetur. Wannan abu ya tada kura a kasar nan, wanda yasa 'yan kasa suka rinka korafi suna masu nuna adawar su ga wannan Karin farashi.
    Hakan tasa Shugaba Abacha yin dogon tunani da nazari akan lamarin. Na farko dai bai kara farashin man fetur ba sai bisa wasu muhimman dalilai, sannan kuma shi ba shugaba bane mai son uzzurawa al'ummar daya ke mulka, kamar yadda ake yawan jiyo shi yana cewa "an gina gwamnati ne don al'umma, ba don aci riba ba",  don haka sai ya Kirkiro da wani asusu, wanda zai ragewa al'umma radadin talaucin da suke ciki, zai kuma ciyar da kasar gaba. Sunan asusun shine 'Petroleum Trust Fund' (PTF), sunan shugaban asusun daya nada shine Janar Muhammadu Buhari, sai wani  mai suna chief Tayo Akpata a matsayin sakatare. An kuma kaddamar dasu a watan Maris na shekarar 1995. Daga nan shugaba Sani Abacha ya rinka turo musu da kudade, sukuma suna gudanar da ayyukan alheri. 
    Da fari, al'ummar Najeriya basu gaskata gaskiyar Shugaba Abacha akan wannan kuduri ba, amma daga bisani hakika kowa ya gani a Kasa. Ga misalan aikace-aikacen da Asusun ya gunadar:-
    1. Fannin lafiya ya samu babban tagomashi, domin kuwa an gina manyan asibotoci a karkashin asusun, an kuma gyara kusan kowanne babban asibiti a kasar nan.
   * Sannan an siyo Motocin daukar marasa lafiya (Ambulance) masu yawan gaske tare da rarrabasu izuwa asibitocin kasar nan.
   *An tura da tabarau ga asibitoci don rarrabawa masu matsalar idanu kyauta.
   * An siyo kayayyakin kula da masu cutar kanjamau tare da magunguna a karkashin shirin (HIV/AIDs Intervention programme), inda ake bayar dasu kyauta ga mabukata.
   * An bude ofisoshin sayar da magunguna a karkashin tsarin (PTF drug Revolving fund) a duk manyan asibitoci, inda ake siyarwa da jama'a magani kasa da yadda farashin sa yake a kasuwa ko a sauran shagunan da bana gwamnati ba. Akan haka ne ma aka taba kama wani jami'in gwamnati yana son karkatar da akalar magungunan, daga karshe shugaban asusun Buhari ya fusata da hakan, sannan ya kai jami'in gaban kuliya inda aka garkame shi.
    2. Gine-gine.  Wannan asusu, yayi gine-gine masu tarin yawa akasar nan. Sannan an kawar da rashawa a tsarin kwangila, domin asusun yana kwace kwangilar sane ga duk wanda yayi masa  wasa.  Misalin gine-ginen sune;
  *Ginin rukunin gidaje a wuse dake abuja(Residential estate) don sawwakewa ma'aikata mallakar muhalli cikin rahusa. *Fara Gina Matatar ruwa a okpella.
* Gina babban titin express dake tsakanin Enugu da onicha.
* Sannan an gyara wasu manyan tituna a sassan kasar. Inda aka zuba musu kwalta mai inganci tare da gina musu magudanan ruwa. 
   3. Ilimi. Wannan asusu ya samar da tallafi ga fannin ilimi. An gina makarantu masu yawa a cikin wannan shiri.  Har yau  gine-ginen  dakunan karatu a jami'o'I da kwalejoji wanda asusun PTF ya gina suna nan dauke da tambarin asusun. Al'umma shaida ne, asusun ya rarraba littattafai da abin rubutu kyauta ga dalibai.
   4. Abinci. Asusun ya samar da kayyakin abinci a farashi mai rahusa,inda ake siyarwa mutane a farashi kasa da farashin kasuwa.
   5. Ciyar da tattalin arzikin kasa gaba. Wannan asusu yayi dabarar baiwa 'yan kasa kwangilar duk wasu ayyuka da zai gabatar. Sannan kuma yana sanya sharadin cewa dole ne dan kwangila ya siyo kayansa anan gida najeriya (sai dai idan abinda ake bukata ba'a yinsa a gida). Akan haka akace kamfanonin magani irinsu Emzor pharmaceuticals, dana siminti kamar Leferge dana fenti misalin IPWA ltd da wasunsu sun amfana har suna daukar ma'aikata. Wannan abu ya taimaka wajen kara habaka tattalin arziki, tare da samar da aikin yi.
   6. Samar da motocin sufuri masu zirga-zirga da jama'a akan farashi mai rahusa a karkashin shirin (PTF subsidise commercial vehicle)
     A karshe, Bayan rasuwar Janar Sani abacha, Shugaba Obasanjo ya sauke shugaba Buhari tare da nada  mallam Haruna Adamu shugaban asusun.  A wannan lokacin asusun na dauke da kudi sama da Naira biliyan dari. Shine akace Shugaba Buhari ya tara ma'aikatansa tare dayi musu jawabin bankwana, sannan yace duk wani abu da akeson bincikawa yana nan a rubuce. Daga nan ya sauko daga saman bene ya shiga motar sa ya nufi Daura.
   Obasanjo yayi bincike matuka kafin ya rufe wannan asusu, amma duk adawar sa ga Marigayi Sani Abacha bai taba fitowa fili ya zargi asusun PTF ba, hukumar EFCC kuwa bata taba gayyatar Shugaba Buhari don tuhumar sa da almundahana a cikin asusun ba.
   Dafatan Allah yajikan Janar Sani Abacha, Allah ya taimaki Shugaba Buhari akan shugabancin kasa da yakeyi. Amin
   Daga Sadiq Tukur Gwarzo
             08060869978

