Thursday, 28 December 2017

TARIHIN MAITAMA SULE DAN MASANIN KANO

MAITAMA SULE DAN MASANIN KANO

An haifi marigayi Yusuf Maitama Sule ɗan masanin kano a ranar 1 ga watan Oktoban shekara ta 1929 a birnin kano.
   An sa masa suna Yusuf ne, saboda sunan Mahaifin Madakin Kano Mahmudu, dom haka Madaki yana kiran sa da suna Abbana. Sunan Maitama kuwa an sanya masa shine sabili da Galadiman Kano Yusuf, saboda an yi amfani da makamai sosai lokacin yakin basasar Kano, don haka ake kiran duk wani Yusufu da suna Maitama.
  Madakin Kano ya yi wa Mahaifin Maitama, Abba Sule Danmuri, mukamin mai kula da dukkan al'amuransa na gida da kula da Dawakai.
   Maitama Sule na ɗan shekaru 4 mahaifiyarsa Hauwa wacce ake kira 'Yarkayi ta rasu. Ita kuwa Allah yayi tane mace mai ban dariya, mai raha, ba ta fushi, shi ya sa duk bukin da ya tashi ita ake kira ta yi ta magana a gidan buki, halinta da iya maganarta Maitama ya gado.
  Madakin Kano ya saka Maitama Sule a makarantar Elemantare ta Shahuci a cikin watan Janairu, 1937, dama tun kafin akai sa makarantar boko, suna yin karatun alkur'ani a gida.
   A ka'ida shekaru huɗu ya kamata ayi a elemantare, amma saboda hazakar da Maitama Sule ya nuna shekaru biyu kacal yayi aka bashi damar ɗaukar jarabawar zuwa midil.
  A wancan lokacin ne kuma Maitama Sule ya fuskanci kalubalen da bai taba fuskanta ba a rayuwarsa kasancewar a lokacin ne mai ɗaukar ɗawainiyarsa a rayuwa ya rasu cikin shekarar 1939. Aka bar kujerar Madaki, tsawon shekaru biyu, ba'a naɗa kowa ba, har sai a shekarar 1941.
  Bayan haka ta faru, sai Gaba ɗaya ɗawainiyyar Maitama Sule ta koma kan Mahaifinsa Abba Sule, wanda a wancan lokacin kuma ba shi da karfin da zai iya ɗaukarta. Sai da ta-kai Abba Sule, ya saida duk wani abunda ya mallaka har da suturunsa na sawa dan ya ɗauki ɗawainiyar 'ya'yansa, a lokuta da yawa haka suke kwana da yunwa.
  Ranar da suka samu ɗan abin taɓawa, a daren gasasshehen rogo ne za su ci su kwanta. A karshe Maitama Sule ya shiga makarantar Middle, a wannan datsen an kai matsayin da Maitama ko suturar da zai sa ba shi da ita, kayan makaranta kawai sune kayan sanyawarsa.
  A shekarar 1943 Maitama ya shiga kwalejin Kaduna, yana ɗan shekaru 13. Maitama, ya kammala karatunsa na kwaleji cikin shekarar 1948, ya kuma kama aikin Malanta, a makarantar Middle ta Kano.
  Maitama Sule ya tsaya zaɓen majalisar wakilai, yana takara da  tsohon Malaminsa a makaranta, watau Malam Aminu Kano, wannan zaɓe ya gudane a Central Office, wannan abu ya faru ne a 1954.
  Lokacin da aka faɗi sakamakon zaben Malamin, zaɓen ya bada sanarwar cewa Maitama Sule ne ya lashe wannan zaɓen.
 Ana fadar haka kuwa sai Mallam Aminu Kano, ya juyo ya cewa Maitama Sule: ina tayaka murna, saura idan kaje kuma ka ba mu kunya.
   Maitama Sule ya cewa Aminu Kano, "Yallaɓai wallahi, ba zan ba ka kunya ba". Suka riko hannun juna suka fito tare, wanda suka fara gamuwa da shi shi ne Ado Bayero, inda ya rike hannun Maitama Sule, ya nufi inda magoya bayansa suke, ya ce sun ci zaɓe.
   Maeigayi Maitama Sule Ya zama ministan tama da karafa a janhuriya ta farko. Sannan Bayan faɗuwar jamhuriya ta farko, ya dawo gida Kano, inda ya rike mukamin kwamishinamai kula da kananan hukumomi a gwamnatin Audu Bako. Ya rike mukamin shugaban hukumar sauraren koke-koken, jama'a ta kasa a gwamnatin Msrigayi Janar Murtala.
Yayin da a shekarar 1979 ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar NPN, sai dai Shehu Shagari ne ya lashe zaben.Har ila yau, gwamnatin Shagari ta naɗa shi jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya watanni bayan kammala zaben.
A can ne kuma ya jagoranci Kwamitin Musamman kan Yaki da Wariyar Launin Fata na majalisar, wanda masu sharhi ke ganin ba karamin matsayi ba ne.
  Hakazalika, bayan da Shugaba Shagari ya lashe zaɓe a shekarar 1983 ya sake nada Maitama Sule Minista Mai Kula da Tafiyar da Kasa, wato mai taimakawa shugaban kasa kan yaki da cin hanci.
  An taba ruwaito shi yana cewa: "Kowanne mutum yana da baiwar da Allah Ya yi masa. Allah Ya ba 'yan arewa kwarewa ne wajen shugabanci. Bayarabe wajen dogaro da kai da kuma kyawawan dabi'u. Igbo suna da baiwa wajen kasuwanci da kuma kere-kere. Allah Ya halicce mu daidai kuma kowa da baiwar da Ya yi masa."
Wasu sun yi amfani da wannan kalami nasa wajen bayyana damuwa game da yadda 'yan arewa suka mamaye fagen shugabancin kasar.
A shekarar 1957 gabanin Najeriya ta samu 'yancin kanta, marigayi Maitama Sule shi ne ya kewaya da Sarauniyar Ingila Elizabeth yayin da ta kai ziyara Kano yana yi wa jama'a bayaninta.
  A karshe, Ya rasu a watan yulin shekara ta 2017, ya bar 'ya'ya 10 - maza hudu, mata shida.
  Da fatan Allah yajikansa Amin

TARIHIN MALLAM AMINU KANO

MALLAM AMINU KANO

Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

An haifi marigayi jajirtaccen ɗan siyasa Mallam Aminu Kano a birnin kano,a shekarar 1920.
  Mahaifinsa Mallam Yuduf, muhuti ne a kotun Alkali dake kano.
  Mallam Aminu kano yayi elementare da midil ɗinsa duk a Kano, sannan ya samu gurbin karatu a kwalejin katsina, yayin da bayan gamawar karatunsa ya soma aikin koyarwa, har kuma lokacin da gwamnati ta baiwa wasu malaman makaranta a Nigeria gurbin karatu izuwa Ingila, ciki kuwa har dashi kansa.
  A wannan tafiya karo karatu zuwa ingila ne suka soma haɗuwa tare da abokantaka da Sir Abubakar Tafawa Balewa, sannan bayan dawowarsa gida Nigeria ya soma karantarwa a kwalejin Bauchi, inda anan ake ganin alaka ta haɗu tsakaninsa da Marigayi Mallam Sa'adu Zungur.
  Daga nan fa sai Mallam Aminu kano ya shiga rubuce-rubuce da wayar dakai dangane da karɓar yanci daga turawan mulkin mallaka da kuma sarakuna.
  Ance ya zama sakataren kungiyar malamai da Tafawa Balewa ya kafa kuma yake jagoranta mai suna 'Bauchi Discussion circle'.
  Ashekarar 1948, mallam Aminu Kano ya zamo shugaban Makarantar horas da malamai ta Maru dake sokoto, haka kuma ya zamo sakataren kungiyar malamai ta Arewacin Nigeria.
A wancan lokaci, yayi kokarin ɗaukaka darajar makarantun Allo na arewa don karantar da Alkurani ga Dalibai.
Haka kuma yana sokoto, ya shiga kungiyar siyasa ta Jamiyyar Mutanen Arewa, wadda daga baya ta sauya izuwa NPC.
   A shekarar 1950, mallam Aminu kano ya jagoranci wasu jama'a suka sauya sheka daga Jamiyyar Mutanen Arewa izuwa kafa sabuwar jamiyyar siyasa mai suna
 Northern Elements Progressive Union (NEPU).
  Wannan jam'iyya ta Mallam Aminu kano, tana kunshe da malamai da sauran mutane masu ra'ayin kawo sauyi a Arewa, irinsu Magaji Dambatta, Abba Maikwaru da Bello Ijumu.
 A zaɓen shekarar 1951, jamiyyar NEPU ta mallam Aminu kano ta tsaya takara a kano, kuma ta samu gagarumar nasara.
  A shekara ta 1954, mallam Aminu kano ya tsaya takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano amma baiyi nasara ba, inda Marigayi Maitama Sule Dan masanin kano ya kayar dashi zaɓe.
  Amma a Zaɓen shekara ta 1959, mallam Aminu kano ya sake yin  takara kuma yaci, inda ya zamo ɗan majalisar kasa mai wakiltar gabashin kano, har kuma a majalisar ya samu mukamin mataimakin bulaliyar majalisa, a lokacin jamiyyar Nepu da NCNC sun samar da haɗin kai ga juna.
   Bayan anyi juyin mulkin shekarar 1966, mallam Aminu kano ya cigaba da koyarwarsa da kuma gwagwarmaya kamar yadda ya saba, kuma bai sake rike mukamin gwamnati ba har sai da aka karɓe iko da gwamnatin Aguiy Ironsi, Janar Yakubu Gowon ya zama shugaban kasa da kakin soja, gabannin soma yakin Basasa kenan, sai aka naɗa Malla Aminu Kano kwamishinan Lafiya.
  Daga nan kuma ba'a sake sahale damar yin jam'iyyun siyasa ba sai bayan shekaru 12, inda gwamnatin Soja ta bada damar kafa jamiyyu a shekar 1978, anan ne Mallam Aminu Kano da Sam Ikoku, da Edward Ikem Okeke suka kafa jamiyar 'People Redemtion Party' PRP.
 A shekara ta 1979, jamiyyar PRP ta tsayar da Mallam Aminu Kano takarar shugaban kasa amma baiyi nasara ba, sai dai jamiyyar ta tsira da kujerar gwamnoni biyu.
  Tun a zamanin Jamhuriya ta farko, Mallam Aminu kano a matsayinsa na jagoran NEPU, shine ya jajirce wajen yaki da takurar Sarakuna ga talakawa. Domin kuwa ada, kowanne talaka sai ya biya haraji nasa, dana 'ya'yansa maza, da kuɗin kan ɗaki, da kuɗin sana'ar duk da yake yi, sannan kuma duk da cewa an daina cinikin bayi, amma akwai duddugen bautar da talakawa a lokacin daga sarakuna.
 Saboda haka,  Mallam Aminu kano da gudunmuwar du Tafawa Balewa da Saadu Zungur da wasunsu, ya shiga ya fita har aka hana sarakuna yin waɗannan aikace-aikace duk kuwa da irin tsana da tsangwama da mabiyansa yan Nepu suka sha.

 Hakika ba za'a taɓa mancewa da mallam Aminu kano ba matsawar ana batun baiwa mata 'yanci, da hana sarakunan mulki nuna karfi ga talakawansu da kuma kawar da bambancin kabilu tsakanin 'yan Arewa dama mutanen Nigeria baki ɗaya.
  Mallam Aminu kano shine ya tsaya kai da fata don ganin Jihar kwara ta faɗo yankin Arewa, bisa yadda ya gamsar da alumma cewar tarihin asalin tafkin kwara na Arewa ne duba daular da Shehu Usmanu ɗan fodio ya kafa wadda ta tsallaka har tafkin kwara.
   Daga nan kuma ya hori mabiyansa su zamo masu taskance tarihi don gudun asara a ragowar rayuwarsu, kamar yadda aka jiyo shi yana cewa
 "Matukar ba muyi tarihi ba
Matukar bamu rubuta tarihi ba,
 Matukar bamu zakulo mutanen mu na baya da sukayi aiki nagari ba,
  Zamu kasance muna lika Lambar LENIN data MAOTETUNG".

(Lenin shugaban rasha ne na lokacin, Mao kuma shugaban China. Don haka Mallam Aminu kano na nufin idan har mutum bai kiyaye tarihin ingantattun mutane acikin al'ummar saba, da sannu zai zamo yana kaunar shugabannin wasu al'ummar daba tasa ba).
  Allahu Akbar, akarshe Allah ya karɓi rayuwar Mallam Aminu kano ranar 17 ga watan afrilun shekara ta 1983, sa'ar da ake tsaka da kaunarsa. Kuma mabiyansa sun haɗu daga gsruruwa a kano, sunyi tattaki ɗauke da jan kyalle, don numa alhinimsu ga wannan rashi.
  Da fatan Allah yajikansa Amin.

TARIHIN MALLAM AMINU KANO

MALLAM AMINU KANO

Sadiq Tukir Gwarzo, RN.

