TARIHI: YADDA JIHADIN FULANI YA KASANCE A KANO (1803-4)
Kashi na ɗaya.
DAGA SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
08060869978
GABATARWA
Shehu Usmanu bafillatani ɗan fodiyo ɗan Usmanu ɗan salihu ɗan Haruna ɗan Muhammadu Gurɗo ɗan Jaɓɓo ɗan Mamman samba ɗan Misirana ɗan Ayuba ɗan Baba ɗan Abubakar ɗan Musa Jakollo, babban masani, mai yawan jarumta, mai yawan tausayi da tsoron Allah, Allah ya kara masa yarda, shine ya jagoranci yakin Jihadin fulani wanda aka soma a shekarar 1803 miladiyya a wasu sassan kano da Gobir, daga baya kuma ya karaɗe kusan dukkan garuruwan dake kasar hausa dama makwabta.
Ance an haifeshi ne a garin Maratta, wajajen shekara ta 1754. Yayi yawace-yawacen neman ilimi a garuruwan dake tsohuwar kasar Gobir da sassan Kasar Nijar, koda yake ance mahaifinsa shine ya soma karantar dashi, amma daga baya manyan malumma irinsu Mallam Jibrila sun karantar dashi ilimi har kawo lokacin daya tumbatsa ya zamo malami mai karantarwa shima.
Shehu ya zauna a Gobir yana koyar da ɗalibai addinin musulunci bisa tafarkin sunnar Annabi Muhammd (s.a.w) har izuwa shekarar 1802 da saɓani ya soma shiga tsakaninsa da Sarkin Gobir Yumfa, sai ya tashi yabar garin.
Babban dalilin yin jihadin Shehu Usmanu akan karfafa Addinin islama ne. Domin a zamaninsa, ya kalli yadda aka sarayar da addinin musulunci a aikace, ake kuma ikirari dashi a baki. Ya kalli yadda ake aikata miyagun ayyuka na shirka da tsafi da ayyukan masha'a a bayyane cikin al'umma, da kuma yadda idanuwan sarakuna suka rufe da zalunci ga mabiya gami da mulkin fir'aunanci..
Sai dai, kasancewar wannan rubutu kachokan ɗinsa akan jihadin fulani ne a kasar kano ba akan jihadin shehu Usmanu bane baki ɗaya, don haka ba zamu zurfafa akan tarihin Shehu Usmanu R.A ɗin ba.
Da fari dai, ya kamata a sani cewar wannan tarihi, masani Qadi Muhammadu Zangi ne ya rubuta mafi yawansa a littafinsa mai suna 'Taqyidil Akbar' wanda aka rubuta a wajajen shekara ta 1860 zamanin mulkin sarkin kano Abdullahi ɗan Ibrahim Dabo, sai kuma wasu sassan-sa da muka samo daga wasu takardu na tarihi waɗanda turawa suka taskance tare da aikewa kasarsu bayan sun kwace kano, da kuma abinda muka samu na daga karin binciken tsoffin marubuta irinsu Mallam Ibrahim Ado Kurawa wanda ya rubuta littafin 'The Jihad in Kano', fassarar littafin 'Taqyidil Akbar' ɗin kenan mai ɗauke da sharhi.
SOMAWAR YAKIN JIHADI A KANO
Ta hanyoyi uku mutanen wancan zamani suka rinka samun labarin Shehu Usmanu bn Fodio.
Hanya ta ɗaya itace ta hanyar rubuce-rubucensa da yayi a harsunan arabi, hausa da fulatanci. Musamman wakokin daya rera da hausa.
Hanya ta biyu itace hanyar wa'azi da Shehu kanyi ga matafiya ko ɗai-ɗaikun mutanen da duk ya haɗu dasu.
Hanya ta uku kuwa itace Karamar shehu. Tayadda mutanen dake nesa dashi sukanyi mafarkinsa yana kiransu izuwa musulunci, ko kuma yana musu wa'azi akan bautawa Allah ɗaya ba tare da haɗa masa kishiya ba.
Qadi Muhammadu zangi da kansa ya ruwaito cewar yaji daga Malam Sulaimanu, sarkin kano na farko a Jerin sarakunan fulani cewar a lokacin da baffansa mai suna Dikoye ya ziyarci Shehu Usmanu, sai kuwa ya nuna masa babban waliyyin nan na Digel watau Muhammadu kwairanga yace 'ai kuwa nasha ganin wannan a mafarki yana mini wa'azi da tsoron Allah, yana tambayar yaushe zanzo ziyara ga Shehu Usmanu?'