Sunday, 19 May 2019

LABARIN BOKONI, MAFARAUCIN DA YA ZAMA DUTSE

LABARIN BOKONI: MAFARAUCIN DA YA ZAMA DUTSE

Sadiq Tukur Gwarz, GGA
     08060869978
      A gabashin garin Rogo dake cikin jihar Kano, akwai wasu tarin duwatsu masu tsohon tarihi, waɗanda ake tsammanin wani abin mamaki ne ya faru har aka same su shekaru sama da dubu ɗaya da suka gabata.
Manya daga duwatsun sune ; Tayaka, Namijin Bokoni da Amaryar Bokoni.
Dutsen Amaryar Bokoni yana da tsayi da kuma doro, sannan a saman sa akwai kogo da kuma wuraren zama waɗanda kamar an yi sune don hutawa. Sai kuma wasu duwatsu masu kama da tanderu a ƙasa. Ana kiran kogon dutsen da suna 'Zauren Amaryar Bokoni'.
A saman dutsen Tayaka kuwa, wasu duwatsu ne a jere masu siffa irin ta buhunan hatsi.
Daga nam sai dutsen Namijin Bokoni da ke nesa kaɗan da waɗannan manyan duwarwatsu, wanda bishiyoyin kukoki suka yiwa geman ya.
Labarin Bokoni
Daga abinda muka ji a wannan yanki, Bokoni jarumi ne irin mutanen zamanin-da, zamanin da kusan maguzawa ke nuna jarumtar farauta a cikin kungurmin dazuka.
Don haka a wancan lokacin Bokoni ya tsallaka wata masarauta tare da neman aure. Kuma cikin sa a aka bashi duk kuwa da kasancewar akwai wanda yake matukar sonta.
Da aka yi biki aka watse, sai masu ɗaukar amarya suka taho da ita zuwa gidan Bokoni dake wannan yanki inda ya zama Rogo ayau.
Sai dai zuwan su keda wuya sai ga mahara sun yo gungu sun nufo su da nufin ɗauke amarya baki ɗaya. Wanda hakan ya tashin hankulan dukkan mutanen dake wurin.
 Ance tawagar Amarya nan take ta watse, kowa ya shiga neman mafita.
Anan ne Ango Bokoni ya shiga neman tsari daga abinda yayi imani dashi. Don haka akace ya roki rikiɗewa zuwa dutse tare da Amaryar sa.
Ance abinda ya faru kenan tsawon zamani da ya shige wanda zuwa yau sai dai tashin zance.
Daga bisani duwatsun sun zamo maɓoyar ɓanyan namun dazuka wamda har ta kai ga mitane na shayin gittawa ta yankin ma baki ɗaya.
Sai dai labarin yayi kama da abinda aka ce ya faru a Dutsen Amare dake Ƙasar Ƙaraye, inda ake iya hango alamar dutse mai kama da Amarya tayi lulluɓi. Da wasu duwatsun masu kama da gangunan kiɗa.
Don haka babu wani binciken kimiyya zuwa yau daya taɓa tabbatar da aukuwar irin waɗannan lamurori.
Amma dai  muna iya gaskata wuraren a matsayin tsoffin mazaunan maguzawa da suka rayu shekaru masu yawa da suka gabata.

Sunday, 5 May 2019

LABARIN TSOHON SOJA A LANDAN

LABARIN WANI TSOHON SOJA A BIRNIN LANDAN
Sadiq Tukur Gwarzo

Marigayi Mal Aminu Kano ya ruwaito labarin Tsohon soja a birnin landan a littafin sa 'Hikayoyin Kaifafa Zukata'.
  Ga labarin yadda yake:
Lokacin da aka ƙare yaƙin duniya na biyu cikin 1945, an sallami sojoji dubbai. Kowa kuwa an ba shi kuɗin sallama tare da godiya.
  A Ingila, an sami wani soja da aka sallama da irin wannan kuɗi. A lokacin yaƙi shi ya kasance direban manyan motoci ne.
  Saboda haka, da ya karɓi ƴan kuɗin sa sai ya tafi ofishin Birnin Landan mai kula da ɗaukar direbobin motocin haya na cikin gari.
  Da zuwan sa sai aka tura shi wajen injiniya mai jarraba direbobi kafin a ɗauke su aiki. Injiniya ya jarraba tsohon Soja ya tabbatar babu matsala kuma yana da ƙwarewa
  Daga nan sai ya tafi dashi ofis, ya ɗauki takardar ɗaukar aiki ya cike sunan sa da shekarun sa da dai sauran ababen buƙata.
  Bayan ya ƙare sai Injiniya ya miƙawa tsohon soja takardar yace ya sa hannu.
  Tsohon soja yace "Ai ban iya rubutu ba".
  Injini ya ce "KASH, Ai kuwa dokar majalisa ta hana a ɗauki jahili aiki. Don haka na yi baƙin cikin rashin ɗaukar ka wannan aiki"
  Shikenan, tsohon soja ya tafi gida yana ta saƙe saƙen abin yi. Daga ƙarshe ya yanke shawarar soma sayar da kayan miya a gefen titi a Birnin London.
   Ya fara da ƴan kuɗi kaɗan, amma wasa-wasa a cikin shekaru biyu sai gashi da kuɗi har fam dubu biyar.
  Nan fa ya fara tsorata kada ɓarayin gari su gane yana da kuɗi su bige shi su ƙwace, har wataƙola ma su ji masa ciwo ko ma su kashe shi.
Saboda haka, sai ya yi shawarar kai kuɗaɗensa Banki ajiya.
   Ya tattara kuɗaɗensa ya maƙe a aljihun rigar ruwansa ya tafi banki. Da zuwa sai kai tsaye ya wuce ofishin manaja. Ya zaro fam dubu biyar daga aljihu ya zube a kan teburin manaja. Manaja yayi zunbur ya miƙe saboda ganin tarin kuɗi irin wannan, nan da nan ya sa aka kawo masa shayi, sannan ya shiga cike masa takardar ajiya a banki.
Bayan da manaja ya kammala aikin sa, sai ya miƙawa tsohon soja takardar tare da umartar sa ya sanya hannu a jikin ta.
Nan fa ɗaya.. Tsohon soja ya dubi Manaja yace "Ai ban iya rubutu ba"
Manaja ya riƴe baki don mamaki yace "Ba ka iya rubutu ba? amma har ka iya tara wannan maƙuden kuɗaɗe haka? Ai kuwa inda ace ka iya rubutu da karatu, da maza maza zaka zama miloniya"
  Tsohon soja yayi murmushi yace "Sam Ba haka bane, da ace na iya rubutu, da yanzu direban babbar mota zan zama, ina ɗaukar fam ashirin duk wata.."
Ƴan uwa, ita rayuwar mutum aiƙaddarar sa ce. Duk kuwa abinda bawa ya nema bai samu ba, to haƙiƴa da sanin Allah, kuma idan yayi haƙuri Alheri sai ya biyo baya.