An haifi marigayi jajirtaccen ɗan siyasa Mallam Aminu Kano a birnin kano,a shekarar 1920.
  Mahaifinsa Mallam Yuduf, muhuti ne a kotun Alkali dake kano.
  Mallam Aminu kano yayi elementare da midil ɗinsa duk a Kano, sannan ya samu gurbin karatu a kwalejin katsina, yayin da bayan gamawar karatunsa ya soma aikin koyarwa, har kuma lokacin da gwamnati ta baiwa wasu malaman makaranta a Nigeria gurbin karatu izuwa Ingila, ciki kuwa har dashi kansa.
  A wannan tafiya karo karatu zuwa ingila ne suka soma haɗuwa tare da abokantaka da Sir Abubakar Tafawa Balewa, sannan bayan dawowarsa gida Nigeria ya soma karantarwa a kwalejin Bauchi, inda anan ake ganin alaka ta haɗu tsakaninsa da Marigayi Mallam Sa'adu Zungur.
  Daga nan fa sai Mallam Aminu kano ya shiga rubuce-rubuce da wayar dakai dangane da karɓar yanci daga turawan mulkin mallaka da kuma sarakuna.
  Ance ya zama sakataren kungiyar malamai da Tafawa Balewa ya kafa kuma yake jagoranta mai suna 'Bauchi Discussion circle'.
  Ashekarar 1948, mallam Aminu Kano ya zamo shugaban Makarantar horas da malamai ta Maru dake sokoto, haka kuma ya zamo sakataren kungiyar malamai ta Arewacin Nigeria.
A wancan lokaci, yayi kokarin ɗaukaka darajar makarantun Allo na arewa don karantar da Alkurani ga Dalibai.
Haka kuma yana sokoto, ya shiga kungiyar siyasa ta Jamiyyar Mutanen Arewa, wadda daga baya ta sauya izuwa NPC.
   A shekarar 1950, mallam Aminu kano ya jagoranci wasu jama'a suka sauya sheka daga Jamiyyar Mutanen Arewa izuwa kafa sabuwar jamiyyar siyasa mai suna
 Northern Elements Progressive Union (NEPU).
  Wannan jam'iyya ta Mallam Aminu kano, tana kunshe da malamai da sauran mutane masu ra'ayin kawo sauyi a Arewa, irinsu Magaji Dambatta, Abba Maikwaru da Bello Ijumu.
 A zaɓen shekarar 1951, jamiyyar NEPU ta mallam Aminu kano ta tsaya takara a kano, kuma ta samu gagarumar nasara.
  A shekara ta 1954, mallam Aminu kano ya tsaya takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano amma baiyi nasara ba, inda Marigayi Maitama Sule Dan masanin kano ya kayar dashi zaɓe.
  Amma a Zaɓen shekara ta 1959, mallam Aminu kano ya sake yin  takara kuma yaci, inda ya zamo ɗan majalisar kasa mai wakiltar gabashin kano, har kuma a majalisar ya samu mukamin mataimakin bulaliyar majalisa, a lokacin jamiyyar Nepu da NCNC sun samar da haɗin kai ga juna.
   Bayan anyi juyin mulkin shekarar 1966, mallam Aminu kano ya cigaba da koyarwarsa da kuma gwagwarmaya kamar yadda ya saba, kuma bai sake rike mukamin gwamnati ba har sai da aka karɓe iko da gwamnatin Aguiy Ironsi, Janar Yakubu Gowon ya zama shugaban kasa da kakin soja, gabannin soma yakin Basasa kenan, sai aka naɗa Malla Aminu Kano kwamishinan Lafiya.
  Daga nan kuma ba'a sake sahale damar yin jam'iyyun siyasa ba sai bayan shekaru 12, inda gwamnatin Soja ta bada damar kafa jamiyyu a shekar 1978, anan ne Mallam Aminu Kano da Sam Ikoku, da Edward Ikem Okeke suka kafa jamiyar 'People Redemtion Party' PRP.
 A shekara ta 1979, jamiyyar PRP ta tsayar da Mallam Aminu Kano takarar shugaban kasa amma baiyi nasara ba, sai dai jamiyyar ta tsira da kujerar gwamnoni biyu.
  Tun a zamanin Jamhuriya ta farko, Mallam Aminu kano a matsayinsa na jagoran NEPU, shine ya jajirce wajen yaki da takurar Sarakuna ga talakawa. Domin kuwa ada, kowanne talaka sai ya biya haraji nasa, dana 'ya'yansa maza, da kuɗin kan ɗaki, da kuɗin sana'ar duk da yake yi, sannan kuma duk da cewa an daina cinikin bayi, amma akwai duddugen bautar da talakawa a lokacin daga sarakuna.
 Saboda haka,  Mallam Aminu kano da gudunmuwar du Tafawa Balewa da Saadu Zungur da wasunsu, ya shiga ya fita har aka hana sarakuna yin waɗannan aikace-aikace duk kuwa da irin tsana da tsangwama da mabiyansa yan Nepu suka sha.

 Hakika ba za'a taɓa mancewa da mallam Aminu kano ba matsawar ana batun baiwa mata 'yanci, da hana sarakunan mulki nuna karfi ga talakawansu da kuma kawar da bambancin kabilu tsakanin 'yan Arewa dama mutanen Nigeria baki ɗaya.
  Mallam Aminu kano shine ya tsaya kai da fata don ganin Jihar kwara ta faɗo yankin Arewa, bisa yadda ya gamsar da alumma cewar tarihin asalin tafkin kwara na Arewa ne duba daular da Shehu Usmanu ɗan fodio ya kafa wadda ta tsallaka har tafkin kwara.
   Daga nan kuma ya hori mabiyansa su zamo masu taskance tarihi don gudun asara a ragowar rayuwarsu, kamar yadda aka jiyo shi yana cewa
 "Matukar ba muyi tarihi ba
Matukar bamu rubuta tarihi ba,
 Matukar bamu zakulo mutanen mu na baya da sukayi aiki nagari ba,
  Zamu kasance muna lika Lambar LENIN data MAOTETUNG".

(Lenin shugaban rasha ne na lokacin, Mao kuma shugaban China. Don haka Mallam Aminu kano na nufin idan har mutum bai kiyaye tarihin ingantattun mutane acikin al'ummar saba, da sannu zai zamo yana kaunar shugabannin wasu al'ummar daba tasa ba).  
  Allahu Akbar, akarshe Allah ya karɓi rayuwar Mallam Aminu kano ranar 17 ga watan afrilun shekara ta 1983, sa'ar da ake tsaka da kaunarsa. Kuma mabiyansa sun haɗu daga gsruruwa a kano, sunyi tattaki ɗauke da jan kyalle, don numa alhinimsu ga wannan rashi.
  Da fatan Allah yajikansa Amin.

TARIHIN MARIGAYI SA'ADU ZUNGUR

MALLAM SA'ADU ZUNGUR

Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

  Mallam Sa'adu Zungur tsohon malamin makaranta kuma ɗan siyasa, sananne ne a duniyar adabi da gwagwarmayar hakkin talaka.
   An haife shi a garin Bauchi, a zuri'ar Limamin Bauchi cikin watan Nuwamban 1914.
Ya kasance mutum mai matukar kaifin basira, hazaka da hangen nesa.
Shine dan arewa farko da ya fara fita daga lardin arewa zuwa wuri don neman ilmi. A 1934 ya tafi Yaba College a Lagos.
Shine kuma dan arewa na farko daya fara rike mukamin siyasa, lokacin da ya zama Sakataren jam'iyyar NCNC a shekarar 1948.
A tarihi Mallam Sa'adu Zungur ne ya fara rubuta korafi ga turawa, yake bayyana musu rashin gamsuwarsa da yadda ake tafi da harkokin gwamnatin arewa ta wancan lokaci.
  Mallam Sa'adu zungur Amini ne ga Marigayi Mallam Aminu Kano, kuma shine wanda ya kafa Jamiyyar Mutanen Arewa, wadda su Ahmadu Bello da Aminu kano suka shiga kafin ta sauya izuwa NPC.
A lokacin rayuwarsa ya wallafa wakoki na wa'azi da jan hankalin al'umma, musamman mutanen arewa.
Allah yayi masa rasuwa a 1959
  Ga wakar Arewa Jamhuriya ko Mulukiya daya rera:-

“Matukar a arewa da karuwai,
yan daudu dasu da magajiya.
Da samari masu ruwan kudi,
Ga mashaya can a gidan giya.
Matukar yayan mu suna bara,
Titi da Loko-lokon Nijeriya.
Hanyar birni da na kauyuka,
Allah baku mu samu abin miya.
Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu mai tanyonsu da dukiya.
Babu shakka yan kudu zasu hau,
Dokin mulkin Nijeriya.
In ko yan kudu sunka hau,
Babu sauran dadi, dada kowa zai
sha wuya.
A Arewa zumunta ta mutu,
Sai karya sai sharholiya.
Camfe-camfe da tsibbace
tsibbacen,
Malaman karya yan damfara.
Sai karya sai kwambon tsiya,
Sai hula mai annakiya.
Ga gorin asali da na dukiya,
Sai kace dan annabi fariya.
Jahilci ya ci lakar mu duk,
Ya sa mana sarka har wuya.
Ya sa mana ankwa hannuwa,
Ya daure kafarmu da tsarkiya.
Bakunan mu ya sa takunkumi,
Ba zalaka sai sharholiya.
Wagga al’umma mai zata yo,
A cikin zarafofin duniya.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya ,
Zaya sha kunya nan duniya “.
“Mu dai hakkin mu gaya muku,
Ko ku karba ko kuyi dariya.
Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.
Gaskiya ba ta neman ado,
ko na zakin muryar zabiya.
Karya ce mai launi bakwai,
ga fari da baki ga rawaya.
Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.
Marigayi Sa’adu Zungur a cikin
waken sa mai suna “
Arewa Jamhuriya ko Mulukiya”.

Wednesday, 27 December 2017

TARIHIN SIR ABUBAKAR TAFAWA BALEWA

7. SIR. ABUBAKAR TAFAWA BALEWA

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

  An haifi marigayi firimiyan ƁNigeria na farko watau Abubakar Tafawa Balewa a garin Tafawa Balewa na Bauchi, a shekarar 1912.
   Mahaifinsa Yakubu ɗan Zala ya fito me daga kabilar Bagire, kuma shine dagacin Lere.
  Tafawa Balewa ya soma karatun alkur'ani dana boko a Bauchi, koda yake ance yaje katsina karatu, daga bisani ya samu gurbin karatu a Kwalejin Barewa ta zaria, yana kammalawa kuwa aka bashi shaidar malinta inda ya dawo Makarantar Midil ta Bauchi ya soma koyarwa.
  Tafawa Balewa ya samu gurbin tafiya Ingila karo karatu tare dasu Mallam Aminu kano, inda ya samo shaidar Malanta na koyar da Tarihi acan, sannan ya dawo gida.
  Da dawowarsa kuwa sai ya zamo wakilin turawan mulki masu kula da makarantu, alokacin kuma an ruwaito yana cewa ya gano yadda rayuwa take tafiya a turai cikin 'yanci da walwala, kuma ya haɗu da mutane masu bin doka ba tare da tsoron komai ba, don haka yana kallon Nigeria da wani yanayi na daban.
  A lokacin ne ya soma kafa kungiyar malamai ta Bauchi, inda suke tattauna hanyoyin samar da cigaba, daga bisani kuma ya tsaya takara kuma yaci zaɓen ɗan majalisar wakilai na Arewa a shekarar 1946.
  A majalisar Arewa suka haɗu da Ahmadu Bello har kuma suka kafa jamiyyar 'Northern People's Congres' watau NPC.
   A shekarar 1952 tafawa Balewa ya zama ministan aiyuka, daga baya kuma ministan sufuri.
 A shekarar 1957 aka naɗa shi babban minista, sannan kuma bisa haɗin guiwar jamiyyarsa ta NPC da jam'iyyar Nnamdi Azikwe, Tafawa Balewa ya zamo Firimiyan Nigeria na farko bayan karɓar 'yancin kai a shekarar 1960. Kuma ya sake tsayawa takara a shekarar 1964 ya lashe zaɓe.
  Ana yiwa Tafawa Balewa lakabi da 'Golden Voice', saboda nasibinsa wurin iya zance da gamsar da mutane. Kuma a wancan lokacin, ya zamo fuskar Afirka, domin yayi aiki tukuru wajen haɗa alaka tsakanin Nigeria da kasashen Afirka, da kuma warware matsaloli tsakanin Kasashen Afirka. Sannan ya cusa 'yan Arewa da dama acikin kunshin mukaman Gwamnatin tarayya.
  Akarshe, lokacin Juyin mulkin 17 ga watan janairu na shekarar 1966, ance wasu sojoji su biyar sun kutsa kai gidan sa inda suka sace shi.. Daga baya kuma aka tsinci gawar sa.
   Da fatan Allah yajiqansa Amin.

TARIHIN SIR AHMADU BELLO SARDAUNAN SOKOTO

5. SIR. AHMADU ƁBELLO SARDAUNAN SOKOTO

DAGA Sadiq Tukur Gwarzo RN.
  08060869978

 An haifi marigayi firimiyan arewa Ahmadu Bello a shekarar 1909  agarin Rabbar na gundumar Sokoto. Mahaifinsa Ibrahim Bello shine ke rike da sarautar Sarkin Rabbar, kuma jika ne ga mujaddadi shehu Usmanu ɗan fodio ta wajen ɗan Shehun watau Muhammadu Bello.
  Ahmadu Bello yayi karatun addini a gida, sannan ya tafi sokoto inda yayi makarantun boko acan.
 A shekarar 1931 bayan ya kammala karatu ya zamo malami mai koyar da turanci a makarantar Midil ta Sokoto.
  A shekara ta 1934 Sarkin Musulmi na lokacin Hassan Dan Mu'azu ya naɗa Ahmadu Bello dagacin garin Rabbar.
 A shekarar 1938 kuma aka kara masa matsayi a sarautance izuwa Dagacin gundumar Gusau wanda samu damar kasancewa ɗan majalisar sarkin Musulmi..
 Ahmadu Bello yana da shekaru 28  a duniya yayi yunkurin zamowa Sarkin musulmi bayan rasuwar Sarkin Musulmi Hassan Dan Muazu, amma bai samu dama ba, yayin da Sarkin Musulmi Abubakar Siddiq na uku ya zamo sarki wanda ya shafe shekaru 50 akan gadon sarauta.
   Sai dai, Sarkin Musulmi Abubakar na uku na hawa mulki, sai ya naɗa Ahmadu Bello Mukamin Sardaunan Sokoto, kuma babban mai baiwa sarki shawara.
   A shekara ta 1944 Ahmadu Bello ya shiga jam'iyyar siyasar nan mai suna 'Jam'iyyar Mutanen Arewa', wadda daga baya aka sauya mata suna izuwa 'Northern Progressive Congress', watau NPC. A shekarar 1948, Ahmadu Bello ya samu tallafin karatu na gwamnati, inda ya tafi Ingila karo karatu..
  Daga dawowarsa kasa Nigeria a wuraten shekarar 1951 sai aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar sokoto a majalisar Arewa, don haka sai ya dukufa aiki tare da sauran yan majalisu na sassan Arewa don ganin an ciyar da yankin Arewa gaba da kuma samar da zaman lafiya tsakanin kabilun Arewa.
  Abinda ya dukufa yi kenan har zuwa shekara ta 1952 da aka soma zaɓe a majalisar Arewa, inda Ahmadu Bello yaci,  ya zama ministan Aiyuka na yankin Arewa.
  A shekarar 1954 Ahmadu Bello ya zama firimiya na farko a jihar Arewa. A lokacin kuma shine shugaban babbar jamiyyar siyasa ta arewa watau NPC.
  A zaɓen 'yancin kai na shekarar 1959, Jamiyyar NPC da Ahmadu Bello ke shugabanta ce ta mamaye mafi yawan kujerun majalisar kasa, don haka sai tayi haɗin guiwa da  Dr. Nnamdi Azikiwe na jamiyar NCNC (National Council of Nigeria and the Cameroons) suka kafa gwamnatin tarayya ta farko wadda ta karɓo 'yancin kai daga hannun turawa a shekarar 1960.
  An nemi Ahmadu Bello a lokacin ya zama Firimiyan Nigeria, amma sai yaki, ya mika kujerar ga mataimakinsa Sir Tafawa Balewa, (wanda a baya shima ya sahale masa zamowa shugaban NPC domin samun goyon bayan talakawa da sarakunan Arewa kasancewarsa ɗan sarauta) shikuma Ahmadu Bello ya cigaba da zamansa a matsayin shugaban (firimiyan) Arewa, yayinda Dr. Azikwe yake rike da matsayin shugaban kasa.
Daga cikin manyan abubuwan da Ahmadu Bello ya kawowa arewa na cigaba, akwai haɗin kai da son juna gami da zama lafiya a Arewa, sai kuma kamfanoni irinsu Northern Nigeria Development Corporation (NNDC), Bank of the North da kuma Northern Nigeria Investments Ltd (NNIL).
 A karshe, an kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji 'yan kabilar Ibo suka jagoranta.
  Da fatan Allah yajikanaa Amin.