Da lokacin Hijira yazo, sai shehu Usmanu ya umarci duk masu kai masa ziyara cewar su janye jikinsu daga sauran mutane masu haɗa bautar Allah da waninsa izuwa wani wuri kawwamamme wanda za'a rinka yin bautar Allah kaɗai.
Shi da kansa ya soma yin hijira daga Digel (garin daya koma da zama bayan tashinsa daga Gobir) izuwa Gudu.
Mun samu a wake cewa:-
" Da ɗai-ɗai da ɗai-ɗai muka taru,
Har kuma karfinmu ya taru,
Shekara bayan shekara muka zamo runduna."
Ance wanda ya soma riskar shehu wurin hijira daga mutan kano shine Mallam Abdurrahman wanda ake kira Mallam Goshi, (wanda kuma aka baiwa mulkin kano da fari bayan an kori Sarki Alwali amma yace baya so) tare da ɗanuwansa Jibrila, malami mai yawan sani da tsoran Allah.
Daga baya dai saura suka rinka binsa a baya, misalin su Mallam Bakatsine, Mallam Danzabuwa, Mallam Yunusa, Mallam Ali Gabuwa, Mallam Usmanu Bahaushe da wasunsu waɗanda mafi yawa sun fitone daga kabilun fulani in banda kalilan ɗin hausawa misalin Mallam Usmanu bahaushe da muka ambata.
HIJIRA DA ABINDA YA BIYO BAYANTA.
Allah ya riga ya sanar da Shehu Usmanu R.A yadda hijirarsa zata kasance tun kafin lokacin yinta. Sheikh Jafar ya ruwaito a mukamarsa cewar Sarkin Muminai Abubakar ya faɗa cewar Shehu Usmanu ya faɗa mini cewa 'Nayi mafarki wasu mutane farare da farin gemu su dubu goma suna addu'a ga Allah. Sai nayi tambaya cewar me suke roko ne haka? Sai aka cemin ai suna rokar maka nasara ne'.
Tun daga nan sai Allah ya kimsawa shehu Usmanu fahimtar cewa ana nufin zaiyi Jihadi ne, kuma zai samu nasara akan makiyansa, zai kuma samu damar naɗa shugabannin dauloli, amma bazai samu damar zuwa aikin Hajji ba kamar yadda yake da muradi.
Don haka, sa'ar da shehu Usmanu yayi nufin soma yakin jihadi, sai ya umarci dukkan waɗanda ke tare dashi su koma garuruwansu na asali, domin lokacin hijira ne yayi. Sannan ya rubutawa almajiransa na garuruwa takardu yana mai umartarsu dayin hijira.
Sakon Kano yazo ne daga hannun Mallam Adamu da Ladan Goje, inda suka danka shi ga Mallam Danzabuwa.
Daga nan sai wakilai suka haɗu, mabiya shehu Usmanu kenan irinsu Mallam Abdurrahman sarkin Bayi, Mallam Bakatsine ɗan kabilar fulani joɓawa, Mallam Jamo daga kaɓilar fulani sulluɓawa, Mallam Dabo daga kabilar fulani Dambazawa, Mallam Danzabuwa daga fulani Danejawa, da kuma Mallam Usmanu Bahaushe daga kabilar Hausawa.
Dukkansu sun tattauna akan inda ya kamata a tafi a matsayin hijira, a karshe sai suka haɗu akan tafiya wani wuri mai suna Fagoje da fulatanci, wanda ake kira Kwazazzabo da hausa. Sunan da akafi sanin wurin kuwa shine 'kwazazzabon 'yar kwando'.
Tun daga nan, sai mutane suka rinka satar jiki suna binsu da kaɗan-da-kaɗan.
Mutanen garin Kanwa da yola sunyi hijirarsu ranar wata alhamis. Su mutan yola sun fara riskar garin Tofa ne, daga can suka isa Durma sannan suka gangara kwazazzabon a ranar 16 ga watan jumada Awwal.
Ganin haka, sai maguzawan dake yankin suka fara tashi suna barin gidajensu da dukiyarsu. Domin ance sa'ar da wasu masu hijira sukazo wucewa ta wani gari dake kusa da kwazazzabon (watakila Dugabau ne) sun tarar babu kowa a garin. Mutanen har abincin su duk sun bari a gidajensu, sai dai akwai wani bamaguje da yake yakar musulmi yana mai kare dukiyarsa.