Saturday, 4 May 2019

TARIHIN BAUCHI 6

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na shidda

Bayan rasuwar Sarkin Bauchi Yakubu sai ɗansa Ibrahimu ya gaje shi. Shikuwa sai da ya shafe shekaru arba'in bisa karagar mulkin Bauchi.
   A shekatar farko ta mulkin Ibrahimu ne ya tara runduna tare da tafiya Angas yaƙi. A can ne ya buga gagarumin yaƙi da mutanen, ya kashe na kashewa ya kama na kamawa, sannan ya koma Bauchi da ganima mai yawa.
   Babu jimawa sai ya sake fita yaƙi zuwa Montwal, yaje ya kore su sannan ya koma Bauchi da zama..
  A shekarar mulkin sa ta biyu ya tafi yaƙi da wani mayaƙi mai suna Hamza. Ya gamu dashi ya yaƙe shi, ya watsa taron rundunar sa, ya kashe na kashewa ya kama na kamawa, sannan ya koma gida Bauchi.
   Bayan shekaru biyu kuma sai ya ciri runduna zuwa Tabula, ya zauna a ƙofar ta tsawon shekaru takwas. A cikin shekara ta bakwai da zaman sa a ƙofar Tabula ne ɗan uwan sa Salmanu ya mutu yana tare dashi. Jim kaɗan da faruwar haka sai ya ƙulla amana da kafiran wajen mazauna dutse sannan ya koma gida.
   Sai dai, Ibrahim sarkin Bauchi ya koma gida da shekara ɗaya ne ya samu labarin cewa dukkan kafiran duwatsu sun warware amanar da aka ƙulla dasu.
  Don haka ya shirya yaƴi ya tafi Das da ake kira Bununu (sunan Sarkin su Mummini) ya yaƙe ta. Daga nan ya tafi Duwa tare da sarkin Kano da Sarkin Zaria da Sarkin Gombe da Shehun Borno suka yaƙe ta.
  Daga nan sai ya tafi Gamawa tare da Sarkin Kano suka yaƙe ta.
 Bayan wannan kuma sai ya tafi Duguri yayi yaƙi da mutanen ta, sannan ya sake komawa Das yayi yaƙi, ya ƙara komawa Duguri ya sake gwabba yaƙi.
   Haka kuma Sarkin Bauchi Ibrahim ya yaƙi Jimbim, amma daga nan bai sake fita yaƙi ba, sai ya tafi Rauta ya zauna yana aikawa da hare hare zuwa abokan gaba, har kuma ya nemi a tuɓe shi daga sarauta a ɗora ɗansa Usmanu.
   Abinda ya nema kuwa shi ya samu, inda aka naɗa ɗansa Usmanu sarki, ya koma Bauchi da zama, yayin da mahaifin sa Ibrahimu ya cigaba da zama a Rauta. 

Friday, 3 May 2019

TARIHIN BAUCHI 5

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na biyar
A lokacin da rundunoni biyu suka fuskanci juna, watau rundunar Sarkin Bauchi Yakubu da ta Mayaƙi Kalumba, sai kowannen su ya buga tambarinsa, mayaƙa suka faɗawa juna da sara da suka, ƙura ta turnuƙe sama, sama ta cika da hayaƙi, yaƙi yayi zafi, ya huru, rana ta zama misalin dare, ba a jin kome sai ƙarar ƙarfe da tsarkiyar baka.
   Sannu a hankali sai duhu ya ƙara duhu, har ya zama abokin gaba baya ganin wanin sa. Sai Sarkin Bauchi yakubu ya baiwa jama'ar sa umarnin suyi ta harbin duhun har sai da duhun ya yaye aka ga Kalumba ya gudu, taron sa kuma ya watse, ya bar tambarinsa da tutarsa da laimar sa da tarkacensa da dukkan wani abu da yake mai nauyi anan suka bar shi suka gudu.
   Daga nan sai Yakubu ya tatttara kayayyakin na su ya aike da su wurin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, sannan ya koma gida Bauchi cikin farin ciki saboda taimakon da Allah Ta'ala yayi gare shi.
  Bayan wannan sai Yakubu ya sake tashin yaƙi zuwa Misau, ya yaƙe su, ya zauna a ƙofar garin su kwana talatin, ya hana su fita har sai da yunwa ta tsananta garesu ya zama suna cin dawakai da jakuna da sauran ababen dake hannunsu.
   Da abin yayi tsanani sai suka watse, Yakubu ya kama na kamawa saura kuma suka ɗai-ɗaice a duniya, suka bar birnin su wofi babu kowa.
   Yakubu ya koma gida ɗauke da ganima mai yawa, ya zauna tsawon wasu shekaru a gida, sannan ya tashi da yaƙi zuwa Tsaure, shikuwa gari ne a arewacin Bauchi, ya iske su suna sauraron sa, alhali bai san sunyi dakon zuwan sa ba, har sai da ya zo kan kan kan da su, sannan suka faɗa masa da yaƙi, ya yaƙe su da yaƙi mai tsanani har sai da ya kore su, ya kashe na kashewa, saura suka gudu suka bar gidajensu, shi kuwa ya ƙone gidajen sannan ya koma Bauchi tare da jama'ar sa
   Bayan wannan sai ya ƙara yin shirin yaƙi zuwa Tufi, nan ma ya same su sun taru a bakin babban dutsen su, ya hau su da yaƙi. Amma sai da yayi yaƙi dasu tsawon shekaru biyar sannan yaci galaba akansu.
  Wannan kuwa shine ƙarshen yaƙe yaƙen Sarkin Bauchi na farko Yakubu, domin daga shi bai sake fita yaƙi ba Allah yayi masa rasuwa. Dafatan Allah ya jiƙansa amin

Monday, 29 April 2019

TARIHIN BAUCHI 4

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na huɗu

Kalumbu mayaƙi ne daya tara taron mayaƙa masu yawa da raƙuma da dawakai marasa adadi, ya rubuta takarda ya aikewa sarkin musulmi Muhammadu Bello ɗan Usmanu bn Fodio da cewa " Ka sani, ni na mallaki abinda yake tsakanin mimi biyu (watau abinda yake tsakanin Mirsa da Malle)" yana mai bashi tsoro, yana yi masa narko da waɗansu baitoci dake cikin Nabinga, yace " Ni ina yi muku tsoro, kada rana ɗaya ta samu gareku domin tsananin ƙina, ranar nan kuwa wuyarta kamar ta ranaku masu yawa ce, saboda wuyar ta za a ga taurari da rana, gari zai zama haske ba haske ba, duhu ba duhu ba, har ku motsad da yaƙi mai hauhawa wanda bashi da misali, yana da kamar dare wanda yake cuɗanya da wani dare".
   Ko da manzon Kalumba ya riski Sarkin Musulmi da wannan sako, sai ya karɓi takarda ya karanta dukkan abinda ke ciki, sannan bayan ya gama ya juya bayanta, ya mayar da amsa da cewa "Na juyad da lamari na ga Allah, babu kuma ƙarfi ga saɓon Allah, dukkan su masu samuwa ne da ikon Allah". Sannan ya baiwa ɗan aike ya koma da ita.
   Sa'ar da Kalumba ya samu martanin sarkin Musulmi sai ya keta takardar bayan ya kammala karantawa, sannan ya hau da rundunar sa zuwa Kano. Ya sauka a ƙasar kano, duk inda ka duba sai jama'a da dawaki kawai ake gani. Jama'ar kano hankalinsu ya tashi, suka firgita firgici mai tsanani.
  Ana haka sai Sarki Musulmi Muhammad Bello ya aikewa Sarkin Bauchi Yakubu da yake yaƙia Das da cewa ya tafi wurin Kalumba ya yaƙe shi. Yakubu yace yaji kuma yabi.
 Daga nan sai Yakubu tara jama'arsa ya shaida musu halin da ake ciki tare da neman shawarar su, inda nan ma suka nuna goyon bayan su ga bin umarnin Sarkin Musulmi Bello.
  Babu jimawa sai Yakubu ya tashi da tawagar sa zuwa Bauchi, ya shiga tara ƴam baka, da ƙarin mayaƙa, sannan ya tashi ya ƙetare ƙasar sa zuwa Kano, ya sauka a wani wuri da ake kira Gantsa inda sansanin Kalumba yake. Rumdunoni biyu suka fuskanci juna, sannam aka soma shirin fafatawa.