Tuesday, 26 December 2017

TARIHIN ALH MUHAMMADU RIBADO

4.   ALH. MUHAMMADU RIBADO
  Sunan Tarka dana Muhammadu Ribadu ba bako bane ga dukkan tsohon ɗan siyasar Arewa, ko kuwa mai yawan sauraren hirar marigayi Maitama Sule ɗan masanin kano.
  An haifeshi a kauyen Ribaɗo, a shekarar 1909, mahaifinsa Arɗo Hamza shine dagacin garin Balala dake Gundumar Yola ta ta tsohuwar jihar Gongola kafin daga bisani a kirkiri jihar Adamawa.
   Yayi karatun addini a tsangayar Liman Yahaya dake kauyensu, sannan daga baya ya soma karatun boko, inda ya soma da Makarantar elementare, sannan midil daga shekarar 1920 zuwa 1926.
  Bayan ya kammala karatun midil, daga baya ya samu aikin koyarwa ga 'ya'yan turawan mulkin mallaka a gidajensu, da kuma a makarantar midil ɗin daya kammala dake yola.
   Haka kuma, da mahaifinsa ya rasu a shekarar 1936, sai ya gajeshi a matsayin dagacin Balala.
  A shekarar  1946 ya samu tallafin karatu zuwa turai, don haka bayan ya dawo gida sai ya kamu da sha'awar siyasa, inda ya tsaya takarar ɗan majalisar arewa a shekarar 1946 yaci, ya kuma sake cin zaɓe a shekarar 1951.
  Tun a wajajen shekara ta 1948, Allah ke ta ɗaukaka matsayin Muhammadu Ribaɗo da mukamai daban-daban a tarayyar Nigeria, domin kuwa ya zamo ɗan kwamitin tabbatarwa da 'yan Nigeria manyan mukaman kasa tun zamanin da aka soma shirye shiryen karɓar yancin kai.
Haka kuma ya zamo wakili a kwamitin Noma na Nigeria, da kuma mamba a kwamitin bada lamuni domin ciyar da Arewa gaba.
  A shekarar 1950 kuwa sai ya samu zama memba a kwamitin gyaran kundin tsarin mulki a Ibadan.
   A shekarar 1952, aka zaɓi Alh Muhammadu Ribaɗo a matsayin ɗaya daga cikin 'yan kasa akunshin ministoci, inda ya zama Ministan Albarkatun kasa na Nigeria.
   A shekarar 1954 kuma, sai aka zaɓe shi a matsayin mataimakin shugaban jamiyar NPC na biyu, yayin daya zamo shine na uku a shugabannin Arewa idan ka fara lissafawa daga Ahmadu Bello shugaban NPC ɗin, da kuma Tafawa Balewa mataimakin shugaban NPC na farko.
  Alh Muhammadu Ribaɗo ya sake zamowa ministan Kasa, Albarkatu da makamashi a shekarar 1954, sannan ya zama ministan Kasa da Fannonin Birnin Tarayya dake Lagos a wanzan zamani a shekarar 1956.
  A shekarar 1960 kuwa Muhammadu Ribaɗo ya zama ministan tsaro, a shekarar kuwa kowa ya sani aka karɓo 'yancin kan Kasa. Don haka shine ministan farko daya soma bunkasa rundunonin soji na kasar nan, tun daga kan rundunar sojin kasa, ruwa data sama, inda ya samar musu da kayayyakin aiki da kuma gina musu barikoki, ya kuma tabbatar da cewar 'yan kasa sun shiga aikin samar da tsaro.
   Ance abokansa a wancan lokaci suna masa lakabi da 'power of powers' Watau 'karfin karfafa', kuma har yanzu ana tunawa dashi a matsayin jajirtaccen ministan tsaro da ba'a taɓa samun kamar sa ba a kasar nan.
 A ranar da Allah ya karɓi rayuwarsa itace ranar ɗaya ga watan Mayun shekara ta 1965 da safe, a ranar kuwa an shirya bashi lambar girmamawa ne tare da firimiyan Nigeria Sir Abubakar Tafawa Balewa, da Kuma firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.
  Allahu Akbar, Alhaji Muhammdu Ribaɗo shine ya kafa ma'aikatar tsaro dake Kaduna, ya kafa  Makarantar horas da soji ta 'Nigerian Defence Academy' a  Kaduna da kuma mazaunin Soji na 'Second Recce Squadron' dake  Abeokuta.
  Kuma har zuwa yau, manazarta na kallon cewa idan da Allah ya kaddara cewar Marigayi Ahmadu Ribaɗo na raye har zuwa ranar 15 ga watan janairun 1966 da sam juyin mulkin da akayiwa su Tafawa Balewa da Ahmadu Bello bai samu nasara ba saboda basirar sa da jajircewarsa wajen samar da tsaro.. Haka kuma da matasan kasarnan basu samu kasar a yadda take ba yanzu.
  Hakika, Nigeria tayi rashin Gwarzon bafullatani mai jajircewa akan lamurori, kuma mutum mai kaffa-kaffa akan dukiyar jama'a.
  Bayan rasuwar Alhaji Muhammadu Ribadu a lagos, sai aka faɗaɗa gidansa ya shige cikin Dodan Barrack, inda shugabannin kasa na soji suka rinka zama tun daga shekarar 1967 har zuwa 1991 da aka komo Abuja.
   Da fatan Allah yajikamsa Amin.

TARIHIN SIR KASHIM IBRAHIM


2. SIR KASHIM IBRAHIM
   An haifi Marigayi Sir Kashim Ibrahim a Kauyen Gargar na gundumar Yerwa, wanda a lokacin shine babban birnin Maiduguri kafin a koma Borno.
 Ya soma karatun addinin sa a gida kafin daga baya mahaifinsa Ibrahim Lakanmi ya shigar dashi makarantar Borno provincial a shekarar 1922.
   Bayan shekaru uku, sai kuma ya samu gurbin karatu a kwalejin horas da ɗalibai ta katsina inda ya samu takardar shaidar malunta a shekarar 1929.
  Daga nan sai ya soma aiki a makarantar middle ta Borno a wannan shekara, a hankali yana samun girma da karɓuwa a wurin jama'a, har zuwa lokacin data kai aka bashi lakabin Shatiman Borno a shekarar 1933. Aka soma kiransa da Shattima Kashim.
 Ya soma siyasa ne a shekarar 1951-52, sanda aka zaɓeshi a matsayin wakili na majalisar arewa, daga nan kuma aka tura shi wakilci izuwa majalisar kasa daga Arewa.
   Ya zama wannan wakili babu jimawa sai kuma akayi masa naɗi izuwa Ministan walwala, sannan ya koma ministan Ilimi daga baya.
A shekarar 1956, aka yi masa mukamin Wazirin Borno, haka kuma ya samu zamowa Gwamnan Arewa ɗan arewa nafarko a shekarar 1962 kuma yana rike da wannan mukamin akayi juyin mulkin ranar 16 ga watan janairu na shekarar 1966 wanda Major Janar Aguiyi Ironsi ya zama shugaban kasar tarayyar Nigeria.
   A lokacin da akayi juyin mulki aka kashe manyan mutane daga arewacin Nigeria, sai aka garkame Sir Kashim Ibrahim a kurkuku, amma daga bisani aka sake shi, ya koma gidansa a maiduguri, ya sadaukar da mafi yawan gidan ga makaranta, sannan bai tsira da komai ba sai kuɗi kaɗan da gidansa da mota ɗaya ta hawa, kuma tun daga nan bai sake komawa harkar siyasa ba.
 Sir Kashim Ibrahim ya rike matsayin Chancellor na  University of Ibadan daga 1966 zuwa 1977, haka kuma ya sake zama chancellor na University of Lagos daga 1977 zuwa 1984.
 Kafin rasuwarsa a ranar 25 ga watan yulin 1990 sai daya shigar da gwamnatin tarayya kara saboda ta hanashi Fanshonsa na Gwamnan arewa domin ya samu abin taɓawa, kuma ya zamo abin so da alfahari ga kowa saboda gaskiyarsa da kiyayewa daga satar kuɗin jama'a tayadda aka rinka saɓyawa jarirai sunansa.
  Haka kuma marubuci neshi, tunda ya wallafa littattafai biyu a zamanin rayuwarsa masu suna 'Teachers guide to Arithmetic' na ɗaya zuwa na huɗu da harshen kanuri. Da kuma 'Kanuri reader for elementary school'.
  A karshe, rayuwarsa abar koyi ce ga dukkan matasa saboda yadda ya sadaukantar da kansa ga gina arewa da kuma irin nasarar daya samu a rayuwa.
  Shine sir Kashim, wazirin Borno, Order of Nigeria, Order of british empire, LLD's.
  Da fatan Allah yajikansa Amin.

TARIHIN HASSAN USMAN KATSINA

3. HASSAN USMAN KATSINA
An haifi marigayi Hassan Usman Katsina a birnin Katsina a shekarar 1933. Shi ɗane na uku ga marigayi Sarkin Katsina Usmanu Nagoggo ɗan Muhammadu Dikko.
   Ya soma makarantar elementare a garin Kankia, sannan yayi makarantar Midil a birnin katsina. Inda daga nan ne ya samu damar shiga kwalejin Barewa dake zaria.
   Bayan ya kammalata kuma ya shiga Makarantar Nigerian school of Arts and Sciences dake nan zaria, sannan ya shiga aikin soja a shekarar 1956.
  Marigayi Hassan Katsina ya shiga aikin soja cikin nasara, duba da yadda ya rinka samun ɗaukaka akai-akai da kuruciyarsa da kuma damarmakin karo karatu, a cikin haka yayi karatu a makarantun the Royal officer training school Ghana, the Mons Officer Cadet School  da the Royal Military Academy Sandhurst inda akace anan abota ta haɗu tsakanin sa da Iliya Bisalla.
   Ya zama laftanal kanal a shekarar 1966, wanda daga nan akayi masa mukamin Gwamnan Arewacin Nigeria a shekarar 1966 bayan hamɓarar da Gwamnatin Su Ahmadu Bello Sardaunan sokoto. Don haka shine gwamnan arewa na biyu ɗan Arewa bayan Sir Kashim Ibrahim.
   Zamowarsa Gwamna a wannan lokaci wayau ne nasu Major Chukuma Kaduna waɗanda akace sune suka kashe su Tafawa 'Balewa, domin samun karɓuwa daga 'Yan Arewa bayan sun karɓi mulkin kasa.
 Don haka sai sukaga cewa Kasancewar Hassan Katsina ɗan Sarauta ne, bashi mulki zai sanya aminci a zukatan sarakuna da talakawan Arewa.
  Watanni goma sha shidda da soma mulkinsa sai akayi jahohin Arewa, inda aka fitar da Jihar Kano, Kaduna, Arewa ta tsakiya da Arewa ta Kudu, a wancan lokacin sai aka karawa Hassan Usman girma a aikinsa na Soja
  An naɗa shi mukamin Army chief of staff daga shekarar 1968 zuwa 1971 sannan ya samu daɗin girma daga shugaban kasa na lokacin Gen. Yakubu Gowon bayan hamɓarar da Major Aguiy Ironsi kenan izuwa mukamin 'Deputy Chief of staff supreme military headquarters'.
  Haka kuma yana da  mukamin Major-General aka naɗa shi Federal commissioner of establishment na tsawon shekaru biyu sannan da kansa ya ajiye aiki watanni biyu bayan kisan Janar Murtala Muhammad a wani juyin mulkin da baiyi nasara ba, zamanin Ulusagun Obasanjo kenan ke kan mulki da kakin soja, a ranar 29th na yulin 1975.
   Tun daga nan kuma ya dawo gidansa na Kaduna da zama, kuma bai sake karɓar wani mukamin gwamnati ba duk kuwa da tayin da shugabanni suka rinka yi masa, sai dai ya bada gudunmuwa wajen kafa jam'iyyun Siyasa.
 Kafin rasuwarsa a ranar 24 ga watan yulin 1995, shi shahararren ɗan wasan Polo ne, kuma ya rike sarautar Chiroman Katsina har zuwa mutuwarsa.
  Haka kuma, tun kafin rasuwarsa wasu mutane suka rinka jefa masa zarge-zarge na laifukan soji. Misali, wasu Inyamurai na ganin ya tsanesu kuma dasa hannunsa akayi musu kisan kare dangi a Arewa a zamanin yakin Basasar kasa, wasu kuma na kokarin shafa masa bakin fentin cewa dashi aka kashe Sardauna.
   Sai dai a zahiri, duk manyan Abokansa sun karyata haka, bisa hujjar cewa ADC ɗinsa ma Inyamuri ne, kuma bashi da hannun kitsawa su sardauna juyin mulki, an ɗauko shine kurum domin a nemi soyayyar 'yan arewa bayan juyin mulki.
   Ance tun bayan shekarar 1993, ba'a sake ganin Marigayi Janar sani Abacha tare da Janar Ibrahim Babangida a wuri ɗaya a wani taro ba sai lokacin mutuwar Marigayi Hassan Usman Katsina, inda mutane da yawa suka haɗu bisa jimamin rashinsa.
  Kuma an sanyawa wurare da dama sunansa a yankin Arewa domin tunawa dashi, mksali shune Hassan Usman Polytechnique.
  Da fatan Allah yajiqansa Amin
   

