Saturday, 27 January 2018

TARIHIN ZUWAN TURAWA ZARIA 2

 ZUWAN TURAWA ZARIA

Kashi na biyu

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Sarkin Zazzau Kwasau ya gamsar da zuciyarsa cewa ko kaɗan ba zaiyi biyayya ga turawa ba, tunda kasar sace ba tasu ba. Kuma ba addini ɗaya gare suba. Don haka ya soma tunanin mafita.
   Akan haka ya aike wa Sarkin Kano Aliyu Babba wasikar neman tallafi, yana mai shaida masa cewar kiristoci sun yawaita a Zazzau, har kuma sun yi kaka gida gareta tare da maisheta mallakinsu, don haka yana neman mafita.
   Ana haka sai rikicin kisan Kyaftin Moloney ya bijiro.
   Shi Kyaftin Moloney, shine Rasdan na Kyaffi. Ita kuwa Kyaffi tana karkashin daular Zazzau ne a lokacin. Kuma Sunan shugabanta wanda yake a matsayin wakilin sarkin Zazzau a Kyaffi shine Magaji Dan Yamusa.
   Akace rannan Kyaftin Moloney ya tara mutane yana musu jawabi, yana karanto turanci garesu, wani bakin mutum kuma yana tafintan abin da duk ya faɗa.
Magaji Dan Yamusa da tarin wasu jama'a duk suna wurin.
  Kwatsam sai rashin fahimta ya dabaibaye tafintan kyaftin Moloney sakamakon tsauraran kalmomin turancin da Moloney ke karantawa, shikuma tafinta sai ya rinka yiwa turancin fassarar kalma da kalma..
   Akan haka ya faɗawa mutane cewar turawa keda iko dasu, da komai nasu. Har matayensu ma mallakin turawa ne.
   Ance kafin a ankara sai ganin kan Kyaftin Moloney akayi yana mirginawa a kasa, Magaji Dan Yamusa ya saro shi.
  Daga nan faɗa ya ɓarke tsakanin mutanen Magaji da dakarun Moloney.
  Daga karshe dai, Magaji Dan Yamusa ya gudu da tawagarsa zuwa kano. Sarkin Kano Alu Babba yaji daɗin abinda Bakonsa yayi, ya karrama shi tare da bashi mafaka.
   Duk da cewar akwai saɓanin inda wannan rikici ya auku, shin a Keffi ne ko a Zaria, amma dai turawa sun ɗora alhakin faruwar hakan akan Daular Zazzau, tunda acikin ikon ta abin ya faru.
  Sannan kuma sun damu matuka bisa abinda Sarkin Kano yayi, wannan yasa suka sake ɗaura aniya da kaimin tafiya kano da yaki duk da cewa daman fakonta sukeyi.
   Ganin haka sai Sarki Kwasau ya soma shirin guduwa, saboda ya tabbatar abinda zai faru ba mai daɗi bane.
  Ya sake aikewa da wasika ga Sarki Alu Babba na kano yana sanar masa da cewar lallai ba-suga ta zama ba, haɗari gagarumi na zuwa garesu.
   Sukuwa turawa sai suka ji tsoron idan Sarkin Zazzau ya gudu da mutanensa, to fa zaije ya haɗu ne da Sarkin Kano su kara karfi, don haka sai suka baza dakarunsu akan hanyoyin Zaria zuwa kano, zaria zuwa Katsina da Zaria zuwa Bauchi, da niyar hana sarkin gudu ko kuma a kame shi idan ya gudo.
   Rannan sai kurum Rasdan na zaria watau kyaftin Abadie, ya aikewa Sarki Kwasau gayyata domin tattaunawa.
  Sarki Kwasau ya fusata da haka, yace don me kamar kyaftin Abadie kirista da yake a kasarsa zai kira shi yazo, don haka ba zai jeba.
   Daga nan sai turawa suka samu yadda suke so, suka turo dakaru masu ɗumbin yawa cikin zaria, suka yiwa fadar Sarki kwasau kawanya, sannan suka shiga suka kama shi tare tafiya dashi Wushishi. Acan suka tsare shi har Allah yayi masa rasuwa.
  Kuma an samu cewar Sarki Kwasau yayi rubututtuka dangane da yadda aka kamashi da halin daya tsinci kansa. Aciki akwai wata takarda mai suna 'Nuzhatul Asiyr' inda ya rubuta cewar turawa sun kama shine bisa kin yi musu biyayya, a yammacin wata ranar jumua cikin kwanaki goman karshe na watan Jumada Ula. (dai-dai da 19-satumba-1902).
   Sannan kuma ya bayyana farin cikinsa bisa yadda suka kamadhi ba tare daya bi umsrninsuba ya zauna akarkadhinsu, hsr ma ya kamanta kansa da mutanen Ashabul Kahfi a wata waka ea aka samu ya rubuta.
  Daga karshe, sai turawa suka naɗa Galadima Salmanu sarkin Zazzau a farkon shekarar 1903.


TARIHIN ZUWAN TURAWA ZARIA 1

ZUWAN TURAWA ZARIA

Kashi na ɗaya

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Tun gabannin mamayar turawa ga daular Zazzau, an samu cewa karfin daular ya ragu nesa da yadda ta kasance a baya sabili da wasu dalilai
   Da fari dai, akwai rikicin cikin gida daya mamaye kabilun fulani da suka jagoranci karɓe ikon Zazzau a zamanin Jihadi saboda neman mukami.
  Ance tun zamanin Sarki na farko aka soma wannan saɓanin  tsakanin Jagora kuma sarkin Zazzau na farko Mallam Musa da wani Ja'e shugaban kabilar fulani Yesgwamawa, amma sai aka bashi sarautar Kajuru aka zauna lafiya.
   Daga baya sai rikicin ya sake kamari bayan rasuwar Sarkin Zazzau Usman Yero, a wajajen shekara ta 1897 kenan.
  Hakan ya samu ne ta yadda kabilu huɗu na fulani da aka sani da mulkin zazzau suka nuna bukatarsu ga mulkin, kabilun sune Mallawa, Katsinawa da Barnawa.
   A cikin masu neman mulkin akwai ɗan marigayi Sarki Yero mai suna Madaki Kwasau, sai Mallam Lawan ɗan tsohon Madaki da kuma wani daga cikin 'ya'yan tsohon sarkin zazzau Mallam Sambo.
   Babban abinda kuma ya samar da saɓani a lokacin shine yadda Galadima ya tsaya kai da fata cewar wani kurma kuma Makaho mainsuna Mallam Muhammd ya kamata a baiwa sarauta. Mutane sunce hakan nada nasaba da kokarinsa na ɗora wanda ba zai iya kataɓus ba a mulki ta yadda zai rinka juya shi.
  Ganin karfin ikonsa yasa waɗancan kabilu na fulani suka dunkule tare da goyawa Madaki kwasau baya domin ya zama sarki. Akan haka suka nemi gudunmuwar Sarkin Kano Aliyu Babba, da kuma rundunar 'yan bindiga da mahaifin Madaki Kwasau ya kafa a zamanin rayuwarsa, shikuwa Galadima sai ya nemi goyon baya daga Sokoto.
   Ana cikin wannan kiki-kaka, sai wazirin sokoto Buhari yazo zazzau da niyyar masalaha. Ya lura da haɗarin dake ciki ainun idan aka ɗora wani ba Kwasau ba akan gadon mulki, tunda yasan yadda Basasa ta kaya a kano, sai kurum ya ɗora Madaki Kwasau sarautar Zazzau.
  Yin haka keda wuya sai wasu daga mabiya da garuruwa suka fara yin bore.
  Sarki Kwasau ya shirya yaki ya tafi Gwari, da Kataf da Kadara tare da tilasta musu yin biyayya a gareshi.
   Abu na biyu kuma da ya sake raunana zazzau shine hare-haren da take samu daga wasu sarakunan hausa misalin Maraɗawa da Ningawa.
  Idan dai ba'a manta ba, a lokacin Maraɗawa na tsaka da kai hare-hare kasar hausa. Bayan sarkin su Dan baskore ya mutu, sai wanda ya gajeshi mai suna Baratiya ya ɗora akan inda ya tsaya.
  Baya danan sai Mutanen Ningi, waɗanda akai-akai suke kawo hari ga birnin Zazzau. Shine har akace sun taba yiwa zazzau ɗin ruwan kibiyoyi a lokacin da suka kawo faɗa zazzagawa suka shige cikin ganuwa suka kulle kansu. Kuma har sun kwace ikon wasu garuruwa irinsu Soba, Dutsen Wai da Kubau daga Zazzau.
  Kari akan haka shine Sarkin Kwantagora Nagwamutse, shima a lokacin ya addabi zazzagawa da hari.
  Duk kuma a wannan lokaci turawa fakare sukai suna kallon zazzau. Saboda ance sun gama lissafa cewar itace cibiyar da zata fi a garesu wajen kafa sansani kafin kaiwa Kano da Sokoto hari.
   Kuma kasancewar akwai turawan mishan dake al'amuransu a Zaria sai ya zamana turawa basu da burki gareta, suna shigowa suyi hurɗoɗinsu babu tsangwama.
  Ana haka sai labari yazowa Sarkin Zazzau Kwasau cewa turawan mishan sun nemi wurin zama a Kano amma sarki Alu ya koresu, sannan rundunar dakarun turawa mai suna 'West African Frontier Force' (WAFF) ta kone garuruwan Remo da Kaje dake karkashin zazzau, kuma da raɗe raɗen zasu kawowa zaria yaki don hana cinikin bayi. Sai kawai sarki Kwasau shima ya kori turawan mishan daga kasar sa suka koma Girku da zama.
   Yin wannan keda wuya sai shugaban waccan runduna ta turawa mai suna Kaftin Kambell ya kawo ziyara ga sarki Kwasau, yace yazo kulla abota ne dashi tare da samar da yarjejiniyar zaman lafiya a tsakaninsu.
  Abinda ya kara kwantar wa da Sarki Kwasau hankali a game da turawa shine yadda suka kame kwantagora tare da korar sarkin su abokin hamayyarsa Sarki Ibrahim Nagwamutse a  shekarar 1901, sannan kuma suka kame sarkin a wani faɗa da sukayi a Maska suka aike dashi garin Lokoja aka tsare.
   Wannan yasa hankalinsa ya kwanta dasu domin sunyi masa maganin abokin hamayyarsa, suka rinka kwararowa cikin zaria suna lamurorinsu.
   Sai dai kwatsam babu aune, sai sarkin Zazzau Kwasau yaji turawa Sun ayyana Zaria a matsayin garin da suke iko dashi tare da kawo wani bature mai suna Kaptin Abadie da akafi sani da suna Mai jimina a matsayin Rasdan na garin, wannan yasa sarkin cikin damuwa da ɓacin rai.
   Ya shiga tunanin mafita a wannan lamari, gashi yana da rauni wajen faɗa da turawa, sannan sarkin Bidda ya aiko masa da gargaɗin kada ya kuskura yace zai buga dasu, gashi kuma yana jin kaskancine ya cigaba da zama a kasansu.
  Don haka mafitarsa biyu ce, kodai ya hakura ya zauna cikin kaskanci, ko kuma ya nemi taimakon sarkin Kano Alu yayi yaki dasu.
  Da tunani yayi zurfi, sai kurum ya zaɓi shawara ta biyu..

TARIHIN JIHADIN FULANI A ZAZZAU

YADDA JIHADIN FULANI YA KASANCE A DAULAR ZAZZAU

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

Saɓanin jihadin fulani daya auku a kano wajajen shekara ta 1803-1804, jihadi a daular zazzau bai auku ba a sai a wajajen shekara ta 1808.
  Dalilin haka shine karɓar kiran limamin yakin Jihadi, watau shehu ƳUsmanu ɗan fodio da sarkin daular Zazzau Isyaku Jatau yayi a zamanin rayuwar sa.
   Sarki Jatau ya aikewa shehu Usmanu sakon mubaya'ar sa a lokacin da Shehun yayi hijira zuwa Gudu. Haka kuma ya aikewa malamai masu yakin jihadi a kano bukatar aiko malami gareshi wanda zai koyar dasu addini, inda akace jakadun sarkin sun haɗu da malaman jihadin kano a gundumar Karaye, har kuma suka aike da Mallam Dan Zabuwa da wasu mutane gareshi.
  Daga baya mallam Danzabuwa ya faɗa ga malaman jihadi cewar sanda ya riski fadar zazzau, ya taras da Sarki Jatau abisa karagar mulki, sanye akansa rawani ne na mabiya sunni da Shehu Usmanu ya kawo saɓanin rawanin haɓe da sarakunan hausawa ke sanyawa kafin zuwan Shehu.
   Sai dai wannan abu ya tayar da kura a zazzau.
  Mutane da yawa basu ji daɗin yadda sarki Jatau ya bijirewa al'adun daya gada ba ya koma kan abinda shehu yazo dashi. Haka kuma yadda yasa aka rushe wurin bautar Iskokai tare da maishesu Masallatai yayiwa mutanen zazzau ciwo, ciki harda manyan fadawa masu faɗa aji ga Sarki.
  Akan haka akace wasu kusoshi a daular irinsu Magajiya, da Iya da Shebagu, da Wagu suka rinka haɗa kan mutane domin yiwa sarkin bore ko kuma a tilasta masa komawa tsohuwar al'ada, amma sarkin sam yaki biye musu.
   Ana haka sai sarkin ya gushe, masu zaɓen sarki suka haɗu akan ɗora ɗansa Makau amma bisa sharaɗai guda uku.
  Na ɗaya akace masa dole ya karya duk wata yarjejeniya da mahaifinsa Jatau yayi da Tubake, watau musulmai mabiya koyarwar shehu Usmanu ɗan fodio.
  ƁNa biyu dole ya hukunta waɗanda suka ɗora sarki Jatau bisa wannan tafarki na bijerewa abinda kaka da kakanninsu sukeyi a zazzau musamman limamin Kona da Limamin Juma.
  Na uku dole ya rushe masallatai da Sarki Jatau yayi, ya maishesu wurin bautar Iskokai kamar yadda suke a baya.
  Aikuwa da hawan sarki Makau mulkin Zazzau, abinda ya soma kokarin cikawa kenan.
  Akan haka yasa aka rushe masallatai har dana Jumu'a, aka maishesu wuraren bautar Iskokai.
  Sannan yasa aka kama Liman Mallam Muhammadu Lawal aka ɗaure a fadan-fadan, daga baya aka kashe shi. Shikuwa ɗaya limanin Mallam Hamidu mai Jan Rago sai ya gudu ya tsira da ransa.
 Koda labarun Waɗannan abubuwa suka riski Shehu Usmanu, sai ya haɗa tawagar mabiyansa karkashin Mallam Musa ya turo su Zazzau domin suyi yakin jihadi anan..
  A cikin waɗanda zasu taimaka masa akwai Mallam Yamusa, da Mallam Abdulkarim, da Mallam Abdulsalam waɗanda dukkansu sai da sukayi sarautar zazzau bayan sun samu nasarar karɓe iko da ita.
  Sai kuma malamai irinsu Mallam Usmanu Sabulu bahaushen kano wanda ya zamo Katukan Zazzau, da Dokaji bafullatani da akayiwa sarautar Galadima, da Mallam Hamma bahaushen kano da akayiwa Dallatun zazzau, da Mallam Gabdo bafullatanin 'Yandoto daya zamo limamin zazzau na farko bayan Jigadi.
  Sauran kuma mutane ne mabiya shehu Usmanu da suka fito daga wurare daban-daban, misalin Tofa, Yandoto, Borno, Katsinawa, Barnawa, Dan Dorori, Yeskwa, Joli, Gadidi, Bebeji da zaria.
  Sai dai tun kafin isowarsu har labari ya iske sarki Makau. Don haka ya tara dakaru masu ɗumbin yawa, ya aike da wasu kimanin dubu ashirin Hunkuyi domin tarar masu jihadi da ɗai-ɗaitasu.
  Ai kuwa dai, an gwabza faɗa da Masu jihadi a garuruwan Hunkuyi da Kudan har kuma an kusa cin galaba akansu, amma cikin ikon Allah sai suka samu taimako daga wasu sarakunan mulki na yankunan.
  Mutum na farko daya basu taimako shine dagacin Kauyen Durum, wanda ya kuɓutar dadu daga dakarun Makau.
  Na biyu kuma shine sarkin Fawan Likoro daya labarta musu yawan adadin dakarun dake gabansu a Hunkuyi. Don Haka sai suka yanke shawarar kauracewa yakin fito na fito, suka sulale ta Kudaru suka shige birnin Zaria ta kofar Bai ba tare da kowa ya sani ba.
   Wasu sunce Sarki Makau da mabiyansa na cikin gudanar da Sallar Idi masu jihadi suka karɓe iko da zaria, amma saboda hujjar kiyayyar Sarki Makau ga musulunci, wasu suka ce sam ba haka bane, yana bayan gari da dakaru yana sauraron yaji yadda ta kaya tsakanin dakarunsa da masu jihadi sai labari ya riske shi cewar masu jihadi sun karɓe ikon garinsa cikin ruwan sanyi.
  Wannan abu sai ya tsorata rundunar dashi kansa.
   Akace sai Sarki Makau yayi kudu tare da wasu tsirarun dakaru da basu wuce dubu uku ba, ya sauka  a garin Kajuru inda ɗan uwansa mai suna Albarka ke shugabanci.
  Daga nan sai sarki Makau yabar Kajuru ya tafi Abuja inda ya kafa mulki acan. Ance kuma shine dalilin da har yanzu ake kiran sarkin Suleja da Sarkin Zazzau ɗin Suleja.
  Shikuwa Albarka sai ya taho zaria tare da ɗan wani malami mai suna Abduljalil dake karantaswa a Kajuru, sukayi mubuya'a ga Mallam Musa, aka kuma karɓe su da martabawa.
  Ance shine Aka baiwa Albarka gida a kusa da Fada, kuma daga gareshi Sunan Unguwar Albarkawa ya fkto.
  Shikuma Ibrahim Tsoho aka bashi gida kusa da gidan wasu masu kakaki, kuma daga nan sunan unguwar Kakaki ya fito.
  Mallam Musa kuwa shine ya zama sarkin Zazzau na farko bayan jihadi. Kuma yayi mulki ne a gidansa dake Unguwar Kwarbai, bayan fadar Zazzau ba tare da ya shiga gidan sarautar Bakwa ba saboda tsoron kada ya sauka daga tafarkin Sunna zuwa aikata abinda sarakunan Haɓe suke aikatawa.
Kunji yadda Jihadin Fulani a Zazzau ya kaya.