Sunday, 28 April 2019

TARIHIN BAUCHI 3

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na uku
  Daga nan sai Yakubu yasa aka gina ramin ganuwa kusa da Inkel da ya ke da zama, akayi gini a wurin tare da sanya masa ƙofofi huɗu, sannan ya taso daga Inkel ya zauna acikinsa tare da jama'ar sa..   Wannan gari yanzu haka shi ake kira da suna BAUCHI.
   Mutane kuwa sai suka rinƙa zuwa gareshi rukuni rukuni suna yi masa mubayi'ar girma har sai da suka yawaita, ya zama suna fita wajen gari suna yin gidaje.  Yaƙi kuma ya rinƙa fita da hare hare zuwa yankunan kafirai.
   Yakubu ya aiki Muhammadu Kusu, da Dawaki Hammada da Yari su tafi yaƙi zuwa zaranda da Felu da Geji da Bulu, suka karkashe su tare da kamo ƴaƴansu bayi. Sannan Suka komo wurin Yakubu cikin aminci da tarin ganima.
   Bayan wannan, sai ya aiki Sarkin Yara Ibrahim ya tafi dutsen Boli da yaƙi. Da ya isa waɗansu sukayi sulhu dashi, waɗansu kuma suka ƙi don haka ya yaƙe su. Sannan ya wuce har zuwa Lago da Gabari yayi yaƙi dasu. Daga ƙarshe ya koma wurin Yakubu da ganima mai yawa.
   Haka kuma saɓani ya auku tsakanin Mallam Yakubu na Bauchi da Sarkin Gwambe Buba Yero,inda har sai da aka gwabza yaƙi a tsakani.
  Yakubu ya ƙetara kogi ya cimma Gwambawa da yaƙi, akayi kashe kashe, daga bisani akayi sulhu. Gwambawa sukayi alƙawari ba zasu ƙara tada fitina irin wannan ba..
Bayann wannan kuma sai Yakubu ya sake shiryawa ya tafi yaƙi zuwa Bununu, da Lere da Pursum da Bukuru sannan ya koma gida. Babu jimawa kuma ya sake tashi yaƙi zuwa Yamyam Ramu da Yamyam Jini. Daga nan sai ya shige Montal da Yargam da wasu wuraren mazauna duwatsu da suke biye da Yargam har zuwa Unkwai da Ɗan chandam.
Daga nan sai Yakubu ya ɗauki haramar yaƙi zuwa Lafiya da Awai da sauran wuraren gishiri. Bayan dawowar sa gida Bauchi ne mutane suka ƙaru wurinsa jama'a jama'a, da suka haɗar da Hausawa da Fulani, da Barebari dama sauran ƙabilu. Hakan yasa Yakubu ya ƙara girman Bauchi daga ƙofa huɗu zuwa ƙofa tara.
  Bayan wannan sai Yakubu ya ɗaura haramar yaƙi sannam ya tafi zuwa Das, ya zauna cikinta yana yaƙi da mutanem ta yaƙi mai tsanani har tsawon shekaru biyu, ya zama yana bin mutanen Das cikin duwatsu yana kisa.. ana kan haka ne kuma fitinar Kulumbu ta motsa tsakanin sa da Sarkin Musulmi na lokacin Muhammadu Bello. 

Friday, 26 April 2019

TARIHIN KASAR BAUCHI 2

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na biyu
  Sa'ar da lamarin Shehu Usmanu ya bayyana, mutane suka taru a wurinsa har suka yi yawa, sai sarakunan Hausa suka fara fushi da hakan, suka zama masu fitinar jama'ar Shehu Usmanu, suna aike musu da hari, suna kisa da kame su gami da siyarwa a matsayin bayi
   Da wannan abu ya tsananta sai jama'a suka yiwa Shaihu mubaya'ar yaki, suka soma gina ramin ganuwa da ɗaura tuta.
  Anan ne Shehu ya Umarci Yakubu ya koma gidasa Bauchi ya kira jama'ar sa zuwa biyayya ga Shaihu. 
   Yakubu ya tashi ya tafi ga mutanensa a Bauchi da ake kira Gerawa, ya kiraye su amma basu amsa kira ba. Sai waɗansu mutane daban ne suka amsa, acikin su akwai Mallam Adamu, da Ibrahimu, da Abdun-Dumi, da Hassan, da Faruku, da Muhammad Kusu, da Muhammad Yaro, da Hammada, da Mallam Badara, da waɗansun su da dama.
   Yakubu ya ja taron jama'ar sa zuwa wani wuri da ake kira Warunje ya zauna, sannan ya tashi zuwa Inkel, mutane na ta zuwa wurinsa a hankali suna yi masa mubayi'a.
  Daga nan sai ya shirya yaki zuwa wani gari da ake kira da suna Kanyallo, ya yaƙe su yayi galaba akansu, ya ƙone gidajensu ya washe dukiyarsu, sannan ya koma wurin zamansa. Wannan kuwa shine farkon yakin sa.
Bayan wannan sai ya ƴara shirya wani yaƙin, inda ya sarauta Galadima Faruku a matsayin Sarkin Yaƙi sannan ya aike su zuwa Miri, da zuwan su kuwa sai suka faɗa musu da yaƙi.
   Anan ma suka karkashe mutanen Miri, suka kamo ƴaƴansu, suka rushe gidajensu, Sarkin su ya gudu, ya tura iyalan gidansa cikin kogon dutse sannan ya karkashe su, daga bisani kuma ya kashe kansa.
  Galadima Faruku ya komo wurin Yakubu da ganimar yaƙi mai yawa cikin murna da farin ciki.
   Daga nan sai Yakubu ya shirya wani yaƙi zuwa Gubi.
  Su kuwa mutanen Gubi ance Kafirai ne masu girman kai, gasu jaruman gaske masu ƙarfin rai, babu mai iya samun su.
   Haka kuma suna zaune ne a wani wuri mai yawan duwatsu da wuyar shiga saboda santsin wurin shigar da kuma ƙafe-ƙafe gami da ƙayoyi.
   Amma duk da haka, sai da Yakubu yaci galaba akan su. Ya kore su suka bar gidajensu zuwa cikin duwatsu, shikuwa ya shiga cikin gidajen nasu, ya kashe na kashewa, ya kama na kamawa. Sannan ya koma gida Inkel cikin aminci da nasara.
  Ai kuwa wannan yaƙi shine ya tsoratar da dukkan kafiran ƙasar Bauchi, musamman mazauna saman duwatsu.