Sunday, 24 December 2017

TARIHIN SARKIN BORNO MAI IDRIS ALOOMA


1. Mai Idris Alooma

Sarkin Borno Mai Idris Alooma shahararren sarki ne wanda sunan sa bazai shafuba a tarihin sarakunan duniya ballantana wannan yanki na Arewa.
  Ance ko dai yayi mulki tsakanin shakara ta 1571-1603 ko  1580-1616, ko kuma wasu shekaru kusa da haka.
   Haka kuma, ana cewar shine sarkin Borno na 15, yayi yakuna sama da guda dubu ɗaya a tsawon rayuwar sa ta mulki, a ciki ya samu nasara a yakuna 330 kamar yadda tarihin wasu yakunan yazo a littafin 'Gazwatu Borno' na marubucin sarkin mai suna Ahmad Al Furtu.
 Mai Idris Shine wanda ya soma samarwa da dakarunsa hulunan sulke na bakin karfe domin yin yaki kamar yadda manyan masarautu irinsu misira da girka suka daɗe dayi.
   Haka kuma, ya horas da dakarunsa da dabaru kala kala, domin kuwa ya ware dakaru masu kai farmaki a jirgir ruwa, ya ware dakaru masu kai harin sari-ka-noke, sannan ya ware rundunar dakaru 'yan lifida.
   Ance a lokacin mulkinsane aka turo wakilai ɗari biyu daga masarautar Ottoman ta Turkiya izuwa babban birnin Borno da yake a Ngazargamu a wancan lokaci domin kulla alaka tsakanin masarautun biyu.
  Haka kuma kasancewar sa musulmi, babban abinda yayiwa daular Borno a musulunce shine masallatai daya gina domin haɓaka ibada da kuma koyar da addini.
  Sannan Hakika, Mai Idris Alooma ya haɓaka tattalin arzikin daular borno, ya haɓaka kasuwanci, tunda ance har kasashen larabawa ake turawa da goro, siliki, da auduga da sauran kayayyaki daga masarautar borno.
  Sannan ya samar da tsaro, yayi yaki domin faɗaɗa masarautarsa, kuma hakika ya samu nasara gagaruma a zamaninsa.
  A zamanin mulkinsa, daular Borno ta faɗaɗa har izuwa Fezzan ta kasar Libya daga Arewa, sannan ta shigo kasar Hausa daga Yamma, hakanan yacinye kabilun Bulala da wasu masarautu a Gabas.
 A karshe, ance ya rasu a wurin yaki bayan anyi masa jina-jina a gefen wani tafki mai suna Alao. Acan kuma akace an binneshi, don haka ake tsammanin Alooma ya samo asali ne daga inda kabarinsa yake.

MA'ADINAN DAKE AREWA 2

3. AMFANI DA YADDA ZA'ACI MORIYAR MA'ADINAN AREWA.

Da yake ma'adinan suna da tarin yawa, sai dai mu zaɓi wasu mu faɗi amfaninsu da yadda za'aci gajiyarsu.
    1. Petroleum.
 Danyen mai kenan, wanda daga gareshi ake fitar da kusan duk wani nau'in mai da injina ke amfani dashi, ake fitar da wasu nau'ikan robobi, magunguna da kayayyakin bukata.Hak'o ɗanyen man fetur a yankin arewa (misalin Maiduguri) zai baiwa yankin damar dogara da kansa da haɓakar tattalin arziki. Tunda Za'a samar da kamfanonin hako mai dana tacewa na gwamnati da masu zaman kansu waɗanda zasu ɗauki ma'aikata don samar da aikin yi, sannan kuma siyar da ɗanyen mai a kasuwannin duniya zai kawowa yankin kuɗin shiga daga kasashen waje, zai kuma inganta sufuri, haɓaka masana'antun mu na gida gami da saukaka farashin man fetur a yankin arewa.
   2. Coal. (Kwal)
 Kasar Amurka ta lissafa shi a matsayin abu na ɗaya da harkar tsaron kasarta ta dogara dashi. Saboda ance ana iya fitar da kayayyakin masarufi sama da dubu ɗaya a jikinsa.
 Misalin su shine, sinadaran da kamfanonin takadda, pensiri, wutar lantarki, kwalta da alminiyon duke amfani dashi.
  Bentunite:
Wannan wata Wata turɓaya ce da ake fitar da magunguna daga cikinta, ake yin kayan kwalliya kuma da ita.
 Hakota inganta samar da ita a yankin Arewa zai rinka samarwa yankin kuɗin shiga daga kasuwannin duniya, zai kuma inganta harkar lafiya.
  Gypsum.
 Wannan Dangin wasu duwatsu ne masu daraja da ake ado na k'awa dasu da kuma magunguna cututtuka a kasashen da suke da cigaban ilimi.
 Misalin su ya haɗa daDiamond, Emerald, Ruby. Dukkandu abubuwa ne masu daraja da k'asa guda na iya dogara da fataucin su.
   Gypsum:
Wannan shine Sinadarin da ake bukata wajen samar da siminti.
  Kamfanonin siminti ma Adhaka dana Sokoto dukkansu sun dogara ne da wannan sinadari.
  Don haka inganta samar dashi na nufin inganta samar da kamfanonin gine-gine, da yalwatar aiyukanyi da kuma saukin muhalli.
   Irom ore.
Daga wannam ma'adini ake samar da k'arafa, waɗanda ake amfani dashi don gina duk wani abu na karfe.
  Zinc/Lead.
Suma waɗannan ma'adinai suna da matukar daraja a kasuwannin duniya. Domin dasu akeyin Harsashi, Talbijin, ceramics da sauransu.
  Uranium
Makamashin da ake sarrafa mkaman kare dangi dasu kuma ake kafa tashar samar da wutar lantarki gagaruma dashi.
   Kasancewar wannn sinadari nada matukar daraja, inganta sarrafa shi zai samar da abubuwan bukata gagarumai ga yankin Arewa.
  Gwal
 Yana zube a kasashen Kano, Zamfara, Niger da wasunsu.
  Shi abune mai matukar daraja da ake dillanci a duniya.
  Matsayinsa kamar na kuɗi ne.
Inganta samar dashi tamkar kafa injin buga kuɗi ne a Wannan yanki na Arewa.

   4. KAMMALAWA
  Hakika akwai babban kalubale dake fuskantar kasarmu, musamman wannan yanki namu na Arewa.
  Kusan a kwanakin nan, duk mun saida yadda ane hako Gwal da wasu ma'adinai masu daraja a yankunan mu, amma gwamnati ta zubawa abin ido ga 'yan kasuwa waɗanda basu da manyan kayan aikin hako waɗancan ma'adinai tare da inganta su.
   Saoda haka, munaganin lokaci yayi da kodai gwamnatocin Arewa zasu mike tsaye don ganin sun kafa kamfanonin da zasu rinka hako ma'adinai tare da fataucinsu a kasuwannin duniya don inganta hanyoyin kuɗin shiga ga yankin da kuma samar da ayyukan yi, ko kuma ayi tsare-tsare masu inganci da zasu baiwa 'yan nasuwa hamshakan kafa kamfanonin, koda kuwa bisa tallafin 'yan kasashen waje ne, eomin daga karshe Al'ummar Arewa ne zasu fi cin moriyar abin.
  Da fatan Allah ya inganta arzikin wannan yanki namu na Arewa, Allah ya bamu shuwagabanni nagari, ya kuma wanzar mana da zama lafiya Amin.

  5. MADOGARA

-1. Fagg, Bernard. 1969. Recent work inwest Africa: New light on the Nok culture.World Archaeology 1(1): 41–50.2.^Duncan E. Miller and N.J. Van

2. Godwin Chukwudum Nwaobi."The Nigerian Coal Corporation: An Evaluation of Production Performance (1960-1987)"(PDF). Quantitative Economic Research Bureau. Archived fromthe original(PDF)on 2011-05-28. Retrieved2008-04-12.

3. Bode George. Geology and Mineral Resources of Nigeria (2009).

MA'ADINAN DAKE AREWA 1

MA'ADINAN DAKE AREWA.





      DAGA
 SADIQ TUKIR GWARZO
   08060869978
http://sadiqtukurgwarzo@blogspot.com




ABUBUWAN DAKE CIKI
1. GABATARWA
2. MA'ADINAN DAKE AREWA
3. AMFANI DA HANYOYIN DA ZA'ACI GAJIYAR MA'ADINAN AREWA
4. KAMMALAWA.
5. MADOGARA





1. GABATARWA

 Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala wa Barakatuhu.
 Hakika, Allah Ta'ala ya albarkaci yankin Arewacin Nigeria da tarin ma'adinai madu ɗumbin daraja da amfani ga tattalin arziki gami da ingantuwar lafiyar al'umma.
   Tarihi ya nuna cewar akwai tsoffin yankuna a Arewa waɗanda ke ɗauke da mutane tun kimanin sama da shekaru dubu biyu da suka gabata, wanda hakan ba komai ke nuna mana ba illa albarkar wannan yanki tun a tsawon zamani, wanda ya sanya mutanen-Da sukan baro yankunansu domin zuwa yankin da a yanzu ake kira arewa domin samun wurin zama mafi inganci, ko kuma farautar abin masarufi.
   Misali, . A shekarar 1943 an samu wasu burbushin katakwaye da burbushin tukwane a wani Kogon dutse dake garin 'Samun dukiya' na k'aramar hukumar Jaba ta jihar Kaduna. Masana sun auna jimawar kayayyakin da aka samu, sun kuma yi hasashen daɗewar su ta riskar wa shekara ta 1000 kafin zuwan Annabi Isa A.S..
 
    Haka nan, an samu wasu sassak'en mutum-mutumai da tukwane gami da wata guntuwar wuka da aka k'era da k'arfe a wani yanki mai suna 'Taruga' dake kusa da k'auyen 'Takushara', kimanin nisan kilomita sittin a kudu maso gabashin birnin tarayya Abuja.
    Akwai maganar Samun wani mutum-mutumin kuma da wasu ɓuraguzai a garin 'katsina Ala' dake jihar Benue.
  Masanin akiyoloji Bernand Fagg Evelyn yayi hasashen mutum-mutumin siffar mutanen da suka gabaci mutanen ne, ko kuma siffar iskokai (aljannu)  ake nufi dashi.
    Haka dai, An samu wasu alamomin rayuwa a garin Jos waɗanda wanzuwan shekarun su ya tasamma shekara ta dubu ɗaya kafin aiko Annabi Isa A.S. Masana da yawa sunyi hasashen waɗancan mutane da suka zauna a tsohuwar Jos, da kuma wasu shigen su da akaga alamun su akan dutsen Kwatarkwashi dake Yankin Zamfara a yau, shekaru dubu uku da suka gabata, Sune asalin zuriyar da k'abilun Hausa, Birum, kanuri, Nupe da Jukun suka samo tsatso daga garesu.
 
  2. MA'ADINAN DAKE AREWA

Kalmar Ma'adinai bisa tsarin masu ilimin tsimi da tanaji na nufin duk wani abu mai daraja wanda ake samu daga k'asa.
   Ma'anar kalmar Ma'adinai ta haɗar da duwarwatsu masu daraja dangin lu'u-lu'u, tama da karafa, da sauran ɗumbin abubuwa masu amfani da Allah yayi tanaji a k'ark'ashin k'asa.
  Zuwa yanzu, kimanin Ma'adinai dubu biyar da ɗari biyu da talatin binciken kimiyya ya gano
 (March 2017, International Mineralogical Association(IMA), kuma kowanne kala akwai yankin da akafi samunsa daga yankuman duniya tundaga sassan Turai da Asia har zuwa nan Afirka.
   Yankin Arewa ma ba abarshi a baya ba, domin Allah ya ajiye mata ma'adinai masu tarin yawa da daraja, bisa wata hikima da masanan falsafa suka gano wadda arewatawa basu ankare da ita ba.
 Wannan hikima kuwa itace:-  Kasancewar kusan kowacce k'asa anan duniya, tana dogaro ne da ma'adinan k'asarta, sai masana falsafa ke ganin Allah na baiwa kowacce al'umma ma'adinai ne gwargwadon yadda zata dogara da kanta, ta ciyar da kanta gaba, kuma tayi maganin Matsalolin ta na rayuwa don ganin ta samu damar bauta masa maɗaukakin sarki.
  Saboda haka rashin sani ke sanya mu bacci da shagala har wasu ke kiran mutanen arewa da cima zaune, watau waɗanda suke dogaro da ma'adinai na yankunansu.
   Ni kuwa a fahimtata, waɗancan mutane suna da gaskiya.
  Domin mun ɗora buk'atun mu kachokan akan ma'adinan yankunansu alhalí muma Allah ya ajiye mana ma'adinan daya kamata mu zaro daga kasar mu, mu sarrafa sannan mu inganta tattalin arzikin mu da lafiyar jikinmu.
    Kamar yadda masana kimiyyar magunguna suke ganin kowacce cuta da Allah yakan jarrabi al'ummar wani yanki da ita, akwai bishiya ko tsirrai ko ma'adinai da za'a samu maganin wannan cuta a wannan yanki. To haka yake a hikimance game da ma'adinai, cewa akowacce matsala da Allah kan jarrabi alummar wani yanki, akwai ma'adinan da za'a sarrafawa domin magance wannan matsalar a wannan yanki.
   Ga wasu daga ma'adinan dake jibge a jihohin Arewa:-
1. ABUJA
-Marble
-Clay
ƳTantalite
-Cassiterite
-ƳGold (partially investigated)
– Lead /Zinc (Traces)
– Dolomite*
2..ADAMAWA STATE–
Kaolin– Bentonite– Gypsum– Magnesite*.
3. BAUCHI STATE–
 Amethyst (violet)–
 Gypsum–
Lead/Zinc (Traces)–
 Uranium (partially investigated)
*.4. BENUE STATE–
Lead/Zinc–
Limestone–
 Iron-Ore–
Coal–
Clay–
Marble–
Salt–
Barytes (traces)–
 Gemstones–
 Gypsum*.
5. BORNO STATE–
Diatomite– Clay– Limestone– Hydro-carbon (oil and gas) Partially investigated) cool– Gypsum– Kaolin– Bentonite
*.6. GOMBE STATE–
 Gemstone– Gypsum*.
7. JIGAWAA STATE–
 Butytes
8*.KADUNA STATE–
 Sapphire– Kaoline– Gold– Clay– Serpentinite– Asbestos– Amethyst– Kyanite– Graphite (partially investigated)– Selenite– Mica (Traces)– Aquamarine– Ruby– Rock Crystal– Topaz– Flopper– Tourmaline– Gemstone– Tentalime*
9. KANO STATE–
 Prrochinre– Cassiterite– Copper– Glass – Sand– Gemstone– Lead/Zinc– Tantalite- Gold
10. KATSINA STATE– Kaolin– Marble– Salt*
11. KEBBI STATE–
 Gold*
12. KOGI STATE–
 Iron-Ore– Kaolin– Gypsum– Feldspar– Goal– Marble– Dolomite– Talc– Tantalite*
13. KWARA STATE–
 Gold– Marble– Iron-Ore– Cassiterite– Columbite– Tantalite– Feldspar (Traces)– Mica (Traces)*.
14. NASARAWA STATE–
 Beryl (Emerald)– Aquamarine and– Heliodor)– Dolomite/Marble– Sapphire– Tourmaline– Quartz- Amethyst (Topaz, gamet)– Zircon– Tantalite– Cassiterite– Columbite– Lamanite– Galena– Iron-Ore– Barytes– Feldspar– Limestone– Mica– Cooking coal– Talc– Cay– Salt– Chalcopyrite
15. NIGER STATE– Gold– Talc– Lead/Zinc
16. PLATEAU STATE–
 Emerald– Tin– Marble– Granite– Tantalite/columbite– Lead/Zinc– Barytes– Iron-Ore– Kaolin– Belonite– Cassiterite– Pyrochlore– Clay– Coal– Wolfram– Salt– Bismuth– Fluoride– Molybdenite– Gemstone– Bauxite
17. SOKOTO STATE
Kaolin– Gold= Limestone– Phosphate– Gypsum– silica-sand– Clay– Laterite– Potash– Flakes– Granite– Gold– Salt
18. TARABA STATE–
Kaolin– Lead/Zinc
19. YOBE STATE–
 Tintomite– Soda Ash (partially Investigated)*.20. ZAMFARA STATE–
 Goal– Cotton– Gold