Wani da ake kira Dan Dayya daga cikin masu hijira ne ya harbeshi da kibiya ya mutu nan take, yana nai cewa tayaya zamu bari kafiri yana yakar musulmi babu dalili kwakkwara?. Wannan bamaguje shine aka soma kashewa a tarihin jihadin kano, kuma wasu sunce sunansa Bimma, amma wasu na ganin Bimma ɗin sunan Dagacin garin Bebeji ne na lokacin.
Anyi wannan kisa babu jimawa, sai sako ya riski dagacin Bebeji. Shikuma nan da nan ya aike da manzo wurin sarkin Kano Muhammadu Alwali, wanda a sannan yana garin Takai. Yana mai sanar masa cewar raunanan nan daka sani, talakawa da waɗanda muke baiwa abinci zakkah suke kuma koyon karatu a makarantunmu sun taru anan suna shirin yin bore, gashi ma har mutane saboda tsoro suna guduwa subar gidajensu, sannan har kuma sun halaka wani shugaba abin girmamawa alhali yana kokarin kare dukiyarsa.
Dagacin Bebeji ya tura wannan sako bada jimawa ba sai ya rasu. Don haka sai dattawan garin suka haɗu suka sake turawa Sarki Alwali labarin mutuwar dagacin na bebeji.
Daga Takai ɗin sai Sarki Alwali ya aiko cewar ya naɗa ɗan marigayin mai suna Gyanako sarautar dagacin bebeji, amma da sharaɗin zai haɗa runduna ya kone gidajen masu hijira, ya kashe mazajensu, ya kame bayinsu a matsayin bayi, sannan ya taso keyar shugabansu gaban sarki yana kaskantacce.
Aikuwa sai Gyanako ya shiga haɗa tawagar yaki, sannan bayan ya gama shiri ya abkawa masu jihadi da yaki a masaukinsu dake kwazazzabon 'yarkwando.
Duk da kasancewar masu hijira sun samu nasarar wannan fatawa, amma an bayyana cewar sunyi rashin mazaje da dama, a ciki harda mallam Ibrahim Melulu, wasu kuma da dama sun samu raunika.
Koda sarki Alwali yaji wannan mummunan labari, sai kuwa a sukwane ya baro Takai izuwa kano domin kulla mai yiwuwa.
Ance akan hanyarsa ta dawowa ya haɗu da wani Malami bafillatani mai suna Mallam Bakatsine wanda yake bafade ga Sarki Alwali, wanda kuma akasari yake baiwa Sarki Alwali sa'a idan zaiyi tafiya yayin dashi kuma sarkin yakan bashi sadaka.
Koda haɗuwarsu daga nesa sai Sarki Alwali ya hango Mallam Bakatsine ya ɗaga masa hannu, sannan ya shige saɓanin abindaya saba ada na kwasar gaisuwa. Tun daga nan sai Sarki Alwali ya soma fuskantar lallai akwai matsala a kano.
Bayan sarki Alwali ya kwana a Jido, kashe gari ya isa kano. Ya tara manyan fadawansa a fada, sannan ya shiga neman shawarwarinsu.
Sai sukace ai wannan ba wani abu bane, masu hijira sun samu nasara ne akan Gyanako da tawagarsa saboda mafi yawan dakarun rundunar ba 'yan cikin birnin kano bane. Don haka kamata yayi a sake haɗa rundunar sadaukai 'yan cikin badala aje a murtsukesu.
Nan fa aka tara sadaukai mayaka, aka wakilta Barde Bakure ya jagorancesu, sannan aka turasu yaki izuwa kwazazzabon 'yar kwando.
Sadaukan nan suka bar gari, suka riski kwazazzabo, suka farwa masu hijira da yaki, aka buga kwarya-kwaryan yaki, mazaje suka zube a kasa, wasu matattu wasu kuma a raunane cikin jini, amma a wannan karon ma sai masu hijira suka sake samun nasara akan dakarun da sarki Alwali ya tura.
Faruwar haka fa keda wuya sai kuma aka shiga baiwa sarki Alwali shawarar cewa kamata yayi a tura wasu jakadu ga masu hijira domin ayi sulhu dasu..

No comments:
Post a Comment