Tuesday, 23 April 2019

Tarihin Bauchi 1

TARIHIN ƘASAR BAUCHI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kashi na ɗaya
ASALIN SUNAN BAUCHIN YAKUBU
Kafin muji asalin Bauchi, zamu fara ne da sanin sarkin Bauchi Yakubu wanda sunan sa yafi shahara tare dana ƙasar.
Ance a karni na goma sha takwas daf da soma yakin jihadi a kasar Hausa, wasu malamai biyu masu suna Mallam Adamu da Mallam Isyaku suka tashi daga Borno zuwa Ganjuwa, inda suka zauna ƙarƙashin kulawar sarkin garin na wasu ƴan shekaru.
  Bayan nan sai suka tashi suka koma Kufu da zama, daga nan kuma sai suka ƙarasa Jetar.
  Anan Jetar ne Mallam Isyaku yayi abota da wani mutum da ake kiransa da suna Daɗi. Shikuwa yana zaune ne a wani wuri da ake kira Tirwin.
   Mallam Isyaku ya kan ziyarci abokinsa Daɗi a Tirwin, sai rannan Mallam Isyaku ya tafi wirin Daɗi inda ya tarar dashi tare da yaron sa mai suna Yakubu.
 Bayan sun gaisa sun soma firar duniya, sai Daɗi yace masa "Wannan yaro da ka gani ɗa ne gareni, kuma shi ne idanuna, Allah kuwa ya sanya sonsa da yawa cikin zuciyata. Ina da ƴaƴa da yawa banda shi amma ina so Allah ya albarkace shi a inda yake duka. Yanzu kuwa na baka shi, ka zama uba da shugaba a gareshi, shi kuma ya zama ɗanka mai-yi-maka hidima, domin ya sami albarkar ka. Inda kake so duka ka tafi dashi, dukkan abinda kake so ya yi maka duka ka sanya shi yayi, domin kuwa ɗanka ne, kai ne mahaifinsa".
   Abinda akayi kenan. Mallam Isyaku ya tafi gidansa tare da Yakubu ya cewa matar sa "Ga ɗanki nan".
Duk inda Mallam Isyaku zashi Yakubu na tare dashi, suna cikin haka har labarin Shaihu Usmanu ɗan Hodiyo ya zo musu. Mallam Isyaku ya tafi tare da Yakubu zuwa wurin Shehu Usmanu, ya zauna acan shekara da Shekaru yana karatun ilim.
  Rannan sai Mallam Isyaku yayi niyyar tafiya ganawa da iyalinsa, amma baya da niyyar jimawa acan. Don haka ya tsammaci cewar idan ya tafi da Yakubu zai hana shi dawowa da sauri, hakan yasa ya shaidawa Shaihu Usmanu muradinsa tare da barin Yakubu a hannunsa. Daga nan sai yayi wa Yakubu bayani sannan ya tafi..
   Allah da ikonsa, sa'ar da Mallam Isyaku ya riski wani gari mai suna Yalwan ɗan Ziyal dake ƙasar Kano, sai cutar ajali ta ka ma shi, anan ya rasu. Don haka sai Yakubu ya cigaba da zama wurin shehu yana karatu, ya zama tamkar ɗa a gidan shehu. Har ma shehu ya aurar masa da ɗiyar abokinsa Mallam Bazamfare watau Yaya.

Monday, 15 April 2019

TARIHIN FULANI SULLUBAWA

TARIHIN FULANI SULLUƁAWA

SADIQ TUKUR GWARZO

Sulluɓawa kuwa jam'i ne na sulluɓe, kalmar da akace an samo ta daga kakansu ko ace asalin wanda zuriyar ta fito daga tsatsonsa mai suna Sisillo. Shikuwa Sisillo, ai miji ne ga bafullatanar nan ta jinsin Toronkawa mai suna Chippowo, kanwa ga bafullatani batoranke Mallam Usmanu Toroddo, waɓda yake kakan-kakan shehu Usmanu Mujaddadi ɗan fodio.
 Don haka ake ɗaukar jinsunan sulluɓawa da toronkawa na fulani a matsayin 'yanuwan juna. (Ado-Kurawa 1989:45-49).
  Asalin sulluɓawa wangarawa ne, watau ana iya cewar kakanninsu ne suka taɓa zuwa kano zamanin Sarkin Kano Muhammadu Kanajeji har suka kawowa garin musulunci. Amma suna da alaka da yarukan Mandigo dana Mandika na yankunan Mali.
   Sunan asalin yarensu shine wakore, daga baya suka nutse cikin fulatanci yayinda suka mance yarensu suke yara fulbe (Usman 1974: 168-169).
  Izuwa yanzu kuwa yana da wuya ko a gidan sarautar kano da jikokin marigayi mallam Ibrahim Dabo ke mulka kaji ana fulatanci, domin tuni sun rikiɗe izuwa hausa zuryan.
  An kuma samu cewar jinsin sulluɓawa, sunfi kowanne jinsi tsari mai kyau acikin kabilun fulani tun kafin jihadin shehu Usmanu, domin kuwa suna da shugabancinsu mai suna 'Sarkin Sulluɓawa' a duk inda suke.
  Kuma a zandam suka soma zama, daga bisani suka rinka kwararowa yankunan katsina, zariya, sokoto da rima da sauran yankunan hausawa.
  Sannan kuma, tun da jimawa suna rike ne da addinin musulunci bisa kyakkyawar turba. Don haka da yakin jihadi ya ɓarke, 'yan kaɗan daga cikinsu ne suka goyi da bayan sarkin gobir, amma mafi yawansu suna cikin waɗanda suka bada gagarumar gudunmuwa wajen samun nasara, don haka nema ɗansu ya samu zamowa sarkin kano.
Wasu jimsunan fulanin da yadda ake gane su sune:

UDAWA : Jakai, rakuma da shanu suke kiwo. Kusan kasar su Niger amma suna fantsaowa har Nigeria.
Bararoji: Suna da fararen shanu, suna siyar da magunguna. Wasunsu nada jakuna.
Hana Gamba: Sunfi kama da Buzaye, suma siyar da magunguna bayan kiwo.
Yaɓeji: Masu fararen shanu
Bakolo: Shanun su babu ƙaho