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU DAN FODIO 6

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU MUJADDADI, DAN FODIO.

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
     08060869978

Kashi na shidda.

YAKIN ALWASA
  Daga nan Sabon gari, Wazirin Shehu Usmanu Dan fodio watau Abdullahi, ya ɗauki runduna ya tafi kasar kabi da yaki, Allah kuwa ya bashi nasara, yaci garuruwa da yawa har ma aka kira yakunan da yayi da suna 'yakin ciye-ciye'.
    Daya komo sabon gari ya taradda sauran jama'a, sai suka tashi izuwa Bukkuyum, sannan suka yi Bunkasau, daga nan sukayi Felan, sai suka shiga Gazurra, sannan suka auka Margai, sai suka isa Rafin Samu, sai kuma gasu a Gwannu.
   Shi wannan yaki da ake kira na Alwasa, azbinawa ne da Gobirawa da sashen dakarun kasashen Hausawa, karkashin wannan babban sadaukin mai suna Abungulu, suka taru tare da nufo Shehu Usmanu da rundunarsa da yaki.
    Koda Rundunar shehu Usmanu ta samu wannan labari na yaki dake zuwa garesu, sai suka shiga shawara, wasu sukace a tashi aje a taryesu a gwabza yaki, wasu kuma sukace a dakacesu su karaso.
   A karshe suka sauraresu, runduna tazo har inda suke ta kafa sansani, sannan dakaru suka firfito, sashensu ya fuskanci sashe. Ba tare da ɓata lokaci ba aka shiga gwabza yaki.
   A wannan rana ma, hakika Allah ya jarrabci Shehu Usmanu ɗan fodio da rundunarsa, domin ance kimani mutane dubu ɗaya ne daga rundunarsa suka rasa ransu a wannan yaki.
   Sun fara gwabza yakin ranar lahadi ne, sannan litinin aka sake wani, talata ma haka, laraba ma akayi, aka sake wani ranar Alhamis..
  Shehu Usmanu yace da mutanensa "Da sannu Allah zai kunyatar da Abungulo".
  Ai kuwa sai da Allah ya taimaka, rundunar shehu Usmanu ta warwatsa wannan runduna, Abungulo da jama'arsa suka ɗai-ɗai ta, kuma bai sake dawowa da yaki ga rundunar Shehu Usmanu ba har Allah ya karɓi rayuwar Shehun.
   (Shi Abungulo buzu ne, sarkin kano Alwali ya sake gayyatarsa bayan ya kasa samun nasara a wancan yaki, ya bashi dawakai dubu huɗu da nufin yazo ya fatattaki masu jihadi na Kano ya kone gidajensu. Daga karshe ya haɗu da ajalinsa a wani yaki da suka gwabza da masu jihadi a Kano kusa da wani gari mai suna Tatarawa kamar yadda Qadi Muhammadu Zangi ya ruwaito a littafinsa Taqyidil Akbar)
    A shekara ta biyu da hijirar Shehu Usmanu akaci kano da yakin jihadi, aka naɗa malami adali Sulaimanu a matsayin sarkinta.
   Acikinta kuma akaci 'yandoto, wata shahararriyar alkarya mazaunar malumma.
   A shekara ta uku da hijira akaci katsina da yakin jihadi, aka naɗa Ummaru Dallaje sarki.
  Acikinta musulmi sukayi yaki da Borno, suka cinyeta, aka naɗa Mallam Zaki Kanuri shugaba, aka naɗa Mallam Yakubu shugaba a Bauchi, Mallam Ishaka a Daura, Mallam Buba yero a Gwambe, mallam Adama a Adamawa, da wasunsu kamar Larliru.
   A cikinta kuma ne Shehu Usmanu da jama'arsa suka sake kawowa Alkalawa babban birnin Gobirawa hari, amma ba'a samu damar cinye garin ba.
   Amma dai, acinkinta har ila yau akaci Mazauri da Kannu da yaki.
   A shekara ta Huɗu da hijirar shehu Usmanu aka samu nasarar cinye Birnin Alkalawa da yaki. A lokacin kuwa farkon shigar kaka ne, Muhammadu Bello ya fita yaki zjmuwa gareta, ya sauka a Lajingo, yayi kwanuka anan, sannan Ranar lahadi ya sauka kusa da alkalawa, ya kwana, da wayewar gari ya shiga yaki da Gobirawa, Allah kuwa ya buɗa masa ya shiga birnin Alkalawa, abinda a baya ya gagaresu.
   A wannan rana aka halaka sarkin Gobir Yumfa, aka kashe mazajensa da yawa, aka kama mahaifiyarsa mai suna Maitakalmi, sannan aka taso keyarta a gaban shehu Usmanu, sai dai kafin azo gareshi tuni har wani Aljani ya riskeshi da labarin wannan gagarumar nasara.
A shekarar ne dai akayi yakin Banna, aka kuma cinye Gandi dukanta. Aka naɗa Mallam Musa zazzau shugaba.
  A shekara ta biyar da hijirar Shehu musulmi suka ketare tafkin kwara da yakin jihadi, suka kafa dauloli acan.
  A shekara ta shidda da hijira shehu ya tashi daga Gwandu zuwa Sifawa da zama. A shekarar aka gina sokoto.
  A cikinta akaci Zabarma da yaki, da Gurma da Kasar Nufe, da kasar Gwari aka kamo sarkinsu a kukume aka tawo dashi Sifawa. A shekarar kuma akaci Borno dukanta.
    A shekara ta bakwai da hijira akayi yakin garin Kwatto, amma ba'a cishi ba, sai dai an samu ganimar yaki mai yawa da arziki a shekarar.
  A shekara ta takwas akayi yaki da Salihu ɗan Babari wanda ya abokanci azbinawa suka kawowa Jama'ar shehu hari.
A shekara ta tara da hijira Hamman ya fita daga Magunga yana cewa shi Mahadi ne, ai kuwa mutanen shehu Usmanu sukayi masa tsinke suka halaka shi.
   A cikinta Jelani ya Azabtar da Azbinawa da hare-hare, suka karɓi hukuncin abinda suka daɗe suna aikatawa ga Shehu da Jama'arsa.
   A shekara ta goma da hijira yakunan jihadi suka je har Bargu.
   A shekara ta goma sha ɗaya da hijira, shehu Usmanu ya baro Sifawa izuwa Sokoto da zama. Ya raya garin tare da mayar dashi shigifar musulunci.
A shekara ta goma sha uku Shehu Usmanu ya soma ciwon ajali.
  Ashekarar ne al'almarin Gagara ya auku.
  A shekara ta goma sha huɗu da hijira Allah ya karɓi ran limamin yakin jihadin tabbatar da Sunnah a kasashen hausa da makwabta, watau Shehu Usmanu mujaddadi ɗan fodio.
 Ya rasu ranar 3 ga watan jumada Auwal, 1232 bayan hijira.
  Da fatan Allah ya rahamsheshi Amin.
  Karshen Takaitaccen Tarihin Jihadi kenan.
 Sauran abinda zaizo bai wuce sanin Yadda sarautar sarkin Musulmi ta kasance ba da kuma gwagwarmayar Rikon sarauta.

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU DAN FODIO 5

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU MUJADDADI, DAN FODIO.

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
     08060869978

Kashi na biyar.

Kashe gari, musulmai suka sake fita jiran Sarkin Gobir da tawagarsa, suka fake tsakanin wasu duwatsu da ake kira Maliba.
  Can kuwa babu jimawa sai ga runduna ta iso gagaruma, sarkin Gobir na tsakiya ana buga masa tambari.
  Koda rundunonin suka fuskanci juna, sai suka aukawa juna da yaki.
  Yaki yayi tsamari, amma sai girgije ya haɗu a sama, aka soma zubda ruwa. Don haka kowa ya koma sansaninsa.
  Da ruwa ya tsagaita, sai kowa ya sake dawowa fagen fama, aka sake abkawa faɗa gagarumi.
A wannan rana, mabiya Shehu Usmanu ne sukayi rinjaye, sune kuma harda rarakar magoya bayan Sarkin Gobir Yumfa da gudu.
  Mutanen Sarkin Gobir dashi kansa suka sauka acan kusa da tafkin kwatto, Wazirin Shehu Usmanu, Abdullahi ya kwashi jama'a izuwa can, mabiyansa suka sha ruwa a tafkin kwatto sannan suka yi kabbara sau uku, suka afkawa Rundunar gobir da yaki.
  Koda rundunar Sarki Yumfa taga haka, sai suma suka suka bugi tamburansu, sannan suka ce dawa aka haɗamu ba daku ba, suka nufarwa mabiya shehu Usmanu da gudu makamai a zare. Kafin kace haka wani sabon yakin ya sake ɓarkewa.
  A lokacin kuwa, sai da aka yiwa Mabiya Shehu Usmanu ɗan fodio kawanya, dakaru dama da hagu, an sanya su a tsakiya, gashi kuma yakinsu yafi ga harbi, tunda dawakansu ance basufi ashirin ba. Su kuwa mabiya sarkin gobir dawakansu basa misaltuwa.
   Amma dai cikin ikon Allah, sai Allah ya warwatsa rundunar Sarki Yumfa tayi ɗai-ɗai.
  Sarkin da kansa yahau ingarman dokinsa ya arce zuwa garinsa, ya bar jama'arsa karkashin takubban mabiya shehu Usmanu, ya bar takalminsa da gadonsa na sarauta, da tamburansa da takobinsa da kayan goro da guzurinsa na alkaki da irinsu.
  Wani mawaki yayi baitin waka akan haka da cewa:-
  Yayi jifa da takardu dan Sassabtama taguwarsa.
  Da guzurinsa, har ma da 'yar sanda tai.
  A haka mutanen shehu Usmanu suka rabauta da gagarumar ganima a wannan waje.
  A cikin wannan shekara ta ɗaya dayin Hijirar Shehu Usmanu ɗan fodio, akayi yakin Mane.
  Sannan a shekarar ne Shehu Usmanu ya ɗauki tawagarsa izuwa Magabci, koda yake wasu sun ruwaito cewar kafin yabar yankin, sai da sukayi kokarin karɓe iko da Alkalawa babban birnin gobir, amma basu samu ikon haka ba, ga kuma yunwa ta damesu, don haka suka bar yankin.
  Acan magabci Shehu Usmanu ya rubutawa sarakunan Kasar Hausa takardu yana mai sanar musu dalilinsa na yin yaki da sarkin Gobir, tare da neman haɗin kansu da tallafinsu wajen yaki don tabbatar da musulunci bisa turbar gaskiya da kuma kawar da bidi'o'i.
   Sa'ar da Sarkin Katsina ya samu wannan takarda, sai ya keta ta. Yayi magana ta ɓatanci ga shehu da magoya bayansa.
  Sa'ar da Sarkin Kano kuma ya samu wannan takarda, sai bai keta taba, amma kuma bai amshi kiran shehu Usmanu ba.
   Amma sarkin Zazzau dana Rumo duk sun karɓi kira, sai dai kuma jama'arsu sun bijire a kaiwa shehu tallafi.
   Shehu Usmanu ɗan fodio ya baro Magabci izuwa sifawa, sannan ya tashi izuwa Barkiya, sai kuma ya karasa Sokoto.
  Daga nan suka nufi Dangeda, suka karasa Godewa duk suna yin yaki tare da samun ganima mai yawa, sannan suka isa Makada, sai kuma suka tashi izuwa Kirare.
  A kirare suka haɗu da wasu jama'ar Katsina da sukayi hijira daga katsina izuwa garesu bayan sunsha matsananciyar wahalar tafiya cikin dazuka. Ance a kalla kwanaki talatin suka shafe suna tafiya daga katsina izuwa wannan wuri.
  Daga nan kuwa, sai shehu da jama'arsa suka tashi izuwa wani wuri mai suna Tsuntsuwa.
      YAKIN TSUNTSUWA
  Ance anan tsuntsuwa ne wata rundunar Azbinawa da Gobirawa suka taru suka kawowa mabiya shehu hari, a lokacin kuwa kusan duk sun bar sansani izuwa neman abinci. Waɗanda suka rage kaɗai basu wuce manyan tawagar ba irinsu Shehu Usmanu da kuma wasu dakaru dake tare dasu.
   Waziri Abdullahi ya fito da dakarun dake tare dashi suka afkawa wannan tawaga da yaki, shehu Usmanu shi kuma ya fita yana addu'ar neman nasara daga Allah.
  Hakika a wannan rana, Allah ya jarrabi Shehu Usmanu da magoya bayansa, domin kuwa akalla dakarunsu dubu biyu ne akace sukayi shahada, kuma sunyi matukar ɓacin rai da haka.
  Da yaki ya kare, sai Shehu yaja zuga izuwa Jiruwa, mil biyu ne tsakaninsa da Alkalawa daga gabas.
   A wannan waje, mutanen shehu Usmanu suka rinka ribaɗi, watau suna kai hari ga garuruwan dake biyayya da sarkin Gobir jifa-jifa har dai daga baya, Sarkin Gobir ya aiko da runduna aka buga yaki dasu, batare da anci nasara akansu ba.
    A wannan shekara dai, Shehu Usmanu da tawagarsa suka shiga zamfara, sukayi yaki da garuruwansu sukaci nasara akansu, wasu garuruwan kuma suka yi mubaya'a ba tare da an gwabza yaki ba.
  Daga nan zamfara, sai rundunar Shehu usmanu tayi Daura, sannan suka shiga Tsingaroƴ, suka karasa Mawadaci, sukaƴyi Dumne sannan suka sake komawa zamfara, sai kuma sukayi Maraɗi.
  Daga maraɗi sai kuma sukayi Dufuwar Mafara suka sauka, suka ɗanyi kwanaki a wajen, sannan sukayi Sabon Gari nan ma suka zauna suna cin garuruwa.
   YAKIN ALWASA

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU DAN FODIO 4

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU MUJADDADI, DAN FODIO.