TARIHIN DAULAR ZAZZAU 7

TARIHIN KAFUWAR DAULAR ZAZZAU

Kashi na bakwai

  DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

3. LIMAMCIN KONA
  Kamar yadda yazo tun a farko, a tarihin Kona, ance wasu malamai ne da suka zo wucewa ta zazzau tun kafin ayi ginin ganuwa, suna neman inda zasu zauna. Sai babbansu ya kalli wani wajen yace musu "Ko nan zamu zauna? "
   Wasu sun faɗa cewar waɗannan malamai daga wani gari mai suna Kulunfardu suke can kusa da Borno, kuma sun zauna a wani wuri cikin kasar zazzau Inda daga baya ya zamo kauyen kona tun a wajajen shekara ta 1350.
  Don haka da aka gina ganuwa sai suka tashi daga Kona suka shigo zazzau.
 An sanyawa  kofar da suka shigo zazzau ta ciki suna Kofar Kona. Sunan Inda suka sauka kuma ya zamo 'Iimancin Kona', domin a lokacin sune malamai masu yin limanci a daular zazzau.
  Haka kuma wannan unguwa ta zamo wurin karantaswa, inda malaman ke koyar da ɗalibai ilimomi na addinin musulunci daga littattafai misalin Bukhari, Jamiu Sagir, Ashafa, Samar-kandi da wasunsu.
   Daga wannan unguwa ne kuma tarihin wasu unguwannin zazzau biyu ya ciro.
  Unguwa ta farko itace Limancin Alfadarai, wadda akace wani balaraben Misra ne ya taɓa zuwa zazzau daga Borno ya sauka a limancin kona. Sunan sa Mal Salihu, kuma a tare dashi akwai alfadarai masu ɗauke da tulin littattafai na addinin musulunci.
   Daga baya sai aka bashi wuri domin ya zauna.
 Inda ya koma da zama ake kira da suna limancin Alfadarai zuwa yau, kuma sai daya fifici malaman kona ilimi har ma ya zamo limamin zazzau.
 Unguwa ta biyu kuwa itace Limancin Iya.
  Ita kuma akace akwai wani malami kuma limami a Kona wanda ya nemi auren ɗiyar sarkin zazzau.
  Kasancewsr sarkin zazzau na lokacin ɗalibinsa ne wajen neman ilimin addini, sai ya aura masa ita.
  Daga nan sai sarkin ya bashi wurin zama dashi da iyalinsa ya bar kona da zama.
  Unguwar da limamin ya zauna ake kira limancin Iya.
4. ANGUWAR JUMA
  Ance wannan wuri na daga cikin daɗaɗɗun wurare a birnin zazzau da ake tsammanin tun kafin gina ganuwa akwai mutane a wurin.
  Amma dai abinda aka tafi akai shine, wurin ya haɓaka ne saboda masallacin zazzau na juma'a da aka gina tun karni na goma shabiyar zamanin Sarkin Zazzau Muhammadu Rabbo.
  Don haka akace ainihin sunan Unguwar shine 'unguwar masallacin Juma'a', daga baya mutane suka yanke shi zuwa Unguwar Juma.
  Akwai malaman Juma fulani da suke zaune a wurin. Ance Su jikokin mallam Abubakar ne da akace ya taso daga Futa Toro ya sauka a 'Yandoto, sannan ya zagaya Katsina, kano da Borno har kuma ya sauka a Zaria.
 5. ANGUWAR ZAGE-ZAGI
Akwai labarai masu saɓani game da tarihin wannan unguwa, amma dai kusan kowa ya yarda cewar asalin unguwar ya samu ne daga wani gida dake wannan unguwa mai suna gidan zage-zagi.
  Wasu suka ce su zage zagi larabawa ne masu yin fatauci da suka sauka a zazzau a karni na goma sha biyar. Sannu a hankali sai auratayya ta haɗasu da hausawa har suka ɓace cikin hausa.
  Akace da kalmar Zak -zak ake kiransu, kalmar data samo asali daga 'Zakkatu', fassarar ta shine takobi da larabci. Ance anji suna yawan cewa 'tazakzaka'  watau karike takobi shiyasa ake ce musu zak-zak, daga baya sunan ya koma zage-zagi.
  Wasu kuma suka ce ai kalmar Zak-zak na nufin tafiya sannu-sannu da larabci.
 A Wata ruwayar kuma ance wannan suna na Zage zagi ya samo asali ne daga wani balaraben Fezzan mai suna Usman bn Ismail wanda ya baro gida bayan rigimar data biyo bayan mutuwar mahaifinsa acikin danginsu a wajajen (1786-1806) har kuma ya sauka a zazzau.
  Da saukar sa sai Magajiyar gari ta nemi izinin sarki ta bashi wannan wuri domin ya gina gida ya zauna. Kuma wata korama dake kusa da wajen ake kira Zage zagi.
  Ita koramar ta zamo kamar dandali ne da ake yin bukin al'ada a duk shekara wanda sarki da sauran mutane ke haɗuwa a wurin ana kiɗa da rawa, abinda wasu ke ganin yayi kama da bikin 'gyaran ruwa ' da aka samu anayi a wasu sassan kasar hausa..
  Amma dai ance a lokacin jihadi mazauna gidan zage zagi basu goyi bayan fulani ba, don haka aka kore su daga gari. Amma daga baya da suka dawo sai aka basu wani matsugunin, aka kuma sauyawa unguwar suna zuwa Unguwar Katuka, amma dai har yanzu ance anfi sanin ta da asalin sunanta.
 6. UNGUWAR KWARBAI
Itace ungjwar bayan gidan sarki.
  Ana ganin sunan ya samo asali ne daga kofar bayan gidan sarki. Watau Kofar Bai.
  Amma wasu sunce sunan daga wasu dakarun sarki ya samo asali waɗanda suka zauna a arewacin unguwar masu suna 'yan kwarbai.
  UNGUWAR MAGAJIYA
Asalin unguwar ance gidan magajiya zaria ne, watau ɗiyar sarkin zazzau Bakwa Turunku.
  Amma daga unguwar aka fitar da Unguwar lalle, Unguwar kaho, da Unguwar magajin aska.
7.  UNGUWAR KUSFA
Shima wannan wuri tsohowar mazauna ce da akace anyi bautar iskokai a ciki tun kafin zuwan musulunci.
  Amma a hankali malamai suka soma zama a wurin.
  Wani mai suna mallam Tankiru akace ya soma zama tare da tulin ɗaliban sa a wurin.
  Daga baya sai mallam Shitu ya maye gurbinsa, wanda ya shahara sosai har ake zuwa daga sassa ɗaukar ilimi gurinsa.

TARIHIN DAULAR ZAZZAU 6

TARIHIN KAFUWAR DAULAR ZAZZAU

Kashi na shidda

  DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
   Sauran sarakunan da akace sunyi sarautar zazzau da shekarun mulkinsu sune kamar haka:- (koda yake akwai saɓanin shekaru daga masu ruwaitowa)
23. Ibrahim 1539-1560
24. Karama 1566-1576
25. Kofa 1576-1578
26. Bako I 1578-1581
27. Aliyu I 1581-1587
28. Ismailu 1587-1568
29. Musa 1598-1599
30. Gabi 1598-1601
31. Hamza 1601-1602
32. Abdaku 1602-1610
33. Burewa 1610-1613
34. Aliyu II 1613-1640
35. Makama Rabo 1640-1641
36. Ibrahim Basuka 1641-1654
37. Bako II 1654-1657
38. Sukwana 1657-1658
39. Aliyu III 1658-1665
40. Ibrahim Dan Aliyu 1665-1668
41. Mamman Abu 1668-1686
42. Sune 1686-1686
43. Bako dan Musa 1696-1701
44. Isiyaku dan Gabi 1701-1703
45. Burema Ashakuka 1703-1704
46. Bako dan Sukwana 1704-1715
47. Muhammadu dan Gunguma 1715-1726
48. Uban Bawa 1726-1733
49. Muhammadu Gabi 1733-1734
50. Abu muhanad Gani 1735
51. Gabir dan Ashakuka 1734-1737
52. Makama Abu 1737-1737
53. Bawo 1737-1757
54. Yunusa 1759-1767
55. Yakubu 1765-1764
56. Aliyu IV 1767-1773
57. Cikkoku 1773-1779
58.Muhammad Maigamo1779-1782
59. Jatau (isiyaku) 1782-1802
60. Makau 1802-1804
Sarakunan zazzau na Fulani Bayan Jihadin Shehu Usmanu ɗan fodio:-
1. Sarkin zazzau Malam Musa 1804-1821
2. Sarkin zazzau Malam Yamusa 1821-1834
3. Sarkin zazzau Malam Abdulkarimu 1834-1846
4. Sarkin zazzau Malam Hammada ( kwana hamsin da uku yayi)
5. Sarkin zazzau Malam Mahamman Sani 1846-1853
6. Sarkin zazzau malam sidi
 ( shima wata ya yi yana mulki).
7. Sarkin zazzau Malam Abdulsalam 1853-1863
8. Sarkin zazzau Malam Abdullahi 1863-1873
9. Sarkin zazzau Malam Abubakar 1873-1876
10. Sarkin zazzau Malam sambo 1881-1890
11. Sarkin zazzau Malam Yero 1890-1897
12. Sarkin zazzau Malam Kwasau 1897-1903
13. Sarkin zazzau Malam Alu dan Sidi 1903-1920
14. Sarkin zazzau Malam Dalhatu 1920-1924
15. Sarkin zazzau Malam Ibrahim 1924-1936
16. Sarkin zazzau Malam Jafa'ru 1937-1959
17. Sarkin zazzau Alhaji Muhammadu Aminu 1959-1975
18. Sarkin zazzau Alhaji shehu idris 1975 zuwa yanzu.
  FADAR ZAZZAU
Ana kiran gidan sarkin zazzau da  suna 'gidan Bakwa', kuma yana nan a unguwar da ake kira kofar fada dake tsakanin Madarkachi da Fadamar Bono.
  Anan ne kusan duk sarakunan da suka hau karagar mulkin daular suke zama.
   Ance tun zamanin Sarki Bakwa Turunku aka gina shi, a wajajen 5036 miladiyya kenan, don haka ma ake kiran gidan da sunan sa.
  Wasu suka ce wani maharbi ne ya bada shawarar ayi gidan anan bisa dalilai na tsaro.
  Da fari, yace wajen kan tudu ne, zai baiwa jagoran gari damar kallon duk abubuwan dake faruwa a Kufena, Turunku, Hange da sauran unguwannin cikin ganuwa.
  Sannan wajen yafi kusa da tsakiyar gari inda da zarar an buga kugen taruwar jama'a, mutane zasu runtomu da gaggawa.
   Wannan fada an gina ta da turɓaya ne, kuma an kasa ta gida huɗu. Akwai Fada inda sarki ke zama da fadawa ayi fadanci. Akwai sashen da sarki ke kwanciya. Akwai cikin gida sashen da iyalan sarki suke. Sai kuma tsohuwar gida inda barorin sarki suke.
   Amma a karni na goma sha takwas, ance sanannan maginin nan mai suna Muhammadu Durungu, Babban Gwani ya sake sabunta gidan tare da gina masa sabbin ɗakuna na kasaita.
  Haka kuma bayan jihadin fulani, sarki na farko watau Mallam Musa bai shiga gidan ba bisa tsoron kada ya zama mai aikata irin abinda hausawan haɓe ke aikatawa kafin jihadi, don haka yayi mulkin zazzau daga gidansa dake unguwar kwarbai.
  Wanda ya biyo bayansa Mallam yamusa shima bai dhiga gidan Bakwa ba bisa wancan tsoro, sai yayi mulki a gidansa dake Unguwar kaura.
  Daga nan sai Mal Abdulkarim da yazo, shi kuma ya shiga gidan Bakwa yayi sarauta, kuma a lokacinsa akace magini Muhammadu Durungu yayiwa fadar gyara na musamman.
  Amma bayan mutuwar sarkin sai wanda ya gajeshi mai suna Hammade yaki shiga fadar, yayi kwanaki yana mulki ya rasu, sarakunan kabilar fulani Bare-bari suka biyo bayansa, suma sai sukayi mulkinsu a Unguwar kaura.
  Abdulsalam yayi nasa mulkin a gidansa dake Unguwar Bishar.
  Mal Abdullahi yayi mulki a kofar Doka.
  Mal Abubakar yayi mulki ba tare daya shiga gidan ba.
  Wanda akace ya komowa gidan shine Mal Sambo, kuma tun daga kansa har yanzu sarakunan zazzau na shiga domin yin sarauta.
   UNGUWANNIN ZARIA DA TARIHINSU
1. Anguwar Zaria
   Nan ne inda birnin zaria yake a yanzu.
Ance asalin sa fili ne babu kowa a wurin. Amma a lokacin da ake gina ganuwar birni zamanin Sarki Bakwa Turunku, sai wata ɗiyar sarki da ake kira Zaria tazo taga wannan wuri, daga nan sai ta nemi mutanen daular Zazzau da akace a lokacin cibiyar su na Turunku su dawo wannan wuri domin bada dama ga magina su kammala ginin fadar Sarki, da ganuwa, da rijiyoyi da kuma gidanta a Unguwar Magajiya.
   Don haka ake ganin tun abaya wurin ya zama cibiyar daular na wani lokaci, amma ana kammalawa sai duk suka tashi izuwa sabon waje.
   Tun daga nan kuma sai zaria ya zamo tsirarun mutane kaɗai ke rayuwa a wurin har zuwa karni na goma sha takwas da wajen ya haɓaka izuwa birnin zaria.
  2. Unguwar Salman Duna
   Ance sunan unguwar ya samo ne daga sunan wata mace mai Suna Salma, mata ga sarkin makera Duna da suka shahara a wajen.
  Wasu sunce wani maharbi mai suna Bono ne ya soma sarar wajen. Shikuma ya kasance miji ne ga zariya ɗiyar sarki Bakwa Turunku.
   Akace wata rana ya fita farauta sai ya riski wurin da ayau ake kira Fadamar Bono, sai ya jima yana farauta har sama da lokacin daya saba idan ya fita gida. Wannan yasa hankalin matarsa ya tashi ta biyo bayansa.
 ( Sai akace anan ne har taga yankin Zaria kuma ta kayatu da zama a wurin saboda ni'iamar ruwa da yake dashi, inda daga baya ta roki mahaifinta ya komo da jama'arsa wurin kafin a gama aikin gina gari. Ance jajircewar ta bisa haka yasa ake kiran wajen da sunanta)
  Amma wasu sunce wannan yanki na Salmanduna sanananne tun da jimawa, domin kuwa sarkin zazzau na farko Gunguma ne ya fara sanyawa aka gyara wurin da nufin fara yin noma a yankin. Daga baya mutane suka soma zama har ya zama unguwa.
  Sannan akwai wani yanki mai suna Babban dodo a jikin unguwar Salmanduna, inda akace a baya matattara ce ta bautar iskokai.
 Har ma an samu ana yiwa wata iska kirari domin shaida ga bautar da akayi a wurin. Ga kirarin kamar haka:-
  Duna na kar kashin kasa
  Arne Na gidan Nabijari.
Ko uwanka na Tsoronka
Bakaka mushagala
  Mai kallabi da hanjin yaro
  Talaka baya iya ajiyeki
Ko ya ijeki me zai baki
Sai dai ya baki bargon doki.
Ba dai ya baki jini ba.
  Wani mutum a wurin mai suna Mal Mahmud Aliyu, ya faɗa cewar  tun a karni na goma shabiyar  wajen ya haɓaka da jama'a sosai saboda waccan bauta da akeyi, kuma sai a karni na goma sha tara ragiwar mutane a wurin tayi kasa.