Saturday, 6 April 2019

TARIHIN NUFE 7: LABARIN MALLAM DANDO 3

TARIHIN NUFE: LABARIN MALLAM DANDO
Kashi na bakwai

SADIQ TUKUR GWARZO
Tun bayan wancan yaƙi, sai Sarki Majiya ya koma Juguma da zama, anan ya cigaba da mulki har ya rasu.
  Akwai watarana da Mallam Dando ya aika masa da cewa "Ka komo garinka Raba da ka tashi". Sai Sarki Majiya ya mayar masa da cewa "Mu Nufawa ɗabi'armu ba mu komawa garin da yaƙi ya ci sai an ƙone shi, don haka zan zauna a Juguma".
Amma dalilin yaƙi tsakanin Mallam Dando da Etsu Isa akan kuɗin haraji ne wanda ƴaƴan Mallam Dando suka rinka zagayawa suna karɓa.
Etsu Isa yace "Ashe Mallam Dando yana son mulkin duniya ne tun da har yake aika ƴaƴansa cikin ƙasashe domin su karɓi haraji? Yana neman duniya domin kan sa ne ba domin mu ba, shine har muka biye masa muka kori ƴan uwanmu suka gudu wani wuri shikuma ya karɓe sarautar su?"
Don haka sai ya aike masa da cewa "Ni bana son ƴaƴanka su ƙara karɓar haraji a ƙauyen mu bayan wannan shekarar".
 Mallam Dando ya aiki manzon sa ga Sarki Majiya a lokacin da ya koma ƙasar Basa da zama da cewa " Ka dawo ƙasar ka da zama, ka sani yanzu babu amana tsakanina da Etsu Isa, bayan na taimakeshi yanzu ya zama abokin gaba ta".
A lokacin ne Sarki Majiya ya koma Juguma da zama saboda al'adar su ta Nufawa da ta sanya ba zai iya komawa Raba ba. Har mutuwa ta riske shi kuwa yana Juguma inda aka naɗa ɗansa Chado ya gaji shugabancin sa.
Shi kuwa Etsu Isa sai ya shirya yaƙi zuwa Raba don tumɓuke Mallam Dando a mulki.
Mallam Dando ya shiga Halwa ta kwana uku da yaji labarin zuwan sa. Ya fita halwa aƙarshen rana ta uku ya bi turba , ƴaƴansa suka fitad da sansani  suna biye dashi  riƙe da makamai har zuwa bakin kogi.
A wannan rana yaƙi yazo har bakin kogin nan ta wani waje da ake kira Jabara, a ranar ne ɗan Mallam Dando Ibrahim ya rasu a idon ubansa, a lokacin da ake tsaka da gwabza yaƙi. Da yaƙi yayi tsamari kuwa sai Etsu Isa ya gudu da tawagarsa ya koma Kaniya da zama. Bai ƙara ɗagawa Mallam Dando kai ba har mutuwa ta riske shi yana sarkin Kaniya, inda aka naɗa ɗansa Mu'azu magajinsa.
Shima Mallam Dando ya cigaba da zama a Raba har mutuwarsa, inda ɗansa Muhammad Saba ya gajeshi tare da ɗorar da yaƙi ga sauran ƙasashen Nufe, har takai ya samu iko sama da kusan ɗaukacin sarakunan dake ƙasar Nufe kafin daga bisani faɗace faɗace su raunana shi tsakanin sa da ƴaƴayen sarakunan nan da ubansa ya gwabza dasu watau Majiya da Etsu Isa da kuma tsakanin sa da ƴanuwansa ƴaƴan Mallam Dando masu biɗar sarauta.


TARIHIN NUFE 6: LABARIN MALLAM DANDO 2

TARIHIN NUFE: LABARIN MALLAM DANDO
Kashi na shidda

SADIQ TUKUR GWARZO

Daga nan sai Mallam Dando ya cigaba da zagaye ƙasar Nufe yana wa'azi da bayar da maganai. A haka ya ƙara samun kyautar wata mace baƙa kyakkyawa ta fuskar bada magani, ya mayar da ita ƙwarƙwarar sa. Itace ta haifa masa ɗa namiji Ibrahimu.  Jimillar ƴaƴayen da aka haifarwa Mallam Dando cikin Nufe takwas ne, maza bakwai da mace ɗaya.
Bayan wannan, sai yaƙi ya auku tsakanin Sarki Majiya da Sarki Idrisu wanda ake kira da suna Etsu Isa. Sarki Majiya ya fita zuwa Gbara ranar litinin cikin watan sha'aban, yayi yaƙi sosai da Etsu Isa inda ya kora shi har zuwa Ilorin, a lokacin kuwa Mallam Dando ya shiga tawagar Etsu Isa, don haka tare dashi akayi wannan gudun neman mafaka. Sa'annan Sarki Majiya ya koma garinsa Raba, su kuma suka cigaba da zaman su a Ilorin.
Ana haka sai wata rana Sarki Majiya yake cewa da mutanen sa " Ku sani ni sarki ne cikakke, ba ni da wani abokin faɗa, gabas da yamma, kudu da arewa".
 Sai wani mabushin Bansanagi, watau Sarewa, yace masa "Ka da kace ba ka da wani abokin faɗa da maƙiyi, ko ka mance da Sarki Isa da Mallam Dando waɗannan da suke zaune a cikin Ilorin?"
Daga nan sai Sarki Majiya ya aika da takardu zuwa ga Sarkin Ilorin yace "Ina neman Sarki Isa da Mallam Dando, ina so ka aiko mini dasu".
Shikuma Sarkin Ilorin sai ya rubuta takardar sulhu zuwa ga Sarki Majiya, amma sai Sarki Majiya yaƙi Sulhu. Ya sake rubuta takarda cewar "Na baiwa Mutanen Ilorin duka gaba".
Sai kuwa Sarkin Ilorin yace "Allah shine muke neman taimako duka a wurinsa, ya taimake mu in yaso".
Sarki Majiya ya fidda yaƙi ranar Jumua cikin watan shawwal, ya sauka a bakin wani rafi da ake kira da suna Ansa. Da saukar sa sai mayaƙan Ilorin suka riske shi, suka auka masa da yaƙi.
Da fari sarkin ya soma cin galabar su inda har ya shiga cikin garin Ilorin, amma sai suka ƙara ƙaimi inda suka kore shi kora mai tsanani, ya koma wajen gari.
   Sarkin Ilorin ya tara malaman Ilorin duka yace ko akwai wani malami wanda zai taimakeni akan wannan abokin gaban?"
  Duka suka ce "Ba mu da wani taimako wanda zamu taimake ka dashi"
 Sai Mallam Dando yace masa "Ni fa ina da taimakon da zan bayar, domin na fuskanci malamai da kuɗi zambar ɗari uku da dubu bakwai na sami asiri"
  Sarkin Ilorin ya ce "To kuwa Zan ba ka zambar dubu saba'in". Mallam Dando yace "Ijarata da kai abin da aka samu a cikin damfamin Sarki Majiya"
  Sarkin Ilorin ya ce " Na ƙara maka da damfamin Sarki Majiya na biyu idan da akwai".
 Sa'an nan Mallam Dando yace a nemo masa mazaje uku, ya fita wajen gari dasu da shirin yaƙi, suka sauka nesa da sansanin Sarki Majiya, sannan yace da mazajen su haƙa masa rami mai  zurfi dai dai da tsawon mutum, sannan yayi bukkah ya ɗibiya ta akan ramin ya shiga cikin ramin  kwana uku, sannan ya fita zuwa Ilorin da hantsi.
  Da shigar sa ya riski Sarkin Ilorin yace masa "Ina sarkin Yaƙin Ilorin?" Sarki yace Aliyu shine Sarkin yaƙi. Sai Mallam Dando yace a nemo masa hankaka, sarkin yaƙi ya biyo ni da tawagar sa da hanzari"
  Ai kuwa nan take akayi kamar yadda yace. Mallam Dando ya aikata asiri a bakin hankakan, ya baiwa Aliyu Sarkin yaƙi shi yace masa " kada ka saki hankakan nan har sai ka kusanci sarki Majiya"
Sarkin yaƙi Aliyu ya fita ta kan ganuwa kusan faɗuwar rana, ya zagaya ta yamma yabi wuraren da Sarki Majiya yayi sansani sannan ya saki hankakan nan, ya tashi fir zuwa laimar sarki Majiya, ya yi ƙara, nan take hankulan kowa na tawagar ya tashi, suka ruɗe, dukkan su suka bazama a guje yaƙin su ya karye, mutanen Ilorin suka samu riba dasu.
   Suka kama dawaki zambar ishirin da huɗu, da mataye ɗari takwas dake cikin damfamin Sarki Majiya.
Sai Mallam Danbo da Etsu Isa suka fita daga cikin Ilori suka koma Raba da zama bayan korar Sarki Majiya. Mallam Dando ya ce wa Sarki Isa "zauna a wannan gari" Sarki Isa yace ni bani zama cikin garin abokan gaban mu. Ni ina nufin zama a wani wuri ne da ake ce masa Jangi" Watau ya yiwa Mallam Dando Musu.
 Daga nan Mallam Dando ya zama mai iko da Juguma, ƴaƴansa ke karɓo harajin sauran ƙasashe duka, har daga baya kuma saɓani ya ƙara aukuwa tsakanin sa da Etsu Isa wanda yayi silar aukuwar yaƙi gagarumi a tsakanin su.