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
     08060869978

Kashi na huɗu.

   Shehu Usmanu Dan fodio yayi godiya ga Allah bisa ni'imar da yayi masa bayan ya sauka a Gudu wurin hijirarsa, sannan ya nemi a gabato masa da gadon wa'azinsa.
    Daga nan sai ya tara jama'arsa duka a wurin, sannan ya hau kan gadon wa'azinsa yana musu wa'azi.
   Anan ne yace musu "Na cire sarautar dukkan wani mai sarauta sai wanda yazo mini nan"
 A lokacin kuwa, Sarki Ashiru ne kaɗai yazo gareshi, don haka da akayi yakin jihadi aka barshi da sarautarsa.
   Haka kuma, shehu yayi addu'a ga mutanensa cewa "Duk wanda ya fitad dani daga gidana, Allah ya fitar dashi daga nashi." Mutane suka amsa da Amin. Akayi addua aka tashi.
   Daga nan sai Kaninsa Abdullahi yazo gareshi yayi masa mubaya'a (ta yin jihadi), sai kuma ɗansa Muhammad Bello shima yazo yayi sannan sai abokinsa Ummaru Alkammu, sai sauran jama'a kuma duka kowa yazo yayi.
  Daga wannan rana, Shehu Usmanu da Jama'arsa suka ɗaura shirin soma yaki da sarakunan duk da basu biyo wannan tsari nasu ba.

 FARA YAKIN JIHADI
Sa'ar da Shehu Usmanu da jama'arsa suka yi hijira, sai Sarkin Gobir Yumfa ya umarci sarakunan garuruwansa da cewar, su kame duk wani mai shirin zuwa ga Shehu Usmanu.
  Ai kuwa sai suka shiga fitinar musulmai mabiya Shehu Usmanu da kisa, azabtarwa gami da kwace dukiya.
   Da wannan hali ya k'azanta, sai musulman da sukayi hijira suka soma fita yakin jihadi izuwa garuruwa.
   Ya zama suna kame kananun garuruwa a hankali har sukazo wani gari waishi Giniga, yaki kuwa yayi tsamari anan.
  Ance duk da an halaka musulmai da dama a yakin, wasu manya kuma daga tawagar Shehu sunyi shahada, amma dai saida sukayi nasarar kame garin. Suka kashe na kashewa, wasu kuma aka kame su.
   Daga nan suka fita yaki zuwa Matan Kari, nan ma suka ci garin da yaki, suka sake nufar wani gari mai suna Wata Alkarya, shima suka cinyeshi da yaki, sannan suka samu nasarar cinye garin K'wanni da yaki.
  A wannan shekara ta farko dai, an gwabza yake-yake masu tsauri, amma cikin ikon Allah duk mutanen shehu ke samun nasara.
   Akwai Yakin Kwato da akayi a shekarar, shikuwa yaki ne mafi girma wanda sai dai a Kwatantashi da Yakin Badar a tarihin kafuwar Musulunci, ko kuma yakin Daukar girma a tarihin Yakin Jihadin mutanen shehu Usmanu a Kano.
  Sarkin Gobir fa sai hankalinsa ya dugunzuma, ya shiga shirin yaki haikan.
  Ya aike da takardu na neman taimako izuwa sarakunan Katsina, Kano, Zazzau, Daura da Azbin, duk kuwa saida suka bashi tallafin daya nema, sannan suma suka ɗaura ɗamarar yaki da duk wani mai alaka da Shehu Usmanu a biranensu.
   Daga nan Sarkin Gobir Yumfa ya fita daga garinsa, ya kwana a 'Bore, sannan yahau ya riski Gamba, yabi ta Makida, sannan ya sauka a Tsara ya kwana. Daga nan sai gashi a Janar-Sarki ya kwana biyu anan yana sauraren wasu k'arin dakaru. Bayan sun isone ya fuskanto Gudu da gagarumar runduna.
   Koda Shehu da Mabiyansa suka ji Labarin yaki na gabato su, sai suka ɗau harama suma.
   Wazirin Shehu, kuma kaninsa, watau Abdullahi, ya taso da rundunar mayaka izuwa gefen wasu gidaje suka sauka suna jira, har yamma tayi basuji komai ba, sai suka koma da baya.
  A kwana na biyu ma suka sake yin kamar haka, amma babu abinda ya faru.
  Sai a kwana na uku ne wasu 'yan uwansu fulani suka iso garesu a sukwane, suka shaida musu cewar daga cikin rundunar sarki Yumfa suka sato jiki, kuma yaki ya kusa zuwa garesu, tunda kuwa rundunar tana garin Ayame ne, tsakaninsu da garin kuwa tafiyar yini ɗaya ce..

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU DANFODIO 3

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU MUJADDADI, DAN FODIO.

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
     08060869978

Kashi na uku

 HIJIRA DA DALILIN TA

  Sa'ar da Sarakuna suka ga jama'ar Shehu Usmanu na tattalin makamai, sai suka fito da k'iyayyarsu a fili garesu.
  Suka shiga hanasu yin rawani, suna hana mata lulluɓi.
  Da mutanen shehu suka ga haka, sai suka kauracewa garuruwan sarakunan, izuwa wani wuri mai suna Gimbana a Kasar Kabi.
   Sarkin Gobir ya aike su komo, sai suka k'i.
  Sai kuwa ya aikewa shehu Usmanu Sammacin kira, nufinsa a wannan karon idan yazo ya halaka shi kota halin k'ak'a.
    Shehu Usmanu Bn Fodio da k'aninsa Abdullahi, da abokinsa Ummaru Alkammu suka tafi ga fadar sarkin Gobir Yumfa.
  Koda Suka shiga gareshi, sai kuwa ya harbesu da bindiga da nufin kone su da wuta, amma maimakon haka, sai wuta ta koma gareshi har ta kusa k'oneshi, ya ruga gida da gudu, sukuwa ko ɗaya cikinsu bai motsa ba.
   ƁBayan ɗan lokaci ya dawo garesu, ya zauna tare dasu, sannan yace musu "Ku sani bani da wani makiyi a fili anan duniya kamar ku" Ya bayyana musu kiyayya a fili.
   Su kuma suka bayyana masa cewar sam-sam basa tsoronsa. Allah zai karesu daga gareshi. Sannan suka tashi suka tafi gida ba tare da sun sanar da kowa wannan ba.
   Shehu yace musu Ku ɓoye wannan abu, muyi addua kada Allah ya kuma haɗa mu da wannan kafiri. Shehu yayi addu'a suka amsa da Amin, sannan suka shafa fatiha suka koma gida.
   A lokacin, sai sarkin Gobir ya haɗa runduna ya tafi yak'i da jama'ar Abdussalamu a Kabi, ya kuwa samu nasara akansu, ya kashe na kashewa, ya kama na kamawa, saura kuwa suka warwatse neman mafaka.
   Wannan sai ya k'ara masa girman kai da jiji-da-kai, yana ɗagawa shi sarki ne mai cikakken iko da ɗumbin nasara.
  Da yake acikin mutanen da aka kama, da yawansu mutanen shehu ne da sukayi hijira, sai mutanen Sarkin Gobir suka taso keyarsu izuwa Gobir, kuma suka biyo dasu ta garinsu shehu Usmani, ta gabas da gidansa ma.
  Wannan yasa mutanen shehu suka kamu da tausayin 'yan uwansu, har suka kasa jurewa suka rufarwa dakarun sarkin Gobir tare da kuɓutar da 'yan uwansu.
  Da dakarun sarkin Gobir sukaga haka, sai suka runtuma da gudu gaban sarkinsu, suka zaro kibbau daga kwarinsu, sannan suka gabatarwa da sarkin, suna masu cewa "waɗannan kibiyoyin jama'ar shehu ne da suka harbe mu suka k'wace duk binda muka tafi dashi".
  Hakan kuwa sai ya fusata Sarkin Gobir Yumfa kwarrai da gaske, yace "Hakika dmsun cimma abinda suka so, amma zasu gani".
  Sai kuma ya aikewa shehu Usmanu cewar ya fita dashi da iyalinsa izuwa wani wurin daban, ya rabu da jama'arsa anan.
  Shehu Usmanu kuwa yace sam bazaiyi haka ba, sai dai duk abinda zai samu jama'arsa ya samesu baki ɗaya.
  Shehu ya aika masa da Cewa "Ni kam bani rabuwa da jama'a ta, amma ina iya rabuwa da garuruwanka, kasar Allah yawa gareta".
   Daga nan Sai Shehu ya shiga shirin yin Hijira.
  Sarki Yumfa ya sake aiko masa da ɗan aike yana rarrashinsa da kada ya tashi daga inda yake. Amma sai shehu Usmanu yace "Hakika, ni bani fita daga kasarka, amma zan sauka a gefen garuruwanka"
  Ai kuwa, sai Shehu Usmanu yayi hijira, yabi ta hanyar Kwarin Gezo, ya shiga ta Demba, yabi ta Kalmalo, ya shiga Farkaji, sannan ya isa Ruwa wuri, sannan ya riski wani rafi da ake kira 'Gudu' dake gefen kasar Gobir ya sauka da hijirarsa anan, a ranar alhamis 12 ga watan zulk'ida, na shekarar 1218 bayan hijirar Ma'aiki Annabi Muhammad tsiran Allah da aminci su tabbata a gareshi.
   Koda ya isa wurin, ya tarar  Aliyu Jedi tuni ya shirya masa masauki.
   Shikuwa Agali, shine ya taho da rakuma ɗauke da littattafan shehu Usmanu...

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU DANFODIO 2

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU MUJADDADI, DAN FODIO.

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
     08060869978

Kashi na biyu

Rasuwar Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo keda wuya sai ɗan uwansa mai suna Yakubu ya gajeshi.
  A lokacin kuma Shehu Usmanu ɗan fodio ya zauna a daular zamfara, har ma yana ganin aikinsa na wa'azi daya shafe shekaru yana yi a yankin ya samu nasara, don haka gudun kada duniya ta ruɗeshi sai ya koma mazauninsa Degel.
  Sarkin Gobir Yakubu kuwa da hawansa mulki, sai ya shiga shirin yaki don tafiya garin Dankace ɗaukar fansar ɗan uwansa Bawa Jan Gwarzo.
  Ance akan hanyarsa ta tafiya, Shehu Usmanu ya aika masa da kira izuwa tafarkin tsira, tafarkin musulunci na gaskiya.
  Kuma ana ganin yayi yunkurin bin kiran shehu Usmanu da fari, amma sai mutanensa suka hana. Sai dai shima koda yaje Dankace da yaki acan hanya ya mutu bai dawo Alkalawa da rai ba.
  Shehu Usmanu ya shiga yankuna makwabta yana wa'azi, shine har cikin garuruwan kasar Kabi (Kebbi) yana kira izuwa musulunci tare da barin shirka da bidi'a, ya tsallaka gulbin Kwara mafi girma a wannan yanki, har ma ya isa wani gari mai suna Ilo (Ilorin) ya kai musulunci, kamar yadda ya faɗa a wakensa inji Wazirin Sokoto Junaidu.
   Bayan Mutuwar Yakubu, sai ɗan Uwansa Nafata ya gajeshi.
  Shikuwa a kullum cikin k'ulla sharri yake ga Shehu Usmanu.
  Watarana sai ya kira Shehu Usmanu izuwa fadarsa. Nufin sa idan yazo ya halaka shi.
   Don haka shima sai ya tara sarakuna da malaman daularsa, ya zauna a tsakaninsu akan kujera, sannan ya hori shehu Usmanu ya shigo gareshi.
   Akace, koda Shehu Usmanu ya shigo, sai kuwa wani kurji dake wuyan Sarkin Gobir Nafata ya fashe, nan take ya faɗi sumamme. Aka ɗauke shi izuwa gida magashiyyan baya iya magana.
   Shehu Ya koma Degel. Yumfa ɗan Yakubu shine yayi masa rakiya a lokacin.
  Sa'ar da zasu rabu, sai shehu ya cewa Yumfa "Ya kai Yumfa, hakika al'amarin ubanka ya kare, alamari gareka yake, kayi kokari" (Yana masa maganar mulki ne)
   Sai Yumfa yace, "Hakika idan na samu mulki, bazan aikata irin aikin da iyayena suka aikata gareka ba, don haka zanyi ɗa'a ga kowanne alamari"
  Daga nan suka rabu, Yumfa ya koma gida ya zauna abinsa.
  Kuma koda Nafata ya rasu, sai aka naɗa shi Sarki.
   Yayi hawa ya tafi ga Shehu Usmanu, kafin ya isa da tafiyar misalin mil guda, sai ya sauka ya taka a kafa bisa makirci. Ashe a zuciyarsa cike yake da fushin shehu da Jama'arsa.
   Koda Jama'ar shehu suka ga Sarki da kansa ya tako a kafa zuwa ga shehu, sai suka rinka cewa "Bamu taɓa ganin sarki kamar wannan ba"
 An ruwaito Shehu Abdullahi kanin Shehu Usmanu yana cewa "Ni kuwa banga komai daga gare shiba sai Makirci"
  Sarki Yumfa yace da Shehu " Bani aikata komai daga binda iyayena suka aikata gareka "
  Shehu Abdullahi zaiyi magana, Shehu Ummaru Alkammu ya hana shi, har sai bayan tafiyarsa sannan Ummarun ya faɗi ga shehu cewa "Hakika, faɗinsa bani aikata abinda iyayena suka aikata, ba komai ke nufi ba sai zaiga abinda iyayensa basu gani ba"
  Daga nan fa Sarki Yumfa na Gobir, ya shiga kulla miyagun dabaru ga shehu Usmanu, burinsa kurum ya halaka shi.
   Rannan, shima sai ya kira Shehu Usmanu izuwa fadarsa, alhali ya gina rijiya ya kafa masu acikinta, yasa an rufe samanta da tabarma.
   Shehu Usmanu ya taho tare da Kaninsa Abdullahi, da abokinsa Ummaru Alkammu.
   Abudullahi yayi nufin zama akan tabarmar da akace shehu Usmanu akayiwa tanaji, amma sai shehu ya hanashi, yaje ya zauna shi da kansa. Suka gama maganganunsu suka kare da sarki Yumfa, sannan suka koma gida ba tare da wani abu ya auku ba.
   To amma, sa'ar da shehu Usmanu yaga jama'a tayi yawa gareshi, ga kuma makircin sarakuna na karuwar musu, sai ya umarci jama'arsa su fara yin tanajin makamai.
  Yace musu " Tattalin makamai sunna ne"
  Sannan kuma sai ya shiga adduar neman nasara daga Allah.
  Shehu ya faɗa a wata wakarsa cewa
  "Allah ka gwada min rinjayar addininka ga garuruwan nan namu na sudan domin darajar Abdulkadiri"