TARIHIN DAULAR ZAZZAU 5

TARIHIN KAFUWAR DAULAR ZAZZAU

Kashi na Biyar

  DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

Akwai daga tarihin zazzau labarin wannan takobin mai suna Zazzau, wadda wasu ke kallon daga sunan ta aka sanyawa daular suna. Akwai masu kallon cewa asalin takobin ta sarki Gunguma ce wadda ya yaki abokan gaba da ita, don haka aka ajiyeta a masarautar bayan rasuwarsa ta yadda kowanne sarki yazo sai yasha alwashi da ita.
  Haka kuma babu takamaimen lokacin da sarkin Gunguma ya soma sarautar zazzau da kuma adadin shekarun da yayi dashi da sarakunan nan goma sha shidda da suka gabace. Watakila hakan ta faru kasancewar zazzau bata da tsohon ajiyayyen rubutaccen tarihi misalin irin na masarautar kano. To amma duk da haka, an hakikance rayuwar sarakunan ta wanzu ne sama da karni na goma sha ɗaya, zuwa kasa da karni na goma sha biyar.
  Haka kuma Leo Africanus ya ruwaito cewar a wajajen shekara ta 5012 miladiyya daular Songhai ta kasar Mali da Sarki Muhammadu Askiya na ɗaya ke jagoranta ta kwace ikon daular zaria. Watakila a lokacin sarki Muhammadu Abu (sarki na goma sha takwas) ne ke sarauta, ko kuma tana iya yiwuwa Muhammadu Abu ya hau sarauta ne da sahalewar torankawan Mali waɗanda suka kawo musulunci Zazzau tunda a jerin sunayen sarakunan nasa ne yafara da Muhammadu.
   Daga nan sai wani abu da akaji akan sarkin zaria na 22 Bakwa Turunku.
  Ance shine mahaifin Sarauniya Amina, da 'yar uwarta Khadija mai lakabin zaria wanda ya taso da cibiyar daular zazzau daga wani wuri zuwa wani.
  Khadija  ce akace ta kafa wani ɗan kauye mai suna zaria, wanda yanzu ya bunkasa har cibiyar daular zazzau ke ciki.
  Ita kuwa Amina anfi cewa ita sarauniya ce wadda sunan ta ya shahara a kasar hausa duk kuwa da kasancewar babu sunanta a jerin sarakunan Zazzau da aka bayar.
  Wasu na ganin abubuwa biyu ne suka sanya haka.
 Na farko akace bata zauna a zazzau tayi mulki ba a sanda ta zamo shugaba, sai kawai ta fita cinye garuruwa da faɗaɗa girman daularta.
   Abu na biyu kuwa shine wanda ake kallon Amina a matsayin sarauniya, kuma shugabar mayaka wadda ba itace lamba ɗaya mai faɗa aji a zazzau ba.
   An samu cewar a zazzau ana kiran 'yar sarki da suna Sarauniya, mahaifiyar sarki kuma da suna Iya. Ance waɗannan mataye biyu nada faɗa aji da matukar tasiri a masarautar zazzau
   Don haka wasu ke hasashen Amina a sarauniya kurum take, watau ɗiya ga sarki Bakwa Turunku, kuma ɗanuwanta shine wanda ya zama sarki bayan rasuwar Mahaifinsu, ita kuwa sai taci gaba da zamowarta sarauniya, wadda ta fita kasashe yaki na tsawon shekaru har kuma ta mutu acan ba tare da tayi aure ba.
   Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya karyata waɗanda ke cewar ba'a taɓa yin wata mace mai suna Amina a zaria ba a littafinsa 'Infaqul Maisur' inda yace a zamaninta ta cinye garuruwan dake makwabtaka da zaria musamman na Nufawa dana Kwararrafawa. Kuma suna biyanta Jizya. Harma sarkin Nufe ya taɓa aika mata da bayi Arba'in da kuma goro dubu goma. Yace kumu Amina tayi sharafi tsawon shekaru 34.
   Amma abu mai gaskata wanzuwar Amina shine wani kufai da ake samu a garuruwan da taci ko ta sauka wanda ake kira da suna 'ganuwar Amina'. Wanda kuma har yanzu akwai ɓurɓushinsa a garuruwa da yawa cikin kasar hausa dana makwabta.
  Kari akan kasashen da akace Amina taci galabar yaki akai baya da kasashen Nufawa dana Kwararrafawa, akwai kasar Gwari, kasar kano, kasar katsina, da kasashen yankin Nasarawa.

TARIHIN DAULAR ZAZZAU 4

TARIHIN KAFUWAR DAULAR ZAZZAU

Kashi na Huɗu

  DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

SARAUTAR ZAZZAU

 Tana iya yiwuwa kafuwar wannan birni na zazzau ne ya samar da yawaitar hare-hare daga masarautun da suka kafu a yankin tun acan baya musamman daga dakarun masarautar Gurara (birnin gwari na yau) a wajajen shekara ta 1140.
  Sai dai kuma da alama yawaitar hare-haren ne ya sanya al'ummar garuruwan shawarar samar da ganuwa a tsakaninsu. Don haka kai tsaye ana iya cewar tashin hankulan mazauna yankunan zzzau ne ya sanyasu samar da ganuwa.
 Amma dai an samu cewar samuwar wannan birnin ya sanya wasu garuruwan sun shige cikin sabuwar daular zazzau domin neman mafaka, yayin da a hankali zazzau ɗin ta rinka haɓaka da faɗaɗa ikonta akan yankuna har wasu garuruwa irinsu Dumbi, Farakwai, Tsauni da Hange suka zamo karkashin ikon ta a farko, daga baya kuma irinsu kauru, kajuru, Fatika, kagarko, lere, durum da wasunsu suka faɗo gareta a baya-baya.
   Sai dai kafin nan, shin wanenen ya soma sarautar Zazzau?
   Kusan duk maruwaita tarihin zazzau sun bada labarin cewar wani mai suna Gunguma shine ya soma sarautar Zazzau, kurum dai maganganu akansa ne suka sha bam-bam.
  Da farko, akwai labarin daya zo cewar shi Gunguma, ɗane ga sarkin Daura Bawo ɗan Bayajidda.
  Akace sa'ar da masarautar Gurara ta takurawa Zazzau da hari, sai zazzagawa suka runtuma gareshi neman ɗauki. Anan ne ya turo ɗansa Gunguma domin ya mulkesu kuma ya samar musu da tsaro.
   Akace kuma a tare dashi akwai mutane goma sha shidda waɗanda sukayi sarautar zazzau ɗaya bayan ɗaya, tun daga kan sarki Matazo daya gaji Gunguma har zuwa kan sarkin zazzau Sukanau.
   Amma a wani zancen, ance wani maruwaici mai suna Al Maqrizi ya ruwaito a wajajen karni na goma sha biyar daga littafin 'Kitab Al Jogirafiyya' na Ibn Sa'id wanda akace shikuma ya jiyo daga marubuci Ibn Furtua wanda ya riski zazzau a zamaninsa cewar sunan asalin daular Zazzau na wani kauye ne mai suna 'Kunkuma', wanda akace sunan kauyen ya samu ne daga wani waishi Kunkuma daya kafashi.  
   Akace Mazaunan kauyen kunkuma kabilar kadarawa ne, suna kiran sarkinsu Bugwom.
   Sai dai saboda yawaitar hare-hare garesu sai suka koma Turunku da zama, daga nan kuma  suka sauyawa garin   suna  zazzau, sunan sarkinsu kuma ya cigaba a matsayin Kunkuma.
  Saboda haka ake kallon sauyawa sunan Gunguma yayi daga Kunkuma.
   Marigayi farfesa Mahdi Adamu ya taɓa kawo maganar haka a wata makalarsa mai taken 'Hausaland and Other Places of Northern Nigeria 1200-1600AD', har yake cewa ba abin mamaki bane don an sauya harafin 'K' zuwa 'G', watau sunan sarkin ya sauya daga Kunkuma na asali izuwa Gunguma tunda larabci kan iya amfani da haruffan 'k' da 'g' a wurare ɗaya saboda kamance-ceniyar su wajen furtawa, to amma dashi da wasu masanan sunyi shakkun zuwan Ibn Furtua kasar Hausa ballantana daular Zazzau.
  A wata fuskar kuma, ance Gunguma wani mafarauci ne Bamaguje wanda ya zagaya wurare kafin daga baya ya zauna a zazzau.
  Wuraren da akace ya riska kafin zuwansa zazzau sune:- Kawuri, Kargi, Rikochi, Wuchichchiri, Turunku, Kufena sannan Zazzau.
   Watakila tasirin Kufena wajen samar da ƴhaɗin kan wannan daula mai suna zazzau ne ya sanya ya zamo shugaba na farko a gareta.
  Amma dai, Waɗannan sune sunayen sarakunan daular Zazzau 22 na farko-farko daga cikin kimanin 61 da akace sun mulketa tun daga kafuwarta zuwa yanzu:-
1.  Gunguma,
2. Matazo,
3. Tumsah,
4.Tumasa,
5. Muswaza,
6. Suleiman,
7. Dimzaki,
8. Nayoga,
9. Kauchi,
10 Nawanci,
11. Macikai,
12. Kewo,
13. Bashirkar,
14. Majidada,
15. Dirahi,
16. Jinjiku,
17. Sukano,
18. Muhammadu Abu (1505-1530)
19. Guda Dan Masukana (1530-1532),
20. Nohir (1532-1535),
21. Kowanisa (1535-1536)
22. Bakwa Turunku 

TARIHIN DAULAR ZAZZAU 3

TARIHIN KAFUWAR DAULAR ZAZZAU

Kashi na Uku

  DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

KAFUWAR DAULAR ZAZZAU
  Da yawan masana na kallon yawan karuwar mazauna waɗannan tsoffin wurare dake kasar zazzau da kuma karancin tsaro a garesu yasa sukayi shawarar ajiye kiyayyar juna gami da yin ganuwa wadda zata haɗe kusan ɗaukacin garuruwan tare da samar da shugaba guda ɗaya. Wannan kuwa shine asalin samuwar daular zazzau.
Marubucin tarihi Abdullahi Smith ya faɗi cewar Zaria ta soma ne sa'ar da gidaje suka soma wanzuwa a waɗancan yankuna. Ya zamana kowanne gida yana cikin ikon maigidan, to sai kuma unguwanni ko kauyuka suka haɗu karkashin ikon mai unguwa.
  Daga baya kuwa sai waɗannan unguwannin suka yanke shawarar samar da babban gari a cikin ganuwa ɗaya tare da zamowa karkashin ikon mutum ɗaya mai suna Sarki.
  Ana tsammanin shugabanin kauyen Kufena ne suka soma assasa wannan shawara, sune kuma suka jagoranci ginin ganuwar wadda ta zagaye yankinsu na Kufena, da kauyukan Dala, Kona, Madarkachi, Tukur- Tukur, da sauransu.
 Tsawon ganuwar ance yakai kimanin mil dubu 24 daga yammaci zuwa gabashi.
  Ance da Fari an sanyawa garin suna 'Garin ɗan zau' ne, watau sunan maharbin daya kafa Kufena, daga baya ne ake cewa Zazzau.
  Sai dai wasu na ganin Zazzau ɗin sunan wata takobin sihiri ce dake garin wadda ake ɗauka ayi rantsuwa ko asha alwashi da ita tun a lokacin maguzanci.
  Baya da haka, littafin tarihin kano ya nuna garin zaria ya wanzu a wani wuri kusa da birnin zazzau na yanzu a zamanin sarki Kanajeji wanda ya kawowa garin yaki har kuma aka halaka sarkinsu a wani wuri mai suna Gadaz.
  Duk wannan, tana iya yiwuwa anyi kafin kafuwar wannan ganuwar ne.
 Wani bature mai suna Dr. Baikie ya wuce ta zaria a shekarar 1862, zamanin mulkin sarkin Zaria Abdullahi, shine ya ruwaito cewar zaria nada gagarumar ganuwa, wadda kaurinta zaiyi kimanin mil goma, sannan akwai kofofi takwas a zagaye da ita. Sai kuma wata kofa da ya gani an ciketa mai suna Kofar kuyambana.
   Shima Paul Staundinger, wani bature ne daya ziyarci zaria a shekarar 1880, kuma ya faɗa cewar a kowacce kofar gari dake zari akwai murfi na katako da ake rufe shi da masakali, sannan akwai dogari dake zama yana amsar kuɗin farin wuri ga dukkan manoman dake shigo da hatsi cikin birnin daga kauyuka, amma shi Paul ɗin da tawagarsa basu bada komai ba.
   KOFOFIN ZARIA DA TARIHIN SU
   Kofofi shidda ne akace tsoffi da aka soma fitarwa tun zamanin da aka ginawa garin ganuwa.
  Kofofin kuwa sune:-
1. Kofar Gayan.
  Ance an sanya mata suna ne daga tafkin Gayan wanda ke kudancin kofar saboda muhimmancin sa ga rayuwar mazauna birnin zazzau.
2. Kofar Kuyambana
  Ance zamanin Sarauniya Amina aka ɓusa wannan kofa, lokacin da taje yaki garin kuyambana ta karɓe ikonsa, ta ɗora wani baranta ya zama hakimi a garin. Sai aka ɓusa kofar tayadda mutanen zaria dana kuyambana zasu rinka saduwa da juna cikin sauki.
  3. Kofar Tukur-Tukur
  Da fari an sanyawa kofar suna ne daga dutsen Tukur-Tukur, kuma da haka aka santa tsawon lokaci.
   Amma sai sunan kofar ya sauya zuwa Kofar Kibau/Kibo a zamanin da Sarkin Ningi Haruna ya kawo farmakin yaki Zaria lokacin mulkin sarkin zaria Sambo. Zazzagawa suka shige cikin ganjwa tare da rufe kofa. Sadaukan Ningi kuwa sai sukayi ruwan kibiyoyiƴga birnin na zaria.
  Ta wannan kofa mutanen da suka ɓullo daga zamfara, kebbi, Yauri da Gobir suke shigowa zaria.
4. Kofar Doka
  Wasu sunce kofar ta samo asali ne daga bishiyar Doka dake wajajen kofar. Amma wasu sunce an saya mata wannan suna ne daga wani dogari mai tsaron ta mai suna Doka.
 5. Kofar Bai.
  Ance ainihi, ana kiran tane da suna kofar Bayan gidan sarki. Daga baya ake yankewa ace mata kofar Bai.
 Kuma ta cikin tane mutanen yankin Bauchi ke shiga Zaria.
6. Kofar Kona
Ance ana kiranta da suna Kofar kona saboda ta cikinta Malaman Kona suka shigo zaria.
 Shi kona wani kauye ne da akace wasu malamai suka kafa. Asalin sunasa ance ya samu ne lokacin da malaman suka zo shigewa suna neman wurin zama, sai shugabansu ya lura da kyawun wurin, don haka yake tambayar sauran malaman cewa 'ko nan zamu zauna?' Sai suka amsa masa da gamsuwar zama a wurin.
  Daga baya da akazo ginin ganuwa sai shashin garin ya shigo cikin birni, don haka suka yanke shawarar barin kauyen nasu na Kona tare da komawa cikin zazzau da zama.
  Waɗannan sune tsoffin kofofin da akace sun jima a zazzau, amma daga bisani an samu fasa wasu kofofin kamar su Kofar Jatau, Kofar Galadima da kofar Matar-kwasa wadda akafi kira da Sabuwar kofa.

