Wednesday, 6 December 2017

MANYAN ABUBUBUWA DANGANE DA ATTAJIRI ALH AUWALU ABDULLAHI RANO (A. A RANO)

ALH. AUWALU ABDULLAHI RANO; Abubuwa 12 daya kamata mutane su sani dangane dashi.

  Daga Sadiq Tukur Gwarzo

1. Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, wanda akafi yiwa lak'abi da A.A Rano haifaffen garin Rano ne mai tsohon tarihi na jihar kano, yasha kwaramniya kala-kala a rayuwa, sannan an tabbatar da cewa a kasuwanci ya samu tarin dukiya ba a Gado ba.
 2. A.A Rano ya fara Gina gidan man sa na farko ne a garin K'arfi ta jihar kano bayan ya bar harkar tireda ya shiga harkar man fetur.

 3. A.A Rano shine Ubangidan Alh. Abdulkadir Musa mai kamfanin Rahamaniyya oil. A.A Rano ne ya d'auke shi aiki, ya kuma sakar masa dama. A yanzu kamfanin Rahamaniyya nada ma'aikata sama da dubu biyar, albashin su ya tasamma miliyan 56 duk wata.

 4. A.A Rano nada gidajen mai kimanin 100 (ko sama da haka) a sassan kasar nan. Ma'aikatan sa sun haura dubu biyar. Kuma yafi d'aukar ma'aikatan sa a gurin daya gina gidan man sa domin ragewa al'ummar wurin zaman banza.

5. A.A Rano nada matattarar taskance tataccen man fetur da ake kira Depot a unguwar Ijegun dake Lagos. Wannan matattara gagaruma ce wadda ake sauke litar mai kimanin miliyan sittin, daga nan kuma sai a rarraba shi izuwa gidajen mansa, a kuma siyarwa sauran 'yan kasuwa.

6. A.A Rano ne wanda ya gina cibiyar yad'a addinin Islama mai suna 'Darus Sunnah' wadda take a unguwa uku ta garin kano. A wannan cibiya ana karantar da ilimin addinin musulunci, ana kuma gabatar da manyan taruka da shirye-shiryen da suka shafi musulunci kamar misalin Tambaya mabudin ilimi da Sheik Ibrahim Daurawa keyi, attajiri Alh Sani kwangila kuma yake daukar nauyi.

7. A watan yulin shekara ta 2014, A.A Rano ya bada tirelar shinkafa kyauta don rarrabawa marayu ta hannun gidauniyar tallafawa marayun jihar kano, sannan ance duk shekara yana cigaba da yin irin wannan aiki.

8. A.A Rano shine shugaban 'A.A Rano foundation', gidauniyar da take tallafawa d'alibai da kudin karatu, tare da biyawa marasa lafiya kudin magani ko kudin aikin tiyata.

9. A watan yuni na shekarar 2016 A.A Rano ya saukewa makwabtansa kab'akin arziki, inda ya rarraba Naira dubu Saba'in da buhun shinkafa  ga gidaje arba'in dake gabas, yamma, kudu da arewa na gidansa. Sauran magidan-tan dake garin Rano da kewaye kuma ya bisu da Naira dubu ashirin da buhun shinkafa.

10. A.A Rano ne mamallakin kamfanonin Rano oil &Gas, Nicabon Petroleum, D'an kano oil & chemicals, A.A Rano LPG, A.A Rano Transport, A.A Rano Farms, Ibal Petroleum da kuma Centra Oil limited company.
11. A.A Rano na ragi a farashin litar mai adukkan gidajen mansa don saukakawa al'umma, sannan a yanzu haka yasha alwashin fara siyar da iskar gas na girki kasa da farashin da ake siyarwa a kasuwa.

12. A. A Rano ne attajirin farko daya ke dukan kirji wajen samarwa da makarantun gwamnati kayayyakin zama dana karatu. A yanzu haka ya sabunta makarantar Rano special primary school tare da samar mata da kujerun zama. Hakan ne kuma yasa wata kungiya taga ya dace ta karrama shi tare dayi masa godiya bisa ayyukan al-heran da yakeyi.
   Hakika wannan mutum karramamme ne a zukatan al'umma...
 Dafatan sauran attajirai zasuyi koyi da ayyukan sa na alheri. Shikuma Allah ya k'ara Albarkatar rayuwarsa data ahalinsa amin.

No comments:

Post a Comment