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU DAN FODIO 1

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU MUJADDADI, DAN FODIO.

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
     08060869978
Kashi na ɗaya

   Gabatarwa
Limamin yakin Jaddada addinin musulunci da kore bidi'a gami da hana sarakuna aikata ayyukan masha'a da zalunci a kasar Hausa dama makwabta shine Shehu Usmanu Bn Fodio.
   Hakika, tarihin wannan yaki ba zai taɓa cika ba har sai an haɗa da wani yanki na rayuwar shehu Usmanu ɗan fodio.
    Shi Bafillatani ne, jinsin toronkawa. Cikakken sunansa shine Usmanu, ɗan Fodio ɗan Usmanu ɗan Salihu ɗan Haruna ɗan Muhammadu Gurɗo, ɗan Jabbo ɗan Abubakar ɗan Musa Jakollo wanda akace ya auri 'yar Imamu Demba, kamar yadda Marigayi wazirin sokoto ya ruwaito a littafinsa Mai suna 'Tarihin Fulani'.
   An haifi shehu Usmanu a ranar wata lahadi ta karshen watan safar, shekarar 1168 hijiriyya (wajajen 1759 miladiyya).
   Yayi karatun Alkurani a gaban mahaifinsa, ya koyi ilimin fikihu bisa mazhabar Imamuna Maliku ɗan Anas a gaban Mallam Abdurrahman ɗan Hamadi, ya koyi karatun littafin ishiriniya da wasu littattafan addini a gaban malamin sa Usmanu Bakabe.
  Haka kuma ya koyi karatun littafin Muhtassar daga kawunsa mallam Bibnoduwa, wanda yake gwani ne a fagen tsoron Allah da ilimi, gami da umarni da kyawawan ayyuka da kuma hani ga aikata mumunana.
  Hakika, ance ta hanyar zama dashi shehu Usmanu ya koyi halayen kirki da gudun duniya masu yawa.
   Baya da haka, shehu Usmanu ya zauna shekara ɗaya a hannun Sanannen Malami Mal Jibrila (wanda ta hanyarsa alaka ta samu tsakanin shehu Usmanu da Mallam Bakatsine) yana ɗaukar karatu. Tare dashi ma sukaje Agadez, sannan malamin ya mika shehu Usmanu ga mahaifinsa yayin da shikuma ya wuce aikin Hajji, domin a lokacin shehu usmanu bai karɓi izinin tafiya Hajji daga mahaifin saba.
   Sannan dai, shehu Usmanu ya zauna da kawunsa Mallam Ahmadu ɗan Muhammadu yana koyon karatu, har ma a wajensa ya koyi tafsirin Alkur'ani maigirma. Daga nan kuma sai ya sake zuwa gaban Mallam Hashimu Bazamfare, inda ya zauna daram yana sauraren tafsirin Alkurani maitsarki tun daga farko har karshe.
   Wannan shine kaɗan daga tarihin karatun shehu usmanu.
 Don haka kamar yadda yake a ɗabia ta ilimi, kafin wani lokaci sai Allah ya cika zuciyar shehu usmanu da ilimi, saboda haka sai shima ya soma bayarwa ga mabukata, a haka har ya zama cikakken malami.
   KIRA ZUWA GA TURBAR MUSULUNCI TA GASKIYA DA BARIN BIDI'O'I
   Ance shehu Usmanu ya fara wa'azi ne da kiran mutane a mazauninsa dake Degel.
  A lokacin, yakan tara mutane yayi musu nasiha da faɗakarwa, sannan kuma yana rubuta musu wakoki da Ajami.
   A wancan zamanin, shehu ya tarar da cewa Mafi yawan sarakuna kafirai ne, Shugabannin su kuma ko dai kafirai ko kuma fasikai. Sannan bidi'o'i sun yawaita a gari, har ma an jirkita addini daga yadda yake.
   Sannu a hankali mutane suka soma karɓar kiran shehu Usmanu, har ya zamo wasu na binsa gari-gari don yin wa'azi, amma ko kaɗan baya zuwa ga sarakuna don neman wata bukata.
   Sa'ar da Shehu Usmanu ya soma zuwa ga wani sarki shine lokacin daya lura mutane sunyi yawa gareshi, kuma ya samu shahara, don haka yaje ga sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo a fadarsa dake Alkalawa yayi masa wa'azi, ya kirashi izuwa addinin musulunci na hakika tare da tsayar da adalci a mulkinsa, sannan ya koma masaukinsa.
   Haka kuma ance a wannan ritsin ne Shehu Usmanu ya tafi zamfara yana wa'azi, har sai daya shafe shekaru biyar acan wajen faɗakarwa. Kuma ance yasha wahala sosai a lokacin, saboda zamfarawa sunyi nisa wurin jahilci da bidi'a.
   Da shaharar shehu Usmanu ta fara yin tsamari, sai sarakunan Hausa suka soma kishi gami da damuwa da lamarinsa.
  Ana haka sai sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo rannan ya aika masa yazo, nufinsa idan yazo ya halaka shi. Sannan kuma ya aikewa malumman yankinsa duka suzo domin su shaida kisan shehu Usmanu da Jama'arsa.
  Sai dai, lokacin da Shehu Usmanu ya riski fadar Sarki Bawa, sai ya tarar ya tafi Sallar Idi, don haka shima sai yaja zugar mutanensa suka tafi.
   Wani abun mamaki daya faru a zamanin shine, Sarki Bawa da jama'arsa suna masallaci don sallar idi sai ga zugar shehu Usmanu tana tahowa, aikuwa nan take mutanen Sarki Bawa suka tashi fuuu izuwa gaban shehu, ance Bawa kaɗai aka bari a wurin. Kuma tun daga nan ya tsorata da lamarin shehu Usmanu.
   Da aka kare sallar Idi, sarki Bawa ya zauna cikin barorinsa da Bayinsa cikin damuwa, yayinda shehu Usmanu ke tare da zugar Malumma sama da dubu suna ta caffa tsakaninsu. Shine har akace da wani abokin sarki Bawa ya lura da  da halin dayake ciki, sai yace masa "Ya sarki, kayi sani cewar mutum ɗaya ba zai iya aikata abinda kayi nufi ba a zuciyarka, sai dai Allah".
    Sai Bawa ya kira shehu Usmanu gareshi, ya umarci a bashi awo na zinariya guda ɗari. Amma sai shehu yace masa " Kayi sani ya wannan sarki, dani da jama'ata bama bukatar dukiyarka, sai dai ga bukatu na a gareka
  Na ɗaya, kabar ni inyi kira zuwa ga addinin Allah a garinka.
  Na biyu kada a hana kowa dake son karɓar addini.
  Na uku ka sanya Alfarma ga dukkan masu hula da rawani.
  Na huɗu ka saki dukkan waɗanda ke ɗaure a kurkukun ka.
  Sannan na biyar a daina amsar haraji mai tsauwalawa daga talakawa."

  Abinda akayi kenan, sarkin Gobir yace " Na baka dukkan abinda ka nema, na kuma sahale maka yin duk abinda kake son yi acikin garin mu"
  Daga cikin fursunonin da aka saki a lokacin, har da Sarkin Zamfara Abarshi.
   Shi kuwa Bawa Jan Gwarzo, sai nemi da shehu Yayi masa addu'a yaci garin Maraɗi da yaki. Saboda an samu a lokacin, adawa tayi tsanani tsakanin masarautar Gobir data maraɗi, har kuma cinye Maraɗin ya gagari sarki Bawa
   Nan take Shehu Usmanu yayi masa addua, yace masa " Na baka maraɗi, zaka kuwa cinyeta da zarar ka sauka gareta, amma kada ka wuce ta"
   Daga nan Bawa da Shehu usmanu sukayi sallama, shehu ya juya da jama'arsa ya nufi Degel, shikuwa Bawa ya tsaya jim yana kallon Shehu yana tunani gami da mamaki. Sannan yakira sunan mutanensa har sau uku yana mai cewa "Jama'ar Gobir!, jamaar Gobir!!, Jamaar Gobir!!!, kunga wancan Bafillatanin? Ina baku labari cewa babu sauran Sarki a bayana, sai dai Uban Unguwa"
   Sai kuma ya shiga tara dakaru da kayan faɗa, domin zuwa murkushe garin Maraɗi da yaki.
   Ace ya tara gagarumar runduna wadda rakuma arbain ne ke ɗaukar mata goran ruwansha, da kayan faɗa masu yawa, sannan suka nufi maraɗi.
  Haka  Kuma kamar yadda shehu Usmanu yayi masa albishir, Bawa yaci Maraɗi da yaki cikin kankanin lokaci.
   To amma da yaga wannan nasarar ta samu, sai yace "Munga adduar shehu, yanzu kuma zamuga aikin Masun mu"
  Kurum sai yaja tawagarsa suka shige maraɗi izuwa wani gari mai suna 'Dan Kace'.
  Ai kuwa da saukarsa a garin, mutanen garin suka ce dawa Allah ya haɗamu ba dakai ba, sai suka rufar masa da yaki, suka kuma samu gagarumar galaba akansa, har takai sun kashe ɗansa da yake matukar so.
   Haka Sarki Bawa Jan Gwarzo ya taho da sauran dakarun da suka rage masa cikin kunchi da ɓacin zuciya, kafin ya iso Birninsa Alkalawa, ajali ya riskeshi a wani gari mai suna Naya...
  

Friday, 22 December 2017

MAFITAR LALACEWAR AURE A KASAR HAUSA

Assalamu Alaikum
>   Matsalolin da suka danganci
> aure, suna daya daga cikin matsaloli masu wuyar magani,
> wadanda kuma a kullum suke barazanar gurbata wannan al'umma
> tamu ta Hausawa daga mai kyau izuwa mummuna.
>   Wataqila wuyar magance musu baya
> rasa nasaba da yadda masu qoqarin magancewar suka gaza
> binciken asalin matsalolin tun daga tushe, yadda a qarshe
> za'a samu nasarar samar da hikimomin da zasu zamo magunguna
> ga matsalolin.
>     Da farko dai, Malaman mu
> sun sanar damu cewa kakanmu Annabi Adam A.S shine farkon
> mutum da Allah ya fara halitta, sai daga baya ya halicci
> matarsa Nana Hauwa'u daga jikinsa, wasu malaman ma sun tafi
> akan cewa daga haqarqarin Annabi Adam A.S na barin hagu aka
> farar da halittar Nana Hauwa'u.
>    Hakanan, baya da fifikon Namiji
> akan mace da Allah Ta'ala yasha bayyanawa acikin littafinsa
> Alqur'ani mai tsarki, wani sahihin Hadisi daga Abu Hurairata
> R.A yace Manzon Allah s.a.w yace" wanda duk ya bada gaskiya
> ga Allah da Ranar lahira kada ya cuci makwabcinsa, kuma ina
> yi muku wasiyya da ku kyautatawa mata domin su an haliccesu
> ne daga qashin qirji, haqiqa qashin qirjin da yafi
> tankwashewa shine na sama, idan kai nufin miqar dashi sai ka
> karya shi, idan kuwa ka barshi sai yaci gaba a karkacen. Ina
> yi muku nasiha da ku kyautatawa mata."
>     Duk wannan, Allah Ta'ala
> na nufin sanar da mutane cewa Namiji shine jagoran mace,
> mace zatayi masa biyayya, shi kuma ya tausasa mata. Wato dai
> ilimi ne aka saukar yadda zamu san kanmu, yadda idan matsala
> ta taso ba zamu rasa hikimar warware ta ba.
>   Mu dauki misalin Mutumin da ya
> sayo abin hawa, mota babur da sauransu. Idan wannan abin
> hawa nashi ya lalace, tabbas mai abin hawan ne zai miqa shi
> wajen gyara, domin abin hawan bashi da ikon zuwa don a gyara
> shi. Ana cikin haka, sai akayi sa'a, wani mai gyara ya
> koyawa wannan mutumi gyaran abin hawan. Yaya kuke tunani? Ai
> kuwa duk a inda wannan abin hawa ya lalace masa bazai rasa
> hikimar da zai gyara kayan saba tunda ya samu ilimin
> gyaran.
>    To ayau, Asalin tabarbarewar
> aure shine Rashin ilimi. Mutane da yawa basu san kansu ba,
> basu da manufar rayuwa a duniya ballantana su san irin
> abokiyar zaman data kamace su, su kuma san hikimar zama tare
> da wannan abokiyar zama. Amma duk da haka kuma, idan yayi
> aure, burinsa abokiyar auratayyar sa zatayi masa dai-dai da
> abinda ransa yake so.
>     Don haka, a gaskiya mun
> dade muna jahiltar kawunan mu. Ya kamata mu san cewa namiji
> da mace ba daya suke ba. Aikin su daban ne, manufar da Allah
> yake son su  cimma daya haliccesu shine Bauta, kowannen
> su kuwa yana bin hikimomi daban-daban don samun cimma waccan
> manufa, amma fa abin da wannan yakeso yasha bam-bam da
> abinda wancan yakeso. A taqaice ma zan iya cewa halittar dan
> Adam ta qunshi jinsin halittu biyu ne, wato halittar namiji
> da halittar mace, kawai dai munyi kama da junane, muna kuma
> rayuwa tare, kamar misalin Bacteria da Archea ga masana
> ilimin qananun halittu.
>     Saboda haka, batun ayi
> aure ace ba za'a samu matsala ba, wannan tatsuniya ce. Dole
> a rinqa samun sabani, shiyasa Hadisin Annabi s.a.w ya umarci
> namiji a matsayin sa na babba ya tausasawa wadda zatai masa
> biyayya wato mace, har ma akai mana hannun ka mai sanda
> wajen jagorancin cewa kada yayi amfani da ruwan zafi, kada
> kuma yayi jagorancinsa ta ruwan sanyi, wato dai anaso yayi
> sai-sa-sai-sa cikin hikima.
>    Kawai dai, ga duk mai son
> warware matsalar sa ta auratayya, ilimi ya kamata ya nema
> wanda ya shafi yadda Fiyayyen Talikai ya rayu da ahalinsa in
> yaso sai yayi hikimar warware tasa matsalar dai-dai da halin
> daya tsinci kansa. Akarshe, Rashin ilimi shine asalin
> tabarbarewar aure, neman ilimi kuwa shine magani. Ku huta
> lafiya. 