TARIHIN DAULAR ZAZZAU 2

TARIHIN KAFUWAR DAULAR ZAZZAU

Kashi na biyu

  DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

KUFENA
   Kufena wani tsohon kauye ne dake yammacin birnin zaria na yanzu, kuma ance ya taɓa zamowa cibiyar masarautar zazzau mai cike da wayewa acan baya.
   Ance wasu maharba karkashin shugabancin wani mai suna 'Dan zau ne suka kafa shi tun wajajen karni na ɗaya. Kuma sun fara zama ne akan tsaunikan dake wurin, daga baya wasunsu suka koma kan tsaunikan yankin Madarkachi.
   Shi kanshi sunan Madarkachi, ance daga kufena ya samo asali.
  Wasu na ganin wani mai suna Madara shine babba cikin masu zama a Madarkachi, don haka idan yazo kufena sai a tambayeshi 'Madara, kachi abu kaza?'
  Wasu kuma suka ce da yake ba lallai hausawa ne kabilar madarkaci ba, don haka idan suka zo kufena sai suke cewa 'Madara kachi' mai makon 'madara kasha'.
  Shi kuwa sunan Kufena, ana ganin ya samo asali ne daga 'Kafe A Nan'.
   Watau waɗannan maharban da suka sauka a wurin nada inda sukayi nufin zuwa amma sai suka ɓige da zaman nan, don haka suke kiran kansu/ ko ake kiransu da 'waɗanda suka kafe anan', daga baya sunan ya sauya zuwa kufena.
MADARKACHI
  Kauye ne dake arewa maso gabashin birnin zaria.
  Binciken kimiyya ya tabbatar da wanzuwar mutane a wannan waje shekaru sama da dubu da suka gabata.
  Haka kuma ana kallon wani  dutse a wurin a matsain wurin bautar Iskokai ga mazauna Madarkachi, har kuma wasu ke tsammanin tana iya kascewa wannan mahsrbin mai suna 'Dala' daga nan yake ya taso zuwa dutsen dala na kano tare da bijirar da irin bautar Iskokai da akeyi a wurin.
  KARGI
 Kauye ne a gabashin Madarkachi, kuma ɗaya ne daga ɗaɗaɗɗun wajen zama a zazzau.
  Mutanen Kargi sun faɗa cewar asalin mazauna Kawuri, waɗanda suka dawo Rikochi, da mazauna wuchichchiri, Turunku, da Kufena, da Zaria ne suka haɗu tare da kafa hamshakiyar daular Zazzau. Kuma wani mai suna 'Madaki Gunguma' shine sarkin daular na farko.
WUCHICHIRI
  Kauye ne dake arewacin garin zaria wanda binciken kimiyya ya tabbatar da alamun daɗaɗɗiyar rayuwa a wurin.
   Ance sunan wurin ya samo asali ne a lokacin da wasu jama'a sukayi nufin cire wasu busassun ciyayi a wurin don yin bukkoki sai abin ya basu wuya, shine wai suke cewa "ciyayin nada wuyan chich chirew.." Har kuma ake kiran wajen wuchichchiri.
  Ance madaki Gunguma da jama'ar sa sun taɓa zama a wurin kimanin shekara ɗaya a wajajen karni na goma sha huɗu. Anan suka kera kwari da baka ta farauta saboda makera da suka zauna a wurin bisa albarkar tama da karafan wurin, sannu a hankali kuma sai manoma, makiyaya da sauran mutane suka rinka kwarara.
  Sauran wuraren da aka tabbatar da cewar shekaru da yawa da suka gabata mutane sun zauna a cikinsu sune:- Tukur-Tukur, Hange-Hangawa, Fara-Kwai, Dutsen wai, Tsauni da Dutsen Pampuri.
  

TARIHIN DAULAR ZAZZAU 1

TARIHIN KAFUWAR DAULAR ZAZZAU

Kashi na ɗaya

  DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

A wani rohoton bayan bincike da wasu gungun masana suka gabatar game da kwayoyin halittar mutanen zariya a ɗakin taro na 'Arewa House' dake Kaduna karkashin jagorancin Farfesa Abdullahi El-kanawy da Farfesa Muzzah Jibrin, sun bada bayanin cewar akwai kamance-ceniya tsakanin kwayoyin halittar zazzagawa da kabilun gwari dana igala.
    A nasu ba'asin, sun faɗi cewar babu abin mamaki akan haka tunda kowa ya sani sarauniyar zazzau Amina ta taɓa tafiya kasar Igala yaki har aka kasheta acan, don haka tana iya yiwuwa anan aka kame sojojinta a matsayin bayi har kuma auratayya ta shiga tsakani tayadda zuwa yanzu kwayoyin halittun suka cakuɗu da juna.
   Sai dai a mafi ingancin zance, anfi ganin cewar zazzagawa, Gwarawa da kabilar Igala sun samo tsatso ne daga tsoffin kabilun da suka soma zama a yankin da ayau ake kira Zaria. Daga baya zariya ta dunkule ta zama kasar hausa, sannan kabilun Igala da Gwari ma duk suka sauya tare da zamowa abinda suke ayau.
  Binciken kimiyya a wasu tsoffin wurare dake cikin gundumar zaria ya nuna cewar lokaci mai tsawo kimanin shekaru ɗaya zuwa dubu biyu da suka gabata, akwai mutane zaune a yankin Kufena, Madarkachi, Turunku, Kargi, Tukur-Tukur da Wuchichchiri.
   Zuwa yanzu, babu wanda keda tabbacin asalin mazauna waɗancan wurare hausawa ne, amma an gamsu da cewar jikokin sune suka dunkule tare da haifar da daular zazzau.
    Masana irinsu Mallam Usman Sulaiman sunbi diddigin tsoffin bayanan da masu bincike suka wallafa kuma suka taskance dangane da wuraren dama yadda daular Zazzau ɗin ta kafu tun asali da rayuwar daular har lokacin zuwan turawa, ga kuma abinda muka samu:-
  Tarihin Mazauna Tsohuwar Zazzau.
1. TURUNKU:- Tukurunku yanki ne dake kudancin birnin Zaria mai cike da tsaunika da ni'imar kasa. Ana ganin waɗannan abubuwa sune suka ja hankalin mutane shekaru da dama da suka gabata suka zauna a yankin.
   Ana kuma kallon wannan wuri a matsayin tsohuwar cibiyar masarautar zazzau wadda ta haɓaka da makurar wayewa tun lokacin da mutum na farko ya fara rayuwa a wurin sama da shekaru dubu ɗaya da suka gabata izuwa lokacin sarautar sarki Bakwa Turunku na zazzau.
  Wasu maruwaita na ganin cewar ainihin mazaunan Turunku kabilar kadarawa ne, domin sune suke kiran sarkin su da suna 'Bugwon', don haka daga baya ne mutane suka maishe da sunan ya koma 'Bakwa'.
   Amma wasu na ganin mutanen Toranke na kasar mali sun taɓa kwace garin a zamanin Muhammadu Askiya  har kuma hakan ya tilastawa mutanen yankin guduwa zuwa yankin Kufena. Don haka sai ake cewa da wurin 'Toranke' don nuna waɗanda keda ikon sa. Daga baya sai sunan ya sauya izuwa Turunku.

Wednesday, 24 January 2018

TARIHIN ALH SHEHU SHAGARI

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO
       08060869978

An haifi Alh Shehu Usman Shagari a shekarar 1925 cikin kauyen Shagari garin da kakan-kakansa Ahmadu Rufai ya kafa. Sunan mahaifinsa Aliyu, mahaifiyarsa kuwa sunanta  Maryamu.
   Mahaifin Shehu Shagari ke rike da mukamin Magajin Shagari, watau kamar dagacin kauyen kenan, sai dai Allah yayi masa rasuwa shekaru kafin a haifi Shehu Shagari, wanda hakan yasa ɗan uwansa Bello yaci gaba da zamowa magajin shagari.

Shagari yayi karatun alkurani a gida, sannan ya fara fita waje neman ilimin zamani. A shekarar 1931 zuwa ta 1935 ya kammala karatun elementarensa a Yabo. Sannan ya tafi midil dake sokoto a shekarar 1936 ya kammala a shekarar 1940, daga nan sai ya tafi kwalejin kaduna yayi karatunsa daga shekarar 1941 zuwa shekara ta 1944.
  Bayan ya kammala kwalejin kaduna sai kuma ya samu gurbin karatu a kwalejin horas da malamai ta zaria inda ya kammala a shekarar 1952 tare da zamowa malami jihar sa ta Sokoto.
  Shehu Shagari ya soma siyasa ne da zamowa akawun jamiyyar NPC, Northern Progressive Party reshen jihar sa ta Sokoto a shekarar 1951 sai kuma a shekarar 1954 aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yammacin sokoto.
   A shekarar  1958, Shagari ya zamo akawun majalisar tarayya, amma a shekarar 1959 sai ya barwa Tafawa Balewa wannan gurbi saboda martabawa. A wannan shekarar kuwa sai aka naɗa shi ministan tarayya mai kula da kasuwanci da masana'antu.
   Shagari ya rinka samun sauye sauyen hukumomi a matsayin sa na minista tun da aka karɓi yancin kai a shekarar 1960 har lokacin da akayi juyin mulki a shekarar 1966, haka kuma bayan Janar Yakubu Gawon ya zama shugaban kasa, an sake baiwa Shehu Shagari mukamin ministan kasa a shekarar 1970
  Baya da haka, a shekarar 1971-75 a lokacin yakin basasar kasa, Shehu Shagari ya zama ministan kuɗin Nigeria, wannan kujera ce ta bashi damar ya rike mukamin gwamna na bankin duniya, ya kuma zama ɗaya daga cikin mutane ashirin 'yan kwamitin bankin lamuni na duniya watau IMF.
  Shehu Shagari na daga cikin waɗanda suka kafa jamiyyar 'National People’s Party' a shekarar 1978 bayan an kashe Janar Murtala, a lokacin da shugaban kasa na lokacin Janar Obasanjo Olusegun ya bada izinin kafa jamiyyun siyasa don mikawa farar hula mulkin kasa. Haka kuma a shekarar 1979 Shagari ya zama ɗan takarar shugaban kasa a tutar jamiyyar tasu, kuma hukumar zaɓe mai zaman kanta ta bayyana shi a matsayin wanda ya cinye zaɓe a wannan shekara.
Shehu Shagari yayi shekaru huɗu yana mulkar Nigeria, sannan ya sake neman takara kuma yaci a shekarar 1983, to amma jim kaɗan da zaɓen,  sai sojoji sukayi masa juyin mulki a ranar 31 ga watan disambar 1983, a lokacin da aka naɗa Shugaba Muhammadu Buhari shugaban kasa Nigeria kenan da kakin soja.
Hakika za'a jima ana tunawa da Shehu Shagari a matsayinsa na Shugaban kasar Nigeria duba da kokarin sa wajen haɓaka samar da Man fetur, da inganta masana'antu, da samar da Injinan aikin gona a shirin sa na 'Green Revolution', da gina tituna da suka sadar da manyan jihohi don  inganta zirga zirga gami da samar da gidaje masu saukin kuɗi a birane da karkarar Nigeria.
Da rarar kuɗin man fetur Shagari ya kammala ginin matatar man fetur ta Kaduna a shekarar, sannan ya kammala ma'aikatun sarrafa karafuna na Ajaokuta da wani irinsa a Delta a shekarar 1982.
A shekarar 1983, Shagari ya samar da kamfanin sarrafa Alminiyon a  Ikot Abasi duk kuwa da talaucin da kasar ke ciki saboda karyewar farashin mai a shekarar 1981.
  A lokacin sai ya maida kasar izuwa dogaro da noma ta hanyar bada taki da iri mai kyau kyauta ga manoma, sanna ya rage kuɗaɗen da gwamnatinsa ke kashewa tare da kara samar da kuɗaɗen shiga daga jamian hana fasa kwauri na kasa watau Custom.
  Sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Shagari sun zargi gwamnatinsa da rashawa  gami da maguɗi a zaɓen 1983. Sannan sunyiwa 'yan kasa alkawarin fitar dasu kangin talaucin da suka shiga biyo bayan karyewar farashin mai a kasuwar duniya
Shehu Shagari yayi rayuwa mai kyau a iya shekarunsa cassa'in da biyu da haiuwa, ya janye jikinsa daga mafi akasarin lamurorin gwamnati dana siyasa don tsira da mutumcinsa, sannan ya auri mataye uku, sune Amina, Aishatu, Hadiza, Allah kuma ya albarkace shi da 'ya'yaye da dama, acikin su akwai Captain Muhammad Bala Shagari Rtd. da Aminu Shehu Shagari.

Shine Alhaji Shehu Shagari, tsohon shugaban Nigeria, Tsohon ɗan siyasa, turakin sokoto, Ochiebuzo of Ogbaland, the Ezediale of Aboucha, the Baba Korede of Ado Ekiti, sannan kuma mai lambar girma ta Grand commander a tarayyar Nigeria watau GCFR.

  Dafatan Allah ya inganta lafiya, yasa kuma agama lafiya Amin.

Wednesday, 10 January 2018

TARIHIN SIYASAR NIGERIA 2

TARIHIN SIYASA A NIGERIA: TUNAWA DA RANAR 'YAN MAZAN JIYA
 
Kashi na biyu.