TARIHIN NUFE 5: LABARIN MALLAM DANDO

TARIHIN NUFE: LABARIN MALLAM DANDO
Kashi na biyar
SADIQ TUKUR GWARZO
Alƙalin Gwari Ummaru ya ruwaito cewa Farkon labarin Fulanin Nufe ya soma ne da Mallam Dando, wanda yazo ƙasar Nufe daga ƙasar Hausa.
Ance shi mutum ne matsakaici wajen tsawo da haske, bashi da kaurin jiki kuma. Ya iske Nufe a zamanin da Sarki Majiya ke mulki. Sai ya zama almajirin sa.
A zamanin da Mallam Dando yazo ƙasar Nufe yana da ƴaƴa uku, Majigi, Abdu Ɓuya, da Etsu Usmanu. Ya rinƙa yawo garuruwan Nufe yana wa'azi har ya isa Daba.
A wannan garin kuwa akwai wata mahaukaciya tana ɗaure cikin mari, ana kiranta da suna Fatsumako.
 Masu magani sunyi har sun gaji ba tare da ta samu sauƙi ba.
Rannan Mallam Dando na shigewa inda take sai tayi ƙara har ya jiyo muryar ta, sai ya tambaya "wanene yake ƙara haka?" sai akace masa "Wata mahaukaciya ce wadda masu magani suka kasa warkad da ita"
  Sai Mallam Dando yace "Ku bani ita ina warkad da ita, in Allah ya yarda".
Da waliyanta suka ji sai suka amsa masa da cewa "Mun baka ita". Mallam Dando ya koma gida ya yi rubutu a alluna biyu, ya wanke, ya zuba a cikin ƙoƙuna biyu ya aika musu. Yace ƙwarya ɗaya ayi mata wanka da ita. Ɗayar kuwa a bata tasha. Sannan ya haɗa musu da turare na hayaƙi da za a yi mata turare dashi.
  Iyayanta suka aikata kamar yadda manzon Mallam Dando ya sanar musu.
  Da aka kwana uku sai Mallam Dando ya tafi don ya ganta, sai yace da iyayen ta "ku kwance mata marin nan". Iyayenta suka yi wa Mallam Dando musu kaɗan, sa'an nan suka yarda suka kwance ta. Mallam Dando ya kaita cikin kafe yace ta zauna nan.
Daga baya sai ya nemi aurenta suka amince masa, bayan sunyi aure ya tafi da ita Juguma suka kwana ɗaki ɗaya. Daga nan bata sake komawa cikin halin hauka ba. Ta sami cikin ɗa Mustafa, sannan ta haifi Muhammadu Saba.
A zamanin da ta haifi Muhammad Saba sai sarki Majiya Zubairu yace yana sonsa, don haka abar shi a hannun sa ya girma.
Akwai wata rana da Sarki Majiya ya shirya zuwa yaƙi Kukuku, mallam Dando ne ya bashi asiri ya kai ya zuba acikin ƙasar, sannan yaci su da yaƙi ya samu dukiya mai tarin yawa. Daya komo gida sai ya aikewa Malamin kuyangi guda biyu a matsayin kyauta.
 Mallam Dando ya karɓe su yayi godiya, ɗaya ya mayar da ita sa ɗakan sa, ita ce Habibatu, ɗaya kuma ya aikewa Atiku ɗan Shaihu Usmanu, hasken zamani, kogin talikai, babban waliyi, itace ta haifi Ummaru Nagwamatse. Wannan duk anyi shine bayan rasuwar sarkin Musulmi Muhammad Bello ɗan Shehu Usmanu Ɗan Fodio.