SHIN YESU KIRISTI UBANGIJI NE KO 'DAN AIKEN UBANGIJI

BARKA DA KIRSIMETI: SHIN YESU KIRISTI 'DAN UBANGIJI NE KO KUWA 'DAN AIKENSA NE?
 
SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
   

A duk Ranar 25 ga watan disamba na kowacce shekara, mabiya addinin Yesu Kiristi suke bkkin tunawa da ranar Haihuwar Annabi Isa A.S
  Haka kuma, Mabiya addinan Islama dana kiristanci, dukkansu sun amince da wanzuwar Yesu Almasihu kuma suna darajanta shi.
  Sai dai, yadda mabiyan kowanne daga addinan suka ɗauke shi keda bambamci.
   A addinin musulunci, an nuna cewa Yesu Kiristi Mutum ne mai daraja, wanda Ubangiji abin bautawa ya aiko domin yayi wa'azi da kaɗaitashi.
  Haka kuma mahaifiyarsa, an yabeta a matsayin mace mai gaskiya. A duba Alkur'ani (3:45) da (19:17)
   Sai dai a kiristance, ba haka abin yake ba.
   Domin kuwa da yawan mabiya addinin suna ɗaukar Yesu Almasihu a matsayin Ubangiji, yayin da wasu ke ɗaukarsa a matsayin ɗa-ga Ubangiji.
   Don haka, wannan saɓani, zai warwaru ne kurum idan mukayi duba izuwa littattafai masu tsarki na waɗannan addinai guda biyu.
  Da fari dai, acikin Suratu Maryam cikin littafin Alqur'ani mai girma, maganar Ubangiji ta faɗi labarin yadda aka haifi Yesu kiristi ba tare da Uba ba, har mutane ke tuhumar mahaifiyarsa da cewa "yake 'yar uwar Haruna, hakika kinzo mana da bakon abu, gashi kuwa mahaifinki ba fasik'i bane, mahaifiyarki kuma ba mai bin mazaje bace".
   Sai kuwa Maryamu tayi musu nuni da Jaririn tana nufin su nemi ba'asi daga gareshi. Har suke cewa gareta "tayaya zamuyi magana da wanda ke cikin zanin goyo?"
  Ai kuwa Sai Yesu Almasihu dake zanin goyo ya amsa da cewar "Ni bawan Ubangiji (Mai suna Allah) ne, ya bani littafi ya kuma sanyani Annabi".
   "Ya sanya albarka a gareni a duk inda na kasance, yayi mini wasicci da Sallah da Zakkah matukar ina raye".
  "Kuma aminci ya tabbata a gareni a ranar haihuwata, da ranar mutuwata, da ranar da za'a tashe ni rayayye".
  Sai Ubangiji yace "wannan fa shine Isa Dan Maryamu.."(karanta har karshen Aya)
 Maryamu: 26-34

A littafin Babil mai tsarki, nan ma ana iya cewa yazo a wurare daban-daban cewar Yesu Almasihu bashine Ubangiji ba.
   Sahabban Yesu kiristi irinsu Matthew, Mark, da Luke waɗanda suka rubuto zantukansa har suka haɗa zantukan izuwa littafin Babil, sun tafi akan cewa Yesu kiristi bai taɓa kiran kansa da suna Ubangiji ba. A duba Matthew 10:18, da Matthew 19:17.
   Abinda wasunsu suka yadda shine: shi ɗan Ubangiji ne, saboda haihuwarsa da akayi babu uba da kuma karamomin daya nuna a zamanin rayuwarsa.
   Haka kuma, ɗaukarsa a matsayin ɗan Ubangiji na nufin kasancewarsa Mutumin kirki nagartacce, don haka ba shi kaɗai ba, duk wani nagartaccen bawa sukan kirashi ɗan Ubangiji. A duba Matthew 23:1-9 don a tabbatar.
   Shikuwa Paul, wanda shima Maruwaicin Babil ne, ya aminta da cewar Yesu Kiristi ba Ubangiji bane.
  A cewar sa, yesu kiristi ne wanda Ubangiji ya soma halitta, don haka yayi amfani dashi wajen halittar sauran halittu kamar yadda yazo a Colossians 1:15 da 1 corinthians 8:6.
     Saboda haka, kasancewar Paul, John da sauran manyan maruwaitan littafin Babil mai tsarki, sun tafi akan cewar Yesu Almasihu shine halittar Ubangiji na farko kuma mafi daraja, har ma Paul ɗin ya ruwaito a Babil cewa yaji Yesu na faɗin "The Father is greater than I". Watau "Uban, ya fificeni" sai waɗanda suka biyo bayansu sukayi shishshigin ɗora masa lak'abin shi ɗan ubangiji ne, wasu kuma sukace shi Ubangiji ne kachokan.
  Ga kaɗan daga ayoyin Babil da suke nuna Yesu Kiristi ba Ubangiji bane, bawan Ubangiji ne kamar yadda muka kawo Yesu ɗin ya faɗa da bakinsa daga Alkur'ani:-
   "Men Of Israel, listen to this:Jesus of Nazareth was a Man accredited by God to you by miracles.." Acts 2:22
 "God Has raised this Jesus"
 Acts 2:32
 "God Raised up his Servant"
 Acts 3:26
  "The Lord of Abraham, Isaac, and Jacob, the Lord of our fathers, has your holy servant Jesus"
 Acts 3:13
  A wani kaulin ma, shi da kansa Yesu Almasihu ya faɗi cewa bai san ranar da za'a tashi alkiyama ba, don haka shifa bawan Ubangiji ne (Matthew 24:36).
 A Wani wajen kuma an ruwaito Yesu Kiristi yana neman taimakon 'Eloi', ko 'Eloh' wajen tabbatuwar ayyukansa, kamar yadda akace ya faɗa yayin da Yahudawa zasu halaka shi cewa "ELOI, ELOI, LAMA SABACHTANI  (Markus 15:34. )
Ma'ana,  "Ubangijina,  Ubangijina, don me ka yasassheni?"
  Don haka, idan har Yesu ya kasance ubangiji, me zaisa ya rinka neman taimakon wani kuma, sannan me zaisa me ya rinka faɗawa mutane da kansa cewar shi Ɓbawa ne ga ubangijinsa ELOHIM?
  Koda yake, wannan k'in gaskiyar karamin aiki ne ga manyan malamaii mabiyansa idan muka kalli Babil, Song of Songs (5:16), inda kai tsaye akayi busharar zuwan wani Annabi mai suna 'מַחֲמַדִּים' cikin harshen yahudawa (wanda aka fassara haruffan da m-ħ-m-d-y-m, ake kuma furtasu da meħmadim ko
maħammaddīm don girmamwa bisa karin 'im'), amma kai tsaye sai sukace sam kalmar ba Annabi Muhammad take nufi ba, wai tana nufin wani wanda kowa keso ne ko kuma wani mafi cancanta..

MENENE SUNAN SA?

Akwai wasu Mutane 'yan ɗarikar Jehovah daga cikin ɗarikun kiristoci masu zagayawa gida-gida ga 'yan uwansu kiristoci suna tambaya menene sunan sa? (Suna nufin menene sunan Ubangiji)
 Sai kaji kirista yace "Ubangiji"
  Sai suce "Ubangiji ai ba suna bane, abin bauta ne".
  Sai su kara tambaya, "to menene sunan sa?"
  Sai kaji kirista yace "Sunan sa Uba (Baba God)"
  Sai suce masa "shin Ubanka Ubangiji ne?"
  Nan take kirista zaice "A'a".
  Sai su sake tambayarsa, "to menene sunan sa?"
  Idan yayi shiru babu amsa, sai suce  "Jehovah shine sunan sa".
  Waɗannan kalmomi guda huɗu da ake kira Tetragammation, sun hana kowa yabisu dalla-dalla don zakulo asalin ma'anarsu.
   Amma idan ka tambayesu, menene 'Je-ho-va-h', sai suce maka 'Y-H-W-H', watau kalmomi huɗu da suka zo a littafin Babil mai tsarki na yaren Ibraniyanci.
  Kasancewar tsohon rubutun Ibraniyanci da Larabci babu wasulla, waɗancan kalmomi na YHWH (ko JHWH saboda matsalar J da ake sauyata da Y a larabci, kamar misalin Jacob da Yakub, Jesus da Yesus, Joseph da Yusuf, W kuwa har yau a wasu yarukan da lafazin V suke ambatonta) kaɗai sunzo da maimaicin akalla sau 6,823 acikin Babil.
 Saboda haka, mabiya ɗarikar jehovah sun gamsu cewar Kalmar JHVH (YHWH) sunan Ubangiji ne daya kira kansa da kansa a littafi mai tsarki sama da sau dubu shidda, to amma kalmar ELOHIM (YHWH ELOHIM) ce ke tare da waɗancan haruffa a mafi yawan lokuta.
   Idan muka kalli kalmar 'ELOHIM', zamuga kalmomi ne biyu a haɗe, watau ELOH da kuma IM.
  Da Fari, ita IM, ɗango ne na girmamawa ga ELOH a yaren Annabi Ibrahim A.S. misali, idan za'ace Ibrahim yana da girma, sai a kara masa IM, ya zamo 'Ibrahimim', kamar yadda idan aka lura har yanzu yaren yahudanci da wasu yaruka na bin wannan tsari.
   Saboda haka 'ELOH' shine sunan, wanda shima zamu gane ainihinsa idan muka kalli yadda Larabci ke kiran duk abinda Ibraniyanci ya kira da 'EL' da lafazin 'AL'.
  Don haka, kalmar 'Eloh' ta yaren Ibraniyanci na nufin 'Aloh' kenan a larabci.
  Kalmar da idan mukaci gaba da mai-mai-ta-ta a zukatanmu zamuga ta sauya daga Eloh, Eloh, Zuwa Aloh Aloh.. Zuwa Allah Allah..
 Wannan ke nuni da cewa kalmomin 'YHWH ELOHIM' da suka zo a Babil na Ibraniyanci ba komai suke nufi ba sai 'YA HUWA ALLAH' a larabci, kusan Aya kenan ta farko a Suratul Ahad, da Ubangiji yace "Qul Huwallah..." (watau kace shine Allah)
   To waɗannan kalmomin fa, sune sukazo a Babil sama da sau dubu shidda.. Abinda Allah ke faɗawa Manzonsa Annabi Isah A.S shine "ka sanar musu da cewa Ubangijinka Shine Allah.." Kuma abinda Yesu Kiristi yayi ta sanarwar kenan, amma har zuwa yanzu Ubangiji baisa 'yan uwanmu kiristoci sun gane cewar Allah ne sunan ubangiji abin bauta da gaskiya ba.
   Marigayi Sheik Ahmad Deedat Rahimahullah yana Cewa dangane da wannan batu "Idan da Malaman kiristoci zasu sanar da Mabiyansu wannan abu, tabbas da lokaci yayi wanda musulmai da kiristoci zasu haɗu wajen bautawa Ubangiji makaɗaici".
   Daɗi akan haka, shine kalmar nan ta ELLELUYA, wadda babu kiristan dabai santa ba.
  Har ma sukan ambace ta aduk sanda suka so godewa Ubangiji, kamar yadda Musulmai ke faɗin Allahu Akbar don tsarkake Ubangiji.
   Ya kuwa ishemu misali idan muka kalli kalmar Ibraniyanci ta ELLELU-YA muka musanya ta da zubin larabci izuwa ALLELU-YA.. (muka sauya EL da AL)
  Sai mu kalli waɗannan kalmomi:-
  ALLELU YA
  YA ALLELU
  ALLAHU YA
  YA ALLAHU
  Ku tambayi kanku, don girman Allah akwai banbanci ko babu?
  Sheikh Deedat, Zakir Naikh da sauran malumman musulunci duk sun tabbtar da cewa Ya Allahu shine asalin Kalmar Elleluya.
  Don haka, aduk sanda kaji malaman kiristoci na faɗin "Praise the Lord!" sukuma suna amsawa da "ElleluYa!!!" kasani cewa "Ya Allahu" kurum suke ambata a sauye.
  Allah da aka ambata a Linjila, shine aka sake ambata a Alqur'ani mai tsarki, amma k'alilan daga mutane ke fuskantar haka.
  Hakika, Tsarki ya tabbata ga Ubangiji mai tsarki da Buwaya. Allah kayi daɗin tsiranka ga Shugabanmu Annabi Muhammad (s.a.w) da sauran Annabawan Allah masu tsarki. Amin.