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
  08060869978

Turawan mulkin mallaka sun rinka shugabantar talakawan yankin Arewa karkashin sarakunan mulki na gargajiya abinda ake kira a turance 'Indirect Rule'.
   A lokacin, an ragewa sarakuna karfin iko ta hanyar samar da wani tsari mai suna 'Native Authority' (NA) wanda ya kunshi Sarki mai kula da talakawa da karɓar haraji, sai Alkali mai kula da shari'o'i, da kuma Ma'aji mai kula da baitil malin abinda sarakuna suka tatyara. Don kowanne sarki zai fita likaci-zuwa-lokaci tattaro haraji da jangali wanda turawa suka kakabawa ga 'yan kasa.
   Sannan kowanne magidanci tilas ya tanaji kuɗin da zai biya a matsayin haraji akan kansa da wurin kasuwancinsa. Sannan akan 'ya'yansa maza ma akwai haraji da ake biya.
   Kasancewar yankin Arewa bai tumbatsa da masu ilimin zamani ba, wutar neman 'yanci da kawar da talakawa daga wannan kunci bata soma ruruwa da wurwuri ba a yankin, abinda kurum akafi sani shine an haramta cinikayyar bayi, to amma biyayyar da talakawa ke yiwa sarakai bata canza ba, duk kuma wanda yayi yinkurin tada kayar baya ko bore yanzun nan zai haɗu da fushin 'yandoka.
      Mutumin da kusan za'a iya cewa shine ya fara kawo tunanin samar da kungiyar kwato yanci a yankin Arewa shine Mallam Sa'adu Zungur bayan yaje Lagos yin karatu yaga yadda su Dr Nnamdi Azikwe da Herbert Macaulay dasu Awolowo ke fafuti ga yankunansu, sai ya assassa kafa wata kungiyar malamai mai suna 'Zaria Literary Society' a shekarar 1939 sa'ar da aka tura shi aikin koyarwa a makarantar kula da lafiyar muhalli ta zaria. Daga baya sunan kungiyar ya sauya izuwa Zaria Improvement Union a shekarar 1941.
 Sa'adu Zungur ya shiga faɗakar da masu ilimin boko 'yan uwansa na zamanin cewar zaluncin da turawan mulkin mallaka sukeyi a kasa yayi yawa, domin ba haka akeyi a kasarsu ba. Sannan yace akwai bukatar kowanne majalisar Sarki ta N.A akwai zaɓaɓɓun wakilai masu bada shawara kamar yadda akeyi a Ingila zakaga akwai majalisu da suka kunshi wakilcin kungiyoyi da talakawa karkashin masarauta, waɗanda kuma suke da faɗa aji a wasu lamurori.
    A shekarar 1943 kuma sai wani ɗan gwagwarmaya mai rajin kwatar 'yanci shima ya kafa kungiyar nemarwa mutanen arewa mafita daga kunchin da suke ciki mai suna 'Northern Elements Progressive Association' NEPA bayan ya samu ganawa da Dr Nnamdi Azikwe shugaban NCNC. Matashin ɗan kabilar Ebira ne mazaunin kano, sunan sa Habib Raji Abdullahi.
   A bauchi kuma, sai Mallam Sa'adu zungur da wasu malaman makaranta dake koyarwa a kwalejin Horarwa ta Bauchi irinsu Mallam Aminu kano da Abubakar Tafawa Balewa suka sake kafa wata kungiyar mai suna 'Bauchi General Improvement Union', daga baya suka tashi wata mai suna 'Bauchi Discussion circle'.
    Ana haka sai jahohi suka rinka kafa kungiyoyinsu bisa ganin yadda 'yan boko 'yanuwansu ke kafa kungiyoyi don samar da cigaban jihar su. Ilimi da wayewar kai na zagayawa kenan sannu a hankali.
  A kan haka kungiyar Samarin Kano ta kafu, wadda Su Abdulkadir Adamu ɗan Jaji suka kafa, sannan Kungiyar samarin Sokoto  ta kafu wadda su Shehu Shagari, Ibrahim Gusau, Ahmadu Bello da Sani Dingyaɗi suka shiga a Shekarar 1947.
   Waɗannan kungiyoyi sun kira zama domin samar da haɗin kai a zaria a tsakanin shekarar 1947 zuwa 1948 amma zaman ya tashi babu nasara bisa zargin akwai 'yan leken asirin sarakuna acikin mahalarta taron.
   A wannan lokaci kuwa, zamanin mulkin Shugaban kasa Sir. Arthur Richard ne, wanda yayi sabon kundin tsarin mulki har ya sahalewa majalisar yankuna harda yankin Arewa damar zaɓen wakilai, to amma gwamnonin turawa na arewa da sarakuna basu bada damar kafa jamiyyar siyasa ba. Don haka zaɓen da akayi na shekarar 1946 kusan indifenda akayi shi.
  A wannan zaɓen na 1946, aka zaɓi Alh. Muhammadu Ribaɗo ɗan majalisa daga Borno, aka kuma zaɓi Abubakar Tafawa Balewa ɗan majalisa daga Bauchi duk a zauren majalisar Arewa.
   A shekarar 1948 Sa'adu zungur ya tafi Lagos don fafutikar kafa Jam'iyyar Al'ummar Nigeria ta Arewa JANA (JANA), anan ne kuma ya zamo akawun jamiyyar NCNC tasu Dr Azikwe.
  A likacin kuma sai waɗancan kungiyoyi na arewa suka sake kiran zaman tattaunawa na biyu a Jos, wanda anan aka haɗu akan ya kamata a kafa kungiyar cigaban yankin Arewa mai suna 'Northern Progressive Congress' (NPC).
  Wani Likita mai suna Dr R.B Dikko ne ya zamo shugaba, sai su Yusuf Maitama Sule, Abubakar Imam, Sa'adu Zungur, Aminu Kano, Yahaya Gusau, Dr. Rafi da sauransu suka zamo a kunshin jadawalin shugabannin kungiya.
   A shekarar 1949 aka kama Habibu Abdullahi Raji da wasu mabiya kungiyarsa ta NEPA aka garkame a kurkuku bisa zargin su da sukar mulkin turawa ta hannun sarakuna, aka kuma cigaba da muzgunawa duk wani da yake aibanta Turawa ko sarakunan gsrgajiya.
  Sai dai duk da haka,  'yan boko basu karaya ba tunda a shekarar 1950 kungiyar NPC ta shirya zaɓe a kano, anan ne kuma manyan mutane suka shigo ciki waɗanda ake ganin sarakuna ne suka ingizo su domin karɓe ikon kuɓgiyar tare da dakushe haskenta, anan aka shiga zaɓe kuma aka  kawar da matasa irin su Yusuf Maitama Sule waɗanda aka kafa kungiyar dasu daga kunshin shugabanci.
   Ana haka sai NPC ta soma rabuwa gida biyu, ya zamo ana samun saɓanin ra'ayoyi, da rashin fahimta musamman sa'ar da Mai
-Martaba marigayi Sarkin Kano na Lokacin Abdullahi Bayero ya bayar da lasisin kafa Sinima a kano, sai wasu sukace hakan daidai ne, wasu kuwa suka ce ba dai-dai bane, wannan abu tozarci ne ga addini, suka shiga rubuce-rubuce suna sukar abin.  
  Ana cikin haka Sai a shekarar 1950 wani mai suna Bello Ijemu ya bada shawarar kamata yayi akafa jamiyyar siyasa, ya kira masu ra'ayi irin nasa mabiya kungiyar NPC irinsu Abba Mai kwaru, Yusuf Maitama sule, Magaji Dan Baffa, Baballiya Manajan Banki da wasunsu suka kafa jamiyyar NEPU ranar takwas ga watan takwas da mutum takwas.
  Wannan jam'iyya ta NEPU, ana iya xewa manufofinta kachokan adawa yake da sarakunan, tunda kullum cakakinsu don me shugabancin jama'a zai zama gadon-gadon maimakon a bajeshi mai bukata ya tsaya zaɓe kamar yadda kasashen da sukaci gaba sukeyi a duniya.
  Daga nan kuwa sai adawa ta soma shiga tsakanin kungiyar NPC da jamiyyar NEPU. 'Yan NPC sukace sun haramtawa duk wanda yake Kungiyar NPC yin NEPU, suka kuma samu goyon bayan sarakuna sannan suka rikiɗe izuwa jamiyyar siyasa.
   A lokacin, Maitama sule da Aminu kano da wasu suka bar NPC zuwa NEPU, shikuma Sa'adu zungur ya bar NPC ya cigaba da zamansa a NCNC. Sai fa adawa da sukar juna ta shiga tsakani, mabiya na zagi da cin mutunci.
  Haka siyasa taci gaba da tsamari a Arewa, kowanne ɗan siyasa na ganin yafi ɗanuwansa kishin Arewa da kokarin samar da cigaba a yankin. Haka kuma a lokacin da Sa'adu Zungur ya kai shawarar cewa ya kamata jam'iyyar sa ta NCNC tazo ta haɓaka ilimi da rayuwar matasan arewa, sai yaga shugabanninta sunyi fatali da abin. Wannan yasanya shi dogon nazari tare da barin jam'iyyar, ya gane ashe ra'ayin 'yan kudanci kurum yake karewa, gashi kuma jahilci yayi katutu a Arewa,mutane da yawa sunfi gane suje duyi karta su likawa masu molo kuɗaɗensu, basu cika maida kai ga abinda ya shafi cigaban yanki ba.
  Bayan dogon nazarin abinda ya kamata yayi, sai kurum ya rera shahararriyar wakar nan mai suna 'Arewa Jamhuriya Ko Mulukiyya' domin farkar da mutan Arewa kada su bari 'yan kudanci su hau kansu su danne..

TARIHIN SIYASAR NIGERIA 1

TARIHIN SIYASA A NIGERIA: TUNAWA DA RANAR 'YAN MAZAN JIYA
 
Kashi na ɗaya.

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
08060869978

Tarihin siyasar Nigeria kusan yana tafiya kafaɗa da kafaɗa ne da tarihin samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka, da kuma wasu abubuwa da suka wakana kafin wanzuwar hakan.
  Da fari dai, gwamnatin ingila ta ayyana ɗaukacin yankunan da ayau ake kira Nigeria bisa karkashin ikonta a ranar 1 ga watan janairun shekara ta 1901, har kuma ta aike da sojoji domin karɓe ikon yankunan baki ɗaya.
   Yankunan Kano da Sokoto ne kusan na karshe da suka faɗa hannun turawan mulki a wajajen shekara ta 1903 zuwa 1904. Tun daga nan kuma Sir Lord Luggard ya zamo shine ɗaukacin shugaɓan tarayyar Nigeria.
   A wancan zamani, babu maganar kafa jamiyyar siyasa, ko kungiyoyi. Maganar biyayyar dokokin turawa kurum akeyi ta hannun sarakuna. Kuma akwai doka da hukunci mai tsanani ga duk wanda yayi shelar neman 'yanci daga turawan mulki.
 Mutanen arewa nada matukar jahilci a fannin ilimin boko duba da kalilan daga cikinsu ne suka sanya yaransu a makarantun zamani. Don haka, kururuwar kafa jam'iyyun siysa da neman 'yanci bata soma kaɗawa ba da wuri-wuri a yankin.
    Sir Lord Luggard, ya gudanar da mulkinsa ba tare da kulawa da ra'ayin 'yan kasa ba, sai dai bisa umarnin kasar sa ingila. Amma duk da haka, yana da majalisa ta jeka na yika, mai ɗauke da wakilai 26 waɗanda suka kunshi wasu daga sarakunan gargajiya a kudanci, waɗanda kuma akasari karɓar umarni ne kurum ne aikinsu, kuma ba zaɓensu akayi ba a siyasance.
    Sai a zamanin mulkin Sir Hugh Clifford ne aka soma kafa ɓurɓushin dimokaraɗiyya a Nigeria. A wuraren shekara ta 1920 ya bijiro da kundin tsarin mulki sassauka, wanda aka lakabawa sunansa, wanda kuma ya sahalewa 'yan kudancin kasar nan damar zaɓen wakilai huɗu daga cikin 'yan majalisar kasa ta jeka na yika.
   Koda yake, sauyin da ya kawo daga gwamnatin Luggard shine kafa majalisu guda biyu a kasa. Daya itace majalisar zartaswa, wadda turawa ne zallah a cikin ta. Sai kuma majalisar kasa mai ɗauke da wakilai 46.
   Acikin waɗannan wakilai 46, kusan kafataninsu turawa ne da gwamnati ta naɗa suke kula da kasuwancin Lagos, kano, Calabar da Phortharcort, sai kuma guda 6 'yan kasa da gwamnati ta naɗa a matsayin wakilai.
 Acikinsu akwai mutum ɗaya yana wakiltar 'yan kasuwar Afirka, ɗaya yaana wakiltar gundumar lagos, ɗaya Egba, ɗaya Ibo ɗaya kuma Oyo. Babu ko ɗaya daga arewa.
   Wakilai huɗu kuwa akace an sahale a shiga zaɓe domin a zaɓosu. A lokacin an bada wakilai uku a lagos, wakili ɗaya kuma daga Calabar.
Saboda haka, a wannan shekarar ta 1923 sai Herbert Macaulay yafara kafa jamiyyar siyasa a Nigeria mai suna 'Nigerian National Democratic Party (NNDP)' domin shiga zaɓen cike gurɓi na majalisar kasa da kuma samar da shugabancin birnin Lagos.
   Herbert Macaulay daman sanan-nen ɗan gwagwarmaya ne kuma mai ilimi tun a wancan lokaci. Tunda kuwa ya karanci fasahar kasa da safayo a Ingila tun gabannin shekarar 1900. Kuma ya shiga kungiyar dake rajin kawar da cinikin bayi a yankin Afirka.
   Sannan tun kafin wannan lokacin, yana takun saka da turawan mulkin mallaka, musamman yadda yake fafutikar kwatowa 'yan kasa yancin kai.
   A shekarar 1908 Herbert Macaulay ya bankaɗo al-mundahanar da wasu jami'an mulki turawa sukayi wajen gina titin dogo, wanda kowa ya sani da arzikin Nigeria ake yinsa.
   Sannan a shekarar 1919, Herbert Macauley ne yakai kara izuwa majalisar Ingila yana nemawa wani shugaban yankinsu da aka kwace masa fili. Kuma ya samu nasara, inda majalisar ta zartar da hukuncin a biya waccan shugaba diyyar daya nema.
  Anyi zaɓe na farko a ranar 20 ga watan satumbar shekara ta 1923. Ance a lokacin, waɗanda sukayi rijistar kaɗa zaɓe a cikin mutum dubu 99 mazauna lagos mutum dubu 4 ne kachal. Saboda haka an shiga zaɓe cikin lumana da kwanciyar hankali babu tasgaro, saboda duk ɗan kasa cike yake da tsoron idan ya aikata laifi turawa zasu hukuntashi.
  Bayan an kammala zaɓe, sai aka ayyana wakilai masu suna: Crispin Adeniyi Jones, Adeyemu Alakija da Egerton Shyngla na Jamiyyar NNDP ta Herbert Macaulay a matsayin waɗanda suka cinye zaɓe, don haka sun samu rinjaye akan 'yan takarar da suka fafata dasu zaɓe daga Jam'iyyar 'Peoples Union' wadda  John K. Rindle da Orisadipe Obasa suka kafa. Sai kuma wakili ɗaya wanda yaci zaɓe ba tare da jamiyya ba daga Calabar.
   Ana haka sai Herbert Macaulay ya kafa kamfanin jaridar 'Nigerian Daily' da yake wayar dakan al'umma bisa kuncin da suke ciki na mulkin mallaka. Kuma jamiyyarsa ta samu tagomashin cinye zaɓuɓɓukan da aka gudanar a shekarar 1928, da kuma na shekarar 1933.
    Amma bayan shekaru biyar da kakar zaɓe ta kewayo, za'a sake shiga zaɓe a shekarar 1938, sai ya zamana wata jam'iyar yarabawa mai suna 'Lagos Youth Movement' wadda Farfesa Eyo Ita ya kafa ce ta lashe kafatanin zaɓen, ta ture Herbert Macaulay da jamiyyarsa ta NNDP gefe.
   A shekara ta 1937 kuwa sa'ar da Dr Nmandi Azikwe ya gamo karatunsa a Amurka har ya soma aikin jaridar 'West African Pilot' a Ghana, sai ya komo Nigeria. Anan suka haɗu da amininsa Oloye Davies wanda ya karanto Sharia a Ingila, suka shiga waccan jamiyya ta yarabawan lagos tare da ɗaukaka ta izuwa 'Nigerian Youth Movement'. Suka haɗu da zaka-kuran mutane irinsu Ernest Sissie Ikoli, Samuel Akisan, James Churchil Vaughan, Kofo Abayumi da wasunsu suna ta rajin wayarwa 'yan kasa kai ta hanyar rubuce-rubucen jaridu. Babbar maganar su itace "bamu yadda da mulkin mallaka ba, 'yancin kai da dimokraɗiyya muke da bukata".
   A haka aka tafi har wuraren shekara ta 1944 zamanin da  Sir. Arthur Richard ke shugabancin Nigeria, inda rikicin kabilanci ya raba Dr. Nnandi Azikwe a matsayin shi inyamiri da jamiyyar Yarabawa ta NYM, sai kurum yazo ya haɗu da Herbert macaulay suka cigaba a Jamiyyar Herbert ɗin a lokacin mai watau NNDP wadda ta sauya izuwa
 'National Council of Nigeria and the Cameroons (NCNC)'.
   Awannan lokaci, sai shugaban kasa Richard ya samar da sabon kundin tsarin mulki, wanda ya rage yawan zaɓaɓɓun 'yan majalisa da wakilan 'yan kasa ya kuma kara adadin 'yan majalisar da-ba zaɓaɓɓu ba.
 Sai kuwa Dr Nnamdi Azikwe da Herbert macaulay suka shiga fafutukar yaki da wannan tsari. Suka shiga suka, suna bin yankuna suna wayar da kai da kuma neman tallafi domin tafiga zuwa Ingila suyi zanga-zangar nuna adawa da wannan kundin mulki a gaban majalisar kasar.
  Ana wannan rintsi ne Herbert Macaulay shugaban NCNC ya rasu, sai Dr Azikwe da yake matsayin akawu ya zama shugaba.
   A shekarar 1945 aka haramtawa Dr. Azikwe fitar da jaridarsa ta 'Africa West Pilot' bayan ta wallafa wasu zantuka dangane da yajin aiki a kasa wanda gwamnati tace basu da tushe balle makama. A shekarar 1947 kuwa aka sake zaɓen 'yan majalisu, har kuma Dr. Nnamdi Azikwe ya zamo wakili zaɓaɓɓe a wannan majalisa ta lagos karkashin inuwar k'anwa jam'iyyar sa ta NCNC mai suna National Democratic Party (NDP).
   A shekarar 1951 kuwa sai sabon kundin tsarin mulki yazo daga Shugaban kasar lokacin mai suna John Stuart Macpherson, wanda ya tsinka wakilan Nigeria izuwa yankunan ta, ya kuma bada damar kowanne yanki ya zaɓi 'yan majalisun sa a wata majalisa karama. Daga waɗancan majalisu  na yankuna ne za'a zaɓi wakili zuwa majalisar kasa.
   A lokacin, jam'iyyun NCNC da 'Action Group' ne suka fi samun tagomashi.
  Ita jam'iyyar 'Action Group' ta yarbawa ce wadda Chief Awolowo ke shugabanta, kuma ya zamo zaɓaɓɓen wakili a karkashinta. Jam'iyyar tana da goyon bayan rusasshiyar jamiyyar 'Northern Youth Forum' (NYF) ne mai adawa da Dr. Azikwe.
   Shi kuwa Dr. Nnamdi Azikwe  ya samu cin zaɓen yanki a majalisar kudanci karkashin jam'iyyar tasa NCNC, amma sai dai Chief Awolowo na Action Group ne mutumin daya fishi samun tagomashi a majalisar, don haka shine ya samu damar tafiya babbar majalisar kasa..
   Wannan kusan shine a takaice yadda siyasa ta faro a kudancin Nigeria kenan, saura muji yadda ta kasance a yankin Arewa.

SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 9

TARIHI: SARAUTAR SARAKUNAN MUSULUNCI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na tara.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

SARAUTAR SARKIN MUSULMI ATTAHIRU NA BIYU DAN SARKIN MUSULMI ALIYU DAN MUHAMMADU BELLO.

  Daga karshe shawara ta cimmu, aka yiwa Attahiru jikan Muhammdu Bello sarauta.
  A shekarar farko turawa basu fara komai ba, suna ta neman haɗin kai daga jama'a.
   A farkon shekara ta biyu sai suka sanya wa jama'a Jangali. A karshenta kuma suka sanya haraji.
   A shekara ta uku ne fitinar Satiru ta taso.
   Abinda kuwa ya faru shine:-
Akwai wasu unguwanni a kudancin sokoto masu sunaye Boɗinga da Dange, ance sai wani mutum mai suna Danmakaho gaurin Kauyawa da wasunsa suka shiga tara mutane a garin Satiru, har sai da suka tara jama'a da yawa da nufin ɓallewa daga turawa.
   Farkon abinda suka fara shine yanka wuyan wani mutum mai suna Yahaya saboda yayi sallar idi ba tare dasu ba.
  Daga nan sai kisan wasu mazaje 13 da mace ɗaya a kauyen Tsomau gami da kone garin.
   Labari sai ya iske baturen mulki Mai Farin Kai (Mr. Burdon) lokacin kuwa yana shirin tafiya Dungurun ne. Don haka sai ya aiko da takarda ga turawan sokoto domin suyi bincike kafin ya dawo.
  Ana haka sai turawa uku da likita ɗaya suka taso izuwa satiru don ganewa idonsu abinda ke faruwa. Ai kuwa zuwansu keda wuya bayan sun zauna, sai mutanen Satiru suka hausu da sara da suka, sukayi gunduwa-gunduwa dasu, suka ɗauke bindigoginsu.
  Daga nan fa sai mutanen satiru suka soma girman kai da buwaya, suna bin garuruwan makwabta suna kara magoya baya da kisan duk wanda yaki musu biyayya.
  Bayan jimawa kaɗan Mr Burdin ya komo sokoto. Sarkin musulmi yaje ya gaisheshi, sannan ya tura takardu duk manyan sarakuna suzo sokoto irinsu Sarkin Tambuwal, Sarkin Mafara, sarkin Danko, sarkin 'Burmin Bakura, sarkin Gobir Isa, da sarakunan Zamfara.
   Bayan kwanaki sai Marafa ya nemi izini aka bashi, ya taho da runduna don murkushe mutanen satiru, amma akayi rashin nasara akan sa, mutanen satiru suka kara girman kai.
   Daga nan sai askarawan Turawa suka iso sokoto daga Kano, kwantagora, Dungurum da Lokoja. Aka haɗa runduna aka nufi satiru.
   Da turawa suka isa, sai suka girke kayan faɗansu. Mutanen satiru ma suka fito garesu suka jeru. Turawan nan kallon su kurum suke yi. Babu jimawa mutanen satiru suka nufo askawan turawa a sukwane.
  Sai da mutanen Satiru suka zo kusa, sai masu Igwa suka durkusa kan guiwowinsu, suka fara harbawa. Nan take hayaki ya turnuke sama, kafin kace haka gawarwakin mutanen satiru kurum ake gani a kasa hululu cikin jini.
  Wani sahun ya kara tasowa ga turawa, nan ma akayi masa kamar yadda akayiwa sahu na farko. Aikuwa babu jimawa sai ragowar suka arce.
  Bature  Mai Farin kai ya shiga garinsu, ya huta, sannan ya bada umarni a kone shi. Karshen wannan fitina kenan wadda ta ɗauki tsawon shekara ɗaya da kwana ashirin.
  A shekara ta huɗu da zuwan turawa suka tursasa sarakunansu bada 'ya'yansu a koyar dasu ilimin boko, a lokacin ma babu makaranta a sokoto.
 A shekara ta takwas kuma suka gina Baitul Mali.
   A karshe dai, Allah ya karɓi ran sarki Attahiru na biyu bayan ya shafe shekaru 12 da watanni 2 a mulki a shekarar 1915.
  Da fatan Allah yajikansa Amin.
Sauran Sarakunan da suka mulki sokoto bayansa sune:
-Muhammadu dan Ahmadu 1915-1924
Muhammadu dan Muhammadu 1924-1931
Hasan dan Mu'azu Ahmadu
1931- 1938
Siddiq Abubakar III
 1938- 1923
Ibrahim Dasuki
1923-1988
Muhammadu Maccido
1988- 2006
Sa'adu Abubakar
 2006-

Alhamdullahi. Karshe kenan!


SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 8

TARIHI: SARAUTAR SARAKUNAN MUSULUNCI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na takwas.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.


SARAUTAR SARKIN MUSULMI ATTAHIRU DAN AHMADU DAN ABUBAKAR ATIKU

  Anyi masa mubaya'a mulki a wurno gidan waziri Buhari. Daga nan ya taso zuwa sokoto da zama. Acan ne Sarkin kano Alu Babba yazo gareshi yayi masa mubaya'a tare da jaddada tubansa bayan karewar Basasar kano da rasuwar sarkin kano Tukur.
   Sarkin Musulmi Attahiru ya yafe masa, ya kuma aura masa 'yarsa, sannan ya ɗauki hanyar komawa gida.
   Akan hanyarsa ne ya sauka a Gadi ta kasar zamfara. Da yammaci sai kuwa ga matarsa a sukwane tazo gareshi daga kano. Anan take sanar masa cewar turawa sun kwace kano. Don haka sai tsoro ya kamashi, ya sulale da dare ya gudu ba tare da jarumansa sun sani ba.
   Da gari ya waye jaruman Sarki Alu suka nemeshi baya nan, sai wazirinsa Ahmadu yayi musu jagora suka sukwano da nufin dawowa kano. Amma kafin su iso sai suka haɗu da turawa, suka gwabza yaki, waziri Ahmadu yayi shahada, saura suka tarwatse.
   Anan kuma sai Wambai Abbas yaja ragowar tawaga da suka tarwatse suka tafi kano tare da yiwa turawan cikinta mubaya'a, har kuma daga baya suka naɗa shi Sarkin kano.
   Sa'ar da labari yazo sokoto cewar turawa na zuwa daga kano, sai aka shiga shawarwarin abin yi. Wasu suka ce ayi tattalin yaki dasu. Wasu sukace a nemi sulhu dasu. Wasu kuwa sukace sai ayi hijira tun kafin su iso.
   Sarkin musulmi Abdurrahman kuwa sai ya karkata akan ayi hijira. Daga nan mutane suka shiga tattalin kayayyaki. Aka shiga siyen takalma, alfadarai, jakuna, rakuma da sauran kayayyaki domin yin hijira. Aka sanya ranar tashi.
  Ana cikin haka kwatsam sai ga labari cewar turawa na daf da sokoto. Sai kuwa niyyar hijira ta warware, aka shiga shirin yaki dasu.
   Sarkin musulmi ya fita bayan gari ranar wata jumu'a ya kafa sansani, ya aika da masu neman labari suje suyi Sharoro.
   A wannan yammaci masu sharoro suka gama hangawa suka dawo basu ga kowa ba. Wayewar garin asabar ma haka. Sai can da yammaci har nutane sun fara sakin jiki da zuwan turawa akaga kura ta turnuke, turawa suka harbo bindiga ta kashe mutane. Jama'ar sarkun musulmi ta kwana cikin shiri.
   Da wayewar garin Lahadi sai aka fita yaki. Aka soma fafatawa, amma cikin kankanin lokaci aka kashe mutanen sarkin musulmi masu yawa, wannan yasa yaja zuga ya gudu yabar sokoto, sannu a hankali har kasar Gombe inda Allah yayi masa rasuwa daga baya, bayan ya gwabza faɗa da turawa a wani wuri da ake kira 'Burmi.
  Dafatan Allah yajikamsa Amin.
   Bayan rasuwarsa, sai Sauran mutanen dake tare dashi suka rabu, wasu suka dawo sokoto, wasu kuma suka nausa izuwa gabas, suka sauka a wani wuri mai suna 'Shehu Talha', suka naɗa Muhammadu Bello ɗan marigayi sarkin da turawa suka kashe Attahiru a matsayin shugaba. Har yanzu kuma ɓurɓushin sa suna can garin.
   Amma da turawa da turawa suka tarwatsa tawagar yaki a sokoto, shima waziri Buhari sai yaja zuga yayi nasa wuri. Yaje wani kauye mai suna Dinawa kusa da wurno ya sauka.
   Babu jimawa sai turawa suka aiko masa da takarda cewar ya komo sokoto. Waziri Buhari yahau da mutanensa ya nufi sokoto. Ya iske turawa sunyi dandali a gabas da birnin sokoto. Ya aike musu gashi nan tafe, suka yi masa izinin shiga birni.
   Aikuwa koda mutane sukaji cewar waziri ya komo birni, sai waɗanda suka gudu sukayi ta dawowa.
   To daga nan sai turawa suka nemi shawarar wanda za'a naɗa sabon sarki..
  

SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 7

TARIHI: SARAUTAR SARAKUNAN MUSULUNCI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na bakwai.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