Wednesday, 20 March 2019

HIKIMAR IYA MULKI

HIKIMAR IYA MULKI: LABARIN MADAKIN KANO MAHMUDU

Marigayi Mallam Aminu Kano ya ruwaito a littafinsa 'Hikayoyin Kaifafa Zukata' cewa:
   An bamu labari cewa a zamanin marigayi madakin Kano Mahmudu, talakawan wani ƙauye a ƙasar Bichi sun yi bore  bisa biyan haraji.
Bayan sun ƙi biyan harajin, har ma dagacin ƙauyen suka kora da jifa.
Lokacin da dagacin ya isa ga Hakimin Bichi, sai nan da nan Hakimi ya aike dogari da yaran hakimi don a binciko masa lamarin.
Ai kuwa dogari da yaran hakimi suma basu tsira ba, domin da zuwan su sai suka tarar mutanen garin sunyi shirin yaƙi mazansu da matansu, sun fito da karnukan su na farauta, suna masu riƙe da masu, kwari da baka da gatura. Don haka ba jimawa suka ranta a na kare zuwa gaban Hakimi.
Ganin abu ya kai haka sai hakimi ya aika zuwa ga Sarkin Kano. Daga nan kuwa aka sanar wa Razdan na kano.
  Shi Razdan bai yi wata-wata ba sai ya gayawa baturen ƴansanda cewa a tafi da shiri zuwa ƙauyen a kamo masu boren.
Amma da wannan magana ta dawo gaban Sarki, sai Madakin Kano Mahmudu ya yi wuf ya ce yana roƙon Sarki ya bashi dama ya soma zuwa da kansa kafin a je da ƴan sanda.
Da turawa suka ji wannan sai suka ce fau-fau haka ba zata yiwu ba. Tun da har mutanen sun ɗauko makamai, maganin su ƴan sanda masu bindiga.
Duk da haka, Madaki ya dage cewa yana roƙo a bari ya fara zuwa tun da shine Kansila mai kula da hakimai, haraji da sauran irin su. Kuma mutanen ƙauyen suna tare ne da matansu da ƴaƴansu duk a garin.
Da ƙyar dai turawa suka yarda ya je.
Ai kuwa da zuwan sa garin Bichi, sai ya aika ƙauyen da saƙo cewa Sarki ya aiko shi gare su, don haka yana so su taru dukkansu a cikin shirinsu, kada a rage kowa.
Kafin a ce mene ne wannan, mutanen sunyi cincirindo a bakin kasuwar ƙauyensu mazansu da matansu. Suna cike da fushin komai zai faru sai dai ya faru.
  Ba jimawa sai ga Madaki tare da Hakimin Bichi, da dagacin ƙauyen, da malaman hakimi sun ƙaraso wurin. Wuri yayi tsit ana sauraron aji saƙon Sarki.
   Sai Madaki yace "Jama'a Sarki ya gaishe ku, ya kuma ya gaishe ku. Ya ce in gaya muku cewa ya sami labarin abinda ya faru tsakanin ku da mai garinku wanda har abu ya kai da tashin hankali.
To kuyi sani, abinda Sarki yace in faɗa muku shine Sam bai taɓa cewa ku biya haraji ba. Saboda haka kun yi gaskiya da kuka ƙi biya."
Nan take wuri ya ɓarke da sowa ta godiya da cewa 'Allah ya bar Sarki, Allah ya bar Sarki'.
Sai Madaki ya cigaba da cewa "Amma abinda Sarki ya gaya wa mai garinku ya karɓa gare ku shine kuɗin arziƙi. Don haka ya turo ni in ware masu arziƙin cikin ku da matsiyatanku don mu sallami matsiyatan, masu arzikin su biya".
  Nan fa wuri yayi tsit. Sai wannan ya dubi wannan yace "yo waye zai yarda a kira shi matsiyaci?".
Daga can sai wani dattijo yace "Ranka ya daɗe duk cikin mu ba matsiyaci, saboda haka muna so mu je mu kawo".
Madaki ya basu lokaci aka tattaro harajin ƙauyen tsaf ba tare da anje da bindiga ba, wanda a wancan lokacin yawan harajin bai kai ya kawo ba.
Don haka Sahabi Mu'awiyya ya taɓa faɗawa ɗansa Yazidu cewa "Idan za ka biya buƙata da harshe, kada ka sa alƙalami. Idan kuwa da alƙalami ne, to kada ka sa takobi".

BARKWANCIN HAUSAWA

BARKWANCIN HAUSAWA

Acikin kowacce ƙabila a duniya, bayan tatsuniyoyi da karin magana da zambo da habaici, ana samun abubuwan da ake kira 'barkwanci'.
Shi Barkwanci ba batsa bane, ko ɓatanci ga wani. Ba kuma karin magana bane, kawai dai wata hikima ce mai ban sha'awa a tsakanin mutane.
Misali, idan mace tana da jika ɗa namiji, takan kira shi da suna 'mijina', shikuma yace 'matata'. Wannan barkwanci ne.
Ɗan mace da ɗan Namiji suna baiwa juna kuɗin shara a watan Muharram, wato watan cika ciki ko ace watan farkon shekarar hijiriyya. Wannan ma barkwanci ne.
Idan yaro ba ya jin magana, sai a kira shi da suna 'mai kunnen ƙashi'. Idan matar aure ta gamu da wani mai suna irin na mijinta ko ɗanta na fari, ba zata kira shi da sunan ba sai dai ta sakaya da wani sunan. Waɗannan duk barkwanci ne.
Haka ma ƴaƴaye basa faɗin sunan iyayensu saboda barkwanci.
Sannan idan mutum yaje baƙunta wuri, zaka ga baya cinye duk abinda aka kawo masa saboda barkwanci. Amma bayan ya kwana biyu a wajen sai ya rinƙa share abincin da aka kawo masa Kaf saboda barkwanci.
   Idan an tambayi marar lafiya 'yaya kaji da jiki?', sai kaji yace 'Mun gode Allah', ko yace 'da sauƙi', koda kuwa yana cikin tsananin ciwo ne. Wannan fa duk barkwanci ne.
Idan kuwa mutum ya samu wani abin alheri sai kaji yace 'kaga gamu dai' saboda barkwanci.
Watau dai, barkwanci a taƙaice hanya ce ta kyakkyawar tarbiyya mai sanya mutum yin dogaro ga Allah wajen faɗar abinda yake ciki, ko kuma ya nuna kunya da ladabi ga jama'a.
Haka kuma abu ne da yake koyar da jurewa wani abu kamar misali ciwo.
Don haka marigayi Mallam Aminu Kano (Allah yajiƙansa amin) yace ya kyautu a rinƙa koyar da barkwanci da sauran ɗabiu kyawawa na Hausawa a gida da makarantu don ɗorar da tarbiyya kyakkyawa ga yara masu tasowa. Rashin yin hakan kuwa shine zai sanya yara su tashi da son kallon sinimar iya sata ko kashe mutane ko wulaƙanta iyaye ko malamai ko sarakuna da dattijai da rashin tausayi, har kuma kaga sunyi zurfi wajen kwaikwayon raye-rayen batsa da ashariya da raina haƙƙi.