Wednesday, 6 December 2017

TARIHIN GWAGWARMAYAR MULKIN FULANI A KANO 3

TARIHI: MULKIN FULANI A KANO, DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na uku

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN
     08060869978

Yaki a Santalmawa, Jijitar, Sankara da Kunchi tare da Kwache garin Rano.
   Daga nan sai rundunar yaki ta cigaba da tunkarar Daular Dantunku. Sannu a hankali suka riski garin Gasakole, inda aka fafata yaki gagarumi da rundunar Dantunku. Rundunar Sarki Ibrahim Dabo tayi nasara tare da sake nausawa suna masu fuskantar Kazaure.
  Suka isa Santalmawa, nan ma suka gwabza yaki tare da kwace ikon garin daga sadaukan Dantunku. Daga nan sai gasu a garin Jijitar, nan ma suka gwabza yaki kuma suka sake samun nasara.
   A garin Sankara ne dakarun Sarki Ibrahim Dabo suka samu gagarumar nasara, saboda shirin da Dantunku yayi musu ta hanyar tara damin sadaukai a garin da niyyar yi musu sukuwar sallah. Aka naɗa wani mai suna Arɗo Hunturɓe jagoran runduna.
  Koda jagorar rundunar Sarki Ibrahim Dabo maisuna mallam Ali  yaji wannan labari sai shima yayi shiri, ya kara tattaro dakarun dake biyayya da sarki Ibrahim Dabo daga kabilun fulani, hausa da kanuri, sannan ya zube su a wuri ɗaya cikin shirin ko-ta-kwan.
 Ai kuwa Kwatsam sai ga mutanen ɗantunku sun kawo musu hari, babu ɓata lokaci sai yaki ya ɓarke.
  Ance ko mutum ɗaya daga rundunar mallam Ali bai rasa ransa ba, amma sun karkashe abokan gabarsu da dama tare da watsasu inda suka ruga izuwa iyakokin daulolin Borno da Damagaram domin tsira da rayukansu.
   Baya da haka, anyi yaki a Malikawa, anan ma fulani sunci gagarumar nasara sun kuma samu ganima.
   Daga nan sai akace sarki Ibrahim Dabo yayo hawa izuwa garesu.  Yayi musu wa'azi da jinjina, sannan ya tashi Mallam Ali da runduna ta tafi kunchi ta buga yaki da dakarun garin tare da kwace shi daga hannun sadaukan Dantunku.
   Bayan nan ne sai sarki Ibrahim Dabo ya juyo da runduna da nufin komowa Fagge don ya yada zango kafin yaki ya kare. Amma sai labari ya iskeshi cewar Dantunku yayi shiri da mutanen fagge zasu tara itatuwa su kunna wuta idan dare yayi, wanda zai nuna alamar sadaukansa ne suka sauka a wurin, in yaso sai a shammaci dakarun Sarki Ibrahim Dabo a kawo musu hari ta baya.
   Ai kuwa dajin haka sai suka zauna cikin shirin kota kwana. Suka isa fagge da dare, suka tarar anyi kamar yadda aka sanar musu.
   Babu jimawa kuwa sai ga runduna ta auko musu da yaki, amma da yake cikin shiri suke, sai suka ce dawa Allah ya haɗamu ba daku ba, nan danan wuri ya rinchaɓe, har safe ana yaki, sannan rundunar da ɗantunku ya aiko ta ruga cikin rashin nasara, suka bar kayayyakin amfani masu yawa a matsayin ganima ga dakarun fulani.
  Bayan yaki ya kare, dakarun sun cigaba da zama cikin shirin tsammanin koda Dantunku zai kawo musu hari da kansa, amma dai hakan bata auku ba.
  Daga nan sai suka riskarwa garin Rano da yaki. Daman kuwa yana ɗaya daga garuruwan da fulani basu karɓe ikon suba a zamanin jihadinsu, don haka masarautar ta zamo dandalin da ake shiryawa fulani bore.
   Sarkin Rano mai suna Barwa ya tarbe su da yaki, amma babu wata fafatawa gagaruma aka kasheshi tare da kwace ikon kasarsa baki ɗaya.
Yaki da Dantunku a garin Danyaya
     Bayan shekara ɗaya, sai Dantunku ya shiga neman taimakon sarakuna na kusa dashi masu irin akidunsa, inda ya tara gagarumar tawagar sadaukai. Sannan yayi hawa da kansa ya nufo kano.
   A bakin tafkin sabon ruwa rundunoni biyu suka haɗu suna fuskantar juna a ranar wata lahadi sha shida ga watan rabiyul awwal. Mutanen ɗantunku a hagu yayin da rundunar Sarki Ibrahim dabo take a dama.
   Bayan anyi cirko-cirko ns ɗan lokaci, sai kuma aka shiga faɗa da juna. Masu kibbau na harbawa, mazaje kuma suka shiga saran abokan gaba da masu gami da takubba.
   Ana haka sai aka ga kura ta turtuke, tayiwa wajen duhuwa na tsawon lokaci.
  Bayan ta lafa sai akaga sarki Ibrahim Dabo ya bayyana a wurin shima yana saran abokan gaba da kansa. Wannan abu sai ya raunana zukatan Dantunku da mutanensa, suka tarwatse da gudu.
  Ance ganimar da aka kawowa Sarki Ibrahim dabo a wannan rana gagaruma ce, wadda ta haɗa da  bayi mata, dawakai, da kayan faɗa masu daraja.
  Daga nan fa Dantunku ya zamo ya kunyata a idon duniya, yayinda sunan Sarki ibrahim Dabo ya ɗaukaka a birni da kauyuka, har maguzawa ma da kansu sun tsorata da sha'aninsa, har kuma akai masa lakabi da chigari.
  Kunji asalin kirarin da akewa kano mai taken kano ta dabo chigari.
  Bayan nan sai Dantunku ya saduda. Ya tura takarda ga Sarkin musulmi Muhammadu Bello a sokoto yana mai nana tubansa a fili, sannan ya aike da Arɗo Hunturɓe ya nema masa afuwa da yafiya a gurin sarki Ibrahim Dabo.
   Shikenan kuwa sai aka yafe masa, ya zamo ya tuba daga boren da yayi, ya kuma koma musulmi cikakke.
   Wanda ya tuba na karshe daga waɗanda sukayi bore ga sarki Ibrahim Dabo shine wani sarki mai suna Kashakori.

No comments:

Post a Comment