10. SARAUTAR SARKIN MUSULMI ABDURRAHMAN DAN ATIKU
 (Danyen kasko)
Anyi masa mubaya'ar sarauta a gidan waziri Buhari bayan rasuwar Sarkin musulmi Ummaru, sannan ya taso daga Kauran Namoda ya nufi sokoto.
  Akan hanyarsa ya sauka a Gora, ya aika cewar Sarkin Mafara yazo gareshi, sarkin mafara yace bazai iya zuwa ba saboda rashin lafiya, amma ga galadima nan ya amsa mubaya'a..
 Sarkin musulmi yace baya amsar mubaya'ar galadima, sarkin yakeao yazo da kansa, amma sai sarkin Mafara yaki yaje.
  Rannan bayan sarkin Musulmi Abdurrahman ya isa gida Sokoto, sai aka sake aikewa sarkin musulmi da cewar husuma ta auku tsakanin sarkin Mafara dana Burmi, har sarkin mafara ya kame Birnin Tudu dake ikon sarkin Burmi.
  Sarkin musulmi ya aike zuwa Mafara cewa ya saki wannan gari indai ya tabbatar Birnin Tudu na sarkin Burmi ne, idan kuwa ba nashi bane to ya aiko da jawabi mai daɗi gareshi.
   Sarkin Mafara ya aiko da cewar Birnin Tudu ba na sarkin Burmi bane, na Namai-barau ne, shikuwa nasa ne. Yanzu kuma Ibo ke ikon ta, shima kuma nasa ne.
  Sarkin musulmi ya aike ga waɗannan sarakunan da cewa suyi sulhu a tsakanin su, amma sai sarkin Mafara yaki ya karɓi sulhu.
   Sarkin musulmi ya aike da sako Mafara cewar matsawar sarkinsu bai karɓi sulhu ba, to yaki na zuwa daga gareshi..  Mutanen Sarkin Mafara suka haɗu da jakadan sarkin musulmi a wani wuri mai suna Rini suka harbeshi da kibiya, sannan sukace sun ɗauki faɗa da sarkin musulmi.
   Sarkin musulmi ya aikewa Sarkin Anka wannan abu, amma shima sai aka tarar yana goyon bayan Sarkin Mafara ne.
   Daga nan kuwa sai sarkin musulmi ya hori a buga tamburan yaki, yace mutanen Anka da Mafara sun zama abokan gaba, sannan ya aike da sarkin zamfara Ummaru ɗan Mahmudu gabas, yace ya rinka aikewa da hari mafara.
   Ya kuma hori Sarkin Rafi Alhaji daya zauna a Magami ya kuntatawa mutanen muradun da hsre-hare.
  Sannan ya aike jarumai domin su zauna tare da sarkin Burmi a Modocci don maganin harin da abokan adawa zasu iya kawowa.
  Haka kuma ya umarci sarkin Sulluɓawa shuni daya rinka kai hare-hare ga Anka da Mafara babu sassautawa.
  Yace da Magajin gari ya tafi Maru ya tara jarumai su tafi sukai hari ga Mafara.
   Ya umarci sarkin Danko Ali yazo su haɗu a Laje don su kaiwa abokan adawa hari.
  Da sarkin Mafara yaga haka, sai ya aike wa sarkin Gobir neman taimako. Sarkin Gobir Almu ya tashi da gagarumar runduna zuwa Mafara, suka tafi ga sarkin Burmi suka buka yaki har sau uku ana gwabzawa amma basu samu gagarumar nasara ba, anan nema aka halaka Bawa ɗan sarkin Mafara.
  Daga nan sai sarkin musulmi ya aiki jarumai su tsare wababe, sannan yahau zuwa Mafara da yaki, ya buga yaki dasu da fari sannan ya koma gida.
  Bayan ya komo gida sai mutanen Mafara suka saduda, suka aiko neman sulhu saboda kuntatar da akayi musu.
   Sarkin musulmi yaki amsa musu, ya cigaba da shirin yaki abinsa.
   Amma da suka matsu sai suka kori sarkinsu Buzu, suka aika da rawaninsa ga sarkin Burmi domin ya nemar musu sulhu da sarkin muslmi.
  Da sarkin musulmi yaji abinda sukayi, sai yace indai da gaske ne suna son sulhu, to sai sabon sarkin da suka zaɓa ya zo gareshi.
   Daga nan Sabon sarkin Mafara da sarkin zamfaran Anka suka taso izuwa ga sarkin musulmi suna masu neman amana, suka haɗu dashi a Gandi, yace su saki duk bayin da suka kama a yayin wannan rikici, sukace sunji zasuyi yadda duk yace.
  Yace kuma bai yadda da amanar suba har sai sun bashi bayi dubu.
  Sai da suka bashi kuwa sannan ya aminta dasu.
  Sannan yace ya mayarwa sarkin Burmi birnin Tudu, suka ce sun yadda,.
  Ya hori sarkin mafara da jama'ar sa duk su daina al'adar nan tasu ta ahi( atire) da aka sansu da ita, ya rarraba yankuna kuma ga sarakunanda suka taimakeshi a wannan yaki.
 Ya baiwa Alhaji Maradun, ya raba wasu yankuna tsakanin sarkin Mafara Laje da Sarkin Danko Ali.
  Bayan duk an kare wannan, sai ya shirya zuwa Argungu da yaki, yaje ya kai mata hari ya dawo gida.
  Bayan ya dawo ya kai yaki Ruwan Bore ya kame waɗanda ke ciki, sannan ya sake shiryawa zuwa Argungu a kashi na biyu.
  Bayan ya dawo dai, ya sake kaiwa Ruwan Bore da Argurgu hari a karo na uku.
  Daga nan sai yaron turawa mai suna Adamu yazo masa. Yazo tare da yaron sarkin zazzau, da gaisuwa da hajoji da suka saba aikawa ga sarkin musulmi. Sarkin musulmi yaki amsar gaisuwarsu ya kuma koresu.
  Daga baya sai aka shirya gyara da turawa, sarkin musulmi yaci gaba da karɓar gaisuwarsu..    Ana kan haka kuma sai ƙlabari yazo cewa turawa sun kone Nufe, sun cinyeta da yaki..
   Koda sarkin musulmi yaji haka sai ya daina amsar gaisuwarsu. Amma kuma labarin ciye-ciyen garuruwa daga turawa ya zamo yanata karuwa a kullum.
  A haka har sukaci Bauchi, sarkin Bauchi ya gudo zuwa kano.
  Rannan bayan an kare Basasar Kano lokacin da waziri ya sauka a zariya sai kwatsam ga turawa sun dira da rundunar su ta yaki, suka ce sai a saki bayi duka, aka sakesu.
Suka tsare waziri a zazzau.
  Suka sa dogarai biyu a kowacce kofa, amma akwai wata kofar da waziri ya sulale ya bar zazzau zuwa kano da ba susan da itaba, daga kano ya komo sokoto abinsa.
   Sai Ya zamana zazzau ta fita daga ikon sarkin musulmi.
 Sannan Gwamna Lugga ya aiko da wasika zuwa ga sarkin musulmi da Cewa:-
Bayan gaisuwa, Ka sani, idan shekara ta kewayo, zamu zo gareka, idan kana wurno zamu sauka a sokoto, idan kana sokoto kuwa zamu sauka a cikinta.
   Sai sarkin musulmi ya juya takardar tasu ya maida jawabi da cewa
"La Haula Wala kuwwati Illa Billahi"
 Ya aike musu dashi.
  Sai dai bayan watanni 6 sai Allah yayi masa rasuwa, yana da shekaru 75 a duniya, yana kuma da shekaru 12 bisa mulki.
   Kabarinsa na nan a Wurno.

Haka kuma Azamaninsa akayi basasar kano. Kuma a zamaninsa turawan Faransa suka kone Salame da dare, mutane suka firgita matuka.
  Da fatan Allah yajikansa Amin.
   

SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 6


TARIHI: SARAUTAR SARAKUNAN MUSULUNCI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na shidda.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.


4. SARAUTAR SARKIN MUSULMI AHMADU DAN ATIKU
  Kwanaki uku da rasuwar sarkin musulmi Aliyu sai aka yiwa Ahmadu ɗan Abubakar Atiku ɗan shehu Usmanu mubaya'ar sarauta. Yayi alkawari da tsayar da gaskiya da adalci, ya hori mutane da abubuwa huɗu: na ɗaya su bar sayar da gonaki, na biyu subar amsar gunki, na uku su amsa kiran alkalai, na huɗu su amsa kiransa idan ya nemesu tafiya izuwa yakin jihadi.
   Akwai daga yake-yakensa yakin Karaziru, da Yakin Sauwa, da yakin ruwan Bore, da yakin Gumi.
  Shine sarkin daya rayad da Cimmola, ya gina birni acikinta, da masallatai har ake sallar jumu'a aciki.
  Kuma a acikin wannan gari Cimmola ya rasu bayan yayi shekaru bakwai da wata biyu da kwana 26 yana sarauta, yana da shekaru 60 da haihuwa.
  Da fatan Allah ya rahamsheshi Amin.
 
5. SARAUTAR SARKIN MUSULMIƁALIYU NA BIYU
  Shine Aliyu ɗan sarkin musulmi Muhammadu Bello, kuma shi ya kasance ɗan uwan Sarkin musulmi Aliyu na farko ne.
  Anyi masa mubaya'ar mulki a Chimmola bayan kwanaki huɗu da rasuwar Sarkin musulmi Ahmadu ɗan Abubakar Atiku.
   Daga nan sai ya taso izuwa Wurno da zama, shine na shidda da sarautar sarkin musulmi idan aka soma lissafi da shehu Usmanu, amma na biyar daga Muhammdu ƁBello.
 Yayi watanni goma sha ɗaya da kwanaki 19 bisa sarauta ya rasu yana da shekaru 60 da haihuwa. Kabarinsa na nan a wurno kusa dana mahaifinsa.
  Da fatan Allah ya jikansa Amin.
    6. SARAUTAR SARKIN MUSULMI AHMADU RUFAI DAN SHEHU USMANU.
   Kwanaki biyar da rasuwar sarkin Musulmi Aliyu, sai akayiwa Ahmadu Rufa'i ɗan shehu Usmanu mubaya'ar mulki a masallacin wurno.
   Bai jima awurno ba ya komo sokoto da zama, ya gyara masallatai da gina sababbi, ya rayar da garin sosai, kullum kuma yana cikinsa har ma ana cewa aduk tsawon zamanin sarautar sa kimanin shekaru biyar bai fita daga sokoto ba sai sau uku kacal.
  Na farko domin tafiya ginin birnin Silame.
  Na biyu domin korar kafirrai daga Kware sanda suka sauka a wata alkarya mai suna kayama.
  Na uku ya kara fita zuwa Kware domin ta'aziyyar ɗan uwansa Mallam Isa ɗan shehu Usmanu bin fodio.
   A zamaninsa, an samu zama lafiya da kwanciyar hankali a daular musulunci.
   Shine sarkin daya soma yanke hannuwan 'yamfashi idan an kamo su tun bayan rasuwar Shehu Usmanu.
   Ya rasu yana da shekaru 61, bayan ya shafe shekaru 5 da watanni 6 da kwanaki 20 bisa sarauta. Kabarinsa na sokoto shima.
Daftan Allah ya jikansa amin.

7. SARAUTAR SARKIN MUSULMI ABUBAKAR NA BIYU, MAI RABAH DAN SARKIN MUSULMI MUHAMMADU BELLO.
   Daga nan kuma sai aka yiwa Abubakar mubaya'ar sarauta a sokoto.
  A zamaninsa anyi yake-yake a kalla guda uku.
 Sune:- Yakin gidan karari, da yakin Farintau da yakin Madarumfa.
  Wannan sarki ya zamo mai tsoron Allah da kamanta adalci ga mabiya, ya rasu a wurno yana da shekaru 63 da haihuwa. kabarinsa na nan kusa dana mahaifinsa Muhammadu Bello a wurno. Dafatan Allah yajikansa amin.

8. SARAUTAR SARKIN MUSULMI MU'AZU DAN MUHAMMADU BELLO
 Daga nan sai akayiwa Jikan shehu na karshe a jerin sarakunan musulunci sarauta, watau Mu'azu ɗan muhammadu Bello a wurno.
   A lokacinsa yayi yaki mai tsanani da Sabon Birni, amma bai samu nasarar cinyeta ba kuma yayi kokarin samar da zama lafiya ga masarautarsa.
   A karshe ya rasu yana da shekaru 68 da haihuwa bayan yacika shekaru 4 da watanni 9 yana mulki.
Kabarinsa yana nan a sokoto kusa da hubbalen shehu.
 Allah yajikansa amin

9. SARAUTAR SARKIN MUSULMI UMMARU DAN ALIYU DAN MUHAMMADU BELLO.
  Daga nan sai akayiwa Ummaru mubaya'a  nan cikin masallaci Bello a sokoto.
  A yake-yakensa akwai yakin Sabon Birni, inda yaje domin ɗaukar fansar uba gareshi, marigayi sarkin musulmi Mu'azu.
  Haka kuma ya kai yaki Argungu da Madarumfa.
   A zamanimsa ne turawa suka yawaita shigowa kasar sokoto, har aka gane cewa su ba sharifai bane kamar yadda a baya suke ɓoye kansu domin su samu ikon yawo cikin kasa da yin ciniki.
   A waɗannan zagaye na turawa suka san kasa dukkanta, suka san koramu da garuruwan kasar hausa, suka isa ga sarkin Musulmi sukayi cinikayya da mu'amala dashi har zuwa rasuwarsa.
  A zamaninsa turawa sun bashi agogo don sanin lokaci, da wani gado mai yin fifita da mafitai idan an zauna akansa, da gambuna masu fenti da sauransu.
  Haka kuma a zamaninsa, yakan yi zama lokaci lokaci da sarakunan gabas a kauran Namoda.
   Kuma a kauran Namoda ɗin ya rasu, yanada shekarun haihuwa 69 bayan yayi shekara 9 da watanni 10 bisa kan sarauta.

SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 5

TARIHI: SARAUTAR SARAKUNAN MUSULUNCI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na biyar.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

3. SARAUTAR SARKIN MUSULMIƁALIYU BABBA DAN MUHAMMADU BELLO
Anyi masa mu baya'ar sarauta ne a birnin sokoto, cikin masallacin shehu Usmanu tsakanin bayan sallar azahar zuwa la'asar kwana bakwai da rasuwar basambonsa Atiku.
   Shidai ya kasance mai kyawawan ɗabiu, wanda baya wulakanta jama'a, kuma mai rikon addini da horo da ayyukan kwarrai, gashi da son zumunci..
   Yakin sa na farko zuwa Muniya ne.
 Yayi wasiku ga sarakuna na gabas ya sanya wurin gamuwa, sannan ya taso suka gamu a wani wuri d ake kira Riyojin kura, suka yi shiri suka aukawa Muniya, amma basu samu cinyeta ba suka komo da baya.
   Daga nan yayi shirin yaki zuwa Adabka, yaje da kansa ya yakesu yayi rinjaye akansu.
  Bayan ya dawo sai mutanen Tozai sukayi bore, bisa shugabansu Maiyaki.
 Sarkin Musulmi Aliyu yahau garesu ya fatattaki garin har sai da dukkansu suka gudu suka bar gagarumar ganima.
  Daga nan sai yakin Gummi. Ance Sarkinsu ya fita izuwa ɓawar Yari da gayyarsa duka, amma rundunar sarkin musulmi ta yi galaba akansu.
   Bayan ya koma gida sai yayi tattalin yaki zuwa Gobir, daya isa yaga lallai ko anyi yaki babu nasara sai ya dawo gida.
   Sa'ar da shekara ta kewayo sai ya shirya yaki zuwa Madarumfa ya gamu da sarakunan gabas, nan ma yaga jama'ar sa nada rauni, sai ya komo gida.
   Hakakuma ya sake ɗaura aniya zuwa Zauma da yaki, ya tura ɗan uwansa Ahmadu ɗan marigayi sarkin Musulmi Abubakar Atiku yaje yacisu da yaki.
   Daga nan ya haɗa runduna zuwa Tsibiri da yaki, yaje ya samu rinjaye akansu ya dawo.
   Sai kuma ya sake haɗa wata rundunar zuwa Gayari, ya tafi da kansa da dakaru yayi yaki dasu ya ribace su.
   Daya dawo gida kuma sai ya sake haɗa wata tawagar yaki, ya tura ɗan Uwansa Halilu ɗan Hassan ɗan shehu Usmanu zuwa Tagada da yaki, Allah ya basu nasara kuwa suka komo gida da ganima.
   Ana cikin haka sai sarkin Haɗeja Buhari ɗandidi yayi bore daga biyayyar sarkin musulmi. Sarkin musulmi ya tashi waziri Giɗaɗo zuwa gareshi da runduna. Yaje ya yakeshi ya kore shi, ya naɗa ɗanuwansa Ahmadu Dodo a kan sarauta.
   Bayan komawar waziri Abdulkadir ɗan Giɗaɗo sokoto, sai maishishshigi Buharin Haɗeja ya kara motsawa da fitina, nan ma sarkin musulmi ya aike masa da ɗan galadiman waziri Ahmadu Dangiɗaɗo, watau kani ga waziri Abdulkadir don ya yake shi.
  Suka tafi izuwa Haɗeja, suka sake shiri sarkun ta, sannan suka nufi maɓoyarsa bayan an koreshi a Takoka, amma dasuka gamu a wannan karon sai Buhari ya samu nasara akansu.
   Bayan nan, sai aka sake tura Waziri Abdulkadir ɗan Giɗaɗo ga Buharin Haɗeja da tawagar yaki, anan ma basu samu nasara akansa ba.
  To daga nan ne sai Masarautar kano ta karɓi ragamar yakin, shikuma sarkin musulmi Aliyu ya cigaba da mayar da hankulansa akan makwabtansa.
   A wannan lokacin, sarkin musulmi ya aike da tawagar yaki bisa jagorancin sarkin kabi Muhammadu Moyijo zuwa Tumba amma basu samu nasara ba suka komo gida. Babu jimawa kuwa sai aka sake tura wata tawagar bisa shugabancin Sarkin yaki Abdul Hasanu ɗan Aliyu Jedi, anan ma ba'a samu wata nasara gagaruma.
   Daga nan fa sai garuruwa suka soma yin bore ga sarkin musulmi. Saboda suna ganin kamar karfinsa ya ragu sosai.
 Acikin garuruwan da akwai kasar zamfara, da jerma da Kabi.
A lokacin kuma musulmai har sun fara karaya da tsoro.
   Sarkin musulmi Aliyu ya tafi da runduna zuwa Kabi don yakar su. Su kuwa kabawa suka gayyato yanuwansu daga mauri da Jerma, aka gwabza matsanancin yaki a Mera, musulmai sukayi nasara da ikon Allah, aka halaka sarkin su Namabe, aka wargatsa tawagar Augi.
   Bayan runduna ta koma gida, sai sarkin musulmi ya sake haɗa tawaga zuwa Argungu da yaki, akayi karamin yaki acan amma ba'a cita ba aka rabu.
  Babu jimawa da komowarsa daga yakin Argungu, sai akace masa sarkin Baura ya aukawa jihohin Burmi da yaki.
  Nan da nan ya haɗa runduna, ya tafi da kansa har zuwa Tumba, ya tarar sarkin Baura ya gudu, yasa aka bishi a dawakai amma ba'a riskeshi ba,  sai ya dawo gida.
   Haka kuma Sarkin musulmi Aliyu ya samu labarin Mai-shish-shigin nan Maiyaki tsohon sarkin Tozai daya gudu, ya tafi kwatarkwashi yana haɗa runduna don kawo hari.
 Sar Sarkin musulmi yayi shirin yaki ya nufi kwatarkwashi. A lokacin ana cikin tsananin zafin rana da kishirwa, mutanensa nata surutu amma bai kula suba. Sai da akazo za'a buga yaki, sai mutanen kwatarkwashi suka gane ashe Maiyaki ya gudu daga garesu. Don haka babu fafatawa mai tsanani suka mika wuya.
  Sarki Aliyu ya komo gida, akan hanyar sa ya shigo ta hanyar Burmi ya sauka Kasara, wasu daga rundunarsa suka kai yaki Mafara suka dawo, ya tashi izuwa Barbuni, ya sauka yayi umarni akai yaki zuwa Bakura, sannan ya komo gida.
   Yawan yakunan daya hau a zamanin sarautarsa guda 20 ne, ya gyara masallatai a zamaninsa da kuma ganuwar birane. Shine na farkon sanya kofofin karfe a gankwar birane don rufewa.
   A zamaninsa ne wasu mutanen kasar gabas sukayi hasashen zuwan Mahadi, suka ɗaura ɗamara suna jiran bayyanar sa don ya shige musu gaba ya kaisu garin Makkah.
 To amma daga bisani sai aka shafe lamuransu, 'yan kaɗan na mabiyansu ne sukayi saura kamar yadda akace Shehu Usmanu yayi busharar zuwansu a lokacin rayuwarsa.
  A karshe, Allah yayi masa rasuwa a Wurno yana zaman ribaɗi, yana da shekaru 53 da haihuwa, yana kuma da shekaru 17 bisa karagar sarauta.
  Da fatan Allah yajiqansa amin.

SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 4

TARIHI: SARAUTAR SARKIN MUSULMI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na huɗu.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

Bayan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya huta a gida, sai kuma ya sake ɗaura haramar yaki zuwa Anka a lokacin kaka.
  Daya gama haɗa rundunarsa, sai ya fita Wurno, ya riski wani gari Mada-rumfa akan hanya, ya cishi da yaki, ya warwatsa shi, ya kuma kafa ɗansa Ibrahim shugaba a garin.
  Sannan ya wuce gaba izuwa Bakura, nan ma ya kwace ikonsa, ya kuma ajiye ɗan ɗan Uwansa Ahmadu shugaba.
 Daga nan ya wuce Anka, yayi yaki da ita mai tsanani, ya samu nasara sannan ya koma gida.
  Ance Muhammadu Bello yayi yakuna akalla guda 47 waɗanda shine yayi jagorancinsu da kansa yana kan karagar Sarkin Musulmi, amma babu wanda zai iya tantance adadin yakunan da akayi a lokacin mulkinsa sai Allah.
 Haka kuma ance bai gushe ba yana yaki don ɗaukaka addinin Allah har saida lamurra suka koma dai-dai kamar sanda Shehu Usmanu yake raye.
   Wuraren da Muhammadu Bello ya zaune sune:-
 Da fari ya fara zama a Yamulu tsawon shekaru biyu a lokacin shehu na Degel yana ribaɗi, watau kai hare-hare da kuma taryar abokan adawa idan sunzo da hari. Sannan ya zauna a sokoto nan ma don Ribaɗi, ya kuma zauna Gwandu don Ribaɗi.
  A halin sarautarsa kuwa, ya zauna a Karandai, sannan Magarya, sannan wurno, kuma nufinsa ya rasu yana yawo garuruwa domin ribaɗi.
Har ma an jiyoshi yana cewa "Hakika mazaunin ribaɗi, idan ya mutu anan aka turbuɗeshi acikinta, ba za'a naɗe takardar saba. Zai zamo ana rubuta masa lada a kullum kamar yadda ake rubuta masa a lokacin rayuwarsa, daga nan har ranar tashin alkiyama".
  Don haka yayi wasiccin cewa koda ya mutu, kada a binne gawarsa a sokoto ko kuma awani wurin sai a wurno.
   Haka kuwa akayi, ya rasu da marece na ranar alhamis, 25 ga watan Rajab na shekarar 1253 hijiriyya, a wurno.
 Maganarsa ta karshe kalimatussashada ce sau uku, sai kuma Ayar Al-kur'ani maigirma.
 Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya rasu yana da shekaru 57 da watanni 11. A lokacin kuma yana da shekaru 21 bisa karagar sarkin musulmi.
  Don haka a wurno aka binne shi. Kuma har yanzu acan kabarinsa yake.
  Dafatan Allah ya rahamsheshi Amin.

2. SARAUTAR SARKIN MUSULMI ABUBAKAR ATIKU
Bayan kwana bakwai da rasuwar Muhammad Bello, sai akayiwa Abubakar Atiku mubaya'a.
  Shikuwa ya kasance ɗane ga Shehu Usmanu ɗan fodio, watau kaniɓga Muhammadu Bello.
  Kuma ya kasance masanin sirruka.
  Har ma ance mahaifinsa ya sanar dashi sirruka 115, shikuwa sai ya sanar da 15 ga jama'a, ya bar 100 bai sanar da kowa ba.
 Amma ga maison samun sirrikan daya sanar, sai ya nemi lityafin 'Tabshirul Ikhwan' na Abdulkadir Macciɗo Waziri.
    Yake-yake
  Bayan Sarkin Musulmi Abubakar Atiku ya hau gadon sarauta, sai kafiran amana na zamfara dana gobir suka warware alkawari, don haka sai yayi tattalin yaki, ya fuskanci Burmi.
  Yayi tafiya har ya iske birnin Damri. Ya iske sarakunan zamfara sun taru cikinsa, yayi faɗa dasu, kuma ya samu nasara.
  Sannan ya ɗaura yaki ya isa karkarar Katsina, yayi sansani anan, sannan ya zabura zuwa birnin Cikaji yayi yaki dasu mai tsanani, yayi zamansa kwanaki da dama, sannan ya koma gida.
   Daga can kuma ya ɗaura yaki zuwa zurmi, ya aike Abdul Hasanu ɗan sarkin yaki Aliyu Jedi, ya fita garesu da runduna, yayi faɗa dasu ya komo gida.
  Sannan yayi tattalin yakin Attabu (yakin gayya) wanda ya kira sarakunan gabas ya gamu dasu acikin kasar zurmi. Ya tashi ya nufi Gobir, ya kokarta ya riski Tsibiri, ya sauka Rumka, ya iske mutanen Gobir, katsinawa, Azbinawa da mutan Borno sun taru acan.
   Ya fara yaki dasu tun hantsi har la'asar. Allah ya bashi nasara ya karya su  ya koma gida.
  Sanna ya ɗaura yaki zuwa kasar Gummi, ya kwana 8 ya ɓata abincin karkararsu duka, suka firgita dashi, sannan ya komo ta zurmi, ya dawo gida.
   Da lokacin kaka yayi, sai ya sake gayyatar sarakunan gabas, suka zo da shirin jihadi, suka fita da yaki har Zamfara, suka fuskanci Gobir.
   Ya shiga cikinta yayi sansani, Ya kwana uku, sannan ya nufi tsibiri da yaki. Mutanensa suka aukawa tsibiri da yaki mai tsanani. Anan suka wanzu har kwanaki biyar.
   A cikin haka sai ya lura mutane jikinsu yayi sanyi da yaki, don haka ya juyo ya tsallaka gulbi, babu wani alamun ciwo jikinsa.
  Lalura ta sameshi ranar 27 ga watan Ramalana, ya zamo ana ɗauke dashi a wuya har suka iso wani wurin da ake cewa Nasarawa cikin kasar Zamfara duka sauka.
  Ya kwana 18 anan, sannan yahau zuwa Kuturu. Ranar  alhamis kuwa ya rasu anan.
 Don haka Kabarinsa nanan a Katuru. Da fatan Allah ya gafarta masa Amin.
  Sa'ar da aka kare jana'izarsa, sai waziri Babba Abdulkadir ɗan waziri Giɗaɗo ɗan Laima yayi ban kwana da sarakunan gabas suka koma gida.
  Zaɓaɓɓun da suka rasu kuwa a lokacinsa akwai ɗan uwansa Buhari, da Alkali Bi'ali, da Mustafa marubucin shehu Usmanu, da mallam ishaqa da Mallam Mani da wasunsu.
  Sarkin musulmi Abubakar Atiku ne sarki na farko daya rasu yana dawowa daga yaki.
  Daga nan sarakunan Sokoto suka zaɓi Aliyu Babba ɗan Muhammadu Bello ɗan Shehu Usmanu ya zama sarkin musulmi.

SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 3

TARIHI: SARAUTAR SARKIN MUSULMI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na Uku.

Daga Sadiq Tukur Gwatzo, RN.

A farkon shekara ta biyar da hawan sarautar sarkin musulmi Muhammadu Bello yakai hari Kalabaina, ita kuwa kawa ve ga Sarkin Gobir Aliyu.
   A wannan yaki ne waba'i mai yawa ya auku, inda mabiyan Muhammadu Bello marasa adadi suka mutu.
  Acikin shekarar dai, anyi yaki da Azbinawa har sau biyu.
  Haka nan yayi yakin cinye Nabatsame, ya kuma yi yaki da Maraɗi a karo na biyu. Sannan kuma yakai yaki har Gawakuke.
   Akwai daga labarin yakinsa da Azbinawa, inda Sarkin su Ibra da Sarkin Gobir Ali da sarkin Katsina Randa suka gama kai tare dayin shawara a tsakaninsu, suka kudurci kawowa Sarkin musulmi Muhammadu Bello gagarumin hari.
  A lokacin sai suka shiga tattalin yaki, suka shafe watanni uku suna gayyatar dakaru daga sassa mabanbanta, har sai da suka haɗa gagarumar runduna.
  Sannan sarkin Azbinawa Ibra ya kwaso rundunarsa ya soma kawowa wasu garu-ruwan musulmi hari.
   Akan haka suka kwace garin Katuru, suka yi murna kwarrai da haka. Tsammaninsu sun hau hanyar da zasuyi galaba akan Muhammadu Bello ne, ashe kuwa tanadi Allah Ta'ala yayi musu.
   A lokacin kuma, sarki musulmi na zaune a Wurno ne.
  Don haka koda labari ya riskeshi, sai shima ya shiga shirin yaki babba, sannan ya fita daga wurno wata ranar juma'a bayan sallar jumu'a.
  Suka fara sauka a Giyawa suka kwana da safe sai gasu a Shinako, sannan suka karasa Lajingo suka kwana biyu.
   A cikin Lajingo ne ya haɗu da sarakunan garuruwan hausa na fulani da aka naɗa a gabas, a ciki har da Sarkin Kano Ibrahim Dabo, sun kawo ɗauki ga wannan yaki da za'a nufa.
   A wannan wuri kadirawa suka kulla alkawari gaban sarkin Musulmi cewa babu gudu babu ja da baya a wannan yaki, sai dai a mutu.
   Daga nan runduna ta tashi, babu wanda yasan adadin jaruman cikinta sai Allah.
   Sannu a hankali suka riski Randata, sannan suka karasa Buleci suka yada zango.
   Anan Buleci, Allah ya nuna karamar Sarki Muhammadu Bello, domin sun sauka ne akan wani tudu busasshe wanda babu komai akansa sai ciyayi marasa kyawu da kananun itatuwa
  A lokacin kuma yanayin zafi ne, don haka kishirwa ta dami mutanen wannan runduna.
   Tun ana jurewa har mutane suka fara galabaita, suka soma yanke kaunar rayuwa da tunanin mutuwa, don haka sai akai shawarar a sanar da sarkin musulmi halin da mutane suke ciki.
   Koda aka sanar masa, sai yace "kowannen ku yaje ya gina rijiya a inda ya sauka, insha Allahu zai samu ruwa aciki".
   Haka kuwa akayi, ruwa ya samu, akasha akayi girki aka baiwa dabbobi, sannan aka yi wanka.
 Farin ciki da karfin jiki ya dawowa mutane. Akayi ta mamakin karamar Sarki Muhammadu Bello.
   A wannan wuri sukayi kwanaki har zuwa daren sallar layya, sannan suka hau dawakai suka cigaba da tafiya, suka sauka a Riyojin Lema, suka yi sansani. Aka hana kowa hura wuta a cikin daren nan.
  Da safe suka zabura suka isa Tilla Gawakuke, nan ma sukayi sansani cikin shiri domin sun sani tanan ne Ibra zai fito musu.
   Daga kusan wucewar sa'a guda sai ga Ibra da sarkin Gobir Ali da sarkin Katsina Randa da rjndunoninsu sun iso.
   Rundunoni suka fuskanci juna kafin daga bisani yaki ya ɓarke a tsakaninsu.
   Ba a ɗauki lokaci ana fafatawa ba, sai ga Ibra ya ɗafe bisa ingarman dokinsa ya sheka da gudu tsakankanin tudunnai, bai waiwayi saurin kiran mai kira ba. Daga nan fa sai rundunarsu ta watse, kowa ya shiga gudun neman tsira.
   Rundunar musulmi suka bisu abaya suna kisan su.
 Anyi wannan abu ranar talata.
  Sarkin Musulmi Allah ya yarda dashi ya kwana biyu anan bayan yaki ya kare, sannan ya tashi izuwa Dutsen Zale, aka kama kafirai kamar dubu aka kashe su da yanka.
  Sa'ar nan ya hau ya nufi Gawon Gazau, musulmi sukayi sansani anan, suka kwana bakwai sannan suka kai hari ga Sarkaki suka ci galaba akanta.
   A lokacin nan, sai da takai musulmi suna kwana basu tsoron wani mutum kafiri ko guda ɗaya.
   Daga nan sai Muhammadu Bello yayi sallama da Sarakunan gabas yayi musu godiya suka koma garuruwansu, sannan shikuma ya tashi izuwa Lajinge, ya ɗanyi sauraro kaɗan, ya ɗora ɗansa Fodio mulkinta.
  Bayan nan, sai ya wuce izuwa Shinako, nan ma ya ɗora ɗansa Aliyu mulkinta, sa'ar nan ya koma wurno da zama.
   Da Sarkin musulmi ya sauka gida lafiya, sai ya gode Allah daya mai dashi gida lafiya, ya kumahori musulmi da kasancewa masu yawan tuba ga Allah..